Showing 129001 words to 132000 words out of 175193 words

Chapter 44 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

520

faWi, kafin takai ?asa yasakar mata wata irin gula da gwiwar hannunsa har sai data gantsare, cikin fushi ya caf kota yafara zabga mata maruka hagu da daman kuncinta kamar zai tsinke mata fuska, hakan bai wadatar dashi ba sai ya koma loda mata naushi a fuska da goshi yana zazzzaga mata zagin Wibar albarka .

"Shegiya tsinanniya matsiyaciya annoba, muna zaman zaman mu makirar uwarki ta shigo gidan mu ta saka mana kwan annoba, wallahi sai kin bar gidan nan, Shegiya marar hankali, wato saboda kin kwashe kayanki daga gaban ma aiki shine kike shirka da tsafi ko?

"Ri?e hannunsa ya Aminu yayi ganin jini da ruwa yana fita daga bakin Rashida ga a hakwaranta guda biyu da Aliyu ya cire mata garin naushin bakinta sukayi tsalle suka watse gefe.

*KUTSE*

*PAGE 55*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Dukan tsiya ya Aliyu ya naWa mata duk da yadda su ya Aminu da kuma su ya mansur harda hajja daketa kukan ya saketa amma hakan bai sa ya kyaleta ba har sai daya Salla mata ?afa Waya, ban da uban tar kaWe daya jijji mata a hannu san nan ya ragar gaza mata fuska wanda idan a asibiti ka ganta bakasan duka akai mata ba sai ka rantse haWarin mota ne ya rutsa da ita, Rashida taga bala'i ganin idonta haka taga rashin imani iya ganin ta, dan da gayya ya Aliyu ya Salla mata ?afa yace gobe yaga da ?afar da zata fita yawon neman asiri da shirkar, da yaga ma hajja na neman yi masa baki sai kawai ya figi Rashida kamar kayan wanki ya shige Waki da ita tare da kullewa da mukulli ya dunga lodarta kamar ya samu ?aton gardi, dan ya lura hajja tanada rauni mai tsanani akan Rashida duk kuwa da irin Abinda take aikatawa.

Cikin tashin hankalin bugun dasu ya Aminu sukewa ?ofar Wakin da ya Aliyu ya kulle ya juyo yana bugawa ?ofar harara kamar ita ce tayi masa laifi, kukan hajja yake jiyowa tana ka tausayawa marainiyar Allah Aliyu, dan Allah karabu da ita kada ka kashe musu yarinya na shiga Uku, Aliyu, Aliyu.

Shi kansa ya Aminu ransa yafara Saci da irin dukan da ya Aliyu yake yiwa Rashida, gashi dan rashin mutunci yanajin kukan uwar sa da magiyar da take masa amma ya?i ko sauraren ta Abinda yake gabansa kawai yake yi, hakan yasa ya Aminu cikin fushi ya saka ?afa tare da dage ?arfinsa ya bugawa ?ofar naushi duk da yasan ba Sallewa zatayi ba amma a ?alla idan yaji wan nan bugun ya buWe haka, da sauri ya Aliyu ya kalli ?ofar san nan ya haure Rashida wacce ta daWe da suma yana faWin tsinanniya matsiyaciya san nan ya nufi ?ofar ya buWe, yana buWewa kuwa ya Aminu ya sakar masa mari a fuska yana faWin.

"baka da hankali ne Aliyu? Taya zaka saka yarinya a Waki ka dunga lodarta kamar a filim dambe? Idan ka kasheta fa? Ya Aminu ya ?arasa yana hankaWe ya Aliyu baya wanda ya tsaya yanata sakin hucin dukan da yayiwa Rashida da kuma Sacin ran marin da ya Aminu yayi masa.

Baya su hajja suka rufawa ya Aminu wanda ya dur?usa a kan Rashida yana salati da sallallamin ragar gazar da ya Aliyu yayi mata, a gigiece kuma ya Wago yacewa ya Aliyu

"Kasheta kayi Aliyu? Shikkenan ya kasheta hajja, munshiga uku.

*Hajja*

Ita daman ba ishasshen Lafiya ba ai kuwa dajin wan nan Wanyen aikin na ya Aliyu jiri ya kwasheta ta yanke jiki zata faWi, Allah yaso ya Aliyu yana an kare da ita yayi saurin tareta tafaWa jikinsa a sume.

Kuka ya karimatu da nusaiba suka saka suna sun shiga Uku sun lallace.

*Asibiti*

Taimakon gaggawa aka shiga bawa Rashida wacce take halin rai kwafai mutu kwafai, dan da farko ma sun zata hatsari tayi har sunce su kirawo police, amma da yake likitan abokin ya Aminu ne nan ya faWa masa Aliyu ne ya ragargajeta shine hankalin sa ya Wan kwanta ya kalli Aliyu wanda yaci magani yace.

"Haba gadanga, meyasa zakayi wa ?anwar ka haka? Bakasan ita ba namiji bace? Gaskiya baka kyauta ba, dan Allah ka kiyaye kuma ka dunga kai zuciya nesa.

Banza ya Aliyu yayi masa bai kulashi ba hasalima Wakin da aka kwantar da Hajja ana saka mata ruwa ya nufa zuciyar sa sam babu daWi da ganin halin da hajja ta shiga a dalilin sa.

Rashida ta daku ta gurzu iya gurzuwa dan ko motsi batayi duk da ta suma ta far faWo yafi sau a irga kafin ta samu kanta, akan fuskarta kuwa an mata Winki kusan uku dan yadda ya Aliyu a ragargaje mata fuska tsaf zata iya ruSewa idan ba'a Winke ba.

*Bayan kwana biyu*

Rashida ta farfaWo kuma sosai jikinta yayi kyau, daman ita hajja bata kwana ba a ranar su ya Aminu suka tafi da ita gida, ya karimatu ce a wajen Rashida duk da ba'a son ranta ta zauna ba dan dai ya Aminu ya ro?eta tane shiyasa ta zauna Win.

Rashida nada ga kwance amma hawayen inda ta tsinci rayuwar ta yanzu take, batasan Abinda ta tsarewa ya Aliyu ba ya tsaneta, daman can baya ?aunarta dan badan hajja na tsawatar masa bama da tuni ya daWe dayin ?uli ?ulin kubura da ita, to ita bazata ce komai ba, ai tasan a gaban Nasir komai yafaru kuma duk wani namiji mai kishi dason Matarsa bazai bari ayi mata wan nan cin kashin yana gani ba.

Tasan nasir na sonta da ?aunarta dan haka bazai zuba ido yana gani ayi mata wan nan Wanyan aikin ba, dan haka tasan duk inda yake yanacen yana fafutukar Waukar mata fansa, hawaye ne suka sulalo daga gefen idonta ta kalli ?afarta wacce ke sa?ale a jikin ?arfe tana ayyana da tasan Abinda zatazo ta tarar a gidan hajja kenan da batayi gangancin barin kaduna ta tawo kano ba, data sani kadunan ta zauna ko kuma ta wuce agadez wajen dangin babarta tunda tasan babu mai ?aunarta a cikin gidan Hajja, Waya hannun ta Waga tare da share hawayenta tana tunanin Abinda yasa tatawo kanon.

*****

Safa da marwa Rashida ta dungayi na ina nasir yatafi? Me zaije gidan yayi? Shin Maryam tana raye? Idan ma tana rayen ta samu lafiya? Kai ta girgiza tana

"Inaaaaahhhh, bazai yiwu ba, mai duma ya sanar dani Maryam bazata taSa samun Lafiya ba ko zata shekara dubu sai dai ta mutu a haka.

Kuma ita babban abin ba?in cikin tama shine yadda akayi asirinta ya karye tun bata gama cimma manufarta akan Nasir ba, tayi dana sanin rashin sakashi ya saki Maryam saki uku tun tana da damar juyashi da kuma bashi umarni.

?aki ta koma ta kwanta tana kukan tafiyar da nasir yayi, meyasa bata bi bayan shi ba, wayar ta ta Wauka ta fara kiransa a waya amma wayar bata shiga dan ca ake mata wai layin a ?asa yake dan haka bazata iya samun saba, batasan cewar tun a hanya Nasir ya cire layin ya karya shi ya zubar ba, dan a ranshi yake cewar yana komawa gida zaiyi swapping Win tsohon layinshi.

A wan nan ranar Rashida bata runtsa ba saboda wasi wasi da fargaban kar dai Nasir ya koma gida sunyi ido huWu da Maryam? Rashin nutsuwar ne yasa da sassafe ta shirya kayanta dana zita dan su koma kano, tayi niyar tana zuwa jikin hajja zata faWa ta saka mata kukan kurciya itama akayi mata ta Sata sai da kyar ta dawo hayyacin ta, dan tasan kwarai hajja zata yarda da ita kuma ta tausaya mata, batasan cewar Abinda zata tarar ba da bata zo Winba.

*****

Dafata ya karimatu tayi domin wan nan tunani da kuma kukan da Rashida keyi yafara damunta, kofin hannun ta ta mi?a mata wanda shayine a cikinsa wai dan tasha kota samu kwari, kai Rashida ta girgiza Alamar bazata shaba, kafaWa itama ya karimatu ta Waga tace.

"Kinga malama idan zaki saki jiki kici abincin da likitoci suka ce kici domin samun lafiyar ki kici, kin wanibi kin damu kinata tunanin Abinda kece da kanki kika jawa kanki, wallahi Rashida duk son zuciya ta kin damani kin shanye domin ke harda rashin tsoron Allah da zalunci a lamarin ki, yanzu ace mace mai hankali mai son gamawa da duniya lafiya zata aikata abu kamar haka? Duk nasihar da hajja take miki dason nuna miki rashin dacewar zalunci amma ke abinna ki ashe kullum ?ara ta'azzara yakeyi? Gaskiya kin shayar damu gubar mamaki, kuma wallahi tallahi banga laifin matsiyaciya cin dukan da Aliyu yayi miki ba, dan makaho bazai son ana kallonsa ba sai an tsunkulo shi, dan haka wan nan ta zamar miki izina idan kinada tunani, shashashar banza da hofi kawai.

*Rashida*

Cikin wani irin ?unci take kallon ya karimatu, bata tanka mata ba har sai data gama maganar ta san nan cikin rashin kunya tace.

"Ai dole kice kinji daWin Abinda ya Aliyu yayi min tunda ba ?anwar ki bace nusaiba, da hajja ce ta haifeni ai shima bazai soma yi min wan nan izayar ba, kuma wallahi tallahi Allah ya isa tsakanina dashi bazan yafe masa ba wallahi, kuma ita hajjan da tana sona ai da......

Wata irin sha?a ya karimatu ta kaiwa Rashida tana zazzare mata idanuwa tace.

"Yarinya tsaya matsayar ki karki jawo Abinda zaifi ?arfin ki, dan idan kikace zaki zagi hajja a gabana imanina zan cire da tsoron Allah na na murWe miki wuya ki mutu kowa ya huta wallahi, dagani sai kai a Wakin nan ruwan cikinki zan haye na matse hancin ki na kasheki daga baya ko bursunne nayi muddin wajen kare mutuncin hajja ne, ke, ki kiyaye ni karki kuntowa kanki kurar dazata rabaki da rayuwar ki.

Kakari Rashida tafara tana mi?awa nusaiba wacce ta shigo da kayan abinci hannu alamar ta taimaka mata, da sauri nusaiba ta ?araso tana innalillahi, yaya, menene haka? Kiyi ha?uri, da kyar hannun ya karimatu ya SanSaru a jikin wuyan Rashida shima dan taga dama ne amma nusaiba batakai ?arfin da zata ci galaba a kanta ba.

Tana cire hannun nata ta zari mayafinta tana cewa

"Idan kinje gida ki sanar da Hajja bazan ?ara zama da wan nan annobar ba, dan wallahi idan na cigaba da zama da ita wataran sai dai azo a tarar da gawarta a kan gadon nan dan tsaf zan gama da rayuwar ta.

Tana ida faWar haka tayi fitarta ta rabu dasu.

Ha?uri nusaiba ta shiga bawa Rashida tana ganin bai ken ya karimatu dan batasan abinda ya faru ba.

*Nasir*

Bazai ce bai damu da halin daya ga Rashida ba a lokacin da ya Aminu ya Waukota da niyar kaita asibiti ba, sai dai ba wai sone ya saka ya damun ba kawai daman shi Mutum ne mai tsantsar tausayi da kuma jin?an na ?asa dashi, dan haka a ranshi so yake yaji a wane irin hali Rashida take a yanzu, bai ?ara zuwa gidan hajja Waukar su halima ba tun daga ranar, yabari ne hankali ya kwanta sai ya kuma wai wayar su, kuma cikin ikon Allah washegari sai gasu hajja ta saka drivern ta ya kawo su da tulin kayan su, ranar kuwa ba ?aramin jin daWi sukayi ba musanman da sukaga Maryam ta warke kum ga ?annen su sunata wasa dasu.

Bazai manta yadda su ya zulai sukaita murna da jin daWi ba a sanda suke sanar dasu halin da Rashida take ciki, umma kuwa da maryam bazaka ce ga halin da suke ciki ba amma tabbas yaga wani yalwataccen haske da farin ciki akan fuskar Maryam a yayin da ake basu labarin.

*Ramadan*

TaSa Nasir yayi yana cewa wai meke damunsa ne ya zurfafa a tunani haka?

Rashida Ramadan, kalmar data fita daga bakin Nasir kenan, da sauri Ramadan ya matsa baya yace

"Me? Ban gane Rashida ba? Me Rashidan tayi? kodai ta mutu ne?

Kai Nasir ya girgiza yanaji gaban sa na faWuwa a sanda Ramadan ya ambata wa Rashida mutuwa, to yaya ne? Ramadan ya tambaya zuciyar sa naWan sokawa da Sacin rai.

Biron hannun sa nasir ya ajiye yace.

"Wallahi Ramadan tun ranar da mukabar Rashida a wan nan halin nake tunanin ta, bawai sonta nake ba kawai dai tausayin ta ya cika mini zuciya, so nake kawai nasan a cikin halin da take ciki.

Cikin Sacin rai Ramadan yace dalla ware kabamu waje, kai yanzu bakaji kamar kayi saSoba da kake ambatar sunan Rashida a bakinka? Gaskiya ina tunanin soyayyar Rashida wata gundumemiyar mummunar ?addara ce a gareka, in banda haka, matar data cutar daku mafi munin cutarwa itace kake tausaya wa? Gaskiya na tausaya maka Nasir, kuma bari kaji na faWa maka

"Wallahi duk ranar dana kuma zuwa wajen nan kayi min zancen wacce da?i?iyar matar taka muddin ba zancen sakinta zaka min ba wallahi bazaka sake ganina ba.

Yana gama faWin haka ya tashi tare da wancakalar da kujerar dayake kai yafice, kiransa nasir yayi tayi dan yadawo su cigaba da lissafi amma Ramadan yayi kunen uwar shegu dashi ya?i juyowa bare ya saurare shi.

Tsaki Nasir yayi yanajin daman baiyi masa zancen ba da yanzu suna nan sun cigaba da lissafin daya ?agu ya ?are, daman tunda ya Sata shi Ramadan shine ya zama c.e.o a shagonsa dan bazai yarda dukiyar nasir ta salwanta ba, shine ya tsaya kai da fata ya dunga tafiyar da komai na harkar dukiyar Nasir, kuma Alhamdulillahi ya ri?e amana komai yana tafiya dai-dai fiye da yadda yake tafiya a hannun Nasir Win, shine fa kusan sati kenan suketa faman lissafe lissafe duk da Nasir Win yace shi basai anyi wani lissafi ba amma Ramadan Win ya?i ya kafe yace sai anyi.
*KUTSE*

*PAGE 56*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Jikinta yayi kyau sosai dan sosai ta tasamma abinci da kuma irin magungunan da take sha, daWin daWawa ga kulawar da Nasir yake bata sosai, wan nan kulawar da yake bata ita ce ta taimaka mata wajen farfaWowar rayuwar ta, yau Kimanin watanni biyu kenan da samun warakar Maryam kuma da dawowar Nasir

Maryam da Nasir ne a tsaye suna saka kayan umma a cikin mota domin yau ce ranar da umma zata koma gida bayan Waukar shekara guda da watanni biyu da tayi a tare dasu Maryam, kuka sosai Maryam tayi da tafiyar da umma zatayi dan ason ranta tafison umman ta zauna da ita har abada domin tanajin daWin ganinta a kusa da ita, firr umma ta?i yarda da ?udurin maryam duk kuwa da magiyar da Nasir yake aikawa umman, murmushi kawai umma tayi tace

"Nima inason ganina a Wakin nawa mijin duk da baya raye, san nan idan nadawo nan na zauna bazan ji daWi ba tunda na baro makwafta da kuma abokanan arzu?i, dan haka kuyi ha?uri kawai dan tafiya zanyi bazan zauna ba.

Da wan nan umma ta kashe bakin magiyar su domin sunga Alamar kamar bama sauraren su takeba.

Nasir, Maryam, kulu da kuma mahbub da muhibba aka tafi raka umma, sukam su halima suna makaranta domin tun lokacin baya Ramadan yamayar musu da makarantar su ta zama a wuni har islamiyya dan idan suka fita sai rana ta faWi ake kuma ganinsu, dan haka ba'aje dasu ba dan aranar zasu dawo ba kwana zasuyi ba.

*Rashida*

A Sangaren ta kuwa taga rashin gada da rashin soyayya danginta a cewar ta, ta?i yadda kwata kwata ta karSi laifinta dan itafa gani take kamar ita ce ake zalunta, dan a sanda ya karimatu tayi tafiyar ta gida ?in dawowa tayi duk da mitar da Hajja ta dungayi mata akan ta koma Win amma fafur ta?i yarda tayi zamanta a gida.

A lokacin ran hajja ya Saci harta Wan haWa kayanta kala uku tace ita zataje jinyar Rashida tunda tana raye, a wan nan lokacin shi kuma ya Aliyu ya kafe kai da fata yace wallahi Hajja bazataje ba sai dai idan baya raye, duk yadda hajja taso zuwa gurin Rashida haka ta ha?ura ta zauna sai delu Waya daga cikin masu aikin hajja ce taje ta zauna da ita har tagama warkewa aka sallameta, ba?in cikin wan nan abin da akayi mata yasa koda aka sallameta daga asibitin bata koma gidan Hajja ba sai ta koma gidanta tayi zaman ta a cewar ta tasan nasir yanacen yana kewarta, shi kuwa Nasir yama manta da zaman wan nan gidan dan tunda ya dawo baima yi tunanin saba balle yaje ya gansa, butu-butu Rashida ta tarar da gidan kamar anyi ya?i a cikinsa saboda ?ura, ganin bazata iya aikin wan nan wahalar ba ga jiki da take fama dashi dan har yau bata gama warke ba, a wayarta tayi browsing wani kamfani masu wankin gida da gyara nan kuwa tayi musu waya da suzo su gyara mata gidan.

A ranar sukayi komai suka gama san nan daga bisani ta biyasu kuWin su suka ?ara gaba, tun wan nan ranar ta zauna zaman jiran Nasir domin a tunaninta gani take yana nan tafe wajenta.

A Sangaren hajja kuwa sosai tayi Allah wadai da hali irin na Rashida wanda batasan a inda ta koyo wan mummunar al-?ibilar ba, dan ita dai tasan kaf dangin baban su babu asararren da Rashida zata Wauko halinsa, ajiyar zuciya ta sauke data tuna da dangin uwarta waWanda basu gaji arzu?i ba sai tsiya, addu'ar shiriya tayi wa Rashida san nan a take ta tsawatar wa da ya Aliyu mai cewa zaije gidan nata, kuma wallahi su saka a ransu idan yaje sai ya rataye ?ar iska ya kawo musu gawarta.

A wan nan watanni biyun da Rashida tayi tana jinya bayan ta koma gidan ta harta tashare wajen wata guda babu nasir kuma babu labarin sa, wata zuciyar tana ingizata dataje gidan Maryam tasan zata samesa ko kuma taje kasuwa ta sameshi acen, kauda zancen zuwa gidan Maryam tayi amma zuwa kasuwa kuwa babu fashi koda zaiyi mata korar kare, a Sangare guda kuma kullum sai ta kira wayar maman mu amma magana Waya ake faWa mata cewar layin baya aiki amma kullum a cikin jarrabawa take, jitake kamar tatafi agadez Win amma tana tunanin karta tafi kuma Nasir yazo nemanta bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login