Showing 30001 words to 33000 words out of 188741 words

Chapter 11 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9861

shi, shi kuwa ya yi gadinsu har aka fara kiraye kirayen sallar asubahi

Farkawa YUSUF ya yi yana yin hama kadan hadi da son bude rinanun idannuwansa ya sauke dubansa cikin idannuwan mahaifiyarsa da kuma mahaifinsa dake daf da ita yana taba goshinta da wuyanta

Murmushi ta sakar masa, haka shima ya mike ya nufi bayi yana dan sake mikar da jikinsa dan jin du ya ririke

Kulawa ya yi da kansa ya dauro alwallah ya fito yana jin jikinsa du a ririke saboda rashin wanka da brush

Yana soke mayafin Nan a aljihunsa mahaifinsa ya karaso ya mika hannayensa yana cire masa sarkar nan dake wuyansa
Yana cireta ya saka a aljihunsa kasa kasa ya ce" Mu je masalaci"

Kallon fuskarsa yake yi da mamaki harda tunanin toh fa, sabon salo MEYE wannan din kuma? Ko dai shi din ma bashi da lafiyar?
Shi kuwa ya yi gaba yana boye yannayin da yaron nasa ya shiga a ransa suka ba Nurse din damar shiga ta taimakawa Mama ta yi wanka da alwallah da sallah , wace ta nuna yanzu kam zata iya jikinta ya warke ba sai an kamata ba, ama Duda haka likitar ta ki tafiya tana kula da ita har ta gama aka gama gyara dakin nata aka saka turare mai sanyin kanshi aka barta

A waje kuwa sunna gama sallar ya fito ya je wajen da Ishak ke tsaye da manyan ledoji dauke da kayan abinci da su fruits

Nuna masa ya yi ya bashi dan mahaifinsa na nan kuma baya so su dagawa mahaifiyarsa hankali a kan wannan

Jiki ba karfi Ishak ya bashi ledojin ya koma cikin motar da fatan samun lafiya wa mahaifiyar YUSUF din tare da fadin yanzu direbansa zai kawo masa motarsa da tufafinsa a ciki sannan ya tafi da ky din gidan a hannunsa

Yana juyowa ya ga Hon BELLO tsaye kofar asibitin yana kallonsa, zuwa lokacin haske ya fara yi sosai a garin

Fuska ya hade dan ya riga ya san yanzu zasu hau sama su fado, domin ya ga Ishak din da yake gudun ya gani
Yana isowa kunnayensa suka jiyo masa Muryar mahaifinsa yana fadin" Me yasa ya juya?"

Dakatawa ya yi yana kallon mahaifin nasa, ya sake kallonsa da kyau sai kuma ya dan dauke dubansa ya ce" Yana da uzuri ne"

Murmushi Hon ya yi ya mika hannayensa ya ce" Kawo na rage maka kayan"

Wannan karon kasa boyewa mamakinsa ya yi, har ya dan ja baya kadan yana kallonsa kafin ya ce" Me yake faruwa ne?"

Hon Bello ya zuba masa ido ya ce" A ina fa?"

YUSUF ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Na ga yanzu Bama gabanta , kuma ka ci gaba da wani abin daban Abu"

Murmushi ya yi yana riko ledar dake dauke da jus ya ce" Bani Ni haba ya ina so in taya ka kana wani kiyawa"

Baki ya saki yana kallonsa, sai kuma a hankali ya ce" Ina son dibarwa wannan yarinyar da ta kwana a nan"
Yana fada ne yana nuna daidai dakin da RAUDA take, daidai lokacin ne kuma Raudar ke cikin fadan a cire mata abinda yake hannunta gida zata je, Aminu sai faman kwatanta mata yake yi ama ta nuna masa ta ji sauki gida take so

Samun kansa ya yi da nufar dakin ya murda ya shiga kai tsaye yana sauke dubansa a kan Aminu dake tsaye, da Nurse din dake tsayen itama rike da dan kwanon nan nasu na likitoci, sai RAUDA dake tsaye rike da abin gado sai luuuuuu take yiwa ido saboda abin magani ama fadi take yi gida zata je a salameta

"Me yake faruwa?" Ya iya furtawa bayan ya kare mata kallo ya juya yana kallon Nurse din da Aminu

Nurse din ta ce" Sir, zuwa na yi dan na cenza mata karin ruwan nan, na tarda ita ta farka shine tace ba za'a saka mata ba gida zata je yanzu yanzu"

YUSUF ya kalleta da dan mamaki a fuskarsa ya ce" Ke da baki da lafiya zaki tafi gida?"

Idannuwanta ta dauke daga fuskarsa tana saukewa kan Aminu, a raunane ta ce" Ina son gida Aminu, ta yiwa uncle a gida ya kwana yana nemana, Ni gida zan je!"

"Ki yi hakuri y'ata a cire maki sai a kaiki gidan, zauna a cire maki" Abu ya fada a tausashe yana karewa Rauda kallo da son karantar yannayinta

Ajiyar zuciya Rauda ta ringa saukewa ta zauna saman gadon, hakan ya sa sket dinta tatarewa sosai har kamar cinyarta dake fara sol zata bayyanar da kanta, duk kuwa yadda ta yi dan ta rufe jikinta hakan ya gagara sai kanta da ta sada kasa cike da jin kunya da takaicin zaratan mazan dake dakin a irin wannan lokacin jikinta na son bayana

Har dan dukawa Nurse din ta yi wajen amsa umarnin Hon ta karasa ta cirewa Rauda sannan ta saka abin goge jinnin nan ta goge mata ta danne mata da auduga

Da kula sosai Abu ya dubi Aminu, zuwa lokacin Yusuf ya fice ya nufi dakin mahaifiyarsa , ya ce" A me kuka zo ne?"

Aminu ya ce" Sir, ai da daidaitar tawa ce aka yi accident din, tana nan police station sun ce idan an gama fitar da sakamakon wanda bashi da gaskiya nima sai sun buga min takarda na biya diyyar yawo da ita ba awo, zamu tsayar da adaidaita ne"

Hon ya dan gyada kansa ya laluba aljihunsa ya ciro abin saka kudinsa ya ciro kudi masu dan kauri ya bashi da kula ya ce" Ku shiga ku je, sannan ka sanar min gidan su yarinyar zan zo da dare dan na basu hakuri na sanar masu hatsari ne kuka yi , Ni da YUSUF in sha Allah"

Sosai Aminu yake godiya, yana so ya nuna masa ba sai sun zo ba dan kar su ga wulakanci gurin Mama, sai dai ya kasa fadin hakan, Rauda kuwa a lokacin ta shiga wanke bakinta koda da bakin ruwa ne, dan ji take du a takure, Bama kamar jikinta ji take yi kamar kazantar duniya ta tare a kanta

Yana ficewa ta fito tana tambayar Aminu wayarta da mayafinta da pos dinta
Ya bata wayar da pos din, ama bai san inda mayafin yake ba, dan haka suka fice tana jinta wani iri duda a garin yan mata na fita ba mayafi, ba wani abin bane a garin

A cikin asibiti kuwa Abu na karasawa dakin ya samu YUSUF zaune yana ciyar da mahaifiyarsa wace take zaune itama ram da ita tana masa fira yana murmushi

Yana shigowa YUSUF din ya zuba masa ido, idannuwansa cike da yannayin son yin tambaya, ama ya gaza yin, shi kuwa Hon karantarsa ya yi tsaf sannan ya nemi waje ya zauna ya bude wani abincin da kula ya yi bismillah kafin ya kai bakinsa ya ce" To wai haka ake yiwa budurwa? Sai ka tafiyarka dan tana rigimar gidansu za'a kaita? Lalabasu fa ake yi ko su dagawa mutun hankali walahi"

Dan dakatawa ya yi da son kaiwa mamansa abincin a bakinta ya dan kallo mahaifinsa, kasa kasa ya ce" Ba budurwata bace"

"To ama kama sonta ko?" Ya katse shi da son lalle sai ya ja shi surutu

Da sauri ya dube shi, sai ya samu kansa da sakin dan murmushi dan sarai ya kula wani sabon salo ke dawainiya da mahaifinsa wanda ba zai sakankance ba sam, a hankali ya ce" Allah ya raba Ni da soyaya, adaidaita fa muka hada, ana ta wani bata hakuri tana shirme ai sai a barta ta yi yadda take so!"

Ido Abu ya dan zarro, ya ce" Kai, ikon Allah, aya, Ni kuwa ta bani tausayi, kuma kamar tana tsoron kar iyayenta su ga bata dawo gida ba, sun tafi dai yanzun da dare sai mu je mu na iyayen nata hakuri mu fada masu a inda ta kwana dan ga dukkan alamu bata saba kwana a waje ba gaskiya"

Mama ce ta ce" Yarinyar da suka samu hatsari ko Aban YUSUF?"

Aban Yusuf ya amsata, ta ce" Nima fa na so gannin jikinta dan nan ya shigo da jinninta a jiki, dole ta damu iyayenka ba cen sunna cigiyarka, Ni da nice ai ba zan iya barci ba sai na ga yara mace ta dawo gefena ta kwonta, karma su daketa su ƙi yarda Ni walahi dama rakata ka yi ranka shi dade"

A hankali Yusuf ya sake debo abincin ya nufi bakin mahaifiyarsa da shi a ransa yana ayana' anya kuwa damuwarta gidan ne? Koda yake ance tana da Kani ko?, a da ba zan bi Abu gidansu ba, but zan so na ga marikiyartar nan da idona!'

Haka suka ci gaba da fira hankali kwonce har likitan Mama ya zo ya salameta suka nufi gidanta


Tafe suke cikin adaidaitar ita da Aminu , dan ba yadda bata yi da shi kan ya je zata zo ya kiya ba, domin bata so ganninsu tare ya jaza masa wata fitinar ama sai ya nuna mata ko daya zai rakata su je tare sai su fadi abinda ya sameta ko dan marikinta kar hankalinsa ya tashi

Banki suka je, ta sauka ta shiga dama idan zata fita duk wani abinta mai mahimmanci da ya shafi katin shedar yar kasa ne, katinta na banki ne takan fita da su saboda tsaro , takardun ta na makaranta kuwa dama a gidan inna suke da na haihuwa da sauransu domin akoy ranar da ta taba barin takardun ta na makaranta aka saka masu wuta akace ba'a san an bar fitila mai kananzir a wajen ba........







😍😍😍😍☹️☹️

🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*


*PAID BOOK*


_Bismillahir rahamanir-rahim._


*12*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳



Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*





Tana shiga ta je layin cirar takarda ta cira ta saka hannu a abinda take da bukata ta kai ta ajiye ta shiga layi, basu da yawa kasancewar safiya ce kuma Laraba ce ba mutane sosai , su hudu ne a layin daukan sako

A hankali layinta ya zo ta shige dan dakin ta gabatar da dukkan abinda ake so sannan ta zauna aka duba mata kudaden
A lokacin da aka sanar mata ko nawa ne a cefa sai da ta dan zarro ido dan mamakin yawansu sannan ta saka aka bata ƙadan a cikinsu , jaka dari biyar ta samu wata leda ta daure cif ta fito ta shiga adaidaitar tana tunanin lalle zata siyawa Aminu wata adaidaitar idan ta siyawa Uncle dinta abin hawan shima in har ta fada masa daga inda kudin suka fito in zai amince, domin ta san waye uncle dinta a kan lamarinta da samari, sam baya so tana amsar kudin kowa, yana yawan ce mata ne Rauda duniya ta lalace, ki daina amsar silen kowa, dan ba kowa ke kyauta dan soyaya ba a wannan zamanin na yanzu, da yawa zasu baki ne dan suma su nemi lalata ki, duk rintsi Rauda ki kama mutuncin kanki dan gobe na yi alfahari da ke kin ji?, ire irin abinda yake fada mata kennan idan yana cikin halin da ba na maye ba in ya ga kudi a wajenta, dan ya san bata siyar da komai, duk inda kudinta zai fito daga wajen samarin dake zarya a wajenta ne

Sunna shigowa aanguwarsu ta ringa jin hankalinta na neman tashi

Bata gama jin hankalinta yana neman barin jikinta ba sai da ta ga police biyu a kofar gidansu da uncle dinta, da iyayen Aminu da Mama da Farisa
Muryar mama kadai ake ji tana rizgar kuka tana fadin" Yaya a ji yaya nake rikonta? Idan ba'a godewa rikon da nake yiwa yar nan ba ai ba za'a zageni ba, Umar sharin da zaka min kennan? Dan yau kadai ka kwana ka ga bata kwana a gida ba zaka tuhumeni? Yau ta fara aka fada maka? Ai ba yau ta fara kwana a titi ba, kuma Ni nan zan shaidi kaina a kan ban san inda ta kwana ba , yaushe ma ka fara zama ba maye har da zaka dauko min police kan a duba maka y'a? Ai ga iyayen Aminu nan sun ce rabonsu da shi jiya ta yi kiransa da dare yana cin abinci ya tsallake ya tafi suma basu san inda yake ba dan sun nemi wayarsa bata shiga,, a garin Damagaran kuwa garda gardan mutane kamar su ai sun fi karfin a sace su sai dai idan abokin shashancinta ne sunna inda suke tare!"

Saukar Rauda daga cikin adaidaitar tana zubawa Uncle ido da mutanen dake kofar ya saka kowa juyowa ya zuba masu ido

Kallon da aka shiga masu ya saka Aminu salamar dan sahun da gagawa ya karaso ya mikawa uncle hannu bayan ya mikawa mahaifinsa sannan ya shiga bayanin abinda ya same su a jiya, cewar sun dauki sir YUSUF BELLO ne suka samu hatsarin da dole suka kwana asibiti, ya sanar masu daidai wajen da lokacin, hakan ya saka police din da ya yi aiki a jiya kuma su suka auna wajen ya ce" kwarai an yi haka, dan yanzu haka adaidaitar tana wajen mu an ce sir yace a barta a nan wai, "

Bayanan da Aminu ya yi bai saka Uncle daina kallon hannun Rauda ba, dan koda ta saka kudin dake jimke a hannunta a leda ana iya gane ko menene a cikin ledar, shin daga ina ya dauketa suka dauki sir din zasu je ina suka samu hatsarin?

Jaje da fatan Allah ya tsare gaba suka shiga yiwa junna bayan tafiyar yan sandan, Mama kuwa sai ya zamto magangannun da ta yi a zuciyar uncle kadai suke tsaye kikam, domin sun soke shi ainun sun kuma samu waje sun zauna daram dakam har aka watse Aminu ya masu salama kan zai je ya yi wanka ya koma police station ya ji yaya zasu kare da su kan adaidaitarsa

Jiki babu karfi Rauda ta shigo falon itama bayan uncle ya shige, Mama ta bi bayansa da yarta sai itama ta shiga tana jin dari darin yannayin baban nata dan ba zata tuna ranar da ta ga fuskarsa a haka ba

Hannu ya mika mata yana kallon ledar hannunta

Jiki ba karfi ta karaso ta miko masa ledar tana jin wani irin nauyi yana neman lulube mata jiki da zuciya

Hannunsa na rawa rawar da shaye shaye ya hadasa masa ya cira ledar ya ciro kudaden da suka saka gabansa faduwa, hakama na Mama wace ta zarro ido tana matsowa tamkar zuma da kanshi

A rikice ya saki kudin, Mama ta tare tana zarro ido ta nufi dakinta da sauri ta daga gado ta cusa ta dawo wufff tana jin uncle na fadin" zaki fada min gaskiya ko kallona zaki tsaya yi ne Rauda? Daga ina kike? Wa ya baki kudin nan? Me ya miki ya baki kudin nan? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une "
Sai kawai ya silale yana dora hannayensa saman kansa hawaye suka shiga zarya a kumatunsa yana kallonta a lokacin da kirjinta ke sama sama hawaye na wanke mata fuska ya ce" kin san cewa tun jiya har yau a tsaye nake kan kafafuna? Babu inda ban je ba har gidan su Bara'atu da gidanta, tun ina gane hanya har na rasa hanyar bi, Rauda waye ya baki kudin nan har haka? Ina kika je? Ina mayafinki? "

A irin wannan lokacin Rauda na cikin yannayi biyu ne, na tashin hankalin yannayin uncle dinta, da kuma wani iri gannin itace aka titsiye kan wa ya bata kudi , kuma daga ina take

Mama kuwa ƙarara tashin hankalin gannin yannayin uncle ya nemi damunta har ta kasa hakuri ta tare shi da fadin" to wai me kake nufi Umur? Yaya zaka wani tisata kana son sai ta fada maka inda ta samo kuɗi?, in dai zata samo din ai da kyau zata kama min wahala da ku a gidan nan tunda kai ai hoto ne , kwarar shinkafa baka kawo mana bale cefane, ga wuta ga ruwa ga haya, ga diyar yaya ta yau da gobe, kuma kudin nan sisi ba zan baka ba dan bashi nake binta, ina dalili mutun sai kace wani na Allah , ko mema ya hannaka zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login