Showing 153001 words to 156000 words out of 188741 words
(Astagfrullah), To kennan su dinma makafin ne ta yiwu fiye da sauran al'umma? kuma a furucin Hajiyar ta sake shiga a cikin tunani, da gannin tabas ta riki rubabiyar igiya, domin abin kamar na mahaukata? Shin a me ta dauki gidan sarauta ne? duk inda take tunani sun shalaketa, walahi in me take tunani sun fi ta, sai dai a daidaita zama a dubi junna dan a zauna lafiya, ama ita nan har mai nema ce?......., mutumen dake zaune a gidan sarauta kansa sai ya baka abubuwan tsari masu yawa bale SARAKAI!, kofa yake shi tsafi ai kuma gaskiyar mai shi, ama ita tana tsoron irin yadda ake nuna har yanzu Amnah ta gaza zama cikakkiyar mace mai yanci da takama da aure irin na kowa ya saka take tunanin anya ba hanyan biri ne ake yi a tsakanin junna ba? ....Uhum, ta yiwu wanda suke dako ya jima da gannin makwoncinsu, dan haka ta mike da sauri tana karfafa masu gwuiwa ta fara ficewa dan ba zata so wata fitina ta haɗa su da YUSUF ba, duk wanda ya san shi a da, zai kiyaye shi a yanzu!
Tunda ya tafi sallah RAUDA ta sake kuntata zuciyarta da tunanin eh lalle auren nan ba dai ita RAUDA ba
To mana ai kowama zai ce ba dai RAUDA ba, Yaushema ta rasa miji harda wani zai kuma amsa sunnan mijinta?
burinta ta koma makaranta ta fara sana'a mai kwarin gaske, shikenan. Sai a ce haka?, me kennan? ya sameta a bagas walahi in dai a haka ta zama matarsa to tabas ta gama zubewa har kas
Idannuwanta ta rintse tana sake daukan damarar yaki da shi, dan YUSUF ba shine mijin da take mafarki ba, ita ai Bama ta son mai mace, kuma bata son namiji mai takama!
Mikewa ta yi tana kabe jikinta kamar wace ta yi dati ta juya ta bude kofar a hankali ta fice ta nufi hanyar baya dan in dai Allah ya taimaketa a bude ta nan ne kawai zata iya guduwa ba tare da an hannata fita ba, dan ta sani in dai ta wajen babbar kofar falonsa ne babu inda zata je ba tare da izninsa ba
Da sauri ta kama kofar part din Mah ta bude ta shige har tana waiwaye ta sauke ajiyar zuciya da sauri ya nufi dakin Mah ta tura ta shige ta maida kofar ta rufe tana sake sauke ajiyar zuciya ta juyo da nufin yin salama idannuwanta suka shiga cikin na Mah , hakan ya sa ta.........
Happy juma'a yan uwa
Ta juyo da nufin yin salama idannuwanta suka shige cikin na Mah, Hakan ya sa ta ja da sauri ta tsaya tana kallon Mah din ta kasa yin salamar
Mah ta bita da kallo daga sama har kasa, yannayinta ya ganar da ita ta ji abinda ya faru, dan haka ta dauke dubanta a kanta ta idasa zama saman kujerar falon tana fadin" Inaga a fitar baby an koya mata rashin salama!"
Da sauri ta kai hannunta tana shafa fuskarta, sai kuma ta karaso tana cire takalmin kafarta ta haye saman kafet din tana dan murzar hannayenta muryarta a rarrabe ta furta" Mah, ina ina yini, ina gajiya"
Mah ta sake dagowa ta biya da kallo tun daga sama har kasa, a tausashe ta furta" Lafiya alhamdulilah, ina kika baro tufafin ki?, wannan din na waye? a ina kika saka? kuma waye ya kawo ki?"
RAUDA ta ringa raraba ido, a hankali ta ce" A gidan Atu ne da na je na cenza, kayanta ne dan zan yi girki, to kuma muna fira yace ace kin aiko wani , shine na zo ban san shine ba, sai kawai ya kawo Ni nan din"
Mah ta sake tsare fuskarta da kallo ta ce" waye yace din?"
RAUDA ta sada kanta, a hankali ta dago tana kallon Mah ta ce" shi Yayanmu"
Mah ta gyada kai, sai kuma ta yi dan murmushi ta ce" Ok, je ki yi wanka ki cire tufafin nan ki same Ni a dakina"
RAUDA ta gyada kan itama
har ta juya Mah ta ce" Baby?"
Da sauri ta juyo gabanta na dan faduwa
Mah ta ce" Me zaki ci in dafa maki?"
RAUDA ta sada kanta tana jin wani irin zabi na sake ratsa mata jikinta dangane da Mah
A raunane ta ce" Komaima zan ci Mah"
Mah ta gyada kanta ta sake mata alamun ta je
Tana tafiya Mah ta mike ta nufi bangaren Hajia
Ta sameta zaune tare da Nana da y'ar gidan Nanar sunna maganar da kana gani zaka gane ba ta dadi bace
Ba tare da ta nuna wani abin ba ta gaisar da Hajia, sannan ta juya dan komawa
Kamar daga sama ta ji Nana na gaisheta, kafin ta rufe baki y'arta ta gaisheta itama
Dakatawa ta yi ta juyo tana kallon su, kamar wace ke son gane in su din mutane ne ko ba mutane ba a zaune, sai kuma ta dan dauke dubanta ta wuce dan har ga Allah bata yarda cewa ita ake gaisarwa ba, ko kadan
A raunane Nana ta kalli Hajia ta ce" Hajia , kin gani walahi Ameerah ce bata son zumunci da Ni, Ni a yanzu bani da abin fada sai dai na ba kowa hakuri, ama dan Allah ki saka baki a cikin lamarin nan , ki duba ki ga yarinyar nan a halin da take ciki, Hajia walahi Bama barci, ance aljannu ke damunta , ance jifa ne, Hajia ga lamarin YUSUF da ta kakabawa zuciyarta, Hajia itama fa jikar ki ce, kuma tana daya daga cikin jikokin ki mafi soyuwa a zuciyar ki, ama sai ki kyaleta ta shiga wani hali a kan abin da kin sani sarai kin fi karfinsa a wajen iyayen YUSUF? shi kuwa idan mahaifiyarsa tace ya yi abu ko meye yi yake yi Hajia, ya'ya za'a yi ace an karra daura masa wani auren tana raye ba da ita ba, dan Allah Hajia ki ceci jikar ki"
Hajia ta sake duban DAYANA, wace ke zaune gaba daya kamar ba ita ba, Dayana ta bushe kau, sai bakin baki da kwala kwalan idannuwa, kana kallonta ka ga zaburariya,
Kai ta girgiza tana kallonta ta yi murmushi ta ce" kin ga, Ni ba zan yi masa wani auren hadin ba kuma, wanda na yi masa ya isa, a gabanan idan yana da damar karra wata sai dai zabinsa, idan har ya yi niyya ya daidaita kansa da ita ba zan hanna ba, in kuma ya ki , ki yi hakuri,......da ace zaki ji shawarata da na baki Nana, kin ga Dayana fa a yanzu ba wai maganar aure ne ya dace a yi mata ba, ya dace ta je ta ga likita tun daga kan na lafiyar jiki, na ƙwaƙwalwa, da na harkar shaye shayen nan, idan Allah ya sa ciwonta bai yi nisa ba sai ki ga ta zama mutun ta yiwu idan ta dawo hayacinta ki ga Bama zata so shi ba, ama a yanzu fisabililahi ko ke aka ce a ba RISLAN irin haka ai kya ce a'a bale YUSUF fa sarki ne, Allah ya sanyaya ko menene ama a ringa yi ana yin abinda hankali zai dauka, Ni nan da kike gani wai ki ce na kasa yafe maki ko me? haba yaushe zan tsaya ci gaba da rike ki a rai bayan Ni na haife ki? ai da kin jima da watsewa, a kulun idan na yi sallah sai na kama sunnayen ku gaba daya da na haifa da wa'inda na rike na rokar maku gafara da shiriya da kariya da kyakkyawan karshe da sakamakon aljanna, ba zan ware ki ba saboda butulcin ki, sai dai zan yi takatsantsan dan kuwa Nana walahi ban yarda da ke ba, ina sakawa raina kina iya cutar da Ni mahaifiyar ki, tunda kika kwashe lokaci mai tsayi kina cutar da d'an zumun ki, ku je kawai Allah ya sanyaya"
Wadinnan kalamai na Hajia sun karra rikita duniyar Nana,
takan ji a duniya ta fi kowa asara a da dan ta zamto mace wace ba zata yi mulki ba kuma ƴaƴanta ba zasu yi mulki ba, sai dai a kwanakin nan da take fuskantar tsantsan tashin hankalin duniya daga kowa ya sa ta fara manta abinda ya jaza mata bakin jinnin ta dawo ta ringa fuskantar rayuwa da abinda ake kira shiga ukun duniya da lahira, domin ko mahaifiyar da ta kawo ta duniya basu da wata hulda ta kusancin da ta wuce hangen nesa da kiyayewa gudun kar ta cutar da ita
Tana gaba, Dayana na biye da ita kamar zata fadi suka fito suka nufi bangaren su
sunna shiga Dayana murya a bude kamar yadda shaye shaye ya bude mata ita ta dubi mahaifiyarta ta ce" Mama, yanzu yaya zan yi kennan?"
Murya na rawa, tana daf da fashewa da kuka ta ce"Hakuri zaki yi, nace hakuri zaki yi kamar yadda kowa ke yi idan ya rasa wani abin, ki yi hakuri da shi, ki yi hakuri nace Dayana!"
Dayana ta sake kallonta kirjinta na dokawa ta ce" Mama, idan ban same shi ba, ina iya mutuwa"
Nana ta kafeta da ido, ido cikin ido ta ce" Sai ki maida hankali!"
Daga nan ta barta nan tsaye ta nufi dakinta ta fada saman gado ta fashe da matsanancin kukan da ta kasa hanna fitowar amon sa, kuka mai gunji da tashin hankali.....
TABAS maganar YUSUF ta tabata a lokacin da yace da ita sai ya adabeta, gashi kuwa yana adabar Tata da muguwar adabar da ko kallo bata ishe shi ba, yana kona duniyarta da shiru da kyautatawa, bai fito ya yi fito na fito da ita ko wata fitinar ba, ama a haka ita ke wahala fiye da kowa a rayuwar nan ta yanzu, ita ta san an gama gamawa da ita, ba ɗan uwanta, ba mahaifiyarta ba mutanen gida da na waje sai daidaikun dake karra tunzurata zuwa karra tsanar YUSUF din, su dinma tana iya rantsewa ingiza wawa suke yi mata
.......wannan kennan.....
Bayan fitar su Nana da kusan minti ashirin ya shigo falon Hajia
gannin bata falo ya karasa dakinta yana salama, kana ganninsa zaka gane yana dauke da magana ne wace ba zai bari ta kwana ba
Hajia dake kwonce saman gadonta ta kama ta zauna tana kallonsa ta ce" MALEEK ne ? Barka da warhaka ina fatan lafiya kake?"
Baki ya fara cunowa, kafin ya jingina da bango yana kallonta ya ce" Shikenan Ni kennan sai a ringa yi min auren dole kina kallo ba zaki hanna ba?"
Hajia ta kafe shi da ido, a hankali ta ce " Auren dole kuma?"
YUSUF ya gyada kai tana kallonta ya ce" TABAS!"
Hajia ta dauko hannunta ta dage habarta ta ce" Da RAUDA din aka yi maka auren dole MALIK?"
YUSUF ya kuma gyada mata kai ya ce" Gaskiya ya isheki hakanan, kin ga daga wannan a barni na zaba, dama shi na shigo in fada maki!"
Har ga Allah Hajia sai ta rasa amsar bashi, ya zamo ta rakashi da ido har ya bar dakin nata ya rufo mata ya tafi sannan ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai, sai kuma ta saki murmushi ta yi addu'a ta sake komawa ta kwonta dan sarai zata nuna masa auren dole, ba dai auren yace ba ko? hum!
" Baki ji ana fadin karfe duka karfe bane? yi a hankali kar ki jimu, ki kuma cinye sumul ki zo nan ki kwonta!" Mah ke fadawa RAUDA dake kokowa da allura zaune gaban plate din abinci
Dagowa ta yi ta kalli wajen da Mah ke nufin ta kwonta, saman gadonta, sai ta dan yi shiru tana tunanin rabonta da kwana saman gadon an dan jima fa, kuma ita ta so su yi magana da Mah ama gaba daya Mah ta ki bata dama, bata san dalili ba
ajiyar zuciya ta sauke ta shiga cin abincin tana tunani a cikin ranta, ita kadai sai ta jinjina kai ta kuma girgiza ta dantse lebe ta kuma dauke kanta
har ta gama ta kwashe kwanukan ta kai kicin ta darwaye ta dawo da sauri ta shige dakin Mah dan bata so su hadu da Salima a yau, bata san yaya zata iya da tambayoyin Salimar ba, bata san ko tana da amsar ba Salimar ba, dan ita dinma bata da amsar ba kanta
da dan gudu ta shige ciki ta karasa ta yi brush ta fito ta kwonta
ta jima tana juye juye kafin ta yi barci, duka Mah na zaune tana kallonta har sai da barcin ya dauketa sannan ta yi murmushi ita kuma ta mike ta haye salaya ta shiga nafila da Adu'o'in tsari wa ƴaƴanta da fatan Allah ya saka albarka a wannan hadin ya kuma kawo sauki a duk wata fitina dake tafe da hadin.......
____________________________________
Har kusan karfe goma sha daya na dare ya nufi bayan gida, wato wajen sirrin da kuma wajen da suke buyan yan jagaliyansu
Taj dake tsaye kikam ne ya yi gaggawar dukar da ƙafarsa kamar yadda ya saba sannan ya mike bayan ya bashi dama
zama yayi saman kujera yana duban Taj, hakan ya sa Taj din zaunawa yana fuskantarsa a tausashe ya ce" Dangane da ISHAK hakane, aiki aka bashi, kuma yana da vidios da yawa da hotuna da voice note wa'inda na yi mamakin dalilin da yasa bai ba mutanen da suka saka shi aikin ba har aka yi nadin sarauta, kuma duk irin yadda ka ture shi a jikinka dan ka ga iya gudun ruwansa bai falasa ba, ama Ni dai na gaza hakuri sai da na bugar da shi sosai na kwaso komai, gasunnan kai nake jira na kona su "
YUSUF ya yi murmushi yana kallon Taj ya ce" Ya cenza nufinsa a kaina ne, shi yasa ya kasa yada abubuwan da ya dauka, zan karra bashi wata jarabawar idan ya cinye zan yafe masa, dan rayuwa ba zai yiwu mutun yace shi da kowa yana rikici ba, kuma idan kace zaka kasance mai riko wata rana ko da kanka ba zaka yarda ba, Allah shi kyauta "
Taj ya amsa da amen sannan ya dora da fadin" Mutanen nan su biyu ne kawai suka fito da sir, dan daudun nan da dayar matar, mahaifiyar Madame na ciki, na kamo dan daudun har yanzu barci yake yi dan na masa allura ne,"
YUSUF ya kalle shi da dan yannayin mamaki ya ce" Are You sure tana ciki?"
Taj ya tabbatar masa hakan ya sa ya yi murmushi ya mike yana fadin" Dan firgita shi dan ina so daga an tambaye shi ya kai ku wajen bokayen matar Please"
Murmushi shima Taj ya yi yana shafa sabuwar askar da ya siyo, shi fa sai ya yi masa yanka dan ubansa dan ya gani meye damuwar da ta saka shi saka hijab?
Tunda ya shigo falon kaurin abubuwan da suka turara ke yi masa maraba, dukda an sa turaran wuta akoy kaurin abin
Dakinsa ya wuce direct ya shige bayi ya bude wata loka ya ciro hade haden wajen Bah ya haɗa ya yi wanka, ya dauro alwallah ya fito ya haye salaya
A kalla ya kai karfe biyu na dare ya sauka daga saman salayar ya nufi dakin nata hankali kwonce ya je ya kama abin budewa ya bude sannan ya kai hannunsa wajen kunna fitila ya kunna, hakan ya sa dakin ya garwaye da haske a lokacin da mahaifiyar Amnah ke kokarin sake hada wani garwashin da boka yace su yi tsakiyar dare su turara a kowani sako da lungun baban falon gidan hakan zai sa ya shaki warin koda baya so, idan har ya shaka an gama shi zai nemeta da kansa ko a gaban waye
A tsorace ta saki kaskon a lokacin da ta juyo da sauri gannin haske ya gama dakin
Shima sai ya yi alamun ya ji mamakin ganninta din nan ya dan juya yana fadin "
shima sai ya yi alamun ya yi mamakin ganninta a irin wannan lokacin, dan haka ya juya da dan saurin magana ya furta" ya Salam, i'm sorry"
Sai kuma ya fice da sauri yana rufo masu kofar
Rikicewa ta karshen tashin hankali sun shiga a wannan lokacin
daga ita har uwar sai suka manta abinda suka so yi, suka shiga kai kawo da tunanin hanyar fita dan a lokacin mahaifiyar ta nuna zata tafi , da kyar suka gane lokaci ya ja komai balakinsu da isar su basu isa su fita a wannan lokacin daga fada ba, a dole suka nemi waje suka yi tsuru tsuru kwanan zaune , dan jira suke yi kiran sallar asubahi ta samu ta fice a gidan, saima suka kasa gane abinda ya zo nema, karshe uwar ta ringa nuna ai kawai kar su daga hankalin su ta yiwu aikin boka tuni ya ci, ya kawo kansa da kansa ne, sai dai tsoro ya hanna su karasa turare turaren nasu da kuma kasa samun bacin kirki har asubahin ta yi suka ringa dako har aka fara fita Masallaci sannan ta samu ta yi wuffff ta fice a gidan
________________________________
Tunda aka yi sallar asubahi Mah ta zaunar da ita a bakin gado tana fuskantar ta ta shiga labarta mata asalin Wacece ita, wanene Bah a duniyarta a da, abinda ya faru da su, irin fitintinnun da ta ringa gani tun daga yan uwanta har zuwa dangin mijinta da wasu mutanen, har zuwa yanzu ire iren abinda ta gani na cenji wanda ya fi rikita mata lissafi, dan a yanzu ana so a cakula ta, a da tana bambance wanda ke sonta da wanda baya son ta, ama a yanzu du an hade mata tunani bata gane komai ƙarara sai dai ta bi da kallo
A hankali ta nisa tana kallon RAUDA dake share yan hawaye lokaci zuwa lokaci tana rike da hannun Mah
A tausashe Mah ta ce" kin ga a jiya, na ji tashin hankalin da ya so rikitani, da kyar na iya hawa salaya na fadawa Allah har na samu sassauci , a jiya ne Hajia ta bani umarni a matsayinta Na uwa a wajena kan a hada aurenki ke da YUSUF , ta nuna na isa da ke zan maki magana, na nuna idan kika ki fa? ta nuna na isa da ke, na fito na je part din Hajia dan na amshi wayar Salima na yi kiran ki dan a lokacin tawa a hannun Hajia sai kawai na tarda Amnah da mahaifiyarta da kawayen