Showing 12001 words to 15000 words out of 188741 words

Chapter 5 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9814

Fada

Tunda aka sanar da shigowarsa fadar ya saka duk wani mai motsin kai daidaita kansa
Ba harkar kowa zai shiga ba, ama kwarjininsa da jinnin dake yawo a jikinsa ya saka duk wani marar ji ke kama kansa idan zai shigo gidan koda na second daya ne

Gannin motocin dake parker ya saka shi dan tabe baki ya bude motar ya fice da hannunsa ya yiwa su Ishak alamun su zauna a ciki kar su fito, dan mahaifinsa na nan , ko me yake tsakaninsa da kakarsa ba zai so mahaifinsa na fada baya ji ba


Bai damu da muryoyin da yake ji sama sama kadan na tashi a baban falon ba
Ya dana kai yana salamar da shi kadai ya ji abinsa a cikin zuciyarsa

Hular dake kansa ya cire bayan ya sauke idannuwansa a kan duniyarsa, mahaifiyarsa, wace bai san cewa harda ita a irin zaman nan ba, duba da ba lafiya ne da ita ba kulun cikin ciwo bai yi tunanin tana nan ba da daren nan, tunda ba gida daya suke da sarakuwarta ba wace ta dora Mata karan tsana tana kiranta da lalura ce zama da ita kulun ciwo har ta karra rikita mata yannayi da masifarta, har hakan ya zo ya shigar da fitinaniyar gaba tsakaninsa da ita , dan ba zai taba iya amincewa yana ji yana gani haka na faruwa ba!

Bai iya kallon kowa ba sai da ya karasa har daf da mahaifiyarsa ya cire hular kansa ya duka har kasa ya kamo hannayenta da ya ji su dumi sosai ya dora a gefen fuskarsa kasa kasa ya ce" Khalb, me kika fito yi bayan na shinfidar da ke dazu?"

Murmushi ne ya subuce mata a saman lebenta, tana kallon yaronta, wai ya shinfideta sai kace yarinyar goye ya dai kofar mata y'a ya sakata hawa gadon dole wai jikinta da zazabi , to bayan fitarsa ne mahaifinsa yace ta fito su gaisar da HAJIA

A hankali ta ce" Baka gaisar da mutane ba BIYA MARADI"

Sai a lokacin ya sauke dubansa a kan mahaifinsa, wanda shi dinma shi yake kallo da tarin abubuwan dake cikin zuciyarsa
Dan musmushi ya sakar masa yana dauke dubansa a hankali daga kansa da girmamawar da ta zame masa wajibi wace mahaifiyarsa ta yi yaki kan dorashi a haka bayan ta fada masa cewar ya guji fushin ubangiji a kansa, babu ruwansa da tsakaninsu, ko me zai mata nasa ido ne babu ruwansa, ama ina, sai da suka yi abinda ya daina gannin girmansu, domin du irin yadda ta ringa gujewa wasu yan wulakanci lokaci zuwa lokaci tsakaninta da su sai da suka ringa yi a gabansa, ya zamto du irin soyayar da kakarsa ke masa shina yake yi mata tsana mai karfi Tata ta shiga zuciyarsa, saboda bata ragawa mahaifiyarsa a gabansa

Sai da ya gama bin kowa da kallo, daga inda yake tsugune gaban mahaifiyarsa ya yi masu gaisuwar jimula ta hanyar fadin" Sanunku dai"

Kanwar mahaifinsa ce ta tabe baki tana dauke kanta a ranta tana ayana' Haka fa, dan so wanda aka daurewa, ana iya zagin namu ya'yan tassss ama banda shi, in iskancin ne da rashin mutuncin ya dame kowa, nan dan rashin da'a har ware kansa ya yi daga cikin familly ama kuma a haka ake masa tarbar da ta fi kowace mutunci a cikin ya'ya, ba damuwa shi din da ake so sai ya kawo abin kunya a wannan ahali da izinin mai sama!'
Sai dai du bacin ranta ba zai fito fili ba, bakinsa a zuciyarta, dan HAJIA dake wajen, dan du abinda za'a fada banda zaginsa a gabanta, basa shan inuwa daya da junna ama kuma kowa ya san tana shayinsa

"YUSUFA, gaisuwar Kennan ?" HAJIA ta fada, da muryarta mai dauke da tsufa da alamun rashin lafiya

Sarai ya ji ta, ama ya yi tamkar baya wajen, har sai da suka ringa mintsininsa bibiyu mahaifiyarsa da mahaifinsa sannan ya yi dan murmushi ya kallo wajen da RISLAN ke masa alamun ya gaisheta mana, ga janwar RISLAN din tunda ya zo kanta ke sade tana wasa da yan yatsunta zuciyyarta na dokawa da rigimar da take son rajabowa kanta

Kansa ya cire ya maida kan hajiar, kamar daga sama ya ce" Sanu fa"
Sai kuma ya daure fuska yana dauke kansa

Sai da HAJIA ta sauke ajiyar zuciya na bacin rai tana kallonsa ta ce" Shikenan gaisuwar? Shin baka ji na karye ba? Ko baka ji ba da ka shigo yanzu ai ka gani ko? Ama maimakun ka min gaisuwar da ta dace da tausayawa sai kace da Ni sannu? Haba YUSUFA "

"Haba HAJIA, haba HAJIA, wai kar ya gaishe kin mana, dan Allah kar ka gaisheta Yusuf sai me? In ba dan sarkafa irin ta HAJIA ba yaya za'a yi uwarsa ta ki ki shi ya so ki? Ba zai taba sonki ba HAJIA ko me zai same ki ya same ki ba damuwarsa bace, to wai da wane zai ji ne? Mutumen dake fama a gidan giya da kuma bin mata yaushe yake da tunanin tausayin wani nasa ko jin kai?" Kanwar mahaifinsa ke fada da yannayin hayaniyar da ta dan lafa bayan shigowarsa

Mahaifinsa me ya fara maganar shima ransa bace ya ce" A'isha kar ki saka mahaifiyarsa a ciki, yaro ne ka haife shi baka haifi halinsa ba, da ace halayar mahaifiyarsa ya yi da mun ji dadi, ama yaron nan sam baya jin magana, ba sai kin hada da mahaifiyarsa ba, bata da laifi a halayarsa, itama babu yadda zata yi da shi ne, giya kuwa da mata ai su ya ba gaba sai hakuri"

Kansa ya sake sadawa sakamakon matse hannunsa da mamansa ta yi
HAJIA itama ta budi baki rai bace ta ce" Kin cuceni Balaraba, ban san me na maki da zafi ba, kin yi tsaye tsayin daka kin hadasa gaba da jikana, Ni da ke sai dai Allah ya saka min dan ba zan taba yafe maki ba, domin inada iko a kan yaron nan kuma Allah ya sani!"

"Dan Allah ku yi hakuri" RISLAN ya fada a sanyaye yana jin zuciyarsa na karyewa, da yake da fashewa da kuka kamar yadda kanwarsa ta fashe da shi dan ana zagin Yusuf , dan sauran ya'yan tunda ya shigo suka fece, itama tana zaune ne saboda Mamanta na wajen, bata san haka zata faru ba da bata zauna ba, shin yaya zata yi da ranta a kan kiyayar da mahaifiyarta ke yiwa Yusuf?, Mamanta na masa kiyaya wace ta kazanta ita gashi Allah ya jarabeta da jarabtar dake neman halaka tunaninta, a Tata kadarar rayuwar tana ji a ranta koda makashi ne Yusuf tana so, ko menene hakayansa ta ji ta gani zata iya rayuwa da shi a haka, dama tana daya daga cikin masu masa yaki a gidan nan, ko yanzu itace ta tunawa kakarsu baya so fa yana waje kishiyoyin mamansa na nan ai kuwa kakar tasu ta salami kowa sai su ya su, gashi su dinma sunna neman daga masa hankali, dan a yadda kansa ke sade daga inda take tana gannin tarin zufar dake taruwa a goshinsa
Itama muryarta a sanyaye sosai ta ce" Mama dan Allah ki yi hakuri ki bar yiwa Yaya biya maradi haka"

Idannuwansa da suka kada suka yi ja ya dago a karro na biyu ya zubawa mahaifinsa su, sai kuma ya dauke ya sake duban mamansa wace kanta ke kasa ba zaka iya gane hallin da zuciyyarta ke ciki ba

Hannayenta dake kafadarsa ya kamo a hankali ya dan murza sannan ya mike daga gabanta ya maida hularsa saman kansa ya juya da nufin tafiyarsa

HAJIA ce muryarta na rawa ta ce" Tafia zaka yi ko kallona ba zaka yi ba?"

HAJIA A'isha ta ce" HAJIA dan Allah ki koyi hakuri da shi, tunda ya nuna maki baya sonki ki yi hakuri mana, Allah ya sa ba shi kadai kika malaka ba bale ki yi kukan rashin jika, ita uwar tasa ya jika ya sha ta iya masa komai in an isa"


"Haba aunty....." Yusuf ya fada a hankali yana sauke mata kaifafun idannuwansa a saman fuskarta tar da tar

A hankali ya dauke ya sauke saman fuskar RISLAN da ya sada kansa saboda jin nauyin dan uwansa, wanda suke kaunar junnansu ama a kulun iyayensu na kokarin hadasa fitina a tsakaninsu, sam mahaifiyarsa bata son tarensu

A tausashen da sosai mahaifiyarsa ta yi mamakin ganninsa a haka ya ce" Ka gani? Sai da nace maka ba zan zo ba, ka nuna min ikon da kake da shi na iya tankwasani ka sakani zuwa wajen da ake kallon idannuwa a wulakanta min mahaifiyata sannan a kirayeni mashayi mazinaci bayan mawakin kansa ya boye nasa kirarin?, RISLAN ka fadawa mahaifiyarka ana dane wasu abubuwan saboda albarkacin albarkaci, dan Allah ta rufa mini asiri kar tarin sunayen lalatacen dake kaina su karu ace bayan shaye shaye da zinar kuma na kara wasu, dan ina mai tabbatar maka irin yadda take jin mahaifiyarta Ni na fita ji, domin Ni ba zan kasance kananzir din daga hankalin uwata ba, har abada, abinda ya sa zan bar nan ba tare da na karya yatsar da aka nuna mata ba, kuma ka yi hakuri ka daina zuwa inda nake na roke ka!"
Daga haka ya fice ya mako masu kyauran kofar da ya yi wani irin karan gaske sannan ya nufi wajen motarsa ransa a bace ya bude ya shiga ya ga babu yan matan sai ishak da direba kadai, dan tunda ishak ya ga ya shiga ciki ya salami yan matan nan dan ya san yau ba show sai masifa

Bayan tafiyarsa shiru ne ya fara zagaye dakin baki daya kafin HAJIA A'isha ta shiga share hawaye kamar yadda ta saba ta ce" Shin yaya zai iya karbar mulkin garin nan? Shin me yake yawo a cikin gidanmu wanda YUSUF ke son falasamu ? Du fadi tashin da ake yi da sauki tunda bai fita waje ba, gashi yana so sai duniya ta san me muke ciki?, Yusuf sai kace annoba a cikin wannan ahali!"

Da sauri Anna ta zubawa HAJIA A'isha ido, zuciyyarta na tafasa sosai da magangannunta
Ya Allah, shin basu san karra bane mutanen nan ko ake yi ta yi wani motsin da za'a ce ta yi ba daidai ba?

Kai ta sake sokewa tana ta hailala da ambaton sunnan Ubangijinta, dan tana so ne har su yi su gama bata tanka su ba, sannan tana nemawa danta tsari daga furucin bakunnansu

Mahaifinsa ne ya dauki magana cikin yannayin da ya riga ya zama jikinsa rayuwar yau da gobe yana fadin"



Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA

🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*


*PAID BOOK*


_Bismillahir rahamanir-rahim._


*6*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳



Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*



Mahaifinsa ne ya dauki magana yana fadin" Wace sarautar? Shima ai ya fito fili ya nuna bata gabansa, kema kin san a matsayin da ya taka a yanzu babu mai tankwasa shi amsar sarautar kauye, Bama zai yarda bane da wannan maganar, Ni ba abinda ya fi daga min hankali irin yadda HAJIA ke saka shi a ranta, ba zata iya hakura da shi bane ko menene oho, tunda ya nuna baya son zama a nan din ai sai a hakura"

HAJIA dake fama da kanta ga kuma abinda ya faru ido rufe ta shiga fada tana fadin" Ni dai abinda kuke min bana so, a kulun fada maku nake yi a kan yaron nan ina iya BATAWA kowa, yanzu da baku masa haka ba ai da bai yi fushi ya tafi na, rabona da shi a kadan an kusa wata biyu, yau dalili ta yi ya zo inda nake kun harzuka shi, Ni bana gannin laifin jikana, na uwarsa nake gani, itace ta bude min hanyar komai ta halayarsa, ta Saïda gadonta ta masa jari bayan ita ta san mu ba matsiyata bane, ta saka du ya tsani kowa sai ita kawai yake so, ba damuwa Allah sai ya saka min ku tashi ku bar min waje Ni na ji da abinda yake damuna!"

Anna ce ta fara sauke ajiyar zuciya ta ciciba ta mike da kyar sannan ta karasa daf da HAJIA ta duka a tausashe ta ce" Allah ya bada lafiya HAJIA, Allah ya huci zuciyarki"

HAJIA ta kawar da kanta bata amsata ba har ta mike ta fice daga dakin gaba daya tana tafiya a Nutse ta nufi hanyar ficewa a kafarta du irin daren da ya tsala

Kasancewar mahaifin Yusuf bai fito da wuri ba sai da ya salami sauran matansa ya je ya yiwa ɗan uwansa salama wanda shine sarki a yanzu sannan ya fito ya nufi motar yana Adu'ar Allah ya sa ta kunna AC kar aje haka ta zauna ita da bata son zafi

Yana karasowa ya ga motar wayam babu ita a ciki gabansa ya yanke ya fadi

Da sauri ya sake dubawa ya ga eh lalle fa bata cikin, hakan ya sa da sauri ya shiga nemanta a farfajiyar gidan dan ya san da wahala ta koma cikin gidan wajen kowa dan kusan tsanar da HAJIA ta yi mata ya sa bata shiri da kowa, kowa ya tsaneta a gidan sai shi da yake son abarsa tamkar ransa

Yana son mahaifiyar Yusuf fiye da tunanin bawa
Ciwon ta bai taba damunsa ba
Bai taba gajiya da tatalinta ba
Duk irin tsakaninsa da mahaifiyarsa ta gaza sakawa ya saki Mahaifiyar Yusuf wace take ikirarin nauyi ce a wuyansa marar anfani, bata da wani anfani a duniya sai na karar da dukiyar yaronta, kulun ita ba lafiya kulun ana hanyar fita da ita neman lafiya, babu irin matsin da bata masu ba dan mahaifiyar Yusuf ta fita daga ahalinsu da kaffafuwanta ama ta jure ta kawar da kai take zaune a gidan ba dan komai ba sai dan yaronta daya jal dake rayuwa cikin gararin yau da gobe da yan uba gaba da baya, wanda abin ya shafo harda Mahaifinsa domin yau da gobe ta saka abinda kanwarsa da wasu ke fada masa a kan yaron nasa shima ya fara kwaikwayar yarensu yana fadin abinda ba ALKHAIRI babu kuma magani ma yaron nasu, tana zaune a wannan ahali ne dan ta sani komai tsiya adu'arta itace a sama da ta kowa dan haifa ta yi, kuma ita ta sani koda kare da sata dadawa da warinta, Allah ya kadarta mata aure a irin wannan ahali bata da yadda ta iya sai hamdallah da neman hanyar gannin shiryuwar yaronta dan babu abinda ya gagari Allah, kuma ko wa zai zagar mata ba zata rama ba, zata fadawa Allah ya isar mata ta hanyar shiryar nata gudan jinninta mai sonta da kiyaye bacin ranta, to in bandama abin fada da baya masu kadan yau har sunna da bakin gorantawa wani abubuwan rashin ji na yau da kullum? To wane ba wane ba makaho a bisa makahon doki!
Kiyaya ce an dasa a zuciyar mahaifiyar mijinta Tata tun kafin ta shigo gidansu, an fadawa mamansa cewar idan ta yarda aka auro irinta to fa zata rabata da danta, sai aka yi rashin dace dan nata na yiwa maman Yusuf makahon so din da cece kuce din mutane suka yi tasiri a zuciyyarta, tun ana boyayiyar kiyaya da shayi har aka dawo yau da gobe da zama waje daya ya sa ake abu kamar a zamanin jahiliyya, sai dai basu sani ba, ciwon da take fama da shi na gwuiyoyi bai taba kwakwaluwarta ba, hakurinta kuwa ta jima da YANKEWA kanta zata ci gaba da yinsa ne da mahaifiyar mijinta kadai, itama dan tana yar halak, duka sauran zata basu amsoshin tambayarsu a daidai lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login