Showing 162001 words to 165000 words out of 188741 words
dan Allah a yi hakuri a yafewa yarinta, kin san ita Amnah bata iya fada ba , sam bata san rikici ba, kunu huce in shaka sunnan Amnah fa, tsorota ta yi da y'ar uwar Tata shi yasa ta rikice, ama gabanan ai ko wani abin ne ga mijinsu sai ya yi masu shara'a ya sasanta su, in ba iya shege ba RAUDA kanwarta ce ai ba wani maganar kishi, Elhaji mu je haba ka huta bawan Allah gajiya ta ishe shi ita ta zo tana wani damun mutane, ku mu je" Ta mike tana mintsinin cinyar Amnah, wace ta dago tana kallonta da mamaki a bude fuskarta da kyau dan ta ga irin yadda jinni ya kwonta, har bata ga shigowar RAUDA da salamarta ba dan tsananin mamaki tana gannin yadda mahaifiyarta ke mata alamun su yi waya da irin yadda ta kada mahaifinta suka tafi komai ba'a yi ba, komai ba'a yiwa wancen mahaukaciyar sauvage din ba, duk irin abinda ta yi mata?
a rikice ta juyo bayan sun wuce , hakan ya sa dan kwalin abayarta faduwa daga kanta ya sauke daga rufewar da ta yiwa fuskarta
Ido Hajia ta zarro tana kallon fuskarta ta ce" Subahannalahi ke, meye wannan a fuskar ki kamar wace mota ta bi ta kai? kaikaikai rufe rufe wannan tsaba tsaba wajen kuncinki hala wani tautau ya zuba maki ruwansa a kanki? subahanallah...."
Mah ma dake murmushin inda RAUDA ta je ya zauna kanta a kasa tunda ta shigo da wani zumbulelen hijab tamkar zai makata a kas dan ya yi mata yawa sosai kuma kan nan a kasa ta ki dagowa ta kalli kowa ta dubi Amnah itama tana fadin" Subahanallah me ya samu fuskarki haka? ko wani abu kika shafa ya kumbura maki fuska?"
Amnah ta girgiza kai tana matse kwallah ta dubi RAUDA tana jin da ace za'a bata bindiga walahi tana iya harbe RAUDA har lahira, sai dai ba laifi wasan yanzu aka fara shi dan walahi sai ta rama, ta fashe da kuka tana fadin" Walahi babu abinda na shafa, jiya ne kawai na fito baban falo dan na yiwa honey sannu da zuwa wannan ta sandeni ta duka min karfe a wuyana ta shiga dukana da abubuwa, ba iya fuskata ba harda jikina du birdi ne, birdi ne wannan din ai na abin duka"
Ido suka karra zarrowa, kamar an juyar da dubansu suka kalli RAUDA wace itama ta zarro nata idannuwan jin wata rantsatsiyar karya tana kallon Amnah da yannayin mamakin nan a ranta ta ayana' ok, na zata ai gaskiya za'a fada har na tsorata, tunda karya kika zaba fine'
A fili ta ce" Ni wai kike nufi aunty Amnah? innalilahi wannan jikin naki duka to da me? ina Ni ina ke aunty Amnah da zan iya ko dukan ki ko me? innalilahi wannan me ya same ki haka?"
Ido ya zarro lokaci daya ya kai hannunsa wajen bakinsa a hankali ya furta " Lah "
Ita kuwa Amnah sai ta ji kamar zata summa Ιan tashin hankali, mikewa ta yi da sauri ta shiga dage abayarta har wajen cinyarta da duwawunta hankali kwonce ba tare da ta yi tunanin hakan wai wani abin a ji kunya bane a gaban iyayenkama bale sirikai, ita dai burinta su yarda da abinda ta fada tana duban RAUDA ta ce" Kar ki raina min wayo kin ji, kin yi kadan na maki karya kin ji? kina nufin du abin nan da kika min baki san kin yi ba? to ko aljannu gare ki baki sani ba? wannan ai karyar banza zaki yi munafuka kwarariyar yar iska.........'"
"kin ga, Amnah ke, zo nan zauna, kuma ki kiyaye wasu furucin a nan dan ba zan dauka ba!" Hajia ta fada da karfi, hakan ya sa Amnah zuwa ta zauna din sai kumbura take tana kallon RAUDA tana harare harare
Hajia ta dubi RAUDA ta ce" RAUDA kin san wani abu a kan abinda take nufi? kin doka mata karfe sannan kika shamaceta?"
RAUDA ta girgiza kai tana kallon Hajia sannan ta mayar da kai ta soke, a ranta tana ayana' A'a kam , ban rotsa mata komai a kai ba, kuma ba fadan shanmata bane tana kallona ina kallonta kuma belt din wandon jikinta ne ai na tatafka mata sai dan marinta da ba yi!'
Hannu ya sa yana shafa gemunsa yana kallon makaryata biyu a gabansa, kuma matansa abinsa
baki ya dan cije yana kallon RAUDA da ta soke kai, ko shi da ace ba shine ba idan ya kalli wannan innocent face din ba zai taba cewa zata aikata ba, sai dai ga shima shedar ta aikata din a jikinsa fa, kuma jira yake alkaliyar ta nemi Shedu zai gabatar da sheda tabas!
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana dubansu a tausashe ta ce" Yaushema daren ya yi bale har a kai loma a hanci?, Ni baban abinda yake bani tsoro gani nake yi kamar ja gaban da ya dace ace ya ja gaba a lamarin gidansa bai damu da gidan ba"
Ta karasa fada a tausashe tana sauke dubanta a kan MALEEK
A hankali ta ce" Ka yi hakuri Allah ya ja da tsayin rai, komai daga farko ake farowa, kuma komai girman mutun da darajarsa in dai magabantasa na raye dole za'a ringa shiga huruminsa koda baya so,"
Ta sake ajiyewa tana kallon sa, a tausashe ta ce" Koda da zabin da kake hange a duniyar ka a nan gaba, dole ka kiyaye yanzu saboda gobenka, MALEEK ya zama wajibi ka dubi gidanka komai girman abinda ke kanka ka basu lokacinka ka daidaita fitintinnun dake tashi mararsa ma'ana ka sauke dukan hankin dake kanka nasu sannan ka zame masu kariya na zama a rayuwar duniya!"
Ta karashe tana kallon Mah, wace ita dinma shi take kallo, kuma sun ga ya sada dubansa alamun dauka yake yi maganar da ake yi masa
Hajia ta dawo da dubanta wajen AMNAH, a tausashe ta ce" Haba Amnah, ko me yake faruwa a tunanina mu zaki fara gani idan kin ga ba'a yi maki adalci bane zaki nemi iyayenki, ....domin a sanina idan iyayen mace suka shiga lamari ya bace ne, ko ba haka ba?"
Amnah ta kalli Hajia, ita idan ta kalli Hajia tsoronta take ji a ranta, bata tunanin zata iya wata fira da tsohuwar nan dan tsoro take bata
Hajia ta ci gaba da fadin" Zaman kishi muka yi da mata kala daban daban a rayuwa, ba wayonmu ko dabarar mu suka kwace mu ba, domin an yi zamanin da mu da miji sai ido, muna ji muna gani miji ya fi karfinmu dan a lokacin ya auro mana shu'umar da ta sa ya dawo gannin munin mu, to idan zama ya yi zama dama an yi haife haife da sauransu kai da miji ai sai kyautatawar yau da gobe, shi kuwa yayi nasa rawar gannin ta hanyar nuna diyauci da darajar da iyali, ama ba wai ci gaba zai yi da gannin mahaukacin kyan nan naki da kike takama da shi ba , komai kyan naki, ki dauki misali a kankin kanki, zaki ga kina son wani abu ki siya, kafin ki siya irin zumudin da kike yi da tunanin idan kika samu ai shikenan kin gama siyan wani abin kuma Ιan wannan din karshe kennan aka baki, sai ki samu ki siya, a hannunki fa abin yake zaki ga wani lokacin ko sati bai cika ba kin rage zumudinsa, wani Sa'in kuwa kikan dauki watanni kamar biyar kina daukinsa, daga baya zai zamo abu da yake da daraja sosai a wajenki kike rike da shi kam da kam, ama ba wai wanda ya fi kyau ko ya fi birgeki ba, idan da zaki samu wani siya zaki yi ki karra ba tare da kin bada naki ba, Amnah haka rayuwa take tsakaninmu da maza, ke matar farko idan har baki iya takunki ba sai kin rasa wannan babar darajar da muke da ita kina ji kina gani, da wannan nake baki shawarar ki yi hakuri, ki iya kawar da kai, ki koyi halaya na manya, ki kasance mai dauke da darajar da mijinki zai rike ki taf, da kishin ba wani ke wato rabuwa da ke, koda ya ga wace ta fi ki a idannuwansa, ta haka zaki fi jin dadin gwagwarmayar rayuwa da rigingimun yau da gobe lami lafiya kin fahimta? ki yi hakuri ku zauna lafiya ke da mijinku da abokiyar zaman ku"
Ta karashe tana kallon RAUDA, wace har yanzu kanta ke kasa,
ita fa har yanzu gani take yi ko tsokanarta MALEEK ke yi dan Allah? wannan abar tausayin me ta sani baiwar Allah harda za'a ce ta daki wannan da idannuwanta ke kiririta?
Sai ta samu kanta da fadin" Zo nan , taho nan in ji"
RAUDA ta dago a hankali daga jikin Mah dan tun dazu Mah ta sa ta dawo daf da ita, ta kalli Hajia ta ga eh da ita din take, dan haka ta mike a hankali ta karasa ta zauna daf da Hajia, Hajiar kuwa ta kama hannayenta tana kallon fuskarta ta kai hannunta wajen fuskar Tata ta ce" meye wannan idon ya yi jajaja ko baki yi barci bane?"
MALEEK ya sake duban Hajia da kyau ya kalli RAUDA itama, sai ya mike yana tsintar dan fruits din tunda da wahala in ya samu abinci kafin ya fita yau kasa kasa ya furta" To ai shikenan Ni na wuce tunda ba'a bukatar shedu"
RAUDA kuwa a sanyaye ta ce" na yi Hajia, girki dai nake , daga kicin ne na taho da aka ce ana kira, shi yasa ban zo da wuri ba"
Hajia ta kalli Mah tana kama baki ta ce"
ππππππππ
Azl 60
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*
Bismillahi rahamanin rahim
Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE
ππΌ Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunchingππ»ββοΈπΊπ .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....
*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
ππΌ Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu ππΌππΌmusamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)
Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nanππΌ (magnifique)
Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account ππΌππΌππΌ (da wa kika ja Madame?)
Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa baπππ sai kun zo
Hajia ta kalli Mah tana kama baki ta ce" Lah, ki ga y'ar nan da neman fitina? waye ya aike ki? haba nima fa safiyar shiga kicin din na maki, haba dai, sai kace ba amarya ba, kin ga kina ji?, ki kula kin ji? a zamanku ki kiyaye haki, ki kuma girmama y'ar uwarki, ita abokiyar zama tana da dadi domin a rayuwa idan har ka zauna lafiya da ita zaka fi kowa jin dadin hakan, saboda yau da gobe ta fi karfin wasa, idan kunna jituwa ko abin dadi ya samu ko na wuya sai kun fara kama junna kafin mu ji, bana son jin wata fitinar kin ji ko?"
RAUDA ta gyada kai tana sada kai, ita kuwa Amnah sai kawai ta mike ta fice , dan ba zata iya gannin wannan abin bakin cikin da rainin hankalin ba, ko a me Hajia ta dauketa? lalle Hajia ta gama daukarta a wata shashasha, wato ita za'a nunawa an fi son wancen banzar tsintaciyar magen a kanta ko? ba damuwa su zuba su gani!
Gannin ya bi ta baya ya tabatar mata bangarensu ya koma, dan haka da gagawa ta je ta karasa ta shiga ta nufi Part dinsa
Tunda ta shigo ta ringa bin yannayin tsarin wajen da kallo
masha ALLAH wajen ya kawatu fiye da tunanin bawa, haka kuma bedroom biyu ne da shi su kuwa sauran part din daidaya ne da dan madaidaicin falo bayan falon nan baba sai dayan part din da tsarinra ya yi ginnin dakunnan a jere wa'inda ke nuni da na yara ne
Tunda aka bude aka shigo ya dakata da bale botur din wandonsa yana kallon falon
gannin shiru sai kawai ya bale din ya dauki abin wanka ya shige ya rufe, ya san da an shigo, abinda ya barawa ransa shine ko waye ya shigo cikin su biyu ne, shi yasa ya shige wankan nan, saboda zaman fada yau dole zai yi
Ya jima sosai a bayin, ya fito yana tsane ruwan jikinsa , a kugunsa da tawul daure mai fadi, sai karamin da yake goge jikinsa da shi ya nufo falon part dinsa ya bude ya fito yana sauke dubansa a kanta
Itama mikewa ta yi tsaye da sauri ganninsa a haka, gaba daya ta gaza dauke idannuwanta a kansa saboda irin yadda ya yi freshh da abin ruwan wankan dake diga a jikinsa
"Amnah, lafiya?" Ya tambayeta da kula yana karasowa inda take tsaye
gabanta ya yanke ya fadi gannin ya nufo ta kai tsaye ba wani tsaye tsaye
Yana zuwa da kanshin sabulun wankansa da irin hucin da jikinsa ke fitarwa da tarin kwarjinin da Allah ya masa ya dan dago fuskarta yana kallo kasa kasa sosai ya furta" Aush, sorry wifey, zai huce, idan bai huce ba zan sa a kai ki clinik lafiya ki ga docter Papalo na tabata yana da maganin ciwon ki....."
Babar duniyar da Amnah ta shiga ta farin ciki gannin wannan kulawa harda ambatonta da matarsa ce ta katse lokaci daya daga tsayen d atake wata irin mahaukaciyar juwa da tashin hankali suka sakata yin baya ta maku a kasa jikin kafet din wajen idannuwanta a waje ta dago a firgice tana kallonsa tana kokonta abinda ya faΙa
Da yannayin ya damu sosai da yannayinta ya ce" Subahanallah, Kai, meye haka? kar ki ji rauni mana yi a hankali........." Ya yi alamun zai duka ya kamata, ita kuwa ta yi saurin dafa cafet din ta mike kirjinta na dokawar da ta wuce misali idannuwanta na neman rufewa ta juya da sauri tana fadin" Am, eem, ina zuwa, bari in je na dawo" Ta fice da mugun sauri, shi kuwa ya mike ya bi bayanta hankali kwonce har falo sannan ya tsaya yana kallon shigewarta dakinta da rufo kofar da ta yi jikinta sai rawa yake yi , hakan ya sa ya sauke murmushi ya juyo hankali kwonce idannuwansa suka sauka cikin na RAUDA dake tsaye da cokali a hannunta , ko me zata yi da shi oho, jikinta dauke da wata mahaukaciyar doguwar riga ruwan maroon mai laushi, gashin kanta daure, a kanta ko dankwali babu tana gaban table din jera abinci ta ga wannan ikon Allah
Da farko murmushin ya dauke dif, dan umarnin da ya samu daga zuciyarsa kennan cewar kar RAUDA ta yi wani tunani a kan lamarin, sai kuma ya kwato yancin girmansa ta hanyar dawo da murmushin saman lebensa ya wani motsa kugunsa sannan ya nufo inda take tsaye da cokalin nan a hannunta tana kallonsa
Kai ta sada da sauri ta ci gaba da aikinta ta hanyar barin wajen zuciyarta cike da kunyar yannayinsa, ko dazun sakin bakin da ta yi ta ga ya fito da wani zani a kugu yana bale bale Tu sunna da wani bamakatarai ya bi wancen abar ne, bayan wannan ina ita ina sake kallon mutumen nan? sam ba kunya a lamarinsa
"Meye zaki wani saka mana ido Ni da matata?"
ya fada yana yafa karamin tawul din a gefen kafadarsa
turus ta tsaya daga abinda ta yi niya ta juyo tana kallon kasa wajen yatsun kaffafuwansa a hankali ta furta" Ban san kunne ba, da ban bi da kallo ba"
Gira ya hade yana fadin" Ki dago ki kalleni ido cikin ido mana, kina wani abu kamar wace ke tsoron mutane?"
Baki ta turo tana sake juyar da kanta ta ce" To ka saka abinda ya dace mana, Ni a haka ba zan iya ba gaskiya" ta karashe tana idasa ajiye kwanon da ta dauka ta cenzawa waje sannan ta ci gaba da gyaran table din , dan kuwa girki suka sha ita da masu aikin bangaren , shine ta shiga gyara wajen dan ita a rayuwa tana da sha'awar girki ko dan ta ci ta more da bakinta
Dan tsai ya yi na alamun mamakin furucinta, ya sake kallonta ya ga da gaske tana kiyaye kallonsa, hakan sai ya bashi mamaki ainun, ama kuma bai tsaya jan abin ba ya juya hankali kwonce ya nufi Part dinsa
A hankali ta tsayar da dubanta waje daya tana jin wani radadin na ratsa mata kirji na abinda ta gani, sai kuma ta kora ta ci gaba da aikinta , bata son shigewa cen ita kadai, ta tabata gajiya zata yi da zaman, bata saba ba ko farko zama waje daya kuma sai Allah ya hadata da Mah itama mutun mai son aiki da tsafta, shi yasa basa zama sam koda yaushe cikin aikace aikacen su suke kala kala, shi yasa yau dinma ta fitowarta dan bata ga dalilin da zai sa ta nade a gado ba
A lokacin da yake fesa turare ya dakatar da sauri kansa na sarawa sakamakon tinowa da ya yi a cikin mutanen dake masa girki harda kuku biyu maza
Ajiye turaren ya yi ya fito