Showing 99001 words to 102000 words out of 188741 words
Abdul harda turanceni?" Aba ya fada da yannayin barkwoncin da ya sakata yin dan murmushi, ama sam bata iya yin dariyar da abin ya dace ya sakata ba, karshe salamarta ya yi dan ya kula ta daina gane yarensa ta mike ta fito daga ɓangaren bakin da aka sauke shi ta shiga tafiya a hankali tana jin tamkar iska na son kayar da ita, bayan ita din masha ALLAH a yanke take sosai, da wahala iska ta yi mata watsawar kara in ba gagarumar iskar dake iya jijigar mota ba
tanfatsetsiyar wayarta, wace tun bayan kwana uku da bacewar Tata Mah ta bata cewar yayansu ya sa aka kawo mata daga shagonsa mai sunna ONLY IPHONE dake cikin gari, wayar da ta ninka Tata a tsada da kyau, ta kampanin iphone din ce da layi harda katin da har yau ta kasa cinyewa duk irin kale kalenta a wajen su youtube ne da instagram da su tiktok bata gama cinyewa ba dan masu nauyi ne
numbar ABDALLAH dake nunawa cewar shine ke kiranta ya sakata lumshe idannuwanta hawayen da suke mata zafi a ciki suka fita ta sauke ajiyar zuciya ta goge fuskarta sannan ya daga a nutse ta yi salama
"Angel, ina gidanku fa, ama ban shigo baban filin wajen MALIK ba, ina daga nan wajen masu tsaro na barin dama, kin ga dare ya yi ba za'a barni shiga da mota har cen ba, Ni kuwa kirjina ke min nauyi bana jin dadin jikina yau"
a hankali ta hadiye yawun dake makogwaronta sannan ta karasa wajen masu tsaron babar kofar yana jinta ta sanar masu su bar shi ya shigo, dan ya riga ya zo ba zai yiwu ta maida shi ba, gashi yace bashi da lafiya dole zata kula da shi
tana nan tsayen har ya karaso aka bude masa ya shigo da motarsa sannan ta karasa ta dan dora hannayenta ta leka kanta taana kallonsa ta ce" why kake son yawon dare tsakanin hanyar nan da bata da kyau kuma baka da lafiya?"
idannuwanta yake kallo yadda suka nuna alamun jika ya ce" Me zai hannani zuwa inda kike banda mutuwa? me zai hannani zuwa na ganki banda mutuwa? na zo na ga amaryana ne, wai kin san an bani ke? za'a tabatar min da ke nan da sati biyu idan ba mutuwa ce ta daukeni kafin lokacin ba?"
idannuwanta da suka yi yaushi ya dora masa, a sanyaye ta furta" Abdallah, kar ka daga min hankali"
murmushi ya yi yana kallonta ya ce" Kuka kika yi?"
da sauri ta dan zarro ido tana kallonsa ta ce" Kuka kuma?"
Kai ya gyada yana kallonta, sai ta yi murmushi ta girgiza kanta kasa kasa ta furta" Ka je gida Please, ka kular min da kanka"
"Sai idan kin min alkawarin zamu yi waya!"
ya fada yana turo baki, hakan ya sa ta yi yar dariya ta ce" Zamu yi waya da kai dan saurayina....."
yana dariya ya girgiza kai ya ce" Allah akoy maganar da bamu gama ba, kuma ke bakya son surutu ta waya, Please ki shigo"
a dole ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tana sauraronsa
yana kallonta ya ce" Dangane da maganar yarinyar da na taba yi maki a lokacin da nake maroko ne, Angel kin ga na fada maki inada matsalar haihuwa, kin san da wannan ko? shine nake tsoron zamanmu ba yara na iya saka ki a damuwa, kin amince mu daukota?"
shiru Rauda ta yi tana nazari, a nutse ta dube shi ta ce" da ka ga ban nuna damuwa a kan maganar rashin haihuwarka ba, dan nima bana son na haihu, ABDALLAH bana son haihuwa saboda yadda duniya ta zama, kwarai akoy na kirki cike a duniya sai dai masu muguntar sun fi yawa, Ni idan aka barni ba zan iya rabar da kowace halitta a matsayin wace zan iya kukan jinni idan ana yi bayan mutuwa ba in aka zalunta da na yi, Abdallah, inada ciwo mai girma da aka haifar min wanda ya saka min tsoron haihuwa, ina tsoron na haihu na tafi na bari abinda na haifa ya fuskanci kwatankwacin rayuwar da na yi ko fiye da haka..............., da da hali, ka barta a hannun da zata rayu ta ji dadi, ka yi mata dukkan abinda ya dace na rayuwa ama kar ka bani"
ta karashe tana sada dubanta, dan sam bata so ta yi kuka a kan wannan maganar
ya jima zuciyarsa na tsintsinkewa, ya jima yana jin zafi a ransa na tashin hankalinta kuma har sai da ya ayana kalmar Allah ya saka mata a ransa, sannan ya furta" ki yi hakuri, ba haka zai hannaki neman farin ciki ba, yara sunne farin ciki, yara sunne kwonciyar hankali, idan har baka haihu ba in Allah ya sa kana da damar dauka ka rike ka dauka ka rike, Allah shi yake da komai, dan iyayenki sun rasu sun barki ba yana nufin kema zaki rasu ki bar baki da jan sawunki ba, komai na Allah ne Angel, ki yi hakuri kin ji?"
kai ta gyada a hankali ta bude motar ta juyo tana kallonsa, a tausashe ta ce" ka huta lafiya"
kasa amsata ya yi har ta fita ta tsaya tana kallo ya juya motar ya fice suka rufo sannan ta juyo tana ta tunanin Allah ya sa yanzu Hajia ta koma bangarenta, dan ance zasu yi zama ita da Bah da YUSUF , kuma tana matukar son yi masa godiya, walahi har a ranta take son yi masa godiya na irin yadda ya kula da lamarin uncle, kai komai ma ya dace ace ga yi godiyar sai dai bata san ta yada zata same shi ba yanzun, rabonta da shi tun a kicin din nan, bayan nan basu kuma haduwa ba, bata san lokacin shigowarsa da fitarsa ba, ama a yanzu tunda ta ga masu tsaron lafiyarsa a cen tsaitsaye ta tabata yana ciki
a nutse take tafiya har ta kama kofar falon ta shiga da salama ciki ciki tana lumshe idannuwanta saboda sansanyan kanshin da ya shige mata hanci da sanyin da ya daki fuskarta da hannayenta
a hankali ta ɗora idannuwanta a bayansa, saboda irin tsayuwar da ya yi hannunsa wajen kunnensa ga dukkan alamu waya yake yi
kasa gaba ta yi ko baya har sai da ta ga alamun zai juyo ta dan motsa a hankali ama kuma bata karaso din ba har ya juyo yana waya din sai dai idannuwansa na sauka a kanta ya yi shiru da maganar da yake yi tamkar ana kwata a bakinsa dan ransa a mugun bace yace, domin zaman nan da aka yi dan a fada masa ne tarewa da za'a yi nan da sati biyu dole zai tare da mace matsayin tasa, da kuma bikin yarinyar nan ko me? da bikin sarautar, mace akace zai tare da ita wace zata zamo zabi ce daga Hajia, tunda da ranta dole zata zaba masa matarsa ta farko kamar yadda suke yi, da ace ta rasu ne sai mahaifiyarsa ta zaba masa
kansa ya dauke gannin ta juyo ta sake zuba masa ido a karro na biyu ta ki dauke dubanta a kansa ya ci gaba da maganar har ya gama ya kashe kiran ya wurga wayar saman kujera sannan ya karasa ya zauna yana jin tamkar kansa zai fashe da ciwon kai
a sanyaye ta karaso inda yake zaune, da farko ta zauna saman kujera nesa da shi kadan sai kuma ta sasabto kasa ta duka jikin kujerar a tausashe sosai ta ce" Barka da warhaka MALIK"
shirun da ta ji ya sakata dagowa a hankali ta dan kalle shi, ta ga yana nan din fa, amsawar ce bai yi ba, dan haka ta sake maida kanta a tausashe ta ce" Dama ina ta so na yi godiya ne, Allah ya saka da alkhairi, na gode, na gode, mun gode , mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi, irin yadda ka fito da Abana, ka kai shi asib......"
"RAUDAH!" ya furta a cen kasan makogwaronsa, wanda ya sa ta dago da sauri saboda irin yadda amon ya ratsa dukkanin sashen jikinta
idannuwansa dake lumshe ya bude a kanta, sun yi jajir ya watsa mata wani kakausan kallo, a kausashe ya ce" Ki bace min da gani!"
da sauri ya sake zuba masa ido, gannin kallon da yake yi mata ya sa ta sake dubansa ta ki tashi din dan sai ta ji kaffafuwanta sun mutu murus, da tsabar tunanin me ta masa? me aka yi?
katse mata tunani ya yi a lokacin da ya mike, hannayen nan nasa dake da girma irin na kakarfan maza ya dunkule ya karaso inda take hakan ya sa da sauri ta yi zaman yan bori tana rukunkume jikinta saboda mugun tsoron da ya kamata na kar aje ya daketa
Rai bace ya ce" na ce ki fita daga idannuwana, ki fita a idona! ki fita a rayuwana tunda ke bakya ji, ki tashi ki bar nan!" ya idasa fada da dan karfin da ya sa Bah dake dakin Mah mikewa da sauri ya fito, Mah na binsa a baya, ita kuma a lokacin da sauri ta mike tsaye jikinta na rawa ta juya da sauri ta yi ciki kuka na kwace mata wanda da za'a saka mata wuka a wuya ta ba zata ce ga takamaiman abinda ya sakata kukan ba,
idannuwan da ya biya da su ya risinar a saman lebenta ya furta" RAUDA, kar ki kawo min garaje a duniyata, RAUDA, kar ki yi abinda zan tsane ki!"
Mah dake tsaye daf da Bah sunna kallonsa gabanta na faduwa da abinda suke ganni a idannuwansu ta budi baki ta ce"
Azl 35
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo
a tausashe sosai Mah ta ce" YUSUF?, me yake faruwa my life?"
a hankali ya sake duban mahaifiyarsa da mahaifinsa dake tsaye sunna kallon sa
kansa dake sarawa ya karra rikewa ga gumi yana haɗawa
da kyar ya iya rintse idannuwansa ya sake budewa, yanzun ba tun karfi yake magana ba dan burinsa ya sauke abinda ke ransa sannan ya nufi dakinsa, yana kallon Mah ya ce" Yaya zaku dauko yarinyar matsayin y'ar cikinku ku kyaleta tana abubuwan nan? ita shikenan bata da lokacin kula maza ne? zance fa ta fito daga motar namiji a irin wannan lokacin, mace ce fa, shikenan ita bata da kamun kai?"
hankali tashe Mah take kallonsa, Bah kuma sai ya harde hannayensa shima nasa hankalin a tashe ama kuma na Mah ya fi nasa
Mah na kallonsa ta katse shi da fadin" Subahanallah, wai wace BABY?, Ni tunda nake ban taba ganninta da wani bayan Abdallah ba, ko wani ya zo wajenta bani da labari?"
da mama yana kallon Mah ya ce" Shi din muharaminta ne da zai ringa zuwa yadda ya ga dama a lokacin da ya ga dama?"
Mamakin Mah ya karru, ta yi gaggawar fadin" A'a fa YUSUF a'a fa, Abdallah ai ba koda yaushe yake zuwa ba, kuma yanzu da aka saka ranar auren su ai shikenan ya gama zama ɗan gida"
ikon Allah kawai ya tsaya kallo kafin ya girgiza kansa ya nufi ciki
da sauri ta daga kafarta da nufin binsa Bah ya rike mata hannu, da hannunsa ya mata alamun kar ta je shi ya bi bayansa
Mah kam abin neman fin karfin ta ya yi, da kyar ta iya komawa ta nufi dakin su RAUDA
Bah na shiga ya wuce bedroom dinsa
zaune ya same shi bakin gadonsa yana rike da kofin da ya jika maganin ciwon kai, dan yana shiga ya dauka ya wurga cikin kofin ya zuba ruwa yana jira ya narke ya sha
"ka tabbata, dan kawai yarinyata ta je wajen mijin da zai aureta a cikin gidan nan ne ranka ya ɓaci haka, ko kuwa bacin ran maganar Hajia ce ta shafeta, ko akoy wani abin a kasa wanda ya dace na sani tunda wuri ko zan iya magance shi?" Bah ya fada bayan ya tsaya yana kallon YUSUF
YUSUF ya dago yana kallon BAH, a hankali dan yannayin da ciwon kan ya kama masa harda ido ya ce" abinda ta yanke ai na san dole zan yi biyayya, babu wani abun a kasa"
Bah ya sake zuba masa ido, sai kuma ya girgiza kai a tausashe ya ce" Ko menene , ya dace ka kula, ka san me yake kaika wannan makurar,, ban saba ganninka haka ba, baka iya fushi ba Son"
murmushi ya kakaro yana sake duban Bah a hankali ya furta" In sha Allah "
daga nan Bah ya juya ya fice dan sam ya ki bashi damar su yi firar nan, sai dai abinda ke cen cikin zuciyarsa na neman lalata farin cikin da yake ciki na firar da suka yi da matarsa, domin tunda ya shige ya zauna yana zayane mata abinda yake faruwa ya so bata hakuri da bakin cewar ba daga shi bane hukuncin zabawa YUSUF macen aure ta fari, kuma ta kwontar da hankalinta in sha Allah ya san Hajia zata zaba masa wace ta dace, sai ta hanna shi yin wannan ta nuna masa to meye a ciki dan Hajia ta zabar masa mace, ko shi bata tunanin idan zai bijire domin fadan da suke yi ba yana nufin baya son Hajia ba, YUSUF na son Hajia fiye da tunanin bawa, dan sabanin da suke samu kuwa ba shine zai dakusar da soyayar da yake yi mata ba
irin wannan halaya nata da suka karra siye zuciyarsa suka saka ya zamo baya iya daina sonta da kaunarta ne, a yanzunma ta gwada masa, shi ya san ita din mai karra ce, mai hakuri ce, mai biyayya ce, sai ga wani gagarumin abu dake iya rikita masu lissafi na neman kutso masu, ya Allah.....ka ƙaryata abinda nake zargi, domin idan har hakane ban san yaya zan iya kawar da kai ina kallo MALIK ya shiga wani halin ba, haka kuma ba zan so na yiwa y'ar mutane dole ba, ita din amana ce a wajena, abar a tausaya mata ce, itama y'a ce, tana da nata zabin kuma tana da ra'ayi, ya rab ko menene ka daidaita min cikin salama.......
da wannan ya je dakin Mah ya zauna saman kujera yana jiran dawowarta
BAH na nufar dakin YUSUF, MAH ta nufi na su Rauda da sauri dan yannayin da ta fice tana kuka sai da ya mugun daga mata hankali
A Lokacin da Mah ke kokarin shigewa bedroom dinsu ne ta ji Muryar Salima na fadin" Me yasa duk abinda ya shafi yayanmu ke mugun daga maki hankali, wani lokacin sai in ga abin bai kai ki yi irin kukan nan ba, sai na ga kin yi kuka kamar zaki sike, shin a nan menene abin kuka haka RAUDA?, haba RAUDA ta yiwu fa kin same shi ne a lokacin da yake cikin bacin rai shi yasa abin ya sauka kanki, ba wai dan ya tsane ki ba, RAUDA yaya za'a yi ya tsane ki kuma fisabililahi?"
ga mamakin Mah, duk irin abinda ke faruwa tana jira ta ji wata maganar ne daban, sai ta ji Muryar RAUDA a sanyaye sosai tana fadin" Salima, kin tabata bai tsane Ni ba?"
itama Salimar sai ta gaza gane komai, kawai ta yi sororo tana kallon Raudar har ta ajiye wayarta ta mike ta nufi bayi ɗan gannin Salima ta ki bata amsa ranta sai ya ringa sosuwa, haka kawai ta ringa jin bacin rai kala kala a cikin zuciyarta da tarin jin haushin Abdallah, ko saurin me yake mata da zai sa a mata aure yanzu yanzu, ita fa auren ne kansa take gannin bata wani shirya ba, to ta barwa Abdul wa yake nufi? lallema sam baya tunani shi kam!
(uhum, 🤔🤔🤔🤔1)
A hankali Mah ta juya ta ki shiga dakin ta nufi dakinta jikinta a mugun sanyaye
Tana shiga ta ga Bah zaune, da sauri ta karasa inda yake ta zauna daf da shi tana kamo hannayensa ta ce" Na shiga uku, ka san tare muka san su ko? Tun yaushe suka san junna? na shiga uku Bah, kar dai , kar dai, to ama kuma in har akoy wani abin tsakaninsu ai da an sani ko? ai ba zasu kyale har a saka aurenta ba ko? wayo Allahna, fushin nan na YUSUF ba banza ba, Ni kam ba banza ba!"
Bah ya sauke ajiyar zuciya a nutse ya ce" na yi iya yina ya nuna min ba komai , ban san wani iri bane YUSUF, Please ki tambayi y'arki cikin hikima, idan akoy wani abin su fada mana tunda wuri dan bana son a zo a hada min tunani,