Showing 126001 words to 129000 words out of 188741 words
fa zai yiwu ba, sai dai na ringa tsintar wasu abubuwa dake iya zubar da kimar dana a banza a wofi? a zuwanta gidan nan, ma'aikata uku ta kora dan jin dadi da isa, a cikinsu harda wace tun kafin a haifi YUSUF din take gidan, wai aikin me zata yi ta tsufa ta yi tafiyarta, sai ita ta saka aka maidata bangarenta, dama ba wani aiki ne take yi ba, tana dai dan abubuwan da ana zasu gagareta ba dan da aka nemi ta zauna ta huta ba zata rasa dukkan abinda ya dace na rayuwa ba, ta nuna dan Allah a barta ta yi aikinta dan idan ta zauna zaunewa zata yi .
An dauki mintina kusan sha biyar Hajia ta shigo ranta bace tana tafe a hankali a hankali duba da jikin tsufa , ama muryarta radau tana fada ta dubi Bah dake zaune saman kujera ta kai zaune itama saman kujerar daidai Hajia ta shigo , bayanta kuwa Amaryar da ake nufin tasa ce ta shigo itama , wace shi gaba daya yake mantawa da ita, dan ya yi waje daya ya ajiyeta tuni, Hajia ta ce" BELLO, ya dace ka tsawatarwa iyalinka kan abubuwan da ake son sako min, wa'inda bana tunanin in zan iya hakurinsu, ita a wa zata kai AMNAH bangarenta ta zauna, ? inace nan MALIK yace ta zauna shine zata zaune tsayin watannin nan a bangarenta tana kallo bata zo ta sanar min ba? me kennan? hanyar da za'a saka yarinya ta raina min jika ake nema dan kuwa an saka ta baudewa umarninsa me ake nufi in ba haka ba? a'a fa, Ni dama na so a duba lamarin nan aka dakatar da Ni, bafa zan dauka ba!"
Ta karashe rai a bace, shi kuwa ya ringa kallon Hajia da ta zauna tana sada kanta a nutse ta furta" Allah ya huci zuciyarki Hajia, ban san hakan zai haifar da matsala ba, kuma ban san baki san tana cen ba"
Hajia baba ta ki bata amsa dan ita abin ya bata mata rai, kuma da ta je yanzu yarinyar nan barci take ta yi, a dakinta a saman gadonta, ita dai rabonsu da junna da iyayenta da suka yi maganar wai a kai kayanta bangarensa ta nuna a kawo bangarenta a ajiye wasu, wasu ta ajiye a na Mah din har ya yi magana, ta nuna bata so a kuma dawo mata kan maganar dan ba zata lamunta ba, idan aka matsa kuwa su je da ita kawai zasu waiwayo su, dan ita diris take jira a san yadda aka yi, dan ba zata taba so ace wannan ce matarsa ta farko ba, uwar yayansa, itama tarbiyya bata isheta ba bale ta ba wani!
Bah ya saka baki sosai wajen ba hajia hakurin shima, dan a yanzu abinda zai iya yi kennan, dan a kashe maganar, ama shima zai ganta ta fada masa manufarta
hakurin da Bah ke badawa kuwa sai ya kular da Mah, gani take yi ita da ta fada masa kennan bai yarda ba? gashi kuma da Hajia ta fada yana tarewa kar a yi magana ko? ba laifi su ci gaba da yi, ita dai akoy lokacin da ba zata dauki abubuwan nan ba!
Uncle Umar kuwa gannin abin zai kacame sai ya yi kamar yana amsa waya ya fice a falon, yana son ya kirayi RAUDA ta basu waje itama, ama kuma ya ga kanta a kasa bata dago ba ko kadan, kuma ya sha mamakin gannin bata fita ba, ko me yasa?
Da kyar Hajia baba ta yi hakurin, Hajia ta mike ta tafi, zuciyarta cike da farin cikin ko ba komai a irin turbar da ta karra dora yarinyar ko a yanzu da wahala su ji dadinta, kuma zata ci gaba dan walahi bakin rai bakin fama ita da ANDIYA, ba zata taba jin dadin sarakuwa ba!
Bayan hajia ta nunawa Amnah wajen da ta zata zauna, ta zauna din sai bin kowa take yi da kallo kasa kasa , Hajiar ta ce" Ka yi hakuri da take abinda ka ce , kuma Ni ban san cewa har yanzu bata cen din ba"
Sai a lokacin ya bude idannuwansa yana kallon rigimamiyar kakarsa, ita dai a yi rikici baya ce mata komai, a yi ta surutu kuwa haka ta fi so
Girarakinsa ya dan hade ya maida dubansa kan Mah, sai dai maimakun ya kalli Mah a kanta idannuwansa suka sake sauka, bugun zuciyarsa ya karra cenzawa kafin ya dauke ya maida kan Mah
A tausashe ya ce" I'm sorry Mah, Ni bata wajena, wajenki na ce ta zauna ai "
Mah ta dube shi itama tana sake daukaka lamarin yarinyar nan, farce ne na kari har a kaffafuwanta, shin ita bata sallah ne?
A nutse Mah ta ce" Me zai sa kace ta je wajena ta zauna? aure ne fa aka daura maku, kuma a wajen naka da bangare bangare har hudu kamar yadda ka sa aka yi, me zai hanna ta je nata ta yi zamanta? YUSUF matarka ce, tana da daraja da kima, ya dace ka kiyaye , idan wani abin kake son yi ba dole sai ka yi yadda duniya zata fahimci halin da take ciki ba, ta je bangarenta da masu aikinta ta yi rayuwarta, wata hudu da da kwana hudu ba wasa bane, Ni kam ta je cen din kawai itama ta gyara gidanta!"
Da YUSUF, da AMNAH, da RAUDA gaba dayansu Mah suka zubawa ido, kowa da abinda ke ransa
Yaya aka yi ya ga duban da take yiwa Mah? idannuwansa dake yawan kai shi wajen da baya son zuwa ne suka kai shi? shi dai ya samu bakinsa da furta" Shikenan, ta je"
Sannan ya lumshe idannuwansa yana sake bude su ya kawo su kanta, a lokacin itama ta zuba masa duban da ta saka idannuwanta cikin nasa tarrr ba tare da ta janye ba
Nasa idanun ya dauke yana hade fuskarsa ya mike yana kade rigar jikinsa dan kuwa zai nunawa duk wani mai kallonsama ya isa ya yin ne! ya juya hankali kwonce da nufin tafiya
AMNAH da farin ciki ya lulubeta, da mamakin dama kawai daga ta ce masa ta je yana yarda tun sarak take zaune tana jiran tsamani?, babu yadda bata yi da shi ba kan ta je ya nuna zai nemeta, sai gashi a yan sekwani an ce ta tare a bangaren da take ta dako da burin ganninta ciki?
Hankali kwonce ta mike din itama, burinta ta fita dogaran nan su fara zubewa tana daf da shi, kuma tunda dai an ce ta je ai yanzu ake nufi, bata cewa kowa komai ba ta nufi bin bayansa hankali kwonce, hakan ya sa RAUDA kasa rikewa, Rauda dai Rauda, a nutse ta sake dagowa tana binta da kallo tun daga sama har kasa a tausashe ta furta" KE?"
πππππππ Ni kam bana son rigima, ke kuma? matar a gaban mijinta? kai jama'a hana Rauda zaki koma hali ko?, a gaban sarakuwarta da kakar sarki zaki ce mata ke?
βΉοΈβΉοΈβΉοΈβΉοΈπ₯Ήπ₯Ήπ₯Ή Ita bonanza din tamu a 1k ce, litafina 22 ciif, a TUNTUBENI BISA NUMBANA KAMAR HAKA 93811618
45
Azl 45
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
ππΌ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunchingππ»ββοΈπΊπ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
ππΌ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ππΌππΌmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nanππΌ (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ππΌππΌππΌ (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa baπππ sai kun zo
KE din da ta fada, ya shiga kunnen duk wani wanda ke falon, da kuma wanda ke baki-baki, ciki har da YUSUF wanda ya ja ya tsaya a lokacin da ya dan shige lungu kadan dan ficewa gaba daya daga falon, hakan ya sa basa ganin sa, sai AMNAH kawai ke ganin sa, wacce itama ta ja da sauri ta tsaya sannan ta dan juyo dan ta gane KE din da wa ake? ko wata ake yiwa magana haka? kuma babban abin da ya sa ta tsaya din kar aje wannan masifaffiyar kakar tasa ce ke kiranta da sunan ke ta ki amsawa ta janyowa kanta balaki, sai dai tana juyowa ta ga idanuwan wannan dake zaune a kanta tsai, hakama na su Hajia a kan RAUDA din.
Da ido RAUDA ta mata alamun dawowa sannan a saman lebenta ta furta" ZO NAN!"
Idanuwansa a kan fuskarta ne, kuma dukkan motsinta shi dai YUSUF sai dai ya sanarwa wani abin da take nufi ba dai wani ya sanar masa ba, hakan ya sa ya sake zuba mata ido da matsanancin mamakin me zata yi? haka su Mah sai suka yi kamar an dakatar da su da Remot duk da matsanancin son su tambayeta lafiya? Sai suka gaza yin magana daga Mah din har Hajia, har sai da wacce mamaki da tashin hankali suka sakata juyowa rai bace ta dawo inda budurwar nan ke zaune tana kallonta ido cikin ido ta ce" Da Ni kike?"
RAUDA a zaune take saman cafet, bata tashi ba sai kafafuwanta da ta dan janye dan kar ta hau mata kafa da wannan arniyar kafar tata tana kallonta cikin ido kasa kasa ta fura" Eh "
Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, wallahi sai AMNAH ta rasa kanta ne ya dau juwa ko idanuwanta ke son rufewa saboda bacin rai
ita dai abin da ta gane shi ne, rai bace har ta manta sirikanta a wajen ta nuna Rauda sama-sama kamar yadda ta saba fada da mutane irin ta ta ce" Kin san ko Ni wacece zaki dube Ni ki ce min KE ZO NAN?, ki kalli jikina tun daga kaina har kafata ki fada min na maki kama da ajebo da zaki raina min hankali? Uban wa kike takama da shi a duniya da zaki dube Ni ki ce min Ke Zo Nan?"
RAUDA ta lumshe idanuwanta, sarai ita tana tune da su Mah na wajen, kuma bakinta ne ya cuceta da ya yi mata kiran yarinyar nan da bai dace ace wani abu ya hada su ba ko da mijinta balle ita banza a banza!
A saman lebenta, bayan ta dan kauda kanta barin da iya shi da Amnah suke ta furta" UBANKI ya tsaya mini!"
Sai kuma ta juyo ta bude muryarta da kyau a lokacin da ta mike, kuma a lokacin ne AMNAH ta zarro ido, hakama shi ya zarro ido yana kallon ta, a bayyane RAUDA ta ce" Ni ban san ki ba, na ga ne kina saurin yin cen kuma kin ga ba hanyar da kowa ke bi ba ne!"
Itama da ta fadi hakan ta ji abin wani iri balle wa'yanda ke sauraronta, kuma sai da ta fada ta gane ta yi rashin azanci domin koda bata san ta ba ta san bakuwa kai tsaye ba zata shigo nan ba, kai abinda yanzu yanzu aka gama maganarta? Sai kawai ta waske ta kalli Mah da ta yi suman zaune, Hajia kuwa tana tafa hannu ta ce" Ba ga irinta ba, wannan fa kanwar mijinki ce, ama bata sanki ba, gashi a rashin sani har tace maki Ke , wannan din ai bai dace ba, kina da wa'inda suka fi su ne? da zaki je ki tare a cen inace Salimar ma nan take da su, ke ki yiwa kan ki karatun ta nutsu kafin duniya ta maki, wannan fa itace mijinta ya rasu kwananan, kenan ko gaisuwa baki yi mata ba?"
Sai kuma Hajia ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yadda AMNAH ke kallonta, domin Rauda tuni ta juya ta bar mata wajen dan kanshin turarenta sam baya birgeta!
Wannan karron Hajia ta sassauta murya tana kallonta ta ce" Wai da bin shi ne zaki yi Amnah?"
AMNAH kam kallonta take yi, tunda ta ambaci Rauda kanwar mijinta ce kanta ya shiga a halin rudu bayan bacin ran da ta shaka mata, wallahi tana iya rantsewa cewar RAUDA ce mata ta yi ubanta, kuma ta kirata da ke, kuma ace kanwar mijinta? kodayake da ta matsawa maman Salima kan Wacece RAUDA duba da an ce shi daya ne d'an mamansa sai tace mata ta yiwu iya ta haifeta kuma ta yiwu ba ita ta haifeta ba, su dai ta ce masu y'arta ce, kuma irin yadda Honorable ma ke kiranta da baby Auta ta yiwu y'ar tasu ce babu wanda ya san da ita dai su tsakaninsu tunda abin kunya ai ba na kunya bane a wajen su!
Tana jin Hajia, amma gaba daya tunaninta ta yadda zata kasance da yarinyar cen ne daga ita dai ita, dan wallahi sai ta nuna mata asalin me ake nufi da dan kwalta, domin sai ta nuna mata da sarautar gidan nasu ta fi ta iya shege, har ita tana matar MALIK, zata yiwa wannan kiran , kuma ta zageta?
A tausashe Hajia ta ce" Zauna Amnah, zo nan zauna"
A dole ta je ta zauna din, ita Kuwa RAUDA a lokacin ta zuba maganin Mah a dan kofinta ta mika mata, bakin nan a cune kamar zata fashe ama ita batama san a cikin yannayin fushi take ba, Mah din dai ke hankalce da ita, shi kuwa tunda Hajia ta fara fada ya yi gaba zuciyarsa da matsanancin mamakin y'ar cen, daga baya kuwa ya yi wuri ya ajiyeta a ransa yana ayyana' Mai hali da wahala ya daina halinsa, idan ka ganta kamar ba zata ciza dan yatsa in aka saka mata ba, bayan duk wani rashin ji a kanta ya kare, Allah shi kyauta, wai matata ta yiwa haka? oh!"
A tausashe Hajia na dubanta ta ce" Bana son idan ina maki magana na ringa yi maki a haka, ko menene halinki wanda kike da a gidanku ya kamata ace kin fahimci yanzu fa dole ko daidaita wasu abubuwan, Amnah ke budurwa ce, auren farko aka yi maki, kuma aure mai darajan gaske, ke ko a idon mijin naki bakya tsoron ki rage daraja ne? yaya za'a yi ki ringa abubuwa kamar ba mace ba? mace fa an santa na da kamun kai da aji, ke ya kamata ya ringa rawar kafa idan ya ganki ko waye shi, ba wai ke ki ringa abubuwan nan ba, namiji fa idan ya rainaka shikenan, kuma kin ga idannuwa fa a kanki, bai dace ace ko wani lokaci aka daga ido ana iya ganninki ba, ina darajarki take? ke da ya dace ace ko Ni sai ta kama zan ga fuskarki? kina bangarenki kina mulki daidai gwargwado? haba dan Allah, yanzun da binshi zaki yi? ki duba fa ki ga jikinki, suturar nan ai ba wace ta dace ace kin bi bayanshi bane shi ya dauki wanka kamar zai je hawan sallah ke kuwa da wannan abin? ki yi anfani da damar ki ki tabatar da kin gyara zamanki da mijinki sannan ki so ahalinsa, ba kamar mahaifiyarsa, idan kika kiyaye abubuwan nan na tabatar maki mijinki zai so ki, zai mutunta ki kin ji?"
A lokacin da Hajia ke yi mata nasiha , irin wace zata fisheta, ita wasu tunani take yi daban na abinda zai fisheta
Kwarai kamar yadda Hajia tace ita din mai daraja ce hakane, kuma tunda ta zo gidan nan suka yi watsi da ita take dauke da haushinsu
Babu ruwanta da wani umarni ya bada ta je bangaren mahaifiyarsa, babu ruwanta da wani rasuwa aka masu, ko menene ya dace ace sun bata kulawa ta daban da ta kowa, ama tsabar son kai suka ki yin hakan kuma yanzu ake son nuna mata fi'ili
Idannuwanta kuwa a kai a kai sai sun sauka kan RAUDA, a bayane take dan dantse lebenta, a zuciyarta tana ayana' Lalle baki san wace Ni ba, dan na yi zaman watannn nan a gidanku ba yana nufin na zama sharar da zaki taka ba, ko Wacece ke zan binciko zan nuna maki Ni din Wacece, na tabata ko waye ubanki ba fin nawq kudi ya yi ba, kuma na tabata du rashin jin ki baki kai Ni ba, zan san dalilin da yasa kika zageni kafin na shake wuyanki har sai kin kusa barin duniya, walahi na amshi tayin masifar da kika min, ko Ni Ko ke!'
(Uhum, a yi dai mu gani, wannan tashin tashina haka)
Hajia a tausashe ta sake fadin" Ki yi zamanki a nan bar dare ya yi a raka ki a mutunce, yanzu zan sa a kwashe kayan ki a kai cen din a kimtsa maki, bai dace ace an ga shigarki da rana haka ba kin ji?"
Kai ta gyada, a lokacin ita kuwa RAUDA ta lumshe nata idannuwan da suka yi mata wani irin nauyi
Kasa kasa ta furta" Mah, zan je na yi girki"
Mah ta sake dubanta, da kula ya ce" Baby zaki iya? Sai na ga kamar baki da lafiya?"
RAUDA ya girgiza kanta a hankali ta dauki jug