Showing 6001 words to 9000 words out of 188741 words
kannunta uku, ita dayar nan uwa maya suka bari a hannun kannin mahaifinta, shi kuwa baya hanawa bale sakawa, inma ka kai masa kararta tsaf yake iya daure mata, Ni dai abinda ba zan lamunta ba da ta wulakanta Ishak, ban san waye ke son numbarta ba na amso na bashi ta wulakanta su, ko ji take ba zata samu biyan bukata a wajensa ba?"
Da ido dayar ta saci kallonta, gaba take ama tana iya fasara yannayinta, a gaskiya a yanzu da take zaune ba kwaliyar a fuskarta ana iya daukanta a bar su, su da suka shafa hoda da ja gira da su jan baki da gashin ido, to ita gashin idannuwanta kadai sun isheta, danma ba fara bace cen cen din nan, ama yannayin fatar jikinta tamkar ta yan Ethiopia wankaku masu rantsatsen hutu, kai kamanunta kansu tamkar wace ta samo usuli daga su, saima hannayenta da kaffafuwanta, sunna da tsafta da kyan kallo, hannayenta kuwa harda yan faratuna take tarawa na ra'ayi mikaku farare tas tas da su, tana dauke da quality masu fuzga, ba wai manyan duwawu ne da ita ko manyan breast ba, a'a, komai dake jikinta ne dan daidai da tsarin halitar jikinta, sai kuma ta iya saka kaya da wasu yannayin dake daukan hankalin har mata ba iya maza ba, sau tari idan ta halarci taron mata kawai zaka ji ana tambayarta wai gashin idon nan nata ne? Wai me take shafawa? Dan Allah me take anfani da shi a lebenta? Dan Allah yaya take yi kaffafuwanta da hannayenta suke haka cikin tsafta? Sai dai ta yi murmushi tace haka Allah ya haliceta, kuma haka din ne , sai dai wanka kawai da ta karra, ko kwali na koda yaushe take sakawa ba bale kwaliya, ama a haka din dai take da nata farin jinin da ya tsolewa wasu ido
Kasa kasa kawar Nafisa ta ce" Fifi gaskiya Atu ta yi sake, Ni idan nice ba zan taba amincewa da haka ba gaskiya, cap, wannan ai sai ta kwace min mijina ina ji ina gani"
Daidai motar ta tsaya kofar gidan su Bara'atu , direban ya sauke madubai sannan ya cire masu sakatar motar
A Nutse ta bude bangarenta ta fito sannan ta je gefen da suke ta saka hannu ta bude masu ta kuma tsaya a kan hanyar fitowar ta saka idannuwanta cikin ma Nafisa, wace sai da gabanta ya fadi ta dan samu kanta da dan ja baya tana kallonta lokaci daya tana fadin" Ke kuwa lafiya?"
Rauda ta bi su daya bayan daya da kallo, sai kuma ta saki murmushi, cikin yannayin da zaka rantse ba zata iya furta wata kalma sama da hakuri ko hailala ba ta ce" Kina da matsala da Ni ne?"
Ba yan matan nan kadai ba, hatta direban nan sai da ya juyo ya zuba mata ido, domin a yanzu ras yana ji dan ya tsayar da amon rediyon motar
Nafisa ta sake dubanta da mamaki ta ce" Wai da Ni kike RAUDA?"
Rauda ta lumshe idannuwanta da wani yannayi ta daga kafarta ta saka cikin motar sannan ta janyo kofar ta rufo da karfin tsiya ta juyo bayan ta ajiye wayarta a aljihun motar tana kallon yan matan gaba dayansu ta ce" Da ke, da kuma ku nake, Akoy mai matsala da Ni ne? Mu warware ta saboda bana son kwonciya da tunanin wani banza, nace inada matsala da ku ne ta yadda zaku ringa wulakantani a gabana?!" Ta karashe a kausashe tana juyowa gaba dayanta
Direban ne da sauri ya shiga yana fadin" HAJIA, kin ga kar ki kula su sauko ki yi tafiyarki, ko me suka maki ki yi hakuri kin ji?"
Nafisa ta cafe maganar tana fadin" Karma ta sauka, ta yi mana abinda zata yi!, da ke din nakkkkkkkkkkkkkk"
K din kawai ya dan fito a karshen furucinta ta samu kanta da dantse harshenta lokaci daya sakamakon dauke fuskarta da Rauda ta yi da mari sannan ta rike mata wuya harda kokarin daneta a cikin motar
Ihu suka kwasa sauran yan matan biyu suka shiga kokarin kwantar Nafisa, sai dai gannin abin na neman zuwa kansu dayar ta bude motar ta fice tana haki har takalminta ya cire saboda yadda ta fito daga motar hankali tashe ta sake duban Nafisa dake kai duka a iska bata samun Rauda din, ita kuma Rauda har idannuwanta sun juye ta rike mata wuya taf tamkar wace zata aikata kiyama
Gannin za'a yi kisa ya saka shi fitowa da sauri ya bude bayan ya damko Rauda ya fizgota da dukan karfin da Allah ya bashi, ama cikin ikon Allah sai da ya wartota da dan kunnen Nafisa guda wanda ya yi fitar karfi ya janyo ya ja mata shatinen da ya farke mata da jinni
Kusan a tare suka saka ihu, shi direban da Nafisar da kuma dayar kawar da ta kasa fita saboda gaba daya Nafisa kanta ta dane garin fadan
Mutane tuni sun fara taruwa a wajen motar a lokacin da ta warce jikinta ta sakar masa harara ta sake ridar motar shi da kansa ya so yin hali irin na mata, wato ya ware muryarsa ya kwala ihun a taimake shi, sai ya ga ta janyo wayarta ne da dan yalolon mayafinta
Ido tuni sun kade mata ta dubi Nafisa dake ihun ta yanka mata fuska murya a dake ta ce" Ban maki komai ba cikin tarin abinda nake son maki, ba kin ce a ce min idan kika ganni sai kin wulakantani ba? Ni zan fada maki gwa da gwa kin ciri katin fada da Ni mai rabamu sai Allah!, dan na maki alkawarin haduwa goma sai na kawo maki hari sai dai ki kasheni, zan nuna maki mayar nake ta kirki idan na riki wuyanki, haka kuma zan nuna maki mai kwacen mazan mutane nake ta hanyar bin duk wani namijin da zai nuna yana son ki, ke sai na zame maki *AZAL* a rayuwa tunda kika zagar min iyayena!, sannan ki je ki sake bincike labarin da kike da ba daidai din bane karamar yar is....."
"RAUDA?" Muryar mahaifiyar Atu ta katse ta
Tun daga kanta har kafarta dake ja ba takalmi ta bi da kallo sannan ta karaso da dan sauri tana yiwa ya'yan Atu magana kan ya watsa mutanen dake neman yin taron idi a wajen ta sake zubawa Rauda ido sannan ta leka motar da kuka da ihu ke tashi
Sai da ta tsorata gannin yadda jinni ya BATAWA Nafisa atamfarta da fuskarta
A tsoracen ta ce" Subahanallah, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, menene duka wannan? Yanzu RAUDA dama baki daina fada irin wannan ba? Me ya yi zafi haka? Kai Usman maza fitar da mota a kai wannan asibiti, ke kuma wuce mu je ciki wuce, dan Allah kowa ya tafi ku tafi kawai , du kun tsatsaya an rasa mai kama masa a kashe fitinar nan sai da ta zama haka? Subahanallah Rauda yau sai na saba maki yau sai na saba maki Rauda!"
Nafisa da ake tarewa tana kuka ita kadai ta san me take ayanawa a zuciyarta, abu daya ta sani in har wannan mahaukaciyar ta mata ila sai ta rufeta dan na zata taba yarda ba, ashe mahaukaciya ce bata sani ba? Da ta san bata da hankali na zata taba yarda su shaki iska daya da junna ba, a irin yadda take kafa kafa da jikinta ita ko fada bata taɓa hada jinni da kowa ba, abu daya ta sani in dai tana fada da kai in ta sakoka a gaba da habaice habaice da harare harare har sai ka ji kamar ka daina fita cikin sa'ani, sai gashi tun kafin abin ya kaisu da haka daga magana wannan mahaukaciyar ta mareta hadi da yi mata rauni? Ba zata iya yafe wannan wulakancin ba
Rauda kuwa bata tsaya ko'ina ba sai cen kuryar su Atu
Tana shiga ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kanta
Jim kadan sai ga mahaifiyar Atun ta shigo , tun kafin ta zauna ta shiga fada tamkar zata ari baki, fada take yiwa Rauda irin fadan da uwa ke iya yiwa y'arta cikin fadan ya ce" Ashe bakya jin magana? Inace nan ma maku maganar fadace fadacen nan kuka ce min kun daina, shine zaki hada jiki da mace har ki mata wannan raunin? Ina anfanin wannan abin da kika aikata Rauda? Ya Salam me ya haɗa ki da ita da zafi? Me yasa wani lokacin bakya kwabar zuciyarki ne? Ko menene idan kika yi hakuri ba Shikenan ba? Mai hakuri yakan dafa dutse , a matsayinki na mace a kulun fada maku nake yi ko muryarku ba kowani banza bane zai ji kai tsaye, komai na mace abin a kilace ne a ririta, komai naki daraja ne da shi, har wancen ya kamo ki ya fitar da ke daga mota? Ya Allah haba RAUDA "
A hankali Rauda ta dago idannuwanta tana kallon maman aminiyarta wace take kira da Mama itama, a sanyaye ta budi bakin da nufin fadin abinda suka yi mata sai kuka ya kubce mata, domin a duniya idan kana so ka ga hawayenta ya zamto zata fadi wani abin da aka yi mata har ya mata ciwo a zuciyyarta
A hankali ta iya furta" ban masu komai ba, har iyayena suka zaga"
Jikin Mama ne ya yi sanyi sosai, ta sani abinda ya shafi iyayen yarinyar na rikitata sosai, ko dan Kadara mai zafi ta daki rayuwarta ne? Idan abu ya shafi iyayenta bata iya yiwa kanta tsawa ko fada, ama du da haka sai ta ci gaba da yi mata fada mai shige da nasiha hadi da gargadin rayuwa kafin ta umarceta kan ta KWONTA ta huta ta kuma share hawayenta Allah ya sanyaya ya shirya
Ta kwonta din, ama bata samu hutun da ya dace ace ta samu din ba sakamakon tinowa da Tata RUBUTACIYAR (litafin KwAte), tabas ta san Tata kadarar mai zafi ce, haka kuma bata cika son tinowa da ita ba saboda a duk lokacin da ta tuna tana iya wuni ta kwana cikin halin kuncin zuciya da bacin rai, kwata kwata bata so hakan ta faru a wannan babbar ranar ba, rana ce ta farin cikin aminiyarta wace ta jima tana hasashen irin wunin farin cikin da zasu yi, sai gashi wata wace bai dace ace ta shiga huruminta ba ta saka ta aiki irin na rashin hankali
A lokacin da ake hada haɗar zuwa a dauko amarya daga wajen da take wuni ta samu ta silibe jiki ba kwari ta fice a gidan ta je ta samu dan sahu ta shige ta nufi gidansu
A lokacin da mai adaidaitar ya tunkaro gidansu sai ta ji inama ace zata iya samun shiga ba tare da ta hadu da kowa ba? Kai da ta ji dadi sosai
Idannuwanta kyam a kan kofar shiga gidan bayan mai adaidaitar ya tsaya ta sauko ta Bude ambulop din nan tana duba kudin ciki ta zaro ta mika masa sannan ta juya ta sake zubawa kofar ido kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi cikin gidan tana rokon Allah ya sa kar ta hadu da kowa
Tana shigowa gidan daidai Farisa na watso ruwan wankin da ta gama tsakar gidan ba abinda ya shafeta da gudun wajen ya cakule
Kallon Rauda ta yi daga kasa har sama ta tabe baki ta yar da robar wankin nan cikin rana ta yi shigewarta cikin madaidaicin falon gidan
Ajiyar zuciya ta sauke sakamakon jiyo sautin Muryar Farisa tana fadin" Mama ga Rauda nan ta dawo fa, dan Allah ta dora maki girkin Ni na gaji da yawa"
Takalmanta take cirewa kunnayenta suka jiyo mata magangannun da suka gama zaunawa a kirjinta masu kayar mata da gaba da hadasa mata bugun bugun zuciya, gashi amon Muryar na Maman matsowa yake yi tana fadin" wace Raudar? Yau da ban ci mutuncinta ba marar mutunci da bata gaji abin ALKHAIRI ba? Ace ana auren a gidan kawar taki masu kuɗi kina babar kawa ba zaki tsaya ki kawo mana abin arziki ba zaki dawo min yanzu? Uban me kika zo dauka a gidan ko dan nice banza da bani da mai tausaya min kika dawo ki ci dan abinda na kurkurta na ajiye? Ina take munafukar banza da wofi wace babu ta sauka a gidansu ta yi ya'ya ta yabanya Shegiya wace ta gaji tsiya?"
Kai ta sauke kasa tana sauke ajiyar zuciya hadi da ambaton Allah a cen kasan zuciyyarta sannan ta dago da sauri tana kallon inda Mama ta ja ta tsaya tana kare mata kallo da wani matsiyacin kallo
Jiki ba karfi ta ciro ambulop din da aka bata, wace ta amsheta ne dan ta ba Mama ko zata samu ta numfasa cikin Salama, tana rayuwa a gidan nan ne dan tana kawo irin gudunmuwar da Mama ta fi so wato kudi, ba ruwanta da sannin ta hanyar da zata kawo mata, ita dai burinta ta ciro ta miko mata, ba godi bare na gode zata tisa kudin da bata bada abin siyarwar da aka Saïda aka kawo mata ba ta irga ta toshe a harshen zani ta boye ba, dan na ita ta haifa ba bale hakan ya dameta , wannan din itace kadai hanyar da RAUDA ke iya samun abinci a gidansu, gidan kannin mahaifinta , marikinta
Ambulop din Mama ta bude ta dubawa, ido ta zarro sakamakon kudin da ta gani a ciki ta dago tana dunanta ta ce"
Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*4*
*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nijar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*
*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
Ido ta zarro sakamakon kudin da ta gani a ciki ta dago tana dubanta ta ce" Wadinnan kudaden duka naki ne? Ama sato su kika yi ko?"
Cikin nauyin harshe da zuciya Rauda ta girgiza kai ta ce" A wajen kai abincin angwaye aka bamu"
Ido Maman ta sake kwalalowa tana fadin" Ikon Allah, shi yasa nace maki yau din nan ki dage bakin rai bakin fama ki warto abinda kika samu kar ki yi sake ko kadan a fi ki ci, ke ce fa aminiyarta ta hannun dama, kin ga dalilin auren nan kema sai na fara maki dan tare tunda an mutu an barni da wahala dan ko shi wanda ya dauko ya kawo min ya zura min ido ina ta fama ina faduwa ina tashi, YANZUN me ya dawo da ke gidan tun warhaka bayan ba'a yi mai kankat din ba, ba'a kai amaryar ba?"
Da kyar Rauda ke iya daga idannuwanta, muryarta a raunane sosai gaban wace bata iya dagawa murya ta ce" Kaina ke min ciwo sosai, shi yasa na dawo gida dan hayaniyar jama'a ta yi yawa a cen din"
Sai da Mama ta yi mata kallon shekeke kafin ta tabe baki ta juya tana fadin" Kin ga, karma ki cire takalmi maida shi, inada panadol a nan bari na baki ki kora da ruwa ki juya, hayaniya ai dole a yi, in banda ɗorawa kai abu kai ba kowa ba kace ba za'a yi maka hayaniya ba, ki wuce kawai ki koma dan WALAHI na tabbata tunda yanzu kika samu wannan wanda zaki samu in an jima sai kaina ya kule wajen irge"
Tana fadi tana nufar dakinta ta dauko maganin da ledar ruwa daya ta dawo ta fasa ta mikawa Rauda dake tsaye har kamar juwa zata bugata da kas ta ce" Sha maza juya ki koma "
Jiki ba karfi ta hadiyi maganin cikinta ko abincin kirki babu a ciki ta juya tana langwui ta nufi kofar gidansu kunnayenta na jiyo mata Maman na fadin kar fa ta dawo