Showing 27001 words to 30000 words out of 188741 words
da wulakantarwa da nuna tamkar laifinsa ya fi na y'arta da d'anta ne, nan fa suka zo suka raba rikicin auren y'arta, an yiwa yarinyar aure da yan watanni da wani kamilin dattijo ya kawo karar cewa yarinyar na hali na bin maza a cikin gidansa har a saman gadonsa, da aka titsiyeta ta nuna eh hakane kiri kiri dole aka raba auren take zaune daram cikin mutane, dayan kuwa kannin RISLAN ba'a cewa komai, lamarinsa sai addu'a kawai, katon barawo ne mai sata a kasa da kasa, sha ba'a magana, maganar bin mata kuwa a cikin masaraitarma sau nawa yana kawo MACEN da ba ta aurensa ba? Yanzu haka da jikarta daya tasa, ama sai ta ringa irin abubuwan nan haka , bai san me yasa take yin haka ba, a ƴaƴanta ita din da kanta RISLAN ne kawai mai sauki, shine mai dama dama mai kamanta rayuwa da jin tsoron Allah
"Da sauki jikinta, ama tana son ganninka, tana daki na biyu ka je YUSUF" Mahaifinsa ya fada a hankali, da murya a rarrabe yana dubansa tamkar ba shi ba
Yusuffff ya zuba masa ido na yan dakiku da karantar sabon salo, hakama yan uwansa baki daya sai suka zuba masa idon sunna mamakinsa
Murmushi sarki ya yi a hankali ya dan dafa kafadarsa, ba dan komai ba sai dan dama shi yana fada masa ya fa kiyayi bakinsa a kan yaronsa ya ja abinsa a jiki shiriya ta Allah ce, shi dai baya ra'ayin mahaifiyarsa gaskiya, ta yiwu hakan ya samu nasaba da irin yadda mahaifiyarsu ta tsani mahaifiyar YUSUF din
Ajiyar zuciya YUSUF ya sauke ya nufi cikin Asibitin, yana so ya ga yarinyar nan yaya nata jikin, ama ya fi jin sai ya ga mahaifiyarsa koda zai iya tunanin wani abin a irin wannan lokacin
A sanyaye ya karasa gaban gadon Mama a lokacin da ya bude dakin ya zuba mata ido yana kallonta
Murmushi ta sakar masa a hankali ta mika hannu tana masa alamun ya zo, lokaci daya kuma tana bin mayafin dake nade a hannunsa da kuma abin jinnin dake gefen rigarsa wajen damtsensa
A hankali ta riko jinnin fuskarta na nuna alamun damuwa tana riko shi tana so sai ya hayo gadon nata tamkar wani yaro tana tataba jikinsa da hannayensa ta ce" Sajan, jinni ne a jikinka? Me ya same ka?"
Sai yanzun ya ga ashe jinnin da dan yawa, sai ya ji dama ya wanke kafin ya shigo, dan a duniya idan kana so ka ga rikicewar mamansa ya yi koda atishawa ce, yanzu zata nemi fita hayacinta
Da kyau ya zauna yana taba fuskarta dake danshin raba yana duba nata hannun mai dauke da abin karin ruwa ya ce" Rohi ba fa wani abu ya sameni na, hatsari ne muka yi a adaidaita, yarinyar dake cikin adaidaitar ce ta bugu, ama ba sosai bane ba fa"
"Yarinya?, ya Salam, budurwarka ce? Ya Allah, ina take ne? Sajan tana ina ne?, ya Allah ga jinni a jikinka ance yar buguwa, Allah ya sa ba wani abu ya samu y'ar mutane ba, tana ina ne? Kaini in ganta" mamansa ke fada tana alamun son sauka daga gadon ita da karrin ruwa ke jikinta hankalinta tashe
Zuba mata ido ya yi yana jin nutsuwa da tarin kauna marar misaltawa a zuciyarsa, a hankali ya rikota da hannayensa yana son sai ta nutsu ya ce" Mahmah, ba fa abinda ya sameta, buguwa ce a hannu tana wajen likitocin, ba budurwata bace, adaidaita ne kawai muka hada da ita ina gagawar zuwa na Ganki, Please kar ki cire karin ruwan ke da ba ce lafiya gareki ba?"
Sai a lokacin ta kalli karrin ruwan, kai ita fa tunda ya shigo ta ji ta warke daga dukkan wani abu da ya tsaye mata a kirjinta , ko yanzu zuwan su sarki da A'isha Sarkin kawai ta iya amsawa gaisuwar da ya mata, yau shine harda tambayarta jiki? Kwarai ta yi mamaki , A'isha kuwa ta zo din ama bata jin lokacin da ta tambayeta jikinta ba, itama bata bukata, dan ta riga kuma ta rantsewa kanta ba zata kuma daukan wannan wulakancin na A'isha ba!
Sai da ya tabbatar da jikinta da sauki sannan ya barta bayan ya sheda mata lekawa zai yi ya ga jikin yarinyar, ita dinma ji ta yi dama zai yarda ta cire karin ruwan su tafi, sai dai ta san yanzu kuma ya zo ba zai yarda da komai ba , sai ta bi tsarin likitoci koda bata so dan ya zauna ya nemi tayar mata da hankali ba komai bane a wajensa a kan lafiyarta
Aminu ya samu tsaye a kofar catégorie din da aka saka RAUDA
Da sauri ya dan duka yana ba YUSUF din hannu dan a dazu bai san waye ya dauko ba sai yanzu da aka gama komai na lafiyar Rauda aka sheda masa wanda ya dauko din, hakan ya bashi mamaki ainun
Da kula sosai YUSUF ya ce" Tashi mana, yaya jikin ta? Ka santa ne?"
Aminu ya dan dago din ama ya kasa mike kafadarsa da ta Yusuf din dan girmamawa ya ce" Alhamdulilah da sauki sun sakata barci dai, na santa biya muradi yar anguwarmu ce, Ni kuwa Ni ke mata dan sahu kulun"
Yusuf ya bude dakin ya shiga yana sauke idannuwansa a saman kanta, tana kwonce lambak tana barcin da karin ruwan ke sakata, an daure wajen da ta ji raunin an dan sasabto mata rigarta sosai
Dauke dubansa ya yi ya kalli Aminu ya ce" Ka je ka sanar a gidansu, tunda da wahala su barta ta koma gida yau"
Aminu ya yi tsai ya rasa abinda zai fada, a zuciyarsa kuwa tunani yake yi waye zai fadawa? Babu wanda bai san Rauda da rayuwar da take yi a gidansu ba, ba zai so Maman Rauda din ta zo nan ta wulakanta ba a cikin mutane, dan haka ya ce" Gidan nasu ne ba kowa ai Sir"
Ido ya sake zuba masa yana son gane yarensa, wani irin gidansu ba mutane?
Kasa hakura ya yi ya ce" Ban gane gidansu ba mutane ba, ina mahaifiyarta ne? In ba mahaifiyarta ai Akoy mahaifinta......ko yan uwanta????!"
Fuskar Aminu nan take ta nuna alamu na raunin maganar dake bakinsa, a rayuwa yana tausayawa Rauda kuma yana yi mata fatan alkhairi, shi da ace yana da dama walahi da ya raba Rauda da rayuwar gidansu, Rauda kusan kowa a Anguwar nan na tausaya mata dan yarinya ce mai mutunta kowa, idan zata wuce sai ta gaishe da kai ko me kake yi, fuskarta da sakewa , du irin ukubar da take gani tana matukar jurewa bata bari tana yawan nunawa kowa ba, in dai ka santa ka san me take gani a gidansu ita da kanninta, Rauda tana gannin jarabawar rayuwa kala kala , a da laifinta ake gani saboda mama ta bi kowa ta fada masa bata ji sai yawo sai menene, sai dai yau da gobe ta wuce wasa kowa sai da ya ga asalin wacece Mama aka dawo daga rakiyarta ake kallonta da halinta
A raunane sosai Aminu ya ce" *bata da iyaye biya muradi, sun rasu a hanyarsu ta dawowa daga kauye da yan uwanta*"
Dukansa ne maganar ta yi? Ko menene ? Bai san lokacin da ya kurawa Aminu ido na yana kallonsa da bugawar da zuciyarsa ta yi
"A yanzu haka tana rayuwa gidan kannin mahaifinta ne, shi kuwa ba mazauni bane, matarsa din kuwa idan har ta zo nan zata daga hankalin marainiyar Allah ne, idan har ba damuwa Ni sai in kwana a waje da safe zan rakata in fada, Duda ba lallai ta yarda ba ita maman nata" Aminu ya idasa fada yana sada dubansa daga na cikin idannuwan Yusuf
A hankali Yusuf ya juyo da dubansa kanta ya zuba mata ido....
Gashin kanta a barbaje yake saman matashin kan da aka dora kanta,
Fuskarta a sake take sosai , lipstick dinta har yanzu yana nan saman jan bakin da ta dan shafa
Idannuwansa ya janye da nufin juyawa suka sauka a kan kaffafuwanta dake bude, farare tas tas da su har faratunnanta tas tas da su , harta tafin kaffafuwanta a idannuwa kawai idan ka kalla zaka ga mai tsafta ce ita din ko halitarta ce haka, dan luwai luwai suke abin shiga ido
Dauke dubansa ya yi ya sake duban Aminu da furucin dake saman lebensa ya ji kamar maganar na neman yi masa nauyi
Tambaya ce a bakinsa
Tambaya ce a harshensa
So yake yi ya yi tambayar
So yake yi ya karra jin bayanin abinda bai shafe shi ba
So yake yi ya ji me Kennan? Yannayinta na iya tashi tsaye ajiye shi a wata matsaya guda , itace irin ya'yan nan ne sangartatu da iyaye suka lalata take gannin daidai take da uban kowa
A dazu furucinta a kan iyayenta ya saka shi tunanin eh lalle iyayenta bata haɗa su da kowa sunna gida ba zata yarda dan ta fito yawace yawacenta a zage su ba!
A yanzu kuma sai, sai, sai yake jin kamar numfashinsa zai tsaya a kan son Sannin *WACECE ITA, ME YASA TAKE IRIN RAYUWAR NAN?* , sai dai ya gaza tambayar Aminu, kwata kwata bin digigin nan ba halinsa bane, abin nan bai shafe shi ba
A tausashe bayan ya lumshe idannuwansa ya bude a kan Aminu ya ce"
Happy juma'at mAh people
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*SAJIDA NIJAR*
*PAID BOOK*
_Bismillahir rahamanir-rahim._
*11*
*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*
*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
A tausashe , bayan ya lumshe idannuwansa ya bude a kan Aminu ya ce" Ka je wajen ka kwana, ina fata kai baka ji rauni ba?"
Aminu ya amsa masa cewar shi bai ji ciwo ba sannan ya fita ya samu wasu maza dake jinyar babansu ya zauna wajensu yana ji a ransa ba zai iya tafiya ya barta ita kadai a asibitin ba, ko mahaifiyarsa ya fadawa ga inda ya kwana ya tabbata zata tausaya mata, kowama yana son taimaka mata, marikiyarta ce tamkar kwalba wajen Shari, tana iya hada maka wani balakin dan kawai ka taimaki Rauda din
YUSUF kuwa bai bar dakin ba sai da ya daidaita abin kusan gadon dake iya shaidawar tashinta, haka kawai ya dan sake zuba mata ido kafin ya fice ya je wajen doctern da ta dubata suka dan tattauna ta sake tabbatar masa a asibitin ana kwana ana leka mararsa lafiya ne, idan ta motsa lalle za'a san motsinta koda abin karaurawar bai yi kuka ba
Daga nan ya koma wajen mahaifiyarsa ya zauna saman kujera sunna taba fira har mahaifinsa ya shigo shima ya zauna saman wata kujerar , nan YUSUF ya mike da nufin tafiya sai mahaifin nasa ya umarce shi kan ya zauna , bayan ya zauna din ya zamto mahaifin nasa na dan hiratarsa, hakan ya sa mahaifiyarsa sakewa sosai tana ta yiwa mijin nata fira, dama ance mai d'a wawa , mahaifin YUSUF sai a lokacin ya samu salama da kwonciyar hankali a zuciyarsa yana tuna yadda suka rabu da A'isha, domin a wajen so ta yi ta ci gaba da zazagin Yusuf gaba daya sai ya ki saka baki, karshema sai ya ce ai sai hakuri da addu'a Allah ya shirya mana shi ya fi ALKHAIRI da la'antar, tunda ya fadi hakan sai ta ringa binsa da wani irin kallo , ko na menene? Allah masani, wani lokacin yakan so yarda da wata magana da abokinsa ya taba fada masa, Akoy wani lokaci da suke jaje irin na familly da rashin jin ya'ya dai da sauransu da abokinsa kuma uban gidansa Mai Damagaran, a ranar ne ya ce da shi" HONORABLE, a cikin yayanka ka kiyayi gagawar furtawa YUSUF wasu kalaman, ka kuma yi kokari ka ringa taro rashin jinsa, domin ku so ko ku ki YUSUF sai ya gaje ku!"
A lokacin ne yace da shi" Mai martaba YUSUF dai nawa? Ai Yusuf ba zai taba duban sarauta ba, ka ganshi a nan ya fada ya kuma fada cewar mu rike kayarmu, ta yaya muke tunanin shi zai zo ya ringa zama gwamnati na masa albashi? , yace idan bamu sani ba mu sani shi ya wuce jiran dauka da umarni daga gwamnati, cewa fa ya yi tunda ya zama karamin kwari gwamna na iya yin yadda ya so da sarki ya rainawa sarauta wayo, ka san shi matsalarsa duk abinda zai ja masa wani raini ko halin karanta baya ciki, gashi Allah ya taukaka shi a cikin kankanin lokaci, a yanzu idan ka ji wanene YUSUF sai ka yi mamaki, ko mu mun san Allah ya dasa shi, sarauta kam idan da rabon Yayanmu sa hau da wuri ta yiwu sai dai RISLAN"
Shine mai martabar ya yi murmushi yace da shi" ba'a cenzawa tuwo sunna komai gyaran da zai sha, gaskiya kuma zanen dutse ce, kai ka san jinnin da ya isa ya hau , tunda kuka yarda muka san da lauje cikin nadi a je a dawo koda kasa ta bini idonmu Akoy kundin labari, arzikinsa kuwa dama haka ake so sai ya ciyar da talakawa da shi, ama fa ya dace kanwarka ta farka daga barci domin *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA* ko ana ruwan muzuru sai ya yi"
A hankali Hon BELLO ya dan juyo ya zubawa YUSUF ido
A zaunen da yake mayafin Rauda ne a hannunsa yana dan gogawa a wajen hancinsa wanda shi da kansa bai san asalin turaren dake jiki yake shaka ba, shi dai ya rike yama manta na MEYE abin dai a hannunsa kamar nasa haka ya masa rikon gaske
Suturar dake jikinsa yake kallo har zuwa sarkar dake wuyansa yar siririya mai ruwan ash, ko karfe ce ko azurfa ce? Wa ya sani
Damatsunansa da suka shake a cikin rigar nan ya zubawa ido har zuwa ƙafarsa dake cikin takalmi kafa ciki ama ba mai nauyi ba
Agogon hannunsa ya zubawa ido da dayan hannunsa dake cikin na mahaifiyarsa a hankali yana kallonta tana ta labari yana murmushi
Murmushin ya samu kansa da saki yana dauke dubansa daga kansa
Abu daya ya sani shine da wahala YUSUF ya wulakanta a duniya, da wahala ya wulakanta saboda baya haɗa su da kowa, bai taba yarda ya haɗa soyayarsu da ta kowa, rabonsa da siyan shinkafar gidansa har ya manta, idan ya bada kudin cefane niya ya yi dan badangarci, ya jima da dauke masa hidimar kannensa, ya jima da fito da mahaifinsa cikin manyan kwarin kasa, domin a kasar Nijar baki daya a yanzu mutanen dake mu'amala da shi, shi da kansa ya san dan tsaya masan da yaronsa ya yi ne ba dan shi karfinsa ya kai cen ba, domin a yadda duniya ta zama idan kai ba kowa bane baka da fada a ji a gaban kowa hakan ne, shi BELLO yana da damar shiga inda ya ga dama a lokacin da ya ga dama idanma bashi da sanaya da mutumen da zarar ya fadawa YUSUF za'a neme shi ne yana zaune a saman gadonsa, lokuta da yawa shine ke yiwa sarki hanyar halartar wani taron , a yanzu dai a Nijar duk wani baba yana daukan mota ne a park din YUSUF, hakama a wasu kasashen makota, YUSUF ya mallaki park park da dama a garuruwa, kuma duk wata babbar mota yana yi mata nata daban ne, ya jima da shiga cikin duniyar bada kwongila a tsarin gwamnati, mutun ne mai nema ido rufe kuma a kulun habaka kasuwancinsa yake yi , ya ki ya matsa daga Damagaran da garin mahaifinsa ne saboda iyayensa,
A hankali mahaifinsa ya ringa jin wani abu mai kama da kunya da jin nauyi
Shin dan sun haife shi ne suke wulakanta shi haka?
Kwarai matarsa tana da gaskiya ya dace ya fara yiwa kansa wa'azi ya duba abinda yake ciki da yaronsa
Daren dai, shi bai samu rintsawa ba, domin YUSUF mahaifiyarsa na yin barci ya KWONTAR da kansa a saman gadon hannunsa cikin nata, dayan kuwa rike da mayafin Nan barci ya dauke