Showing 171001 words to 174000 words out of 188741 words

Chapter 58 - AZAL HAUSA NOVEL

sajida   

12 Jan 2025

9850

kan farin cikinki ......sai dai baki sani ba Ameerah, baki sani ba, an yarda an aura min ke ne dan an san iyayenki, Ameerah walahil azim sarki ya aura min ke ne dan an san tsatson da kika fito, kuma sarki ya fadawa Hajia ta taka a hankali, kar ta yarda ta yi abinda zai bata hutun rayuwa tsakaninsa da ita, ya yarda Kadara ce ta fada tsakanina da ke, domin mahaifinki malamin tarbiyya ne, mahaifiyarki jinnin dan sawani ce, kuma yan anguwa sun sheda tarbiyyar ki!, saboda wannan ne kika samu rayuwar nan da kike gannin ta fi ta kowa muzanta a duniya AMEERAH, me zaki iya cewa da tsatson da AMNAH ta fito da kuma tarbiyarta?!"

ya ajiye maganar dan ya karra sanar mata a shirye yake da ya yi jayayya da ita wannan karron, duka wanda bai taba jin kansu ba zai ji sannan ya dora da fadin" Na ce, me zaki ce a kan tarbiyarta?, me zaki ce a kan mu'amalarta da talakawa?, inace nan na taya ki kashe maganar korar macen da ta yi mata salama dan tana waya a aiki a masarautar nan da ta yi, kuma a dan zaman da aka yi da Ni na abinda ya shafeta kafadata da tawa ke jere a saman kujera a lokacin da ke duwawunki ke kasa dukda kina da ciwon kafa saboda taki SARAKUWAR a saman kujerar!, kin ce an zo da dan daudu da magungunnan da d'an daudun ya kwashe wanda ke tabatar maki koda bata san waye ubanta ba ta san asiri ke tafe da mahaifin da take yiwa kallon uba a gareta hakan har yana birgeta dan kuwa gashi an kawo mata har gida ta kai katon dakinta na sunna , kuma mahaifiyarta ta kwana a nan din, Ameerah so kike yi sai an wayi gari YUSUF ya kore mu daga fada bisa umarnin matarsa zaki yanke jiki ki fadin min ko me?, ko so kike ki ce min ko a tarihi baki san cewa SARKI baya auren muguwar mata a sanin kansa, sai dai idan daga baya zata aikata masa da muguntar a cikin gidansa, rayuwa ta yau da gobe ta sa ta zama muguwar?..........., shine dan kin dauki SARKIN GARINKI abinda kike iya juyawa yadda kike so, da tunaninki zaki yi masa umarnin zama da macen da aka tabatar masa ga abokin shashancinta? kin san girman abin nan kuwa? ace namiji ya ga mutumen da matarsa ke shashanci da shi koda matar kiyayarsa ce kuma ace ya yi rayuwar aure, rayuwar da ba sirri tsakanin mata da miji ? haba Ameerah......." Bah ya karashe wannan karron muryarsa a tausashe, yana dubanta ya ce" Ina laifin ki ce a yiwa yarinyar nan sassauci, a yi lamarinta a siri sannan a dauki nauyin ta, a kilacewa a bata tarbiyya kuma a kaita dakin aure nesa da kasa a bata damar gina rayuwa in har ba hannunta a cikin dinke laya a bakin gawa? ama sai ki ce a rayu da ita a haka bayan ana magana ne ta uwar al'umma ba uwar jikokinki kadai ba, ana magana ne ta gimbiya ba wai matar YUSUF kadai ba, muna magana ne ta gidan tarbiyya ba y'ar aminin uba ba?"
Ya karashe kirjinsa na daukan zafi yana rintse idannuwansa hadi da rike hannunta da karfin da ya sa itama dantse lebenta

A kausashe ya ce" Ba zan iya ba, ba zan iya raka ki a wannan tafiyar ba, idan kuma kika ja zan ja, dan ba zai ce min komai na kai kararki a kan wannan maganar ba, AMEERAH a kan maganar nan zan ja da duk wanda yace zai ja da Ni, kuma ki yi hakuri tunda kika sanar min dole a gaggauta neman iyayen marigariyiyar nan idan sunna raye a sanar masu tashin hankalin nan, hukuma dole zata shiga sannan dole Sarkin garina zai shiga, za'a je a tono kabarin koda an dora wani a kansa, za'a ciro layar nan cikin lokacin mafi sauki, domin ba zan yarda ba dukkan wani abin da ya dace sai an yi ANDIYA sannan a yiwa Amnah adalci, laifukan da kike tunanin nan mun tuba zamu ci gaba da neman tuba a wajen wanda muka yiwa su, kuma zamu jajirce da aikata wasu aiyukan ladan ama ba dai wannan da kike so ba!"
Daga haka Bay ya saki hananyen Mah ya mike ya fice zuciyarsa na karra tukuki......, walahi ransa bai taba Ι“aci da Ameerah ba irin na yau, kuma walahi sai ya yi mata matsanancin fushin da zai bata mamaki, sannan a dole zai dau mataki a kanta koda abin nan ya taba kwakwaluwarta zai fara nema mata magani, dan kuwa irin yadda ta daukaka lamarin rayuwarsu da zafi ya wuce misali!

A lokacin da Bah ke cikin rikicin nan da Mah, YUSUF kuwa ya jima da karasawa falon gidansa baba ya ja ya tsaya ya kalli gabas, ya kalli arewa ya kalli kudu ya kalli yamma, gannin ya rasa alkiblar da ta fi masa sanyi sai kawai ya nufi dakinsa kansa na karra sarawa da matsanancin karfi ya dauro alwallah ya je saman salaya ya zauna hannunsa rike da carbi yana ja yana sauraron masalaci, domin yana ji yana ganni fita masallacin ya gagareshi saboda matsananciyar juwa da ciwon kai , gashi ko kari bai yi ba, sai abin ya yi yawa ya sa ya kasa zuwa masallacin sai a nan dakinsa ya ringa bin salolin nan har ya samu ta isha'i sannan ya lumshe idannuwansa daga kwoncen da yake yana jin wayoyinsa agaji suke nema, ama ya kasa tarda su , daga baya ma sai kukansu ya fara damunsa ya rasa yaya zai yi sai ya rintse ido kawai yana kama sunnan Allah a zuciyarsa

*RAUDA* ta jima rike da wayarta a kunnenta da kuma plate din shayinsa a gefe, tana jin Muryar Mah dake cen kasa, wace ita take cikin wani halin tsaka mai wuya na tunani ta rasa yaya zata yi da tunani kuma rashin gannin ya dawo ya shiga damunta karshe dole ta dauki waya ta neme shi da kanta, ama ba'a dagawa, hakan ya daga mata hankali, ta sani duk rintsi in dai wayarsa na hannunsa yana daga kiranta, shi yasa ta yi kiran RAUDA tace ta je ta gano mata, shine ta dauki lipton dinsa gannin yana inda ta ajiye bai dauka ba, haka abincin rana da na daren sunna yada suke sai ta nufi dakin nasa da lipton din, ama kuma ta kasa shiga dan tsoron abinda zata tarar, ta yiwu ma tare yake da Matarsa


A hankali Mah ta ce" baby, baya nan yayan baku ko?"

Da sauri ta rintse ido ta kama ta bude ta shiga, sai kuma ta shiga kallon dakunnan da tunanin to ina zata duba? duba da daki biyu ne, a hankali kuwa sai ta ce" A'a Mah ban karasa ba, na bude nan din kuma kin ga ashe dakunnan biyu ne ina ne nasan?"

Mah ta dan bude idannuwanta tana dan zarro ido ta ce" Baby dama baki san ina ne dakin mijinki ba? to ina kike ajiye masa girkin da kika ce ke dai kar a kawo maku abinci ke zaki yi?"

RAUDA ta yi tsuru ta gaza amsawa

Mah ta yi dan murmushi ta ce " ki duba wanda fitila ke kunne, idan kuwa duka a kashe ki murda kowane kawai ki shiga in sha Allah ba komai sai alkhairi a dakunnan"

RAUDA ta dubi dakunnan, sai ta ga kwarai dayan da hasken fitila ta kasa, hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya ta nufe shi ta kama ta murda hadi da yin salama ta shiga baza idannuwanta a dakin tana sake yin salama har idannuwanta suka sauka kansa yana kwonce saman salayar nan wani iri kwonci a dukunkunne kamar dan karamin yaron dake jin yinwa

A hankali ta ce" Mah, yana nan, ama anya ba barci yake yi ba kuwa?"

Mah ta dafe goshinta , tunaninta na karra Tabatuwar y'arta kam babu abinda ta sani a maza, duba haka a tausashe ta ce" Duba mana mu gani?"

RAUDA ta karasa ta ajiye lipton din dan nesa da shi kadan sannan ta zauna a hankali ta ce" Yayanmu, yayanmu, barci kake yi?"

Mah ta saki murmushi tana sauraron ta , wai wani Ζ΄aΖ΄ansu uhum

A hankali ya bude idannuwansa yana kallonta, zaman da ta yi da yannayinta ya saka shi zubawa fuskarta ido yana kallonta

"YAYANMU, ga wayar Mah ce"
Ta fada tana cire dubanta a cikin nasa gabanta na faduwa a hankali ta ajiye masa wayar daf da hannunsa sannan ta sada kanta

Sake Binta yake yi da kallo, da kyar ya budi bakinsa a hankali ya ce" Mah?"

Mah ta sauke boyayiyar ajiyar zuciya tana waskewa ta ce " Dama ban ganka bane...., am dama ban ga wulgawarka bane tun dazun"

A hankali ya ce" Eh, bani da lafiya ne"

Da sauri RAUDA ta kalle shi tana jin kamar hankalinta zai tashi, Mah dinma muryarta da yannayin tashin hankalin ta ce"









πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€ Ba eddtng faπŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€
azl63


Muryar Mah da yannayin tashin hankali ta ce" Baka da lafiya? subahanallah, YUSUF na zo ne?"

A hankali ya girgiza kai tamkar tana kallonsa ne ya ce" A'a, ciwon kai ne Mah, da sauki in sha Allah "

Mah ta rasa me zata ce, murya a raunane ta ce" Allah ya baka lafiya, Please ba baby wayar"

Kallon RAUDA ya yi, idannuwansu suka sake shiga cikin na junna, da ido ya mata alamun ta dauki wayar hakan ya sa ta saka hannunta ta dauka ta kara wayar a kunnanta a hankali ta ce" Mah"

Mah ta sauke ajiyar zuciya itama a hankalin ta ce" Baby......, yaya jikin yayanku?"

RAUDA ta sake kallonsa, a kwoncen da yake ba zata ce ga yannayin jikinsa ba, abinda ta sani shine bashi da lafiya, sai dai ba zata iya fadawa Mah haka ba, duba da ita dinma ba lafiyar ta isheta ba, duk irin tashin hankalin da take ciki ta gwamace ta hadiye a hankali ta furta" Da sauki Mah" Idannuwanta ba cika da wata irin kwallar da ta fito daga cikin kirjinta da tsananin tashin hankali ya danne

"Please, ki kula da shi....., idan kin ga bashi da lafiya sosai ki sanar min komai dare, kin ji?" Mah ta fada a hankali tana ji a ranta ko menene yana tare da wace ke iya kulawar da shi da zuciya daya

RAUDA ta gyada kanta ta yi saurin sada kan hawayenta suka zubo sharrrrrrrr har bata san Mah ta katse kiran ba

Da sauri ta mike ta ajiye wayar ta nufi waje, hakan ya sa ya rakata da kallo kafin ya samu kansa da sakin lalausan murmushin da ya fito tun daga zuciyarsa, wanda irinsa ya nema ya rasa wunin yau kaf sai kunci da radadin zuciya

Jim kadan ta dawo hannayenta dauke da kayan abinci ta karaso ta zauna daf da abin sallar

A nutse ta zuba dan madaidaici sannan ta zuba ruwa mai dumi a cikin kofi tana kallon sa a hankali ta ce" Ka tashi ci, baka ci komai ba fa yau"

Shima kallon nata yake yi, a hankali ya ce" Azumi nake yi ai"

Ta turo baki tana kallonsa ta ce" An yi isha fa, Please ka tashi"

Idannuwansa ya lumshe ya ki tashin, hakan ya sa ta rasa yaya zata yi da shi, tana so ta taimaka ta kama hannayensa ta tashe shi ama ta rasa ta ina zata fara, wani irin nauyi take ji a ranta da kunya, tana ji a jikinta ba zata iya cicibar hannayensa ba ta taΙ“a da nata hannayen kai tsaye ba, sai kunyar hakan ya sakata sada kai kawai tana jiran gannin ikon Allah

"Ama, ai ba haka Mah tace ki min ba ko?" Ya fada a hankali yana kallonta

Da sauri ta sake kallonsa, sai kuma ta sake sada dubanta a hankali ta ce" Ban san yaya zan yi maka ba"

Yana kallonta ya ce" Kamani zaki yi ki dagani sai ki bani abinda kike so in ci a bakina , haka ake yiwa marar lafiya"

RAUDA sai ta ji tamkar zata nutse a zaunen da take, ta dube shi ya fi a irga, karshe ya tafka tagumi da kyar ta ce" Ban san yaya zan yi ba, ba zan iya ba, dan Allah ka tashi"

"Bani da nauyi fa"

"Ni kunya nake ji" Ta fada cikin subucewar harshe, a dole ya sa ta ji kunya har ya fada cewar kunyar take ji, shi yasa ta rufe fuskarta da sauri bayan ta ga ya tsura mata ido yana yi mata kallon da bata so

Kansa ne ya karra daurewa, dan ya tabatar da abinda take nufi sai ya tashi ya zauna din, ya miko mata hannunsa dan ta bashi ruwan mai dumin

dauko ruwan ta yi ta miko masa, a nutse ya kama ruwan hade da hannunta ya rike

Da sauri ta kalle shi, ta ja hannunta ama ya ki saki, ta sake ja ya ko saki, nan da nan sai hankalinta ya nemi tashi, karrara tsoronta ya bayyana hadi da tashin hankalinta, har hakan ya hadasa mata da dan barin hannu kadan, wannan karron shine na biyu da hannunta ya hade da na wani hadewa ta kirki din nan ba ta a yi fada ba, hakan ya sa tsoronta kasa buya har sai da ya dubeta da mamaki ya ce" Bari mana, me yasa kike haka sai kace ba ke kila haifi Abdul ba!"

Da wani mamakin da kuma sauri ta dube shi, kai, Abdul kuma? ita RAUDA ce ta haifi Abdul?, sai dai ta kasa magana saboda kin sakin hannunta da ya yi, shi da yace ba zai iya tashi ba harda janyota daga zaunen da take ya shiga shan ruwan zafin dake hannunsu a hankali yana sake yi mata kallon nan da bata so

Ajiyar zuciya kawai ta saki ya sada kanta tana kallon abincin har ya ga dama dan kansa ya saki hannun nata ya ajiye kofin ya lumshe idannuwansa gumi na tsatsafo masa kadan

Shayin ya fara sha, shima sai da ya jima a cikinsa sannan ya dan taba salak kadan ya mike a hankali ya nufi hanyar kofar

yana zuwa ya datse kofar ya juyo a nutse ya karasa wajen sif dinsa ya dora ky din cen sama sannan ya juyo yana cire jalabiyarsa

RAUDA dake tsaye rike da kayan abincin ta yi gaggawar juyawa muryarta na dan rawa ta ce" Am, ban fita ba fa, ka rufe kofar da Ni fa"

Dama ita yake kallo , wato diyar Mah ta gama raina masa hankali, ko kicin zata shiga fa ba hijab take shiga, ama zuwa wajensa ta dankara hijab, shin ko ba'a bata sadakinta a hannun dake iya tabatar mata shin waye a wajenta bane?

Bai amsata ba ya dauki tawul dinsa ya wuce bayi , dan wankan nan da ya saba idan har bai yi shi ba ba zai iya jin dadin jikinsa ba, duda irin yadda yake jin jikinsa da abin zazabi sai ya yi

Yana shiga ta ajiye kayan da gudu ta zo ta shiga dagen dauko ky din, ama cikin ikon Allah ta gaza kaiwa wajen da yake

da sauri ta sauka tana dube duben abin hawa, dan hankalinta ya kasa daukan tana ji tana gani ya shiga bayi daga shi sai zani ya fito ya sameta a dakin nan, to ta kalle shi ta yaya? kai mutumen nan walahi bata san me yasa baya jin nauyin mutane ba sam

kujerar dake ajiye wajen gadon ta dauko da kyar dan nauyi ne da ita ta kawo ta ajiye sannan ta cire hijabinta gudun kar ya kayar da ita ko kar taje ta fado ya shaketa

Hayewa ta kuma yi ta ringa dage ko zata cafki ky din, a haka ya fito daga bayin ya yi turus yana kallon ikon Allah

da sauri ta diro daga saman kujerar ta yi tsuru tsuru tana kallonsa hadi da dan nuna wajen tana sosa goshinta ta ce" Dama, ky din ne zan dauka wai kar na baka aiki na bude kofar na........."
Da wani saurin tana katse maganarta ta matsa sosai dan gannin kamar wajenta ya nufo ai

Bata idasa tunanin nan ba ya janye tawul din dake jikinsa

A haukace ta juya kirjinta na wani irin dokawa tamkar zai fito ta bakinta ya fadi, gaba daya jikinta ya dauki rawa ta rintse idannuwanta, ba wai haka yake karbar ungozoma ba fa, ama kuma kasantuwarsa da gajeran wandon a matsayinsa na katon mutun din da ta hadu da shi rana tsaka dole ya gigita tunaninta

Rigar barcinsa ya dauko da dogon wando a nutse ya saka a jikinsa sannan ya bude wajen turarukansa ya dauki mai sanyin kanshi ya shiga fesawa jikinsa a nutse har ya gama sannan ya ajiye ya juyo ya harde hannayensa yana kallonta a hankali ya ce" kika ce me?"

Da sauri RAUDA ta juyo tana kallon kasa kasa wajen kaffafuwansa, gannin abin tufafi a jikinsa ya saka ta dago tana kallonsa a raunane ta ce" Cewa na yi ka bude min in tafi in kai kwanukan kicin in wanke su in share kicin din kuma in yi aiki mai yawa a cen din"

Baki ya tabe ya bi abincin da kallo a rufe ruf, sannan ya dawo da dubansa, harda hade hannaye ta yi kamar wace ke tsoron wani abin

A nutse ya shiga takawa inda take tsaye, ita kuwa da yannayin tsorata da shi take yin baya baya har suka dangane da jikin abin gadonsa

Rigar dake jikinta ya bi da kallo, mai siririn hannu ya kai idannuwansa har wajen wuyanta sannan ya sauke a fuskarta yana kallonta a hankali ya ce" Me kike tunani wai?"

RAUDA ta yi tsuru tsuru , sai ta bude baki sai ta rufe ta fitar da wani dan sauti sauti a cen cikin makogwaronta wani "UM" ido kuwa sai mucik mucik take masu tana gannin gaba daya ya kare bata gaba

"Tell me, kina tunanin zan yi hvng sx da ke ne yanzu?" ya fada a nutse yana kallonta

a rikice ta furta " Astagfrullah, astagfrullah kai, innalilahi wayo Ni walahi ko a kwakwaluwar Makiyina ban kawo tunanin nan a raina ba, haba dai yayanmu ne kai fa, me hadina da wannan abinma ni? kawai dai tafiya nake son yi daga nan din gaba daya Ni "

Sosai yar kwalar da take sharewa na ta shiga ukun nan ta sake saka shi zuba mata ido, kafin ya sauke wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login