Showing 123001 words to 126000 words out of 188741 words
dan a bayar da abinci ta tashi ta taya raba abinci ba, ba'a taba kokarin yin wani aiki ta mike aka yi da ita ba, kai ko yannayin yadda ta kula tana kallonta lokaci zuwa lokaci sai abin ya dan dameta, dan ita da ita dai gaisuwar kirki irin ta daban din nan ta sirikinka bata hada su ba, domin in zata gaisheta a takaice take ce da ita morning Mah, shikenan abinda ke shiga tsakaninsu, shi dinma tsaf take gane kamar waje ke kure masu shi yasa take yi mata shi?
Ita dai lamarin na son damunta, sai kuma ta ga tsagar idannuwan uwar da yayarta, sosai ta gane kamar an shiga gidan kosasu kuma isasun kansu halaya, sai ta ji hankalinta zai tashi
Ita a rayuwa ta san bata taba raina Hajia ba, kai ko abokanan zamanta sai da rayuwa ta yi rayuwa tafiya ta yi tafiya ta yi hakuri da son dole sai sun fahimci junna ta kawo ido ta zuba masu take sha'anin ta ba tare da ta tsaya sun yi mata ba ,ko wanin abin ya haɗa su ba, haka A'isha sai da ta ga irin yadda take zaune da ita fa da gaske take ba zata kiyaye hakokin zaman tare ba sai kawai ta yanke hukuncin tsakaninta da ita gaisuwa idan ya kama dole, dan a shekaru ta girmi A'isha ba zata tsaya ta wulakantata a banza da wofi ba, haka kurum sai take gannin kusancin bai yi dankon da zata sauka cen ba, ama kuma ta karra yin shiru aka ci gaba da zaman makokin nan har aka yi sati Daya, aka yi na biyu, aka aka zo ake maganar arba'in ya zamo daga baya ko a leke bata lekowa , itama ta share ta yi kamar bata nan, dan a yanzu walahi wanda zai ci gaba da bata wahala mutun daya ne tak, Hajia baba, itama dan uwa ce, ta haifa mata miji, ta isa da ita, kuma ta isa ta gana mata dukkan azabar da ta yi niya, kuma ta yafe mata dan ko Tata uwar ce ke yi mata haka ba zata taba riketa a rai ba, sai dai ta yi mata fatan Allah ya sa kafin ta koma ga Allah ta daina , dan Allah ne ya halice su baki daya, ko me ta aikata a rayuwa shine zai hukunta ta ba wani ba.
Gaba daya sai ta maida hankali kan RAUDA, da su Atu, da yan uwanta wa'inda ke kai kawo, sosai ta basu damar su ta sake masu fuska ainun, ama tsakaninta da su ba maganar auren YUSUF bale abinda ya shafi sirrin zamanta da mijinta ko da dangin mijinta, wanzuwarsu a tare da ita din ya yi anfani sosai dan komai sunne a tsaye a kai , domin ita da kanta ta gane zaman da matan Bah ke yi saboda Hajia na kusa ne, kuma a haka din ma idan suka zauna sai su yi clan din su sunna shan firarsu da dariya da komai, shi yasa ta kauratar da RAUDA ciki gaba daya da zama, bata yarda wani ya tardata ko ita ta fito haka ranta ya kiya, komi ciki ake kai mata har sai kowa ya watse sannan ta fito ya rawata a falo saboda zaman waje daya, gashi zaman nan da take yi a daki cikin ac ba aikin fari ba baki, duda zaman rashin mijinta ne yannayinta ya karra daukan zafi, domin idan ka kalli RAUDA tsaf zata birgeka, tana nan da yannayin mutun mai sanyi a ido, ama idan ta budi baki ko wani abin ya bata haushi tsaf zaka ga akasin hakan, Balle yanzu da take cikin wannan yannayin, sabon hali ta dauka na rashin surutu da wani irin sabon salon bada amsa wa magana, domin idan har ya zamo dole ta yi maganar ne take yi, dan kuwa a yanzu take baby, ko dan ta ga ana shagwabata ta hanyoyi daban daban sai ya zamo baya ce mata komai ta dora kanta a saman Hajia baba ta fashe da kuka, Hajia baba fa jama'a, dan kuwa yiwa Mah dinta rigima abu ne da ya gama zama a jinin jikinta, ko Abdul karami sai ya fashe da dariya idan ya ga ta turo baki ana cewa ta ci abinci ta kiya, Fatar jikinta kuwa ta zama tamkar kwai, dama ita ba wai fara ce kal kal kal ba, ama tana da hasken fata sosai sai kuma ta hadu da hutu, hakan ya sa fatar ke sheki ko bata yi wanka ba, ta rame gaskiya, dan sosai cin abincinta da tunaninta sun yi yawa, ama kuma ramar bata lalata kyan da ta yi ba
haka rayuwa ta yi ta tafiya, Mah na rayuwarta da ƴaƴanta a bangarenta, kuma tunda aka yi rasuwar RAUDA ke takaba a bangarenta Bah baya zuwa dan ziyarar kwana sai dai Mah din ta tafi idan ta tabatar da sun yi barci ita da Salima, domin Salima a nan take kwana tunda abin ya faru, karshema su dai sun ji Bah ya kirayi Salimar da Mah ya basu umarnin ta maido kayanta nan da zama , zai ga in wani ya haifa masa ita!
Ita dai Mah bata da ta cewa, tsakaninta da Salima haihuwa ce dan yarinyar ta maidata uwa, itama kuma ta yarda y'arta ce, duk wani take taken mahaifiyar Salimar kamar ana zubawa a bayan kwarya ce, dan sarai tana hankalce da ita wuri take nema ta samu ta fake yadda zata yiwa Salimar ama abu ya gagara dan Salimar ta ki yarda su kebance daga ita sai ita, Abdul karami kuwa dama ya zama ɗan daki uku, watarana ya kwana wajen Mah, wataran ya bi Bah bale idan yace masa ya zo su je su ci dadi, wataran kuwa ya kwana wajen mahaifinsa domin har yanzu Abah ya ki tafiya, burinsa ya ga ta gama takabar nan sai ya tafi, dan ko da mahaifiyar Abdul da inna suka ringa zuwa wai mahaifiyar Abdul din mijinta ya saketa saboda tunda suka yi aure ta haifa masa mata sau biyu, shine yace ba zai iya ba shi maza yake so dan bakin ciki ai tsohon mijinta namiji ta haifa masa shine shi zata haifawa mace ya salameta ta dawowarta take yan toye toyenta da idarta hankali kwonce , to sukan zo idan sun sha kwana wajen RAUDA da Abdul din, itama sai da ta yi ta yi da shi ya tafi RAUDA yanzu ai ba ita kadai take ba, yace zai tafi, ba wai ya raina abinda ake yiwa RAUDA bane, ba kuma yana nufin shi ya isa ya bata farin cikin da ya fi wannan bane, yana so ne ya kasance da ita , shi dai yana so ya zamo shima tare da ita har ta fita takaba sannan ya tafiyarsa , shi yasa a kulun ta Allah sai ya zo bangaren Mah a ƙafarsa ya tsaya a falon farko da yama ko da magariba tare da Abdul ta fito sun gaisa ya tambayeta tana lafiya ta tabbatar masa sannan ya koma nasa bangaren, a ƙafarsa duk irin nisan gurin, wanda itama hakan ya matukar kara kusantata da shi , hankalinta ya karra kwonci da yarda cewar yanzu kam ya bar abinda ke fitar da bawa daga cikin duniyar tunani ya kai shi ta maye.
Yau tunda sassafe, tana gama Sallah zata shiga tatare gadon da ta kwana sama Mah da ta fita saboda kiran da aka yi mata tun kafin a shiga masalaci ta dawo da kula ta umarce ta kan ta yi wanka ta fitar mata wasu hijab masu tsararan kyau ama kuma rufafu har kasa ta ce ta saka zasu je bangaren Hajia ne ana kiransu
Hankali ta maida ta kimtsa din, ta saka farar Safa, Tuni Mah ta gyara gadon dan haka ta je saman kujera dan ta dan shafa mai kadan idannuwanta na kallon kasa tana irgawa cewar yanzu fa ABDALLAH ya kai wata hudu da kwana uku cirrrr da rasuwa, abinda ya rage mata a takabar da take yi kwana bakwai ce, hakan ya sakata dafe haba cike da mamakin rayuwa, kwonci tashi yanzu irin yadda kwanaki ke gudu dan Adam baya ganewa sai ya ji guri ya kure lokaci ya yi ba damar kara koda minti ɗaya ne zai gane ashe duniyar na gudu
"BABY?, tashi mu je" Mah ta fada bayan ta leko dakin tana gyara zaman hijab dinta
MUN SAKA BONANZA TA NOVELS DINA A KAN FARASHI MAI RAHUSA IN SHA ALLAH, 1K NE KACAL HAJIATA SU 22, KI TUNTUBENI BISA NUMBANA KAMAR HAKA 93811618 THANK YOU 😍😍😍😍😍
Mikewa RAUDA ta yi da sauri ta dauki kan karamin carbinta fari kal irin na sarkafawa a yar yatsar nan ta sarkafa ta dauko zug din maganin Mah na Hausa na ciwon kafa wanda take sha kodz yaushe, shi yasa Rauda bata nisa da shi, kowani lokaci yana kusanta da zarar Mah din ta gilma sai ta zuba mata a dan kofi, dan mai maganin yace ya zamo ta sha shi tsayin sati biyu sosai, tana iya shan ruwa bayanshi dan shi din ba wani da yawa bane ake shan nasa
Sunna daf da shiga, dan ta baya suka bi, wayar Mah ya dauki ringin, hakan ya sa ta yi murmushi dan ta tabata an taru su kadai ake jira, dan aiki ne ya tsayar da ita, kuma sai da ta dauki akwatin nan mai dauke da takardun RAUDA ta kai sannan ta kirawo ta, kuma ko a lokacin da ta kai Bah din na nan da Aba da kuma Hajia, ta yiwu MALIK din ya karaso shima
A nutse Mah ta fara shiga da salama a bakinta, RAUDA na biye da ita a baya itama ta yi salamar kasa kasa tana dago dubanta dan gaisar da mutanen dake falon, a lokacin ne kuma daga Hajia har Bah ke fadin" Baby kin tashi?
Hajia kuwa na fadin" Zo nan autaliya taho nan zauna"
Aba umar kuwa yana murmushi ya sada kansa ɗan a duniya bai san da irin abinda zai iya sakawa mutanen nan ba, ya san bashi da abin basu, sai dai adu'a, shi yasa ya sakawa kansa duk in dai zai yi sallah to sai ya yiwa daya bayan daya adu'a ta alkhairi
A zaunen da yake, bai dago dubansa ba, ama tunda muryarta ta furta Barka da safiya Hajia, Barka da safiya.........da irin sunnayen da Hajia da Bah suka kirayeta da shi ya saka shi jin wani abu mai kama da haushi haushi da mamakin Hajia, dan kuwa bai taba tunanin akoy mutumen da zata so bayanshi a duniya ba, sai kawai ya dan dago da dubansa dan kallon Hajiar, sai idannuwansa suka sauka a kanta a lokacin da ta karasa ya zauna daf da Hajia, ta kare da dora kanta a saman cinyar Hajiar abinda shi bai sani ba, kuma bai taba gani ba kennan, shi yasa ya kalli Mah da sauri da kuma mamaki ya ga Mah din shi take kallo tana murmushi, dan haka ya dan tabe baki kadan yana duban Mah da kyau ya furta" Barka da safia MAH"
Mah ta karasa ta zauna domin da shi kadai ne basu gaisa ba tana dubansa ta amsa da kula sannan ta masa tambayar gajiya, shima ya amsa din
Sai da aka nutsu da gaishe gaishen junnan cikin dabara RAUDA ta silale kasa ta yi zaune daf da kafar Hajia, kanta a kasa a lokacin da Hajia ta yi hamdallah tana dubansu ta ce" Sati biyu da suka wuce na so mu yi zaman nan, sai Bello yace a yi hakuri har ya cika wata hudu da rasuwa sai a yi maganar, shi yasa na dakatar"
Da dan mamaki YUSUF ya kalli Hajia, ikon Allah yanzu kennan har ya yi wata hudu? hakane fa, dan kuwa ya zarce hudun ma
Hajia ta dora da fadin" Dangane da dukiyar matarsa ne, nace a zauna a san matsaya, Ni dai ida so ko menene aka yanke ta koma makarantar ta, ta islamiyya da ta boko, kafin Allah ya fido mata da wani mijin, kamar yadda na maku bayani kafin su karaso kuma akwatin ke gabanku da kuma na wajen MALIK duka da aka hade gasunnan, Malik ya nuna cewar Uncle dinta ke da wannan ikon, shi zai adana mata dukiyarta, nima kuma na yarda, gatanan dai a gabanta dan ta san komai ya sa nace a zo min da ita "
Hajia ta ajiye maganar, Mah da Bah sunna gyada kai alamun hakan ya yi, sai dai shi uncle Umar kansa a kasa yake dai da suka saurara ya dago yana neman damar yin magana, hakan ya sa suka bashi dama
A tausashe sosai ya ce" Ku yi hakuri, ku yi hakuri, ku yi hakuri, ama Ni ba wanda ya dace da rikon dukiya irin wannan bace, san kuwa Ni tsoroma kudaden nan da gidajen nan suka bani, Dan Allah a yi hakuri ama babu wanda ya cencenci ajiyar dukiyar nan sama da HONORABLE ko MALIK, a yi hakuri kar a hadani da rikicin nan dan tsaf barci zai kaurace min " Ya karashe maganar da raha, wace Hajia kadai ta yi yar dariya
Bah shima ya sauke ajiyar zuciya yana dubansu ya ce" Ka san dukiya irin wannan, ajiyar ta ba abu ne mai sauki ba, a wannan zamanin da duniya ta ki gaskiya ko bankin ka kai sai ya zamo ka san me ake ciki me ke shiga yake fita, saboda yanzu duniya ta ki gaskiya sai hamdallah, dukiyar nan in dai ba wata damuwa a sakata a hannun YUSUF , shine zai sakata inda ya dace"
YUSUF kam du sauraronsu yake, bayanan su na saka shi nazartar lamarin har sai da suka gama magana ana ta fadin eh shi zai adana, kanta a kasa ita, shi kuwa yana bin su da kallo sannan ya dan sauke ajiyar zuciya a nutse ya ce" Babu wanda zai ajiye mata dukiyarta sai ita da kanta!"
Gaba dayansu sai da suka dubi fuskarsa, shi kuwa a lokacin da ya ajiye maganar ya dubeta ne, hakan ya sa suka yi ido hudu shi da ita
Kansa ya dauke daga dubanta ya maida kan Hajia, Mah, da su Bah ya ce" Da ace sun haihu, dole za'a yi rabin gado a killace na abinda suka samu har zuwa yadda Allah ya yi, ama a yanzu dukiyar nan tata ce, kuma kudi ne da gidaje, ba zai yiwu a killace su a ajiye har zuwa yaushe? kudi juya su ake yi, saboda komai yawansu idan ba'a juyawa sunna iya zama kadan, gidaje za'a saka mutanen da suka sani su bi daya bayan daya, wa'inda suka zamo ba zasu anfanu yadda ya dace ba za'a saida a gina wasu ko a sayi wasu ginanu, wa'inda zasu anfanu za'a ba manyan ma'aikata haya, ta yadda kudi zasu ringa shigowa a duk lokacin da ya dace kuma in zasu bar gida zasu gyara dukan abinda suka lalata"
Ya dan dakata a nutse ya dora da fadin" Dukiya da ta zama ta kudi za'a yi dogon tunani na abinda za'a dora na kasuwanci, a taba kadan ba da yawa ba a gwada, ta kula da abinta da kanta, ba ina nufin ta je ta tsare ba, daga gida komai ya shiga ya fita tana gani tana kuma bi har a ga abinda ya bada, idan har ya je yadda ake so sai a sake daukan wata hanyar ta yadda kudade zasu ringa shigowa ne yadda ya kamata"
Ya sake dakatarwa da maganar da yake yi, sannan ya dora da fadin" Zai zamo da account daban wanda kudaden kashewarta na abinda ta yi niya ne a ciki, domin rayuwa ce, tana iya son yin wata gwaninta Tata da mutanenta, kuma idan ya zamo tana jin nauyin tambayar mamanta sai kawai ta yi abinta kai tsaye, ama na haramta mata ciyar da kanta ko tufatar da kanta ko yiwa kanta wata hidimar da aljihunta in dai ina ray..."
ya dan dakatar a hankali ya furta" Raye....."
Ya sake dubansu, dan irin yadda fuskokinsu suka yi, ciki harda ita da ta kasa daina kallonsa, dan ko ta dauke idannuwanta sai ta maida kan fuskarsa a nutse ya furta" Babu abinda zata yi da kanta, ama dukkan abinda za'a yi tana wajen da kuma izinin ta, Abubuwan ajiyewa za'a bude wajen ajiya, na rikewa a gida za'a ba Mamanta ta rike mata, Allah ya bamu ikon kiyaye hakin wani"
Kusan gaba daya da amen aka amsa, Hajia kuwa ta wani gyara zama tana murmushi ta ce" gagara kake uban marayu, gagara kake uban talakawa, ja gaba kake uban masu uba, mararsa ubanma kai ne babansu, ka yi naka ka yi nasu ka yi na masu karfi , na mararsa karfinma kai ke yi, Jikan Hajia khadija kake, jika a wajen gagara marigayi d'an Bello da Ameerah ikon Allah...... Dole...."
Kallon da ya dakata yana mata dan niyarsa tafiya saboda yanada abubuwan yi sosai, ama ikon Allah na Hajia ya saka shi yin turus yana kallonta ya sakata dan tsagaitaWa , ama bata yi shiru ba sai da ta kalli Bah ta ce" Yanzu yaya ka ga abinda na fada maka a lokacin da nace maka tabas yadda ka fada MAKIK , MALIK ne?"
Kai ya girgiza kawai a tausashe ya ce" Shikenan? in tafi?"
Kafin Hajia ta yi magana Mah dake murmushin Hajia ta dago da kula ta ce" AA, kar ka tafi, ina son sannin ina matarka? yaya aka yi wata hudu kennan da aure bata hau abinda ya dace ace ta hau na darajar dake kanta ba?"
A tausashe ta fada, sai dai kana kallo zaka gane abinda ta tambaya amsarsa take so,
RAUDA, kanta ke kasa, a hankali ta samu kanta da jin sarawar kai , a hankali ta lumshe idannuwanta ta ki dagowa , dukda ta so mikewa ta bada waje, ama kuma ta kasa hakan dan haka kawai ta ji dole sai ta ji amsar nan!
Hajia ce ta dauki magana tana mikewa ta ce" Ya Salam, wai dama bata bangarenki yarinyar nan? da bakina na ce da ita bangarenki akace ta je ba na Hajia ba, Ina zuwa"
Ficewa ta yi, Mah kuwa ta dauke dubanta daga fuskar Bah, tana kallon gefe daya, a ranta tana ayana' Ba