Showing 84001 words to 87000 words out of 188741 words

Chapter 29 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9874

summa ko ku ci kanku basu ce masu ba suka ficewarsu, hakan ya sa Salima dake ta murna ta nufi mahaifiyar dawowa jiki a sanyaye ta zauna hadi da dan dafe habarta da yatsarta manuniya tana kallon RAUDA dake mata alamun ta ware ba komai

Murmushi ta yi mata ta sada kanta bata iya sakin jikin nata ba, karshe kiraye kirayen sallah ya saka su mikewa kowace ta nufi hanyar da zata daura alwallah dan yin Sallah, RAUDA kam da Abdul ta tafi dakin Salima dan ta fi sakewa a cen, bale yanzu da Mah ta fita

Tun sunna saka ran dawowar Mah har suka fara cire rai, domin su Hajia tuni suka dawo kuma basu sanarwa kowa yadda jikin marar lafiyan yake ba, hakan ya sa suke cikin damuwa dan sunna son jin yaya jikinsa sosai, bale ita RAUDA ta fi damuwa bata san dalili ba, ko dan ta ga a duniya wannan matar dake nuna mata soyaya tana matukar son wannan bawan Allahn ne? Ita dai tana masa fatan samun lafiya har cikin zuciyarta

Gannin karfe tara tana neman yi ta karɓe wayar Salima da Abdul ke buga game din da ko iyawa bai yi ba ta ce maza ya mike ta masa wanka ya cenza kayansa

Kayan da ta dauko ya kalla, riga da wando ne na barci da pant, pant dai pant na mata aka hado a cikin kayan nasa na barci, ita kuwa bata taɓa Sannin wai ba wandon maza bane dan haka tace ya shige su je

Da yannayinsa ya shiga make kafada yana fadin" Aunty, to sai nawa zan yi wankan? Ni dai a'a, mura zata kamani, a'a aunty, kuma ba zan cire kayan nan ba kar aje wani ya dauke min, ina son su"

Da yannayin rarashi tana rike mayafin rigar jikinta ta ce" Abdul dina, mura ba zata kamaka ba, ka ga a nan sau uku ake yin wanka fa, kuma kayanka babu wanda zai dauke, mu je dan albarka na maka wankan ka ji?"

Shi kam sai ya ga abin wani iri, kuma yau auntynsa ce zata masa wanka bayan a da ba ita ke yi masa ba? Abinka da yaro sai kawai ya juya ya diba a guje yana fadin shi dai a'a ba zata yi masa wanka ba, ba zai cenza kayansa ba!


Ido ta zarro, gannin dare ne fa, kuma ga gida na yan gayu ba hayaniya suka cika so ba, gashi a gidan ta jima da gane ba kowa ke ra'ayinta ba,sai ta dauki sauri tana fadin"
Azl 29
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo




Da sauri RAUDA ta biyo bayansa tana fadin" Kai, Abdul, zo nan, baka gannin dare ne ba kyau gudu da dare? Zo nan ina wasa da kai ne?"

Tana fada tana karasowa falo ne, hadi da ja ta tsaya ta rike tsatso tana hada gabas da yama irin bata son wasan nan dan ta kula idan ta ce zata tsaya yi masa dariya yana iya janyo mata magana ne

Kai ya dago daga danna wayar da yake yi ya zuba mata ido, irin tsayuwar da ta yi tana tafka harara ta saka shi juyawa dan gannin abinda take yiwa hararar , gannin Abdul na nufarta yana shashekar kuka alamun yana iya fashewa da kuka ya saka shi tabe baki hadi da girgiza kai a ransa ya ayana' dama kema ba fita rainon kika yi ba, kuma sai Allah ba baki wani rainon, bawan Allah, Allah ya sa kar ta rikita yaron nan'

" Kai, yaushe na fara maka magana kana raina Ni? Nace mu je na maka wanka ka cenza kaya ne zaka wani fita a guje? Ya maka kyau wuce mu tafi!" Ta fada tana zazaro masa ido da nuna masa hanya hadi da fitar da pant din dake hannunta dan da shi a hannunta take nunawa tana yin fadan

Idannuwansa ya kankance yana kallon abin da dukkanin son ya gane abinda ke hannun nata, ita kuma tunda ta fito Allah bai kai hankalinta kan babar kujerar falon na, ko dan ba abinda ya fitar da ita ba kennan, duk kuwa da irin yadda hancinta ke jiyo mata kanshin turaransa wanda zuwa yanzu ta gama gane nasa ne, bata saka cewa shi din ne a wajen ba, dan ta gama hardace turaransa koda baya nan kana iya jiyo kanshin a waje, tsabar nacin kanshin turaran ya sa duk inda ya shiga yakan bar kanshin ne na dan lokaci bale wajen da yake rayuwa

"Wandon waye a hannunki kuma?" Ya fada yana asalin ajiye wayar hadi da zuba mata ido

Har ga Allah bata taɓa kawowa zata ji muryarsa a kusa kusa ba, hakan ya sa ta daka tsalle hadi da yin dan ihu tana dafe kirjinta hadi da kallon inda yake zaune

" Haba bawan Allah sai ka saka na kamu da hawan jinni mana!" RAUDA ta fada, kanta tsaye, ba tare da ta ankara da wa take maganar ba, har sai da ta dasa aya sannan ta sake kallonsa a sace, a hankali ta sunne kwayar idannuwanta kasa kasa ta furta" Sorry Please" sannan ta juya da dan sauri da nufin tafiya

"ZO NAN" ya samu harufan bakinsa da fitarwa a wannan yannayin

Dakatawa ta yi da tafiyar da take yi, a hankali ta juyo tana kallon Abdul da mamakin gannin ya rigayeta zuwa inda aka ce mata zo nan kamar wani babanta

A hankali ta karasa ta zauna saman daya daga cikin kujerun ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya dan bata san irin fadan da zai yi mata ba kuma

Kai ya girgiza yana kallonta ya ce" Ke Ni fa na girme ki, yaya zaki zauna saman kujera bayan ina sama? Kuma ama bakya tsoron Hajia ko?, baki san ta hanna ire irin abubuwan nan ba?"

Dagowa ta yi a sanyaye ta zuba masa ido, ta ga ita din yake kallo , kuma amsarta yake jira, dan haka a hankali ta furta" Ka yi hakuri"

"Ki fadi abinda kike tunani sak ya fi" ya fada yana dauke kansa bayan ya sakar mata hararar

Kai ta sake sokewa, a ranta ta ayana' ikon Allah '

A bayane kuwa ta furta" Dan Allah ka yi hakuri" , ama kuma ta ki saukowa daga saman kujerar , kai ita har ga Allah bata ga me yasa zai ce wai ta sauka na, toh haka kawai dan ya ga Mah bata nan ko?

Ido ya sake zuba mata, tana dago kai ya dauke dubansa ya mayar kan Abdul dake mota mota a falon yana kallonsa, kasa kasa ya ce" kin sha maganinki?"

RAUDA ta sake zubawa fuskarsa ido, ya Salam ta ringa ambata a cikin zuciyarta saboda bugawar da kirjinta ke yi

"Eh na sha" ta fada itama a kasa kasan

"Kina iya tafiya" ya fada yana juyowa ya saka idannuwansa cikin nata

Gabanta ya sake yanke wa ya fadi, da sauri ta mike tana rintse idannuwanta dan jin wani irin gumi ma son tsatsafo mata

"Ji mana" ya fada muryarsa a mugun kasalance

A hankali ta juyo ta zuba masa idon itama, shi kuwa bai risinar da nasa kallon ba yana kallonta tsai cikin ido da kuma bandejin dake goshinta wanda ya mata kamar an yi mata kwaliya ne, kasa kasa ya ce" Mah ta ce, ki kula da kanki"

RAUDA ta lumshe idannuwanta hadi da gyada kanta

"RAUDAH " ya sake furtawa ba dan ya san me zai kuma ce mata ba,

RAUDA ta bude idannuwanta da suka cika da kwallar da bata san ko ta mecece ba

YUSUF ya dauke nasa idannuwan da suka yi Jajajir bai kuma ce mata komai ba, a ƙalla ta dauki minti biyu tana jiran amsarsa har ta sake yin baban motsin da zai sanar masa tana nan fa, dan sai ta yi tunanin ko ji yake ta tafi?

Ba tare da ya sake kallonta ba, a hankali ya furta" good night "

Sake duban fuskarsa ta yi, ta samu kanta da binsa da kallo tun daga kansa har zuwa kaffafuwansa dake cikin fara kar din Safa
Bata san dalili ba, kallon da ta masa na farko ta ji bai ishe ta ba har sai da ta maimaita masa ya kai sau uku, ko wani abu take son ganewa a tatare da shi? Ita dai ta san ta masa kallon da ya wuce Shari'a, wanda ba zata tuna namijin da ta taba yiwa kallon nan ko dan ta gane shin namijin da zai bata kudi ne bata cika yin irin kallon nan ba, bale wannan da ko kusa bata kawo irin abin nan a ranta ba

A hankali ta juya tana jimke hannun Abdul da ya fara gyangyandi ta nufi dakin Salima da shi

Sunna juyawa ya dago kansa ya rakata da kallo har sai da ta bacewa ganninsa sannan ya girgiza kai ya yi dan murmushi ya sake karanta sakon Taj na abinda ya saka shi jiya da kuma sanar masa da ya yi jikin Umar da sauki sosai dan ya fara fira da tambayar wanda ya kawo shi asibitin da tambayar idan da hali a kai shi ya ga danginsa

Msg ya shiga masa typing da turanci yana fadin" Ka ce ya kwontar da hankalinsa ya samu sauki sosai, ka ce masa RAUDA na gaishe shi zata zo su tafi, ina so a gobe gobe ka je gidansa ka min bincike a kan matarsa, kowani bawa baya rasa abinda ke iya dakatar da duk wani farin ciki nasa na duniya, ka gano minenene"

Daga nan ya kashe wayar ya ajiye ta ya lumshe idannuwansa yana jin yadda kansa ke masa nauyi

A dazu mahaifinsa ya farka, har ya ga matansa, kuma cikin ikon Allah sun samu bai daga hankalinsa ba, domin a lokacin da ya tambayi ya jima a kwonce? Aka shaida masa sai ya kama hannun Mah ya jimke kawai yake sauke ajiyar zuciya, a nan ne ita kuma ta zauna daf da shi, ta rike hannayensa cikin irin Tata baiwar, wace Allah ya bata damar tankwasa tashin hankalinsa da bacin ransa ta ringa yi masa bayanan yadda zai gane, har ta kai aya yana kallonta da yannayinta, a nan ne ya yi mata tambayar wa aka naɗa sarauta? Zuciyarsa na tsintsinkewa, dan ba zai taba son a nada cousin dinsu ba, domin kowa ya san me aka naɗa, kuma ba zai so ace sarauta ta shiga hannun Nana ba, dan ta fara bashi tsoro, kuma ya san YUSUF ba zai taba amincewa da sarauta ba, ba zai amince ba, bayan a dukkan tunaninsa da hasashensa bai ga wanda ya dace da ita ba

Shine Mah ta shaida masa wanda ya hau, abinda ya saka shi zarro ido da mamaki, bashi da wani karfi ko kuzarin kirki a jikinsa ama sai da ya jimke hannunta da dan karfin da yake ji a jikinsa ya ringa neman a kirawo masa YUSUF din, a lokacin kuwa YUSUF din na cikin baban daki sunna ta karatun abinda ya shafi sarauta da asalin nauyin da yake wuyansa, a dole aka bashi hakurin cewar zai zo, nan ne doctern sa ya nuna shi kam idan da hali a tsagaita surutun dan kar ya hadu da ciwon kai da na idannu a bar shi ya huta kar a cika shi da surutu, ya farka kwarai, ya yi kyakkyawar farkawa, ama ba'a san me yake boye ba, sai an bi shi a hankali, shine su Hajia suka ce Mah ta tashi su juya ta nuna ita kam babu inda zata je kuma sai YUSUF ya zo sa koma tare, sai gashi YUSUF din bai gama da wuri ba, sai waya suka yi likitan ya nuna masa ya zauna gobe ya zo, sannan Mah ta nuna masa zata kwana a nan, dan har zuwa lokacin ya dan koma barci ne ya farka, kuma idan ya farka din yakan kama hannunta ne ya sakar mata murmushi, ga dukkan alamu haka din yake so.
Shine fa ya zo ya zauna a falo, kowa ya bashi waje yake zaune yana duba wayarsa yana ta amsawa mutanen da bai samu ya amsawa ba, abubuwan ne sun masa yawa, har su RAUDA suka fito suka dakatar da komai ya shiga sabgar da ba tasa ba, sabgar wa'inda a ganninsa bai dace ya shiga ba, ya kananage har ya dage kan sai ya ji wani abu daga gare ta da ya danganci amon murya, ko yannayin nan nata na fada, sai ta karra neman saka shi a tunani har ya girgiza kai ya yi murmushi yana ayana' me yasa komai nata yake daban?'

Sai kuma ya ture zancen ya mike ya je da kansa ya kashe fitilu ya rufe babar kofar sannan ya nufi dakinsa, kansa ba rawani, a hannunsa ya rungume rawanin, shi yana tunanin koda ya yi rowar fuskarsa kamar yadda akace dole sai ya yi, banda cikin gida, baya tunanin zai iya yawo a cikin falon su,da dakinsa zuwa na Mah da rawani sai kace mai gyambo

Daren nan, ya kusan rabawa zukata uku cikin kai da kawon tunanin sarkakiya mai wuyar fassara, domin a irin lokacin da wasu zukatan ke son ture abinda ke saka su murmushi, a irin lokacin ne zuciya daya jal mai cike da kauna da tarin bege ke kwonce a baban Center na kula da lafiyar zuciya ta garin ana bata kula daidai da rikicewar ta da jajircewa da ta yi kan lalle sai an fasa an cenzata domin bata san Yaren ta yi hakuri za warke ba, a lokacin ne mai dauke da zuciyar ya kafawa waje daya ido yana auna shekarunsa a mizani, inda ya tabatarwa da kansa cewar koda babu lalura irin ta jinyar zuciya a yanzu da ya haura hamsin idan ya hadu da ciwon ajali ba abin a firgita bane, san mutuwa ta dauki jariri bale shi, sai dai abu daya da zuciyarsa ke masa naci itace!
Yana son ta!
Yana matukar son ta!
Ta ina zai fara misalta rayuwa babu ita?
Baya misaltawa kansa bale har zuciyar ta buga tashi daya
Ya fi sakawa ransa zata dube shi fa, jinkirin nan da bata waigo ba da gasken gaske lokaci ne
A yanzu da ta sanar masa ance ya zo, sai ya ji salama, sai dai a jiya zuwa yau da ya ji salamar abin na neman kubce masa dan jin bata da lafiya kuma an ki a bashi damar ya zo ya ganta.....
Shin marikanta basu san ba kowa yake da lokacin nan a duniyar ba? Kwarai Allah kadai ya san ranar rasuwar kowani bawa, ama a yadda alamu suka nuna koda baya so dole zai fara hada kayansa

Ba zai tashi ya yi ta tafiye tafiye dan neman magani ba, a haka har ya cinye lokacin ba tare da ya yi mafi mahimmanci a gare shi ba
Ba kuma zai yarda ya yi ta zuba dukiya a kan abinda cikin dashi dari daya ake yiwa hasashen tashi ba, kai koda zai je ya dasa ya fi so idan ya malaketa ta yi jinyar sa.....

Idannuwansa da suka yi laushi ya daga a hankali yana tuna irin firar da suka yi da lauyansa a kan abinda ya shafi dukiyarsa, shi kam bayan na taimakon marayu, gine ginen gidajen marayu, su rijiya da masallatai a wajen da suka dace waye zai barawa dukiyarsa bayan ita?, to ai koda da ransa ita din ce bale idan ya tuna ta yiwu ya rigayeta barin duniyar? Allah shi ke dasa so a cikin zuciyar wanda ya so kuma abin al'ajabin kowa yana so baba da yaro

Wayarsa ya laluba da hannunsa na dama da kyar ya dauko ya shiga buga numbar Salima da adu'ar Allah ya sa ta dauka, dan dare ya yi ta yiwu ta yi barci

A irin lokacin ne RAUDA take kallo a wayar ta Salima dan rashin abin yi, gashi ta sha barci ya ki daukanta ga tunanin da ta dasawa gayar sodi dan bata ga abinda ya kai kare layin ragunnan laya ba!

Sunnan take kallo, haka kawai taji kamar hankalinta zai tashi duba da lokacin karfe biyu ya gota na dare

Da dan gagawa ta daga kiran, muryarta cen kasa ta yi salama lokaci daya tana fadin" Abdallah, lafiya baka yi barci ba har irin wannan lokacin?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da yannayin jinya ya ce " yaya zan iya yin barci Bayan zuciyata na neman fashewa dan ban kaita ta ganki ba?, Please ki bar dattijon saurayinki ya ganki noory"

"Mah ne tace sai na warke" Rauda ta fada a hankali

Ya buda idannuwansa shi dinma a hankali ya furta" idan na mutu fa kafin lokacin?"

Da sauri ta bude idannuwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login