Showing 54001 words to 57000 words out of 188741 words
Mah kuwa ta komawarta daki wajen Bah
Tana zama da yan mintunna ya'yan yayanta da na kanninta da yarta guda da matansu suka karaso har bangaren dan haka ta mike fuska hade ta ce da ya'yan Bah kowa ya je dakinsa tunda ba komai suke yi a falon ba, ita kuma da isa suka cike falon sunna ta firarsu yan matan kuwa sai selfi din kansu suke dauka, babu mai shiga harkar yar uwarta sunna dane danen wayoyinsu, domin kar ku manta bangaren mahaifinsa babu abinda bai zuba ba, koda mahaifiyarsa ba a nan take ba bai rage su da komai ba saboda mahaifinsa da kanninsa da yake yiwa uzuri ainun,
Raudah
Zuciyarta na cikin hali na damuwa da kunci mai girman gaske
An kawo mata abinci mai rai da lafiya da su lipton, kayan kari dai da zata iya cewa bata taɓa haɗawa kanta su ta ci ba, ama ta kasa ci sai milo ta amsa da Salima ta haɗa mata ta bata sannan ta zauna a dan nesa da ita kadan, da katon hijabinta itama ,
Babu hirar da suke yi, ama Salima bata tafi ta barta ba
Sai da ta gama shan milo din ta sauke ajiyar zuciya ta ciro wayarta daga cikin jakar Mah a hankali ta shiga tunanin numbar da zata kira
Da kyar ta tuno ta Aminu mai adaidaita, dan haka da sauri ta lalubo numbar ta danna masa kira
Bata jima tana ringing ba Umar ya daga kiran yana yi mata doguwar salama
A sanyaye RAUDA ta amsa, ta shiga gaishe shi kamar yadda yake gaisheta
A tausashe ta ce" Aminu, yaya Abanmu an ganshi kuwa?"
Aminu mai adaidaita ya ja numfashi ya ce" Walahi Hajia RAUDA har yanzu dai bamu samu labarinsa ba, ama baki ga yadda sojawa da polisawa ke kai kawo a anguwar ba, ai ki godewa Allah , Allah ya ga maraicinki ya bayyana maki mutanen nan a wannan lokacin, gashi yanzu ance wanda ya amshi abin a hannunsan nan kin ga mahaifin sarki ne, na tabata za'a ji abinda Malan Umar ke ciki bi izinillah "
RAUDA ta sake sada kanta, kasa kasa take maganar sosai, ama bai hanna Salima jin abinda take fada ba, hakan ya sa ta dan kalleta sai kuma ta cire dubanta dan ba zata so ta ga kamar ta takurata ba
A hankali RAUDA ta ce" Kana ji Aminu, dan Allah ka je gidan inna, ka ce da ita kar ta bari Abdul ya ji wannan abin, kuma kar a kai shi gidan nan, ka ga yanzun bana nan, idan aka kai shi na tabata Mama zata amshi shi ne ta galaza masa, ba zai iya jurewa ba, dan Allah ka min kokarin nan ka ji?"
Aminu ya tabatar mata zai je da an jima ya sanarwa inna, ta yi ta godiya har sai da ya ji kansa na dagawa dan shi abin samakal alkur'an, sannan suka yi salama
Tana mayar da bayanta jikin kujerar nan a hankali ta lumshe idannuwanta hadi da sauke numfashi a boye tana ji kirjinta na yi mata zafi, wani kiran ya sake shigowa
A raunane ta kalli numbar
Sunnan wanda ta gani ya sakata dan dagawa kadan ta daga ta kara cen ciki ta yi salama
A tausashe ya ce" tare da ke wifey, kin san wani abu? Yau na zo layin baban masalaci na nan maroco na ga wata yarinya marainiya, wifey ina so mu dauketa mu raineta, dan Allah ki ce min kina so kema? Idan kin amince na dauketa na fara gyara takardun ta, a saka mata sunnanki da nawa, yarinyar shekarunta duka duka daya da wata uku, Please ce min yeah kin amince "
Har ga Allah bata wani fahimtar yarensa, shiru ta yi masa har ya dasa aya, da kansa ya gane kamar bata tare da maganar da yake yi, shi kuwa ya yi kiranta da tarin zakuwa ne , dan Allah ya saka masa son y'aya, ama tun a yanzu an tabatar masa bashi da kwon baiwa wata macen bale ta haifo, shekarunsa Kusan hamsin yanzun, dan yan watanni suka rage ya cika hamsin, Allah ya jarabeshi da son RAUDA, shi Balarabe ne, ya san ba wai kyau ne ko fari ya ja shi ba, ya sani ne Allah ne ya dasa masa abin a zuciyarsa kuma yana fatan ta zamo mata a gare shi, shine damuwar ke damunsa idan ya tuna rashin haihuwa fa baban abu ne a duniyar mata, hakan na iya haɗasa masu rashin jituwa, shi din kansa ya san yana son y'aya, sai gashi yau ya ga yarinyar nan, an tabatar masa wai ana shirin mikata ne gidan marayu, dan kakarta dake rikonta ta rasu ta barta ita daya, mahaifiyarta wajen haihuwarta ta rasu, mahaifinta kuwa yana raye ama babu ruwansa da ita, jaririya ce fa, ama har ta zama kaya a hannun mutane, masu taimakon ta suke rike da ita ne suke shirin kaita yafe yana so zai je a kaita sai a mishi takardu ya zo da ita , dan ya shirya tsaf idan ya shigo Nijar auren Rauda shine abinda zai fara yi kafin komai a gabanan
A tausashe sosai ya shiga magana bayan ya kashe tv din dake dan bayani da harshen larabci, ya ce" Hey, Are You crying?"
RAUDA ta sake lumshe idannuwanta, a hankali hawayenta suka shiga bin gefe da gefen idannuwanta, haka kuma muryarta ta kasa fita, sai shasheka dake fita kasa kasa
Gabansa ne ya fadi, da sauri ya kashe ya shiga yi mata vidio call
Da kyar ta iya dagawa ta zuba masa matatun idannuwanta tana kallonsa kasa kasa
A hankali ya ce" Kuka kike yi? Me ya same ki? Kina ina ne?, me ya faru? Kin san inada matsalar zuciya ko? Kar ki saka na samu attack mana , tell me"
Da kyar ta bude bakinta, muryarta mai zaki da sanyi ta shiga fadin" Uncle dina, ba'a san inda yake ba, kana tune shine uwata, shine ubana, shine komai nawa........, an...an...an kawo kayansa da jini a jiki, bamu san yana raye ko ya mutu ba, ban san yaya zan yi........."
Sai kawai ta fashe da kuka tana ajiye wayar ta dora kanta saman cinyoyinta tana yi sosai
Ya Salam, ya Salam yake ta maimaitawa, kafin a hankali ya ce" Hey, RAUDA? Tashi ki ji"
Da kyar ta dago ta dauki wayar tana kallonsa
A tausashe ya ce" Ki daina kukan haka, in dai ina raye ba zaki yi kuka ba RAUDA, zan taho nan da sati Daya in sha Allah , na daina kaiwa wata biyun kin ji? Zan zo, ko a ina yake, ko nawa ake so a bada a sake shi zamu bada, mu yi ta addu'a in sha Allah, yana raye ok??????"
Kai kawai take gyada masa kamar wata yarinya karama, shi kuwa sai rarashinta yake yi, har ta daina kukan sannan ya mata salama dan ba damar jan firar duba da yannayinta
Gaba daya ta manta ba ita daya take falon nan ba, ita sanyin wajenma ya fara shiga kasusuwanta, a hankali ta karkata dan share hawayenta da hijabin jikinta ta ga fari kar din hannu na miko mata abin gogewa a hankali Salima ta ce" INNALAHA MA'ASABIRIN RAUDA"
RAUDA ta dago jajayen idannuwanta ta sauke saman fuskar Salima, ta kasa amsar abin goge hawayen, haka kuma ta kasa daina kallonta
Salima ta zauna daf da ita ta mika hannu a hankali zata share mata hawayen, RAUDA ta rintse idannuwanta, a birkice kuka ya kwace mata, a rikice ta......
🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹
Azl 20
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo
A rikice Rauda ta mike da nufin tafia, da sauri Salima ta kamo hannunta tana mikewar itama tana kallonta ta ce" ki yi hakuri, kar ki ga ina takuraki, kuma ban tsaya dan na ji firarki ba, na tsaya ne dan bakuwar Mah kike , ita kuma tana wajen Bah, bana so na barki ke kadai kuma sai na ji wannan, RAUDA na ji sunnanki a wajen wannan da ya yi kiranki, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ban san girman dacin abinda kike ji ba, dan ban san dacin maraici ba, nakan kamanta a zuciyata ne, sai na ji dacin na nema ya zauta Ni, sai dai alhamdulilah kasantuwarmu musulmai Allah na saka mana hakuri da dangana komai girman rashin da zamu yi a rayuwa, ki yi hakuri, na saurari firarki kaf, in sha Allah uncle dinki ba zai rasu ba, ko a ina yake za'a samo shi, in sha Allah in dai kika samu gannin yayanmu ko? Walahi yana iya fitar maki da shi a kwana kusa, dan masu kawo rashin kirkin nan babu mai gigin kawo masa, ki yi ta addu'a, nima zan taya ki, ama ki daina kukan kin ji? Kowani tsanani yana tare da sauki Rauda, ki zauna ki ci abincin nan dan yiwa kanki horon yinwa ba zai anfaneki da komai ba sai azabtar da kanki da zaki yi, domin idan da yinwa ko ibada mutun zai yita ne wani iri, kin ji?"
A tausashe sosai take maganar, kuma ta tarewa Raudar hanya, a dole sai da Rauda ta saurareta har karshe sannan ta kasa yi mata tsayaya, dan ko ba komai Salima mai kaunar ta ce, mai son ta ga ta saku ta ware ta daina damuwa ce, dan haka ta dauki nasiharta da mahimmanci sosai har ta koma ta zauna ta yi hakuri suka ci gaba da zama da Salimar, danma ita Salimar takan je jifa jifa ta ga jikin iyayensu ta dawo, sai da aka kira sallar magarib ne suka shige ciki har dakin Salimar suka daura alwallah suka shiga gabatar da Sallah
Mah kam ta yi Wunin nan gaba daya tare da mijinta
Ita har ga Allah ta zata kawai Herde ta yi tafiyarta ne, hakan ya sa bata wani leko ba, bata damu da nema masu abinci, bata san wainar da suke toya mata ta wuce tunanin bawa, domin kiri kiri sun kori ya'yan gidan sun baje, sunne harda su shiga kicin, ko a lokacin da amaryar Bah din ta fito dan tunda ta farfaɗo daga summar bata iya rintsawa ba, ta fito ne da nufin zuwa bangaren su Hajia baba dan ta sake yi masu sannu da zaman makokin sai ta samu taron nan na dangin Mah masha ALLAH, hakan sai ya daure mata kai sosai da sosai, ama kuma bata wani kula su ba ta wuce,dan ba zata kula wannan sabon haukan ba, abinda suka sani shine ba'a isa ba fa ace za'a kawo masu wannan matar da ta galabi zamansu da mijinsu wace a lokacin da ta zauna a tare da su ko me ta yi daidai ne a wajen miji, ko zaginta ka yi in dai ya ji sai ya saba maka, baya gannin kwaliyarsu baya yaba masu kamar yadda yake yaba mata, kai dan karshen wulakanci akoy ranar da girkinta ne ta tashi da zazabi Honorable ya shiga kicin sai da yara suka zo sunna murnar yau babansu zai yi girki suka ga haza, gashi sun tsufabma ba wani daina yin nan nan da ita ya yi ba, dan sun sani komai nata daban yake a duniyar sa yanzu kuma dan an yi nadin sarautar son kai da hauka an ba mashayi sarauta ace uwarsa zata tare masu, ba zai taba yiwuwa ba, ya mike inma yana mikewa ya amshi sarautarsa Sannan ya maida matarsa gidanta shi ya fi zame masa alkhairi..
Ratsa mutanen nan ta yi ta shige dakin Bah
A lokacin Mah na saman salaya tana ta addu'a ta gama sallarta kennan, bata kai ga gama shafa adu'ar ba kunnayenta suka jiyo mata tsaki kasa kasa da fita da bugowar kofar, ita dai bata dakatar ba sai da ta gama ta mike ta je ta shafe jikin Bah da addu'a sannan ta fita ta janyo kofar dan zuwa wajen Rauda wace ta yi kiran Salima sau biyu tana tabatar mata sunna tare shi yasama bata fito ba
Turus Mah ta yi cike da mamaki tana kallon sabon salo, wai kiran sallah da usur, danginta ashe sunna nan basu tafi ba?
Kusan kowa kimtsawa ya shiga yi sunna mata sannu da fitowa, hakan ya sake sakata jin kamar ta dakatar da su da wannan shashancin, dan kuwa ita a memorinta babu abinda ya shige mata cikin junna, to in Bama shirme ba in maye ya manta ai uwar d'a ba zai taba yiwuwa ta manta ba!
Kasa zama ta yi, a tsayen nan tana kallon Herde ta ce" Au ashe kuna nan?"
Herde dukda ranta ya kiya da yar uwar Tata ta yi banza da su a falo bata nuna ba, cike da darajata kamar itace yayarta ta ce" Mu je ina kuma mu barki ke kadai Andiya?, yanzu dai mu manyan muke cewa mu tafi, su yan matan nan fa cewa suka yi ba yanzu ba, ban san me suke nufi ba"
Mah ta kasa tantance Hausar Tata, yan matan ta ringa bi da kallo su uku, Musulima, Hindatu, sai Akilah, wa'inda in ba yau ba, zata iya rantsewa ko a titi suka ganta suma da wahala su shaidata dan basu wani santa ba, a lokacin da komai ya kunce tsakanin iyayensu da ita tun kafin a samu cikin YUSUF ne, to ina su ya'yan jiya jiyan nan?
Bata iya cewa komai ba, yan matan kuwa da shiri suka zo kwanan suka zo, domin sun zo da tufafi, kuma wani abu da ta kula a tsakaninsu su ukun kowace bata shiga sabgar yar uwarta, ita abinda ya fi dan tsaye mata a rai to ina zata ajiye su ne?, itama bakuwa take a gidan nan fa, dakinta yana amsa sunnan nata dan baban su YUSUF yace Babu ubanda zai saka komai a ciki dan da mai dakin
Da kula sosai ta ce" To, abinda dai nake gani kar su takura, kin san nan din ba gidana bane, daki daya ne da Ni sai na YUSUF, wanda na tabata ko yau a ciki zai kwana tunda ba'a gama zaman bangaren marigayi ba, "
Herde ta ce" To ai ba wani abu bane dan sun zauna a dakin Mamansu, ko Musulima ta zauna, sauran su koma gida kawai dan bana so a barki ke kadai "
Idannuwa kawai Mah ta lumshe dan hanna kanta shiga matsanancin yannayin da zata fito ta fadi abinda yake ranta, ta yi gumm tana binsu da kallo dan ta yiwa kanta alkawarin sai ta iya gudun ruwan kowa a cikinsu
Matar yayansu ce da ta tabe baki jin maganar Herde ta ce" Aa, su zauna su duka ai ba wani damuwa bane, kin ga yanzu dole sai an tayata abubuwa kar su mata yawa, ga Honorable ga jigilar mai martaba, mu kuma da ace an bamu dama sai mu zauna mu taimaka mata, to wajen ne yanzun a nan bamu da wadatacen fili, sai an koma wajen Mai martabar in sha Allah "
Magana suke yi a tsakaninsu irin na yan uwa , ama kowa neman hanyar da zai shige jikinta ne yake yi, bayan sun manta jikin nan nata sun riga sun masa dukan da komai ya ruguje dangane da su sai abinda ba za'a rasa ba wanda musulunci ya tabbatar a tsakani
Bata kuma tanka masu ba har suka mike sai sake jaddada mata ta kula suke suka tafi , nan ta dawo ta cewa yan matan tana zuwa
Dakin Salima ta je ta yi salama
RAUDA na jin muryarta ta dago kanta da take tufkewa dan daga wanka ta fito kuma ruwa ya dan bata mata kan shine ta warware ya bushe ta shiga maida tufkewar
Sassauta fuskarta ta yi sosai tana kallon Mah ta furta" Mamah, sannu"
Mah ta saki nata fuskar fiye da ta RAUDA ta karaso ta zauna daf da gadon da Rauda ke zaune ta ce" Kin yi wanka ne?"
RAUDA ta gyada kanta ta idasa tufke kanta ta dauki mayafin suturarta ta saka tana sake kallon Mah
Mah ta ce" yaya abincin fa? Kin ci kuwa?"
Ita du banbarakwai take jin tambayoyin nan idan ana mata su ana nuna an damu da itan nan, kuma har yanzu ta kasa sakewa sosai wajen amsawa, ama kuma tana amsa Mah fiye da kowa, a tausashe da girmamawa ta ce" Mun ci tare da Salima ai Mamah"
Mah ta yi murmushi daidai Salima ta fito daga bayi tana gaisheta ta amsa da kula sosai ta ce" Allah ya saka da alkhairi daughter, kin kular min da yarinyata, oya tashi mu je ki kwonta dan ki