Showing 177001 words to 180000 words out of 188741 words

Chapter 60 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9872

san sarai abinda ya hannata barci har ta yi samakon nan ya kuma karra daurar niyar matse mata lamba har sai ta saduda da kanta ta nemi sulhu, ya gaji, ya gaji ainun da ganninta tana wahalar da kanta bayan Addinin Musulunci ba haka yake ba, addinin musulunci sauki ne da shi sosai, kuma Allahn da ya halicemu gafurun rahim ne

Hajia ta saka sandarta ta zunguri kansa tana fadin" Kai dilla in ka ganta a nan ai da kaffafuwanta ta zo , sai ka tambayi mai dakin ko nice na summa ta zo ko? kai dai akoy sarkafar uwa!"

YUSUF ya juyo yana kallonta ya tabe baki kasa kasa ya ce" Wai wani ko kece kika summa, kina nan zaune sai kashe min iyaye kike , an ki a duba kin da wani hijab dinta haba a karkace"

Mah ta saka carbi zata kwada masa da sauri ya karasa kusan Bah ya zauna yana harde hannayensa ya sakarwa Hajia harara wace ke dariya tana fadin" Ja'iri da ka tsaya mana ka ga yadda y'ata zata zane min kai"

Da raha sosai wajen ya fara, sannan suka koma jimamin lamarin nan, inda Hajia ta tabatar da abinda suka yanke ita da Bah, kuma Mah ta tabatar da ta yarda sannan shima ya tabatar da yana tare da abinda aka yanke din kafin ya mike ya nufi bangarensa, hakama Bah ya yi ficewarsa aka bar Mah da Hajia, Mah ta mike ta nufi kicin din Hajia dan ba zata koma bangarenta ba sai komai ya daidaita kuma


Yana komawa ya nufi dakin RAUDA kai tsaye, dan ya tabata bata dakinsa

A lokacin Rauda ta yi wanka tuni ta yi sallah ta shiga saka turare a dakin nata da nufin gamawa ta shige kicin dan ta sama masu abincin kari ta ji ana buga mata kofa

ta dan yi jim dan tunanin ko waye, hakan ya sa ta nufi kofar ta kama ta bude tana buɗe baki ta ce" Wa.............."

Sai kuma ta yi dif a hankali ta yi shiru tana kallonsa

Shigar jikinta ya fara bi da kallo, da kwalin idannuwanta da jan bakin da ta dan shafa madaidaici ya sauke dubansa a kan hannayenta da ta rungume a kirjinta tana kallonsa a hankali ya ce" Morning aunty"

Ido ta kwalalo tana sauke hannayenta da wata irin kunya ta sada kanta ta ce" Lah yayanmu, ban kai da gaisheka ba fa ina mamakin ganninka a nan ne ban san me ka zo yi ba yi hakuri yayanmu, ina kwana an tashi lafiya?"

Shigowa ya yi da kyau ya ce" An tashin dai, lafiya kuma ai sai na zama ango, abinda ya kawo Ni kuwa zance na zo "

"ikon Allah, innalilahi " Ta fada a hankali tana zagaye shi ta karasa ta dauko hijabinta ta karaso zata wuce

hannunta daya ya kama ya janyota a slow ta zo gabansa da dayan hannunsa ya saka ya tareta yana dage gira ya ce" Kar ki gogeni mana kato da Ni, ke wai daga bugawa sai ki wani bude ba hijab dan kin ganni ki saka hijab, to mamanki bata ce maki ba hijabi tsakanina da ke bane ko kallon katon kwarata kike min"

"Na shiga uku" Ta fada tana rintse ido

Ya sake tare fuskarta ya ce" Mun shi shiga uku dai, ina zaki je dan na zo sai kace kin ga mai kwasar zancenki?"

" kicin fa zan je yayanmu" Ta fada tana raraba kalmar, dan ya fara fin karfin ta walahi

"Mu je, ama ki ji tsoron Allah ki daina min halayar nan, sai in mance kece fa, ji wani yayanmu, wata magana a sanyaye bayan na san ba tsorona kike ji ba!" Ya fada yana juyar da ita ya nuna mata hanyar kicin din, a dole ta ja ta tsaya tana kallonsa yannayinta na nuni da rauninta a kansa, jiki ba karfi ta ce" Kicin fa na ce zan je?"

Da girarsa ya mata alamun eh sai me?, hakan ya sa a sanyaye ta ce" Kai Sarki ne YUSUF, me ya haɗaka da kicin? dan Allah ka yi hakuri idan yinwa kake ji yanzu yanzu zan kawo maka ko menene in sha Allah"

Fuskarta ya fara tsarewa da ido, sannan ya sauke duban a kan lebenta..............
Shi yasa ya guji sarauta............
Domin shi mutun ne da ya damu da ahali.......,
a lokacin da Bah ke nuna masa ya dace ya daina zuwa wajen Hajia da wajensa da Mah koda yaushe ya nuna masa shi yasa ya sa aka yi masa hanyoyin nan na baya.....domin ya rayu ne a haka, baya tunanin sarauta zata masa iyaka da iyayensa....uwa uba da RAUDA.
Bai san wani yare zai yiwa RAUDA a yanzu ba, abu daya tak ya sani shine idan kicin take zai iya zuwa ya bare mata tafarnuwa, idan mak'up zata yi yana iya rike mata jaka har a gama, yana iya tayata zabar sutura a shago idan hakan ta kama, yana iya tayata kada miya.........'..

Murmushi ya yi yana kallonta a hankali ya ce" Yinwa nake ji"

RAUDA ta sada dubanta daga nasa kasa kasa ta ce" Ohk, me zaka ci,me zan dafo?"

"You.................." Ya fada daga cen cikin makogwaronsa

A zabure ta kalle shi, tana ruko ido, hakan ya sa ya dan shafa kansa yana murmushi a hankali zai yi magana AMNAH dake nemansa a fujajan , har hanyar fita ta je dan ta je nemansa bangaren Mah Taj ya hannata fitar, shine ta nufo bangaren RAUDA duda zuciyarta na tabatar mata me zai yi a cen? Sai dai kiran da mahaifiyarta ta yi mata ya sa take neman nasa a fujajan dan so take ta je ta ji, wai an kawo samaci daga office din shugaban yan sanda ana neman iyayenta? ko lokacin hawa aikin bai gama cika ba ai, waye zai kai karar iyayenta ita a garin Tsatsunburum? ko waye bako ne, kuma shi shugaban yan sandan yau sai ta nuna masa sunne manyan garin, ta tabata dan bai san ita ke auren MALEEK bane ya kawo wannan gangancin, sai dai tana zuwa ta gansu a irin tsayuwar nan, da kuma irin yadda murmushi ke fita a fuskarsa

Maganarta ke neman bacewa a bakinta, ta kai ruwa ta kai mari ya fi a irga bale da ta ga ya zuba mata ido yana jiran ji daga bakinta hakama Rauda da ta juyo har sai da bayanta ya hadu da kirjinsa ta dan matso gana kadan ita dinma tana kallon Amnah din da jiran jin abinda ya kawo ta har nan wajen

AMNAH ta rintse idannuwanta saboda kanta da ya sarra, ta dantse lebenta ta sake saka idonta a cikin nasa

da kyar ta iya kankaro magana a bakinta harufan ba kaifi ta ce"



Duk yadda ta so yin tamkar bata ga RAUDA ba abin gagarar idannuwanta ya yi da bakinta, duk yadda ta so sharewa ta nuna wajen mijinta ta zo ta gaza hakan, har ta kasa tankwasa harshenta tana duban RAUDA da manta abinda ya shiga tsakaninsu saboda kishin dake ranta nata ta ce" Me kike yi a nan da mijina?"

RAUDA ta sake zuba mata tana kallonta, a zuciyarta kuwa tana ta maimaita adu'ar da ta koyawa kanta a kan lamarin Amnah, domin ta zauna ta yi wani dogon tunani dan ta gano menene wutar tsanar dake ruruwa a zuciyarta a kan Amnah, me ta yi mata da zafi bayan zagin rashin kunyar da rashin tarbiyyar da ta nuna mata bata samu ba a gidansu? ta gane daga su din dai sai auren wannan bawa ta ga gama yarda cewar shi din gagarumar rikicin rayuwarta ne, shi yasa ta zauna ta yiwa kanta shawarar in sha Allah zata koyi dauke kanta a kan wannan matar domin bata tunanin in har tace zata ci gaba da biye mata zasu haifi d'a mai ido, irin yadda idan ta riki wuyanta take ji a ranta bata so ta saki kar wata rana aikin gangan ya kaita aikata dana sani a kan abinda yake nata itama kuma halalinta

tinowa da ta yi natan ne halalinta ya sa ta ji zuciyarta na son daukan zafi da shi bayan yanzu yanzu tamkar ta fito masa a mutun ta sanar masa labarin zuciyarta, a kallon nan da suka yiwa junna a ranta babu abinda bata ayana na tarin kaunarsa da muradin sanar masa ba

Cire kanta ta yi a kansu baki daya bayan ta yi masu kallon tare sannan ta juya da nufin tafiyarta

Ya jima da gane karatun yarinyar nan koda da harara ta yi shi, hakan ya sa ya kasa kyaleta ta tafin ya riko hannunta ya dawo da ita yana kallon Amnah a tausashe ya ce" Amnah, yaya zaki fadi magana irin wannan?, Rauda fa matata ce, ko a dakina kika ganta ta zo dakin mijinta ne bale nan din dakinta ne fa"

A tausashe ya yi maganar, ama sai da ya sa hawaye suka taru a cikin idannuwanta,
hannayensu ta bi da kallo ta sake dora dubanta a kansa, matarsa? har fadi yake yi wai wannan yarinyar mai fada kamar mahaukaciya ce matarsa? ai walahi ko zata tafi tsirara sai ta raba auren nan nasu, ai wannan ba sa'ar su jera bace Bama bale ace su yi kishi, banza da ita!
Itama a tausashen sai dai tana wani daga ido ta ce" Magana nake so mu yi"

YUSUF ya sake riƙe hannun RAUDA dake son janyewa ta tafi, dan bata son abinda zai kuma hadata da wannan mai uwa da uban, salon a tabata kadan ta tarawa mutane iyayenta , ita kuwa da nata basa duniya sai dai ta kalle su ko? Allah ya sa Allah ke bada uwa da uba, ita marainiyar itama ya bata masu hankali da tunani ma kuwa

"Bismillah, ko mu karasa mu zauna?" Ya fada a tausashe yana jan hannun RAUDA ya nufi kujerar ta

Baki bude Amnah na kallonsa ta ce" Sir, wai me yake faruwa? Ni du kaina ya shiga duhu menene zai hadaku hadi irin wannan bayan abinda nake kyautata zaton Ni da nake uwar gida ba'a sauke min shi ba bale wannan ? Bayan wannan sirri ne fa, sirrina ne zan yi a gaban wannan munafukar anamimiyar da bata da mutunci?"

Ido Rauda ta sake lumshewa a nutse ta kawar da kanta kasa kasa ta ce" Kar ka ja min zagi mana mijin Amnah, sakeni in tafi Please"

Kallonta ya yi yana jin tamkar zai rasa nutsuwarsa ta kamewar da yake ta yi dan gudun ya yi abinda za'ace bai kyauta ba, sai ya ji haushinta da tace wai wani wai mijin Amnah, wai shine mijin Amnar? ita wannan ficiciyar y'ar me yasa ta iya neman balaki ne? me yasa take da son a yi balaki ne ? in ba dan gudun a fita ace ba alkur'an yau da ya basu fili sun yi idan suka gama ita kuwa wannan ya hade hannayenta ya yi mata hagu da dama da tsintsiya kwaya dari a kafta kaftan abubuwan nan nata na baya cikin nutsuwa da kwonciyar hankali dan ya koya mata kiyaye harshenta a kansa, mtssss kai kai kai!

Mikewa ta yi itama ta sake shaƙar wani haushin, gannin wulakancin ya yi yawa, a zo har dakinta a raina mata hankali kuma ya kasa yiwa matarsa fada? lallema dan ta yi shiru ne za'a nemi a wulakantata?, rai bace ta nufi inda Amnah ke tsaye

ita kuwa tana gannin ta nufota ta zabura da sauri ta bi ta dayan hannun ta nufi inda yake zaune tana fadin" Walahi kika saki kika kuma taba min jikina sai na kai kararki mai fadan mahaukata kawai, yaushe rabon duniya da hadewar jiki dan an gaya maka magana? ki rama mana baki da baki ne sai dai ki taba min jiki?"

RAUDA ta dake kugu tana kallonta ta ce" Kin ga, ki tafin min a nan kawai, ko menene ai ke kika zo inda nake kike zagina, ki fitar min ko idona ya rufe na maki dukan mutuwa dan ba tsoronki nake ji ba, fita kawai"

Murmushi yake yi a bayane saboda yadda Amnah ta bazo da gudu ta zo wajensa ta tsaya din nan da abinda ta fada da wanda RAUDA ta fada matan, ama taurin kai irin na Amnah sai ta ja tsaki tana fadin" Ni ai na ga tsoron naki nake ji, sai ki min dukan tunda uwata ce ke, ina nan din gidan mijina ne inada damar zuwa inda na so a lokacin da na so in yi abinda na so"

RAUDA ta gyada kai tana kallonta ta ce" Ko? ok ina zuwa!"
Ta yi ciki da gudu tana cire hijabinta ta nufi wajen wayar cazar computarta ta wartota ta cire dayan kan ta bar mai daɗin dukan ta bude wajen kayanta ta warto dogon wando ta saka ta saki zanin nata sannan ta dawo a haukace tana fadin" Bari in nuna maki ban haife ki ba ama zan baki tarbiyya!"

Ganninsa zaune ya gyara zama ya tamabe haba ya saka RAUDA hadiye sauran zancen tana leke leke daga inda take kasa kasa ta ce" Ina take?"

Haba ya sake rikewa yana kallonta, alkur'an bulala ce ta dauko zata zane y'ar mutane, wayo ya bani lamarinta karra daukaka yake yi, yanzu wannan y'ar haka take da rikici?

"Tana inda kika ajiyeta, ke koma min ciki ko in zo in mayar da ke!"
Ya bata amsa yana mikewa tsaye

Da sauri ta bi tsayinsa da kallo ta juya tana fadin" Taraya zaku min?"

Ya bi bayanta hakan ya sa ta afka dakin a guje tana kiran Mah

Murmushi kawai ya yi yana girgiza kai ya fice ya nufi bangaren Amnah yana hana kansa fashewa da dariya, domin RAUDA na yin dakinta ita kuwa ta yi waje da gudu tana fadin tana dakinta dan Allah ya sameta zasu yi magana

Da ya kwonkwasa sai da ta leko ta kofar lekawa sannan ta bude masa tana sake sauke ajiyar zuciya ta ja baya, yana shiga ta rufe ta datse tana sake rintse ido dan walahi ba zata taba yarda jikinta ya hadu da na mahaukaciyar matarsa ba

tana kallonsa ta ce" Honorable yanzu fisabililahi kana kallo matarka zata ringa dukana ama ba zaka dauki kwakwaran mataki a kanta ba sai ta min lahani?"

YUSUF ya yi tsaye kikam, bai yi alamun zai karasa ya zauna Bama a kujerun wajen, kai irin kwallon da yake dan bin dakin da shi zaka gane ba zai taba zama a cikinsa ba, a nutse ya ce" Kin san bata son zage zagen nan, idan kika kiyaye fa babu abinda zata maki"

Tana cikin wani yannayi ne, kana ganninta zaka ga rashin nutsuwa a tatare da ita, abubuwa ne sun yi mata yawa, a yanzu haka ta nuna masa wajen zama ya kai sau uku yana dan sharewa, dan haka ta ringa yawo shi kuwa yana bin kaffafuwanta da kallo , a birkice ta ce " Sai ta ringa wani isa da isa kamar wace ka fara kwana a dakinta, Ni ai Ni ce matarka ta farko, Yaushema ya zo nan din? Ni ai bata isa ta gwada min sonka ba ai ka sani sarai fisabililahi ko?"

Kai ya karra sokewa sai kuma ya dago ya dubeta, a cikin makogwaronsa ya furta" Uhum"

Sai kuma ya ce" Menene maganar da kika ce zamu yi?"

Sai a lokacin ta dan dafe goshinta ta furta" Au, wai su Mom ne suka yi kirana an kawo masu samaci daga gidan polisawa, shine nace kar su je bari in sanar maka yanzu yanzu a yi kiransa ya soke koma meye!"

Cike da tausayin kansa da kansa da kuma karra tsoron lamarin nan yana dubanta da mamakin tun dazu samacin har ya kai masu, ta zo da nufin yin maganar ama ta bige da sanyo nata maganar , maganar banza maganar shirme, iyayenta jama'a? subahanallah subahanallah, shine bambancin haihuwar da Allah ya umarcemu mu yi, da irin wannan haihuwar
Yana dubanta ya ce" A kan me zan saka ya janye maganar? a kan wani dalili aka kai masu samacin"

Itama sai ta tsaya da yawon da take yi ta ce" Naga ai Ni matarka ce, zubar maka da mutunci za'a yi idan aka kai iyayena wai gidan polisawa, ban san dai abinda ake tuhumarsu da shi ba, ama ko menene karya ake yi masu !"

Kai ya kawai saboda ƙarara shirmenta da haukanta yake gani a bayyane
ya juya yana fadin" Idan sun kira , ki sanar masu su je din shi yafi alkhairi, dan ba zan hanna a tuhumesu ba idan sun yi laifi ko su wanene su!"

Daga haka ya fice a dakin ya nufi nasa dakin, cikin nutsuwa ya shiga kimtsawa domin ga dukkan alamu fitar zata kama shi dole

Ita kuwa ta jima a tsaye cike da mamaki da tsoron furucinsa, sai yanzuma wasu abubuwa suka ringa dawo mata da kamar ya ringa kaucewa ko ya fada mata gwa da gwa

kukan wayarta ya sa ta karasa jiki a mace ta daga ta amsa kiran yayarta dake wani irin kuka tana fadin" Ke wai kina gidan uban waye wai? yanzu su Mum na waya da lauyansu yan gidan su kawar nan Tata da suka yi fada ta baya suka shigo har ana ririkesu sai sai sun kasheta da hannayensu, wai samacin da aka kai sunne suka kai, wanda ya zo din ya'yan wannan y'ar Tata ce da ta rasu wai walahi ba zai yi jiran hukuma ba da kansa zai daukarwa kansa fansa, wai mum ta saka laya a bakin kanwarsa aka binne ta da ita, wai yau itama sai ya dinka mata layar a baki, da kyar masu gadi suka fitar da shi anguwar nan an zagayeta an cikata da samari dai jifan gidan nan suke sai da dad ya sa aka kawo sojawa, yanzu hanyar da zamu bi mu fitoma ta gagara, innalilahi ki gayawa mijinki kin san yaransa ne idan ya yi magana sunna ji ama kina cen kina hutawarki!"

Wani irin ihu ta saki tana zaro idannuwa, dan adu'ar da zata yi ta nema ta rasa a bakinta ,
A rikice ta ringa rarumar hijabi tana fadin" Bari in sanar masa, ina zuwa, ganinan Ni dinma , laya kuma? a bakin mataciya? wace laya ce kuma mun shiga uku, laya? laya?"

Ta fito da wayar a hannu ta yi niyar nufar bangarensa ta jin kanshin turare ya gama cika falon baba gaba daya, sai kuma ta ji karar bude kofar baya ta bangaren da yake ajiye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login