Showing 120001 words to 123000 words out of 188741 words

Chapter 41 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9843

gatan da kike yiwa iyalinki a kwana ana nema masa gafara kin ji?"

Hajia ta sauke ajiyar zuciya a zaunen da take hannaye bibiyu a fuskarta, a raunane ta ce" Allah ya masa rahama, yarinyar nan ke bani tausayi, ina matukar tausaya mata, tana son mijinta, gashi yarinyar akoy tarbiyya da mutunci, ashe ba zasu rayu da mijin ba? rasuwar miji baban tashin hankali ne a rayuwa, Allah ya bata dangana da hakurin rashinsa "

Idannuwansa ya lumshe har Hajia ta gama ta mike tana sake tambayarsa jikinsa
Da hannunsa kawai ya mata alamun da sauki, ta so sakawa a kirawo likita ya nuna ya bar shi, hakan ya sa ta fice ta tafi ta shiga neman layin baban malamin fadar dan ta sanar masa, sosai take tsaye kan lamarin sai bugawa take tana fadin mijin jikarta ya rasu, nan da nan har an shiga kai kawon taya zama a cikin daren nan, abu da masu hannu da shuni

TABAS RAUDA ta yi rashi a karro na biyu, rashin dake girgiza duniyar wace ta rasa, rashin da koda babu soyaya sai an girgiza, ita din ta girgiza, domin a lokacin da aka iso da ita a motar asibitin fadar bata san inda kanta yake ba, a lokacin kuwa su Bah sun ji, uncle dinta kasa rike hawayensa ya yi, hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa danma yana tare da mutane ana ta dannarsa, ama haka ya kwana ya je cen inda RAUDA take, ya dawo inda aka shinfide ABDALLAH
RAI KENNAN, BAKON DUNIYA, MUNA SON KA SAI KA FITA A LOKACIN DA AKA DAUKAR MAKA, ALLAH LA BAMU KYAKKYAWAN KARSHE

Tun cikin dare ta farka, sai suka yi mata allurar barci saboda kukan da take yi, Mah kuwa tana wajenta tare da Salima, Atu kuwa tunda duku duku ta karaso itama tun cikin daren mijinta ya fada mata, kwana ta yi tana kuka idannuwanta sun yi luhu luhu, duk idan ka kalle su sai ka tausaya masu

Da sassafe ta kuma farkawa, wannan karron ba da kukan ba, ama kuma idannuwanta ko bude su bata iya yi

muryarta cen ciki ta furta" Mah, har an yi sutura?"

Mah ta girgiza kai

A raunane ta ce" Mah a kai Ni na masa addu'a kin ji?"

Atu ta sake sada kanta wani kukan na kwace mata, hakan ya sa ta fice a dakin, Mah kuwa ta yi jarumta sosai ita da Salima suka maida mata zumbulelen hijab dinta Mah ta sa aka kawo mota har cikin asibitin suka shiga su hudu aka nufi bangaren Hajia da su, inda gawar take

Sunna zuwa Mah ce kadai ta rike hannunta suka shiga wajen da gawar take
A lokacin ana idasa shirya shi, fuskar nan tasa luwai luwai sai sheki take yi , idannuwansa a lumshe suke kamar wanda yake barci

Tunda suka shigo YUSUF ya dago dubansa ya sauke a saman kansu ya ji wani irin tausayinta wanda bai taba ji ba
a nutse ya dauke yana jiran ya ji ta barke da kukan da ta saba, sai ya ji shiru har ta karasa gaban gadon da yake kwonce a hankali ta ɗora lebenta saman goshinsa ta mana masa kiss, fari farin furfurar gemunsa ta dan zubawa ido kafin a hankali ta furta" Allah ya maka rahama mijina"

Mah ta lumshe ido, hawaye suka biyo kumatunta, ta sake kama hannayen RAUDA ta juyota tana kallonta a hankali ta janyota jikinta ta rungumeta, sai ta ringa sauke wata irin ajiyar zuciya hawaye na bin kumatunta a cen ciki ta furta" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une"

Daga nan suka koma bangaren Mah, wanda ya fara daukan mutane domin tunda asubahi gidajen rediyo aka fara sanarwar rasuwar, da kuma wa'inda aka kiraya aka sanarwa, AMNAH kam dala a bangaren su Salima ta kwana, kuma bata cika tashi da sassafe ba, shi yasa bata san abinda ake yi ba har aka fice da gawar Abdallah aka kai shi makwoncinsa na gaskiya

Sai kusan karfe biyu na rana ta farka a barci ta sauko daga saman gadon maman su Salima ta nufi bayi ta yi wanka ta dauro tawul din Salima dake bayin rataye wanda ya jima nan rataye domin ko ita idan ta yi wanka a yanzu ba zata yi anfani da tawul din nan ba sai ta wanke shi, ama ita ta ratayo abinta ta fito tana jin yinwa na neman yi mata ila suka hade da Salima wace ta zo daukan wayar maman nata da ta sakata zuwa ta daukar mata domin sunna cen bangaren Mah gaba dayansu harda Hajia baba , dan tunda Hajia Baba ta je suma suka je babu wanda ya tashi tunda basu ga ta tashi ba

kallon kallo suka yiwa junna, Salima da bata santa ba ta ce " Bakuwa muka yi banda labari, sannu da zuwa"

AMNAH ta sake duban Salima sama saman nan ta ce" Yauwa, Please a kawo min abinci i'm hangry, ina Hajia ne ta shiga ko tana falo?"

irin yadda take magana tana wani kalkaltu ya saka Salima yin sororo tana kallonta, sai kuma ta ce" Ta tafi bangaren Mah wajen makokin mana baki sani ba? " Tana bata amsa ne dan ta ganta tsamo tsamo a dakin mahaifiyarta, ta tabata ko Wacece ta kusa ce dan haka kawai da wahala ka iya ratsa falo biyun nan ka iso nan kuma har da anfani da bayin dakin, lalle ta kusa da kusa ce

"Rasuwa? a ina aka yi rasuwar kuma? Yaushe?" Ta fada tana dakatawa daga niyar cire tawul din da ta yi zuciyarta na rawa dan bata son ta ji maganar mutuwa, ko kadan bata so, abinda ta ki jinni a rayuwarta kennan, idan ta ji maganar mutuwa sai ta tsani wanda ya mata maganar ta daina yi masa magana sam, dan bata son abinda zai taba mata farin cikinta ko menene

Da mamaki Salima ta sake kallonta, to wannan tun yaushe rabintada fit? ko tace anya mutun ce kuwa? to ko aljanna ce ai tana iya gane an yi rasuwa abinda yan wani gari ma suka ji suka zo? ikon Allah
Ajiyar ta sauke ta ce" To Ni kam ban gane ki ba, ki yi hakuri, ama rasuwar nan tun jiya aka yi ta fa, kuma mijin RAUDA ne ya rasu, kowa yana wajen Mah fa, kuma ace wani da yake cikin gidan nan bai sani ba?"

Baki ta tabe, tana yarfe hannunta , itama fa tana ba Salima amsa ne dan ko daga skin dinta ta san ba yaku bayi bace
A gafarance ta ce" Baki sanni ba? Ni ce matar HR EXCELENCY , I'M AMNAH!"

Sai da Salima ya sake kallonta da sauri, dan abin ya shige mata kunne kai tsaye ne
kai ta dauke, cike da mamakin wai da gaske ko a'a?, sai dai tunawa da ta yi y'ar Wacece, kawar mamanta sai ta yarda, ama abinda ya bata mamaki dama a nan aka dauketa? ai ita ta yi tunanin tana bangaren yayansu, kuma wannan abin da ya faru ba wanda ya tuna da ita,
ikon Allah sai ta kasa tafiya har ta bude yar akwatinta ta ciro wata riga irin masu bin jikin nan ba ruwanta ta tube a nan ta saka bayan ta saka breziya da pant

Salima ta dago kanta jin tana fesa turare, da kula ta ce" Aya, ban gane ki ba ai, inai maki oyoyo, ki saka hijabinki mu je wajen Mah din, a cen ne ake zaman rasuwar, mijin RAUDA ne ya rasu kanwar Malik ce!"

Har ga Allah idan aka kirayi sunnan Mah sai ta ji gabanta ya fadi, ko dan an gama fada mata Mah din nan tsaf take iya hannata zama da mijinta ne? mtssss ita dai sam bata son ko sunnan matar, ama kuma sai ta shiga neman hijabin da ta amsa na maman Salima ta dauka ta saka ta dauki tanfatsetsiyar wayarta tana kunna wa dan tun cikin dare da ta gaji da kallon Tiktok ta kashe ta yar barci ya yi awon gaba da ita sai tashin nan da ta yi, bata nemi sallah ba, ko bata yi ne? bata dai yin ba yanzun

Salima haka kawai take gannin kamar AMNAH din nan bata da kamun kai, kuma faratunan dake hannayenta hade da kunshi sun bata mamaki matuka, ama kuma akoy fari, farinta har wani yellow yake yi, kuma idan tana magana idannuwanta a tsaitsaye suke, hakama yannayin maganarta ita kam sai take gannin kamar irin mutanen nan yan duniya haka, ama kuma ba zata yanke mata hukunci haka ba, ta girmamata a matsayinta Na matar ƴaƴanta, ta yi mata jagora sun tafi a mutunce har bangaren Mah, a lokacin Hajia na tausar RAUDA kan maganar cin abinci, firr RAUDA ta ki ta ci komai, ga kuka, ga jikinta zafi, hakan na neman birkita lissafin Mah da duk wani mai kaunarta, domin tunda aka saka ta saka wani katon hijab aka bata carbi aka tabatar mata daga jiya ta dauki nadin amarci a kanta yau na takaba ya kamata, wata hudu cif da kwana goma a duniya, du sai ta sake rikicewa har suka shigo tare , Salimar ta kai wayar wajen Mamanta dake zaune tare da dayar abokiyar zamanta, sannan ta wuce ciki inda Hajia ta shige da RAUDA, wato dakin Mah, hakan ya sa mahaifiyarta rakata da harara a ranta tana jin in sha Allah wannan karron idan ta rike Salima sai ta yi mata tsinanan dukan da zai dawo da ita hayacinta, dan ta kula kyaleta da take yi ne take son fin karfin ta

Zaunar da RAUDA Hajia ta yi bakin gadon nan, ta amshi madara mai dumi da Mah ta kada mata tana kallonta ta ce" Maza sha kadan kadan, ba'a so idan ciki ba komai a ci abu da yawa kuma ba zai yiwu ki zauna da yinwa ba kin ji y'ar nan? yaya zamu yi? Allah ne fa ya amshi abinsa, idan kika yi haka ai baki godewa Allah ba, ki yi hakuri kin ji? mutuwar nan muma ita muke jira, Allah ya kyauta namu zuwan"

Mah ta amsa da amen , ta mikawa Atu kwanon abincin ta nufi wayar dake dakinta tana kukan neman agaji

wayar ta daga a nutse ta yi salama
YUSUF dake zaune a falonsa tare da baki a nutse ya ce" Barka da warhaka Mah, yaya hakuri"

Mah ta amsa a hankali sannan ta yi shiru tana sauraronsa

A nutse ya ce" Akoy daidaikun mutane dake zuwa da maganar bashi, na kansa da wanda yake bi"

Mah ta bude idannuwanta dake dan sade, a hankali ta furta" Aya, ka ga kuwa a jiya Allah bai bashi ikon yi min maganar nan ba, ga fa akwatin da ya bani ban sani ba, ko abinda ya yanke haka din ne, ita daya ce zata gaje shi ko yayane, ga dai takardu na dukiyoyi da kys din gidajen da na motoci da kuma harkar banki, bashin da ake binsa ai ko nawa ne kawai a fadi sai a biya ko?"

Dan shiru ya yi, sannan ya furta" Na biya , wa'inda aka kawo kuma gasu ajiye"

Mah ta ringa godiya, har sai da ya ji kamar yace ya isa ama ya san in ya fada din ma sai ta ga dama zata bari

"Salima yi maza jiko min tawul na goge mata jikin haka, barshi shan madarar ya isa haka" Muryar Hajia ta shiga kunnayensa

A hankali ya dan daga idannuwansa a lokacin da Mah ke fadin" Ina Amnah ne? "

Har ga Allah sai ya rasa wace Amnah, sai da ya ji Salima na fadin" Tana falo wajen su Mama " sannan ya dan yi shiru ya tuna ashe wannan mai kama da birin ce Amnah
Shi kam sai ya yiwa Mah salama ya ci gaba da hulɗar dake gabansa

A cen wajen Mah kuwa sunna samu Rauda ta dan daidaitu suka fito falon Mah karami, a nan Mah din ke sanarwa Hajia abinda ya faru a jiyan

sosai Hajia ta sha mamaki, Bama kamar maganar dukiyar nan, sai ta rasa abin fada, sai adu'ar da ta ringa binsa da ita ta saka Mah ta kai akwatin ta adana tace sai Malik ya nutsu a kai masa abinda ya yanke sai a yi
Mah dai ta adana ama ba Malik zata kaiwa ba gaskiya, Bah zata ba ya ga uncle dinta abinda suka yanke shikenan.

Dare na tsalawa MALIK ya gama salolin da ya saba ya haye saman gadonsa dake gyare fes fes ya shiga kiran SHAHEED a waya yana tunanin ta yiwu yana cen yana barci ko yana ibada

"kai, me kake yi nake ta kira baka daga ba, hala har ka abin an ?" SHAHEED ya fada a tausashe bayan ya bude idannuwansa da suka yi masa nauyi sosai dan barci ya fara sandarsa

Kai ya girgiza ya ki bashi amsar tambayar tasa sai wata tambayar da ya yi masa yana dubansa ya ce" kai, wai kiran nan na meye? ina NAJEEBA"

"Ciki na dirka mata, tana cen tana yan amaye amayenta, na so zuwa suturar wannan bawan Allah, sai dai ban samu zuwa ba, ama in tambayeka ba shine mijin RAUDA ba?"

Da sauri YUSUF ya bude idannuwansa ya yi shiru ya kasa cewa komai sai da shaheed ya ce" Ikon Allah, bawan Allah ashe lokacinsa ya yi, Allah ya masa rahama, dama ba matarsa bace ita, taka ce"

Idannuwan nasa ya kai kan wayar, yana jin wani tukuki na tukarsa

kai ya girgiza a hankali yana maida idannuwansa yadda suke, kasa kasa ya ce" Bana tunanin zan iya , Ni ba namijin da za'a ringa wulakantarwa bane, man sumanta biyu , kuma inaga yanzuma bata da lafiya, in ba raini ba ai binsa take sai na idasa yarda da soyaya......Please daina min maganarta, dan ba zan taba yafe mata ba, yi min maganar dawakan nan da nace maka muna da Muradi!"





🤔🤔🤔🤔🤔 Biya Muradi kamar kana son zuwar mana da bidia
koda yake zamu ga waye zai cika maganarsa
shin zata damekan ne, ko ba zaka yafe matan ba?




a ringa yi ana karbar BONANZA 🥹, a 1k in sha Allah gaba daya LITATAFAINA, a TUNTUBENI BISA NUMBANA KAMAR HAKA 93811618

Azl 44
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo



Sosai Shaheed ya yi murmushin maganarsa, shi dinma ya ki nacewa kan maganar, a ransa ya kudurta zasu yi maganar ne, ama shima in sha Allah sai ya ja ransa, abu daya ya san ya yiwa kansa alkawari, in dai ya sako ƙafarsa da nufin zuwa gaisuwar rasuwar nan ba zai fitar da kafar tasa ba sai ya ga Hajia, gannin Hajiar kuwa mai lasisi zai yi, dan kuwa a zamansa da YUSUF yana iya cewa a kusa kusan nan da wahala wani ya fada masa halinsa, walahi tsaf zai iya sake nuna taurin kai a lamarin, ama idan har manya suka ji, walau su karra kusantata da shi ta yadda ko ya ki ko ya so zai zubar da makamansa ya nemi sulhu, ko su tayata yaglgala masa lissafi ya yadda lokaci daya zai yi saranda ya nemawa kansa mafita da kansa
Maganar dawakan suka yi, yace su Taj zasu je su gani su zabi adadin da ake so sai a yi transfer, dan harkar kasuwanci ce, dawakai kuwa kowa ya sani sai a gidan kiwon mai Damagaran!

Washe garin ma haka aka yi wunin zaman makokin
Sosai Mah ke kula da RAUDA, hakama Hajia dan ita ke tirsasata cin abinci
Atu kuwa tunda safe take zuwa sai magariba ake zuwa daukarta
Salima kam tana nan tare da ita, duk irin dakon da mahaifiyarta ke yi dan ta damketa Allah bai bata dama ba har yanzu

ta wani gefen kuwa Mah wani abu na matukar bata mamaki da dukan zuciya
Ba komai bane sai irin yadda take hankalce da lamarin amaryar YUSUF!
Bata taba gane cewar ba a bangarensa take kwana ba sai da aka yi kwana na hudu ana zaman makokin nan, shima a ranar iyayenta suka zo gaisuwa ta ji sunna maganar ya dace a san inda take zaune dan a kai suturunta gaba daya domin ba zai yiwu a kai bangaren Hajia ba
Sai a nan ta gane wai a bangaren Maman Salima take kwana duk tsayin lokacin nan
Ba wai kwananta a cen ta ga laifi ba, a'a, maman Salima ai uwa ce a wajen YUSUF, haka kawai dai take dan fuskantar yarinyar kamar da wata a kasa
bale tunda take zuwa wajen zaman makokin nan bata taɓa zuwa tunda sassafe ba, wani bin har sai an yi sallar la'asar take zuwa, kuma idan ta zo takan samu kujera inda ba zata takura ba ta yi kwonciyarta tana dana wayarta, ba'a taba tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login