Showing 87001 words to 90000 words out of 188741 words
ta ce" Wai kana ina ne?, baka da lafiya ne?"
Da yannayin muryarsa mai rauni da abin ciwo ya furta" Alhamdulilah"
Idannuwanta ta lumshe, dan sarai ta san me amsar ke nufi, idan bashi da lafiya bai cika yi mata dala dala ba, yakan bi ta da alhamdulilah, tun bata gane ba har ta gane
A tausashe sosai ta ce" Ka kwonta da hankalinka,Abdallah tunda aka baka damar zuwa, na tabata aurenmu ba zai dauki lokaci mai tsayi ba, kuma kar ka damu in sha Allah gobe idan Mah ta dawo daga wajen Bah zan sanar mata, na san zata ce ka zo ne, zamu hadu gobe in sha Allah ka ji?"
Murmushi ya saki, harda sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da hirantarta , ita kuma ta bashi dukkan hankalinta har shi da kansa ya yi mata sai da safe sannan ya kashe kiran ta kwonta................
๐ค๐ค๐ค๐ค Su waye yan team BALARABE SAK????????? KU ZO MU KAFTA
Azl 30
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
๐๐ผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐๐ปโโ๏ธ๐บ๐ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
๐๐ผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐๐ผ๐๐ผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐๐ผ (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐๐๐ sai kun zo
Washe gari da safe Mah ta dawo, kana gannin fara'ar dake fuskarta ka san nutsuwarta ta dawo jikinta, sai da YUSUF ya isa asibitin aka dawo da ita
Tana zuwa jikin y'arta ta fara dubawa sannan ta wuce dakinta ta shige wanka
Sai da ta kimtsa jikinta sosai tana shirin fita dan neman abin kari RAUDA ta buga dakin ta shigo bayan ta bata dama ta ajiye kular dake hannunta da plate da cokali tana kallon Mah da murmushi itama a fuskarta ta furta" Barka da warhaka Mah, yaya jikin Bah?"
Mah ta saki murmushi ta karaso inda take tsaye ta kama hannunta suka zauna tana mata alamun ta zuba mata abincin ta ce" Bah din ku, yana lafiya alhamdulilah, ya yi hakuri sosai ya karbi kadararsa, ko yanzu sunna fira da YUSUF na baro su"
A lokacin da Mah ta furta sunnan YUSUF sai da RAUDA ta ji gabanta ya fadi, ama ta ture ta sakawa Mah cokalin tana murmushi ta ce" Allah ya karra masa lafiya da dangana, ya jikan sarki"
Amsawa Mah take yi, da kula, da wani yannayi na gaske wanda take ji Yawancin lokuta idan tana fira da YUSUF, dan haka ta dubi RAUDA bata son firar tasu ta katse ta ce" Ina Abdul? Ban ganshi ba tun dazu"
RAUDA ta yi murmushi ta ce" Salima ta yi bako shine ta ja shi dan ya rakata"
Mah ta yi murmushin itama tana kallon RAUDA ta ce" ki dan bani labarin soyayarku da Balarabe mana? Daughter kina son shi?"
RAUDA ta yi wani kiskirim dan har ga Allah tana ji a ranta da wahala ta iya wannan firar da Mah, kai, yaya zata iya yin irin maganar nan da Mah kuma?, maimakun ta bada amsa sai ta sunne kanta cike da jin kunya
Mah ta yi murmushi a tausashe ta ce" kar ki ringa sako kunya a zamantakewana da ke, Ni uwa nake a wajenki, kar ki yi tunanin zan dauke ki na ba wani aurenki ba tare da na tabatar da kina son sa ko akasin haka ba, dan Ni na san cewa auren soyayya duk rintsi ya fi auren da ba na soyaya ba dadi, domin kin ga shi zaman aure fa ba wai irin na kunna soyaya bane, zaman aure ibada ne RAUDA, duk macen dake zaune a gidanta komai kudin mijinta ko takaicinsa, komai addininsa da nata akoy ranakun da ake iya wayar gari da tashin hankali, rigingimu kala kala akoy su a cikin gidan aure, kuma da ba kiyaya ta sa ake haduwa da ire irin hakan ba, zama waje daya ne da yau da gobe wace ta fi karfin wasa, baby sai ki ga idan irin an hada auren nan ne motsi kadan ana kai kara ana yaji, rashin hakuri da junna zai yi mugun tasiri wajen gaza jin dadin zaman, shi namijin da halaya ta yau da gobe da kuma gannin hada shi aka yi, itama macen sai ta ga ai ba zata iya wani hakuri ba gaskiya, shine zaki ga wani gidan ko an hakura ana zaunen kulun cikin rigima ake, wanin kuwa rabuwa ake yi, wanin kuwa an hada din ama kuma idan soyaya ta shiga da yarda da junna zaki ga sun zauna kalau, duka aure dai ba kamar na soyaya, dan in yana son ki, zai ringa daga maki kafa wajen wasu abubuwan, ba fa ana nufin zaku zauna kulun ku cikin dariya ba, No, zai zamo ne koda halin a yi rigimar ta kama zai yi mai sauki, kuma idan ya yi fushi da ke zai sassauta maki da wuri ya yafe maki, haka kema zaki kasance mai yi masa uzuri, idan ya baki zaki yi da abinda ya baki ne, in babu zaki kasance mai talafawa ne da dukkan dabarar da Allah ya hore maki, in fushi ya haษa ku da junna zaki kasance mai neman hanyar da zaku shirya kanku cikin ruwan sanyi, tsakaninku dai ba wai babu sama da kasa bane na rigima, akoy sosai, sai dai babu wanda zai ji tsakaninku, shi yasa nace Ni da ina da dama da na ringa kawo shawarar a ringa aurawa kowa wanda yake so"
Mah ta ajiye maganar a nutse da kula tana kallon yadda RAUDA ke dan murmushi
RAUDA kuwa, sauraron Mah take yi tun daga farko har inda ta dasa aya
A zuciyarta kuwa tana ayana' Mah kennan, idan haka za'a bi lalle za'a samu saukin wasu abubuwan, ama kuma da yawa ba zasu yi auren ba, bayan wannan Mah duka kaf Yaren soyaya da sauransu na yar gata ne ba wai Ni RAUDA ba, yaushe zan tsaya batawa kaina lokaci da maganar soyaya? Zan iya yin aure idan ba hali na kara gaba, to rayuwar tawa dukantama ai ta in da hali ko ba hali ce, Allah dai ya sa mu dace"
A fili kuwa a tausashe sosai RAUDA ta sada kanta tana fadin" Hakane Mah, yanzun ma ABDALLAH ne yace na roka masa alfarma yau ya zo ya gaishe ki, sannan ya ga jikin nawa wai"
Ta karashe maganar tana ji kamar wace ta yi wani laifi a harshenta, da shayin furucin bakinta kamar wace ta fadi abin a tuhumeta?, sai hakan ya zame mata sabo, kai, ikon Allah, ita RAUDA? To ko tsakiyar dare ta so yin zance ai yinsa take yi hankali kwonce bale yanzu? Allah kennan
Mah ta yi murmushi , sosai ta so sai ta gama jansa a kasa kafin ya zo gidan nan, sai dai wani tunani da ta yi ya kashe mata gaban jiki har ya saka ta ba Rauda damar ta sanar masa ya zo bayan sallar Isha, dan ba zata so abinda ya sameta ya samu koda makiyinta ba, domin ba zata taba mantawa ba, mafarin abinda ya sa suka fara haduwa da mahaifin YUSUF a anguwa su yi fira dan an hanna masa damar zuwa zance gidansu, ance wai ba yanzu ba sai ta gama digiri dinta, duk yadda ta so su bata dama suka kiya,
Ajiyar zuciya ta sauke bayan RAUDA ta fita a hankali ta furta" BI IZINILLAH, DA ADDU'A, DA KIYAYE DOKOKIN ALLAH, ABINDA YA FARU DA NI BA ZAI FARU A CIKIN AHALINA BA, CIKI KUWA HARDA KE RAUDANA, ZAN SANARWA YUSUF IDAN YA SHIGO, ZAMU BASHI DAMA YA ZO SAU DAYA YA GAISHE MU SU DAN ZANTA KAFIN MU BASHI DAMA TA BIYU WACE ZATA BAMU DAMAR SANNIN WAYE SHI, SAI AURE......ALLAH YA TABATAR MANA DA ALKHAIRI"
RAUDA na komawa ta dauki wayar Salima ta kirayi numbar Abdallah
Ta yi ta ringing bai daga ba dan haka ta Bara masa sako, dan tana kyautata zaton yana barci ko yana wani abin da ya sa wayarsa bata kusa da shi
Karatun novel ta shiga yi , wanda ya kusan cinye mata lokacin dan sam bata jin barci, kuma nata jin ciwon kan, haka kuma ba barinta shiga kicin Mah zata yi ba, tunda su Abdul suka dawo da Salima ta bashi littafinsa na karatun addinin Musulunci suka fice sai ta nutsu a karatun littafi har sai da kiraye kirayen sallah suka sakata ajiyewa ta mike tana mamakin gudun lokacin ta nufi bayi
Bayan sun gama cin abinci Mah ta kiraye su gaba dayansu ta sanar masu tana so su shige kicin uku, sauran biyun kuwa su shiga gyaran falo baba da karami saboda MALIK zai yi baki , kuma RAUDA na da bako
Tunda Mah ta fadi RAUDA zata yi bako Musulima ta samu salama a zuciyarta, har ya zamto ta saki ranta da jikinta kamar sauran suka shiga hada hada, dan ta riga ta sani da ace akoy wani abin da take hasashe da wane mutun in ji mutuwa, bako ko na jinni ne ai sai an tantance in dai wando yake sakawa ba sket ba , saima ta samu kanta da yaba girkin da suke yi harda yannayin halittar Raudar a ranta, dan wani sahihin salihin kyau da Allah ya zuba mata mai sakawa a yaba mata koda ba'a so, domin tun daga kalar fatar jikinta har kirarta ta keru iya keruwa yan falo kuwa sunna cen sunna mopping da cenza su labulaye da bade gidan da turarukan wuta da na ruwa, ya zamo tun kusan magariba idan ka tunkaro falon sai dai kanshi ya yi maka maraba
Abinci kuwa manya manyan kuloli na alfarma ne ke jere saman table , kallonsu kadai zai iya baka sha'awar cin su
Ana kiraye kirayen sallar magaribar Mah ta umarce su kan su je su yi wanka su yi sallah su huta
Har sun juya zasu kama hanya Mah ta yi kiran RAUDA ta sanar mata saman gadon ta akoy abaya ta shirya da ita saboda bakonta
Cike da jin kunya ta wuce dakin na Mah ta dauko Abayar sannan ta debo turaran wuta saboda sabo da ta yi da anfani da shi ko a gidan uncle dinta, ta dawo ta shige dakin SALIMA ta zauna sunna fira da Salimar saboda yan matan da suka rigaye su kama bayin, ta karshe na fitowa Salima tace RAUDA ta shiga, itama tace a'a ta je ta fito sai ta shiga
Yau babu harare hararen nan nasu a tsakaninsu da ita, dama su suke yin abinsu ita sai dai ta kalle su ta yi murmushi bata taษa kula haukansu ba, dan kuwa basa gabanta gaskiya kuma ko me suke takama da shi su suka gano ba ita ba
Abayar ta dora a saman kujera mai raga raga ta saka mata turaran wutar nan sannan ta dauko wandon ta irin na cikin nan ta dora da bra kafin ta shige wankan bayan SALIMA ta fito
Bata wani jima sosai a ciki ba ta fito ta shiga gabatar da sallarta, tana gamawa ta dora ta Isha domin an yi tuni
Cikin nutsuwa ta shiga shirya wa bayan ta sauko kayan gyaran fuskar SALIMA
Tana tsakar caje girarta SALIMA ta shigo, itama ta dandatsa lesh mai shegen kyau ta saka hijab a sama tana ta hidima da bakin da suka zo bayan an gama sallar Isha,
Wayar dake hannunta ta miko mata tana fadin" Kin san kuwa da ABDALLAH ya jima a falo karami? Har sun gaisa da Mah sun jima sunna fira , kiri kiri Mah tace a barshi ya yi jira wai, Ni dai na sanar maki dan Allah ki yi ki gama a zaune kike yanzu fisabililahi?"
Da mamaki RAUDA ta kalli agogon bangon dakin , sai ta ga ashe karfe tara ke neman yi, ikon Allah lokaci yana gudu yanzu, ama bayan ta gama sallah sai da ta yi su turaran wuta a jikinta da sauransu sannan ta zauna ta shiga tsara fuskarta kamar yadda ta saba, wato boyayiyar kwaliyar dake mahaukacin fito da fuskarta da baban sirrin dake saka maza haukacewa a kanta, domin ko kalar saka kwalin da take yi yana matukar tasiri wajen ladaftar da kallon cikin ido ta ce" kina nufin cikin aka shigo da shi?"
SALIMA ta zauna tana kallon yadda ta yiwa girarta sai mamaki ya kamata ta ce" dole zai shigo ciki kar ki manta mutumen da ake saka ran zamowa mijinki ne, wai dama kin iya mak'up?"
RAUDA da ta mike tana kallon call din na sake shigowa nasa ta karasa wajen tufafinta ta sauko su tana fadin" Mak'up sai an iya aunty Salima?, ka iya daidaita fuskarka ya wadatar ban fa shafa hoda ba"
Da sauri SALIMA ta mike jin ana kiranta za fice tana fadin" zamu zauna ne my kawa, Please ki yi ki fito na kai masa abinci ya ki ci"
Murmushi RAUDA ta yi ta shiga kimtsawa
Bayan ta saka Abayar ne ta warware gashin kanta ta caje shi bayanta, bata saka masa ribom na ta dauki dan kwalin Abayar ta bude shi ta dan ninka gabansa kadan ta daidaita shi sosai ta caka dauri irin na zahra Buhari ta ya fito sosai ya hau saman suturarta dan sai ta fito dasss da ita tamkar ka sace ta ka gudu
Turaran ruwa, irin mai kaurin nan, mai sansanyan kanshi ma Madina za bude ta shafa a jikinta sosai dan shi ba'a shafawa tufafi dan yana iya yin dan maski maski, shi ta shafa a matsayin mai domin bata cika son shafa mai ba,sannan ta dauko wayar wajen SALIMA ta nufi wajen kujerun da yan matan nan suke ta saka takalminta plate ta juya ta fice a dakin na tare da tace masu komai ba, ta bar idannuwansu da rakata da kallo har sai da suka kula da sun bita da kallo ne su dukansu sannan kowace ta dauke kanta
A nutse take takawa, kwarai kunnayenta na jiyo mata firar maza sama sama haka, kasancewar su maza in dai suka taru a waje to fa sai surutun nan ya cika waje komai wayewar su
Ita dai bata yi gigin bi ta baban falon ba tana murmushin Salima da ta taho dauke da butar shayi
Alamu ta yi mata da ta mahaukacin haduwa, sannan ta mata alamun zasu hade wai motocin MALIK sun karaso na zata iya tsayawa ba ya ritsata a tsaye
Ita kam sai ta rasa to ina zata nufa? Ta koma ne har ya shige ko kawai ta yi tafiyarta?
Tunawar da ta yi na lalle ya biyo ta wajen karamin falo na ya saka ta karasawa karamin falon , domin shi baban falon akoy hanyar shigarsa, shi yasa ta tafiyarta hankali kwonce tana kallon ABDALLAH, wanda hakan ya sa ta ji kamar hankalinta na neman tashi dan irin ramar da ta ga ya yi
A lokacin da take ta kokarin daidaita kanta tana gannin yadda ya wani zuba mata ido yana sauke mata murmushi mai ratsa zuciyar nan hannayensa bude dan kawai ya tsokaneta domin yakan yi mata haka sai ya bude hannayensa yace ta zo, ita kuma sai ta toge tace ta ki din sannan ta bi shi da harara, hakan na matukar saka shi nishadi
Hannayensa a bude, yana murmushi ya ce" zo jikina masoyiyatah...."
A lokacin da take shirin sakar masa harara gabanta ya kwonci kwonci ya fadi, sakamakon shigowar da MALIKI YUSUF BINE BELLO ya yi, kuma idannuwansa tsai a kansu, kallo irin ya kalli Abdallah wanda ganninsa ya saka shi fadada fuskarsa da murmushi ya mike tsaye dan girmamawa a gare shi, domin dama sun san junna yana siyan manyan motoci a wajensa sai dai basu da wata mu'amala ta kusa da kusa , ko siyan motar wata mota ce da ya so sosai shi kuwa ya ki saidawa sai Honorable ya saka baki ya saida masa ita.........
A hankali YUSUF ya dan so lumshe idannuwansa, sai dai wani irin zafi da sukar da suka masa ya hanna shi abinda ya yi niya har ya sake bude su tarrrr a saman fuskarta da ta nuna alamun damuwar da bata san ko ta meye ba har ta dan dago da sauri zata yi magana ta ga ya kauce fuskarsa daga barinta ya maida wajen ABDALLAH da sam bai san abinda yake faruwa ba domin hannu ne ya miko masa dan su yi musabaha
Idannuwansa ya lumshe a hankali bayan ya kalli fuskarsa, a nutse ya .........
Happy juma'at
Azl 31
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce