Showing 156001 words to 159000 words out of 188741 words

Chapter 53 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9849

mahaifiyarta sunna furuci kamar haka..........."
Ta kwashe komai ta sanarwa RAUDA wace ta kwalolo ido kirjinta na zafi da jin lalle za'a ci uwar sabada ita da Amnah da uwarta dan walahi talahi furucin da suka yi a kan Mah sai ta rama, dan babu ษ—an da aka haifa da jinni da zai zagar mata uwa ta kyale shi, hakan ya sa take dantse lebe tana matse hannu tana adu'ar a gama firar nan ta tarda Amnah su daku idan ya so a rufeta a kurkukun masarautar!

Mah ta yi shiru kirjinta na dokawa a hankali ta ce" Sai gani sanadiyar abinda na jiyo da kaina na nemi babanku aka je aka daura maku auren da ta yiwu zaki ji kin tsane Ni, dan na nuna son kai, na nuna karfin ikon kina min biyayya na kakaba Maki auren da ba lalle ki so ba domin kamar yadda kika sani YUSUF baya ji, Yusuf ya yi zaman bin mata, YUSUF mafadaci ne, baya jin magana a da, a yanzu Ban san ko har yanzu yana aiyukan nan mararsa kyau ba ko ya fasa? abu daya na sani ba kowa zai so aurensa ba, komin mulkinsa ,komai kudinsa ba kowa ne zai so kasancewa tare da shi ba, shi yasa na zaunar da ke dan na roke ki......."

A hankali Mah ya sada kanta, zuciyarta cike da tsoron amsar RAUDA, dan walahi ba zata so ta ji wani abinda zai rikita mata lissafi a kan hadin nan ba, ta ji ta karra tashi da kaunar hadin a ranta bayan doguwar adu'ar da ta yi a jiya, dan haka a tausashe a kuma raunane ta ce" Dan Allah......."

Ta sake yin shiru, a hankali ta saki hannayen RAUDA ta hade nata hannayen a hankali ta sake furta" Dan annabi,......Ki yi hakuri ki amince da hadin nan....koda na wata daya ne tak....koda na sati
daya ne tak ..............'''...


Da sauri RAUDA ta kai hannayenta ta riko na Mah a dan rikice ta ce" Mah"

Mah ta katseta tana fadin" Ki bari na roka, dan na san na taro maki rigima, ki bari na roka dan na san abu ne marar dadi, ki yi hakuri ki bari na roka dan a yau yau nake da muradin ki je gidan cen a matsayin matar gidan, YUSUF Sarki ne, sarauta Allah ke naษ—a bawansa, tunda ya hau sarauta alhamdulilah yana iya yinsa a matsayinsa na sarki, yana kokarin kare dukkan abinda ya dace, sai dai sarki sai da sarauniya, tasa sarauniyar maimakun ta zamo uwar marayu sai ta zamo makiyiyar marayu, ta kori da yawa ta zagi da yawa, ta wulakantar da yawa..... RAUDA kin san yau da gobe, na san har yanzu bata samu damar da take bane, da tuni ta aikata abinda take da niya, sai dai Ni na san karfin ikon mace a kan namiji, duk macen da ta yi niyar rikita maka lissafi cikin hikima zata saka ka aikata mugwayan aiyuka ba tare da ka ankara ba , saima ta Barka a zuwan kai ne ke tsara komai dan ka isa, bayan ita ke tafe da ragamar rayuwarka, Ni na tabata idan ta samu dama sai ta dama tashin hankalin da garin Tsatsunburum zai hargitse da fitintinu na yau da gobe ......... Daughter..........i bg you, ki amince da............"


Da karfi RAUDA ta shige jikin Mah ta rukunkumeta, murya na fita da wani irin sauti cen cikin makogwaro ta furta" Mah, Please ki yi shiru........"

Idannuwanta ta lumshe itama ta rungumeta,
a hankali ta furta" Mah......., ina dalili zaki ringa wannan magiyar bayan kawai cewa zaki yi ke wance na miki miji ki je ki yi biyayya?"

wata irin ajiyar zuciya ta kwacewa Mah, a hankali RAUDA ta sake rungume Mah, a raunane ta ce" Koda mahaukaci ne, ko maye ne, ko marar asali ne in dai ke kika zaba min in sha Allah zan yi biyayya bale wanda kika haifa da cikin ki........, Mah rashin jin sa ya kai nawa ne? koda ya fi nawa nima ai ba jin nake yi ba...., ama a haka kika daukeni tun baki san usulina ba, kika rungumeni kike ciyar da Ni ba tare da jiran na biya ki ba, kike tufatar da Ni ba tare da zagina ba, kika bani muhalli ba tare da mun hada kudin haya ba, karshe kika bani uwa da uba da dangi nawa nima wa'inda nake rayuwa a cikinsu kai tsaye da yanci, shikenan dan ina butulu sai a zauna ana hadani da Allah dan an min miji?......Dan Allah ki daina min magiya kar wani ya ji bayan mu na ji kunya Mah........"

Hawayen Mah sai yanzu suka bale, Walahi ta yi tunanin RAUDA bori zata dora tace bata so, ta zata da kyar RAUDA zata amince da wannan magana, sai gashi cikin kudirar Ubangiji yarinyar ta yi mata ba zata har ta sa ta ji wani irin kwarin gwuiwar da ya sakata sakin dariya bayan ta dago ta hannata kukan

Mah na dariya tana kallonta ta ce" Allah ya miki albarka, kin ga kwonta huta ina zuwa"

Mah ta mike cike da farin ciki ta fice a dakin

Mah na fita RAUDA ta sauke ajiyar zuciya ta sada kanta zuciyarta cike da tunani

Yau Yau zata tare? ..........kwarai kamar yadda ta nunawa Mah ta karba har cikin ranta ta karba din, kuma maganar tarewar zata je din............sai dai abinda yake dan kai kawon mata a zuciya shine..................ba maganar wani abin bayan wannan! daga shi har matarsa sai ta saita masu zama ne!, domin shima haushinsa take ji sosai da sosai!

________________________________

Damagaran

Zaune suke a falonsa, Shaheed da matansa, wato NAJEEBA da Nadia

Tun dazu yake waya da YUSUF, su kuwa sunna fira a tsakaninsu, ama tunda ya furta maganar sabon ango NAJEEBA ta yi shiru tana jiran ya gama

sun jima sunna yi kamar yadda suka saba sannan ya kashe yana murmushi ya juyo inda suke zaune dan meeting aka hada na maganar fita, sunna so a karra masu yawan fita a wata shi kuwa yace bai san zancen ba

Murmushi NAJEEBA ta yi tana kallonsa ta ce" Mai girma bawan Allah, abokinka aure wata da watanni ama ba'a daina kiransa sabon ango ba? koda yake, kaima ai ango ne Yaushema aka baka mu?"

murmushin ya yi shima ya ce" Mai girma baiwar Allah jiya fa muka kara masa wata, ina wannan wace mijinta ya rasu? wace Mah ke riko? ita muka bashi jiya"

Dif ta yi tana zarro idannuwanta, a hankali ta ce" Aban MUHAMAD kana nufin RAUDA?"
Shima ido ya dan zuba mata dan jin ta kama sunnan cirat kafin ya gyada mata kai

Kai ta dauke tana murmushi hadi da dan kada kafarta a ranta ta ayana' Masha ALLAH, yanzu sakon Amnah take ko wa ya zo daidai lokacin da ya dace ya zo, fita kuwa yanzu zan yake ta oga dan idan da hali yauma ka barni na je na yi Allah sanya albarka a wannan aure, domin yanzu Sir YUSUF ya yi aure mai sunna aure?'

Da wannan suka ci gaba da tattaunawa tsakaninsu na tsayar da mafita.........


___________________________________


Tunda tashin busa da hayaniya ke tunkaro dakin Mah gabanta ya ringa dokawa a gudun da ya wuce ka'ida, shi yasa ta yi tsuru ta zubawa Kofar ido har aka bude Hajia ta fara shigowa da sandarta a hankali, sai matan da aka yiwa lakabi da matan daraja wa'inda suke na darajan domin sukan halarci taron daraja ne, hannayensu dauke da akwatuna masu ษ—auke da alkyaba da tufafi da kuma takalmi da sarka na gidan sarauta

Daga bakin kofa masu busar suka tsaya, sai dai tamkar a dakin suke busawar dan ita tuni ta nemi rikicewa, bale da ta ga niyarsu bayi zasu kaita, da girman nan nata wani saka lalle ne zasu yi mata, ko sun manta shekaran jiya ta gama takabar wani mijin da ta aura ko menene?, ko kuwa tarin girmansa ake son karra jaddada mata aka yi hakan da ita?, ita dai ta san wata irin juwa da tashin tsigar jiki suka hannata gane inda za'a nufa da ita, kuma me ake nufi da ita, har aka yi mata rabi da rabin wanka domin kuwa sket dinta a jikinta da karamar riga firrr ta rike su kanta a sade, hakan ya sa matan suka kalli junna suka sakarwa junna murmushi harda Hajia wace wani irin farin ciki ya sake lulubeta ta mika hannu ta karra daukan wata takarda a gefenta ta kara a wace ke gabanta

wani irin turare mai sansanyan kanshi suka yi mata wanka da shi, sannan suka karbi bra da pant din da Mah ta miko masu suka bata, Rauda kuwa da ta karba sai da ta shige bayi ta saka dan kunyarsu ta fi komai damunta a yanzu..................





56

Bayan ta saka din ta labe a bayin har sai da aka fitar da ita tana ji tana ganni su suka shiryata sannan suka zaunar da ita a bakin gadon nan, daya daga cikinsu tana murmushi ta ce" Girma ne, daukaka ce, daraja ce daga Ubangiji kasantuwarki mata a wajen MALEEK, Allah ya karra maki lafiya da nisan kwana, ya sa muna da rabon gannin tsatson ku ke da MALEEK......."
Sai kawai ta ga iyayen matan nan sun kai zaune a wajen kawunnan su a kas

A rikice ta dago ta kalli Hajia tana kokarin tashi, sai ta ga Hajiar ta girgiza mata kai itama ta dan sasabto daga kan kujerar ta dukar da kanta a gabanta
Gaban RAUDA ya karra faduwa, da sauri ta taso ta zo gaban Hajiya ta duka kanta a kasa muryarta na rawa rawa ta ce" Hajia, dan Allah ku rufa min asiri ku dago kanki, Hajia"

Hajia ta dago tana murmushi ta kama hannunta a tausashe ta ce" baki san daraja ce Allah ya yi maki ba? a gabannan zaki ringa gannin manyan mutane na dukawa dan gaisar da ke, bale idan kin yi hali na gari, Allah ya baku zaman lafiya jikata, koma ki zauna dan daga yanzu har zuwa dare masu zuwa gaisar da ke ne zasu yi ta shigowa, dukkan wani abinda suka baki kawarki Bara'atu dake waje ita da Salima zasu amsa su adana har a zo daukan ki, a yau ba za'a yi maki kitso da kunshi ba sai kin yi sati Daya cir a gidanki, idan an kai ki zaki samu lokacin karantar rayuwar mijinki da taki kanki, ki kwontar da hankalinki, ko me kika ga ya shige maki duhu ki nemi mamanki ko ki zo wajena, Allah ya yi maki albarka AMEERAH...(SARAUNIYA)"

Kai ta sake sadawa cike da jin kunya da nauyin Hajiar da kuma matsanancin tsoro na abinda yake wakana a gabanta

mayar da ita suka yi mazaunin ta, aka kawo takardu biyar cif aka ajiye babar cikinsu ta ce" Wannan kyautar Barka da zuwa ne daga kakar MALEEK, takardun manyan filaye ne a anguwar gayu har su biyar , kowani fili ana iya yin ginnin tankamemen gida da masalaci da shagunna a jiki, Allah ya taimaki Ameerah RAUDA tabas kin fara da goshi"

Ita dai kanta a kasa har suka gama suka fice sannan ta ji Muryar su Atu sunna ihun da ya sa ta done kunnayenta ta kwonta ta rukunkume alkyabar da aka saka mata, suka ringa ja ama ta masu banza ta ki tashi, har sai da Mah ta shigo suka nutsu suka bata lafiya, Mah kuwa ta cenza shiga ta dau wanka ta sa aka kawo masu lafiyayen abinci sannan ta fice tana fadin" Ina zuwa, zamu zauna da iyayen Amnah ne dan an sanar masu yau zata tare , Please kar a yi wasa da Sallah da kuma abinci dan baki ne da Ni sosai, kuma ku kiyaye duk sakon da aka kawo kar ku hade waje daya kuma ku kula da masu baku sakon, saboda ta haka an shigi Ameerah da yawa da suka shude?"
Karshe dai a dole suka kyale RAUDA, saboda duk yadda suka so su zanta ta kiya, Atu kanta ta bata dama ta kyaleta da maganar sai sun yi fira, ta sakawa ranta zasu yi ne daga baya, abinda ya kwontar musu da hankali su Dukansu bata wani koke koke, ta sakawa ranta hakuri a yadda ta nuna masu su duka


Cikin sama da kasa da tarin hargitsi aka yi wunin nan, domin a wajen su Rauda kadai aka yi shi shiru shiru, wajen iyayen RAUDA sun nuna bacin ransu ainun na yiwa y'arsu kishiya tun bata tare ba, hakan ya sa Hajia ta nuna masu ta fi su duk wani abinda suke tunanin sunna takama da shi , karshe aka yi rabuwar ba dadi dan kuwa sun tafi ne ba tare da sun samu abinda suke so ba, dan Hajia bata yarda da maganar da ake fadi cewar mahaifin Amnah ya riga ya zama hotiho ba sai yau da ya zo da abokinsa suka yi maganar basu ji dadin yiwa Amnah kishiya ba, bayan tafiyarsu dariya Hajia ta yi ta gyada kanta ta sa aka leko mata wajen Amnah aka sanar mata Amnar na nan da kawayenta uku, hakan ya sa ta basar ta ci gaba da shagulgulanta har dare ya yi aka yi sallar isha'i aka gama

Ana gama sallar isha'i Mah ta sake dinkewa da y'arta, tamkar wace za'a kai wata kasar ko wace za'a ba wani bakon ba wanda aka sani ba haka Mah ke karra yi mata nasiha da fada mata ko meye ta gayawa Allah kuma idan ta ga ba hali ta gaya mata kawai dan ba zata yarda a cuta mata ba, ita dai kukanta take sha, tamkar wannan auren ne aurenta na farko, tarin mutanen da suka zo rakiyar ta kuwa sai da ya tsorata, Hajia ce da kanta a gaba, aka yi mata rakiya har falo baba, daga nan Hajia ta kaita da kanta har part dinta ta zaunar da ita saman kujera sannan ta karra yin abubuwan tsarin da suka amso ta sake jaddada mata rikon azkar da Adu'o'in tsari a kowani motsinta sannan ta fice tana mamakin ba Amnah ba labarinta, ta tatara jama'arta suka tafi tana dokawa YUSUF kira dan ta shaida masa ya san da ya je ya duba kowace kuma ya zama tsayaye a gidansa kar a cutarwa RAUDAH, har fadi take yi yarinya bata cewa komai sai ido kar a je a zazageta ko a taba lafiyar jikinta dan ita ba yarda zata yi ba

shi dai bai ce komai ba dan a lokacin yana cikin buga basket ball ne har a Damagaran suka yi salama ya ci gaba da bugawar, ama hankalinsa a rabe, a dole ya yi masu salama , dama basu wuce su takwas a filin ba , ya su ya su ne ba ya mu ya mu a ciki gaskiya ......ya yi tafiyarsa



A nutse Taj ke tuka shi har suka karaso kofar baya, ya sauka bayan sun yi yar gajeriyar magana ya nufi kofar ya bude da ky din wajensa ya shiga ya rufe a nutse ya kama hanyar falo baba , jikinsa sanye da wandon da ya dara gwuiwa da kyar, rigar kuwa mai yankaken hannu ce, damatsunnan hannayensa da kwaurinsa duka kaf a waje sai motsi suke yi su kadai saboda cika da koshi, gashin kansa kuwa ya fito ya yi sidik a kan nasa

A hankali ya dakata jin Muryar AMNAH da karfi tana fadin" Magana nake yi maki y'ar matsiyata, Ai shine harda fitowa daga wancen akurkin da aka baki kika zauna min a baban falon gidana? ki sani kin sanyo kanki kurkukun ukuba dan sai kin gwamace kida da karatu, sai kin nemi a amshe ki kar na kashe ki, dan walahi da hannayena za.......................kukukukukukukuku wayo ALLAH kan uba, ke Ni kika innalilahi ke!"
Magangannunta suka ringa cenza salo kamar mai aljannu, karshema sai ya ringa jin karar abu kamar duka dai kamar kuma dai wani abin daban

da sauri ya karaso yana baza idannuwansa a falon

Ido ya zarro sakamon ganninta dodar a saman ruwan cikin y'ar mutane ta hade hannayenta tana yi mata tankadeta mareta da dayan hannun mai haษ—e da naushi

ido ya sake zarrowa ya shigo da sauri ya duka ya cicibeta ya dagota da karfi ya......







Hello people, fatan kunna lafiya,shin kin karbi bonanzarki kuwa? a farashi mai sauki na saka aunty, TUNTUBENI a numbana kamar haka 93811618......ki amshi NOVELS DINA a kan 1k in sha Allah....thank you




57
Azl 58
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ•บ๐Ÿ˜ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ sai kun zo






Ido ya sake zarrowa ya shigo da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login