Showing 21001 words to 24000 words out of 175193 words

Chapter 8 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

524

har akayi sallar asuba tana zaune gaban ubangiji tana kai rok'o da koke kokenta.

*****

*Nasir*

tunda aka sallami Rashida ta dawo gida yakejin ta kamar gyambo a cikin jikinsa, shi jifa yake da da halima ruwa saiya tauna mata, lallab'a ta yakeyi kamar kwai a cikin faranti, motsi d'aya idan tayi kaji yace "yaya?

Kwata kwata ya manta da batun Maryam dabai ma san halin datake ciki ba, rayuwar sa kawai yakeyi da rashida wacce ko kad'an ita bata manta da Maryam ba, Maryam tana zuciyar ta kuma duk Abinda take tana tunawa da rayuwar ta, batasan abinda zai kuma dawo musu da hannun agogo baya shiyasa take taka tsantsan da d'eba masa kewa a koda yaushe.

Yau kimanin kwana biyu kenan da sallamo Rashida daga asibiti, kuma yau ta kasance weekend ce kamar yadda take ranar hutun ma'aikata, Nasir ba ma aikaci bane d'an kasuwa ne, amma a haka yawancin weekend bai fiya fitaba saboda shima yanason yasamu hutu kuma ya kasance tare da iyalinsa.

*Nasir*

Wayarsa na d'aki a charge yayinda su kuma suke falo a zaune suna kallo suna d'an tab'a ciye ciyen daya saba siyo musu koda yaushe, tun wajen k'arfe uku na rana ake faman kiran wayarsa amma baima san anayi ba saboda baya kusa da ita, yanzun ma kiran wayar Rashida da akayine ya tunasar dashi ya kamata ya d'auko wayar tasa dan yasan yanzu gab take da cika koma ta cika.

Sai da yabari Rashida tagama tata wayar daya gane da k'anwar ta takeyi san nan yace ta d'auko masa tashi wayar.

Koda ta kawo masa karb'a yayi yafara duba misscall d'in da aka yi masa, cikin mamaki yake kallon misscall d'in mutumin daya dad'e basu gaisa dashi ba wanda bayajin sun tab'a kwana biyu batare da sunyi magana.

Cikin fad'uwa gaba da dokawar zuciya Nasir yatashi a lokacin daya fara karanta message d'in daya turo masa kamar haka.

" _Inata kiranka baka_ _d'aga ba, Allah yayiwa_ _Baba rasuwa_ _d'azu, naso Maryam taga gawar_ _Baba kafin a binneshi Amma Allah baiyi ba._

Da sauri Nasir ya tashi tsaye jikinsa na rawa Had'i da kakkarwa yana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.

" A million ya zari mukullin motar sa ya fice ko sauraren Rashida wacce ke jefa masa kalmar lafiya baiyi ba yatada mota yafice daga gidan.

*KUTSE*

*PAGE 11*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*Nasir*

Cikin wani gigitaccen gudu yake tafiya domin burinsa kawai yabar gari don yaganshi a cikin garin daura, yana tafe yana share hawaye, wai baba ya rasu, kuma har an birneshi batare dashi ba, shikam baiga ranar soyayya da k'auna da baban ya gwada masa kamar shi ya haifeshi ba, kaf garin daura a yanzu bashi da wani dangi na uwa da uba daya zamar masa makwafin iyayen sa kamar baban ba, baba mutumin kirkine, yaso shi a lokacin dayake ganin ya rasa gatan mahaifi, ya k'aunace shi ya rik'eshi ya zamar masa bangon dafawa a lokacin dayake tunanin ya rasa tsanin dazai dafa domin yakaishi ga cimma rayuwar gaba.

"Baima san ya shigo cikin unguwar tasu ba har sai daya fara ganin mutane suna tsaidashi tare dayi masa ta aziyar baba, da kyar ya iya fitowa daga motar yanajan jiki dan gaba d'aya jiyake kamar an saka gorane an daddoke masa gab'ob'in jikinsa.

"Cak, Nasir ya tsaya a dai-dai rumfar da mutane suka cika suka tunbatsa ana ta zaman makoki, bai iya tuna komai ba har sai da suka had'a idanuwa da Mansur amininshi kuma yayan Maryam san nan ya iya tunawa da rayuwar Maryam d'in baki d'aya, kobai tambayeshi ba a irin kallon da Mansur ke masa yasan Abinda yake nufi kuma yake tsammani daga gareshi.

"Maryam, itace fassarar kallon da Mansur yake masa.

"Ina take?

Da sauri Nasir ya kalli mansur wanda ya dafashi yana hawaye tare da tambayar ta , rasa bakin magana yasa Nasir saurin tsugunnewa a wajen yafashe da wani sabon kukan mai cin rai tare da ma'anoni da yawa.

Mutane biyu ne a wajen suka taso suna rike Nasir tare da bashi baki akan yayi hak'uri an san sunyi rashi dan baba mutumin kowa ne kuma mutumin kirkine, suyi hak'uri suyi masa addu'ar samun salama a cikin makwancin shi, da kyar aka zaunar da Nasir akan ta barma yanata kuka a kusa da Mansur wanda ke tayashi shima Amma zuciyar sa fal tunanin inda yatawo yabar Maryam.

Sai da Mansur yaga Nasir ya nutsa sosai san nan yace

"Nasir banga Maryam ba, kuma kamata yayi ace kun tawo tare meya faru bakazo da ita ba?

K'asa Nasir yayi da kansa yana tunanin Abinda zai cewa Mansur dan ko giyar wake yasha shi bai isa yasanar da Mansur halin da ake ciki ba, wanda bama shi ba hattaya baba da a yanzu yake kwance a makwancin shi yasan bazai tab'a yafe masa ba.

Sai da yayi tunanin Abinda zai cewa Mansur san nan yace

"Wato ai yau naje wani d'aurin auren abokinane na kasuwa, munacen wajen reception kaketa kirana a waya, ashe wayar ma a cikin mota na barta, sai da muka gama nazo na d'au wayar kawai naga kiranka, kafin nakai ga kiran kuma sai ga sak'on ka ya shigo na Allah yayiwa baba rasuwa, wallahi mansur ji nayi kamar an bugamin wata allurar tashin hankali, shiyasa kawai ina fad'awa mota a gigice nayo nan batare da duba halin yammaci ko kuma dare ba, ban koma gida ba, ita kanta Maryam d'in bata saniba, kuma ina fatan baka kirata ka sanar da ita ba dan rashin iyaye a wan nan shekarun na Maryam babban tabone wanda zata dad'e tana jinyar sa.

Ajiyar zuciya Mansur ya sauke yace

"shiyasa ai ko dana kiraka a waya baka d'aga ba banyi gangancin kiran Maryam d'in ba, tunda nasan tanada miji kuma shine zan gayawa yasan lugga da fasahar dazai gaya mata mutuwar mahaifin ta.

Numfashi Nasir ya sauke yace

"wai me yasamu baban ne? Ko a waya banji bashida da lafiya ba, sai kawai sak'on mutuwa naji.

Girgiza kai Mansur yayi yana hawaye yace

"lafiyar sa k'alau wallahi Nasir, kasan jibi ne ma za'ayi wa babar mu aiki a cire mata mama d'aya, bawan Allahn nan yana tsaye kai da fata wajen ganin batada hankalin taba, cikin dare yaji tana kuka sosai tana cewa tasan mutuwa ce zatayi idan akayi aikin nan bazata tsira ba, sosai baba yayi mata fyad'a tare da jaddada mata za'ayi aikin nan lafiya k'alau da ikon Allah, ganin dare ya raba yasa yatashi tare da d'aura alwala yayi tsayuwar dare, wallahi yana cikin sallar nan ya yanke jiki ya fad'i, dayake yasamu ya lallab'a babar tamu ta samu barci batasan ma yafad'in ba sai da safe, shine fa ta kirani natawo mukayi asibiti, nan da nan aka shiga bashi taimakon gaggawa ashe ya had'u da ciwon barin jikine, duk da bakinsa ya karkace kuma maganar sa bata fita sosai Amma haka ya dunga kiran sunan ka dana Maryam, har baba yacika yana ambaton kalmar shahada daya dire sunan ka dana Maryam yake cafka, Mansur ya k'arasa yana fashewa da kuka sosai.

Shima Nasir d'in kukan ya tayashi suka cigaba dayi har sai da ransu yafara sanyi san nan suka tsagaita.

Cikin gidan suka shiga inda suka tarar da maman su Maryam babu yadda take domin tuni daman tun suman datai an kira likita ya saka mata ruwa, koda ta farfad'o din ma dai hakan ce ta faru dan bata iya gane komai a wan nan lokacin, cikin tashin hankali Nasir ya k'arasa wajenta tare da kamo hannunta yana mata sannu, dakyar take iya motsa baki kuma koda Nasir ya kwafa kunne a wajen bakinta yake karantar motsinsa sai yaji tana kiran Maryam.

Da sauri ya d'aga yana cewa

"Maryam, Maryam dai? Sai kawai ya juya zai fita, bin bayansa Mansur yayi ya rik'e shi ganin hankalin sa ya bala'in tashi yace

"Me kake shirin yi?

Da sauri Nasir yace

"zan koma gidane Mansur, bazai yiwu ace Maryam bata nan ba, komai dare zan koma na tawo da ita, Insha Allah zuwa da safe Maryam zata shigo garin nan.

Ajiyar zuciya mai nauyi mansur yayi yace.

"Allah ya tsare hanya d'an uwana.

*****

Kuka wiwi Maryam keyi har jikinta na rawa saboda tashin hankalin datake ciki, dukan hannun samira kawai takeyi wacce ke rik'e da ita a cikin jikinta, ta rasa yadda zatayi da Maryam d'in, ita bama tasan wanda ya kirata ya sanar mata da zancen mutuwar ba, ita samiran ta sani ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?domin tagani a status d'in wasu daga cikin 'yan gidan su, ita kanta hankalin ta ba k'aramin tashi yayi ba akan jin labarin mutuwar baban, Amma haka ta zauna taita jimamin abin da kuma yadda zatayi ta sanarwa da Maryam d'in.

Ganin ta kasa nutsuwa yasa ta sanarwa da mijinta wanda bai fita ba saboda lahadi ce, shi kansa Abin ya kad'ashi kuma haka yayi ta tunanin yadda Maryam zataji wan nan al-amarin idan yaje kunnenta, tausaya mata yakeyi saboda duk wani lamari daya faru ita samira ta fad'a masa domin yasan musabbabin zamanta a cikin gidan sa, dan haka sai kawai yacewa samiran tabari gobe insha Allah ma yana off zai d'aukesu da sassafe sai ya kaisu gidan.

To suna cikin maganar nefa sai kawai jiyo ihun Maryam sukayi ta fad'i tana birgima a k'asa tana

"Wayyo Allah babana, Wayyo baba, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah kasa ba gaske bane ba, da wan nan su samira da mijinta suka fito da gudu dan subata taimako, da kyar suka iya d'aga ta tsaye samira ta jinginar da ita a jikinta dan ko tsayuwar kirki ma ta kasayi saboda yadda jikinta yake rawa.

Dare ya rigada yayi shiryasa mijin samira yayita lallab'a Maryam akan tayi hak'uri da kukan tabari sai gobe da sassafe san nan su d'auki hanya zai kaisu da kansa har cen garin.

Sai da Samira ta d'auki wayar Maryam d'in san nan ta lura ashe Whatsapp ta shiga taga rasuwar.

****

Rabon da Maryam tahau Whatsapp harta manta, yo bata da nutsuwar zuciya data ruhin da zata iya d'aukar wayar ma tayi wani danne danne, sai yau taji zaman shirun ya isheta, samira tana cen wajen mijinta, yayin da ita kuma kad'aici duk yabi ya da bai bayeta gashi batajin dad'in jikinta da zuciyar ta, yau haka tatashi sukuku da ita sai yawan fad'uwar gaba dake damunta, har barci ta k'irk'irar wa kanta kozata fita daga yanayin datake ciki amma barcin yak'i zuwa, hakan yasa tatashi tare da janyo wayarta ta bud'e data, nan da nan kuwa sakwanni suka shiga kai kawo a cikin wayar tata.

Sak'on dake sama shine ya d'auki hankalin ta wanda daga k'arshe taga an saka

"Allah yajik'an sa ya karb'i bak'uncin sa.

Gabanta ne yafad'i a ranta tace

"Wanene?

Sai kawai tayi saurin bud'e sak'on taci karo da maganar da akayi.

"Baba kuma sa'i yayi Maryam, wallahi banji rashin lafiyar saba sai rasuwar sa naji, ai danazo na dubasa.

Allah yajik'an sa ya karb'i bak'uncin sa.

Bata samu damar bata amsa ba sai kawai tafita daga chat d'in nata ta tafi kan status, da status d'in 'yan uwanta tafara cin karo duk sun baza hotunan baba suna ta aziyar rasuwar sa, da sauri ta lalubo lambar ya Mansur ta duba nashi status d'in hannunta na tsananta rawa, to anan nefa taji gaskiyar mutuwar da kuma gane waye ya rasu dan sam da daga farko ma ita bata gane ba, shine fa ta yar da wayar itama ta fad'i tanata birgima a k'asa har su samira suka fito suka taddata.

****

*Nasir*

Sai dare san nan ya nufo garin kano, ba k'aramar wahala yashaba a tawowar sa dan haka motar taita bashi wahala yana tsayawa, a k'arshe ma harya yanke shawarar ajiyeta yanemi ta haya ya hawo ya tawo dan yayi alk'awarin a cikin wan nan daren sai ya lalubo Maryam gobe yayi daura da ita.

Koda ya isa maimakon ya nufi gida ya huta sai ya nufi titin daya ajiyeta a wan nan ranar yanata tambaya, wasu mutanen ma dariya suka dunga masa suna wan nan kuwa akwai Kai? Taya zaka ajiye yarinya a waje tsawon kwanaki biyu kuma ace wai yau kazo nemanta? To bishiyace ko kuwa dutse wanda idan ka kafashi awaje babu yadda zaiyi ya gusa saika gusar dashi.

Ganin ya rasa mafita yasashi d'aukar wayarsa ya kira wani abokinsa mai yin tracking da niyar ya bibiyar masa wayar Maryam d'in.

Koda abokin nasa ya d'aga wayar ya sanar dashi Abinda yakeso sai yace masa yayi hak'uri dare yayi, Amma Insha Allah gobe akan aikin nasa zai tashi, da wan nan maganar sukayi sallama san nan ya kaWa kan motar tasa yayi gida.

*Rashida*

Tunda Nasir yafita ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa yadda zatayi gashi idan takira wayarsa ma baya d'auka, k'arshe wayar tasa ma sai ta daina shiga kwata kwata, duk da haka bata daina kiraba har sai da ta sameshi, sai da ta tabbatar ya d'aga san nan ta fashe da kuka tana cewa

"Ina katafi ne? Me yake faruwa ne? Katafi kabarni da tunani, haba mijina.

Runtse idanunsa yayi yanajin shikam damai zai biya wan nan zazzafar soyayyar da Rashida take masa? Kuma nan take ya kauda tunanin yace mata.

"Kiyi hak'uri hankali nane ba'a kwance ba, rasuwa akayi minne shine natafi Amma nashigo gari ma yanzu zanzo gidan.

Yanajin yadda Rashida ta saki ajiyar zuciya tare da furta Alhamdulillahi, Allah nagode maka daka tsaremin mijina.

Kashe wayar Nasir yayi yana mai kifa kai ajikin sitiyari yana mai da numfashi, yanzu bawai tunanin rashida da kuma Abinda take masa naso ne a gabansa ba, yanzu neman Maryam ne a gabansa da kuma rashin makwafin mahaifi da yayi a duniya, shiyasa ya kauda tunanin ya figi motar ya fara tafiya .

"Ina ka saka ina ka ajiye Rashida ta tungayi da Nasir, Abin har mamaki yake bashi shi kansa, kamar wanda ya shekara da tafiya baya nan, wan nan kula da Rashida take masa yana d'aya daga cikin Abinda yasa yakejin bazai iya had'a ta da kowa a tarayyar su ba.

Sai dai itama kanta Rashidan tagane cewar

" tunda yadawo bashi da nutsuwar datake nema a wajensa, gashi duk jikinsa yayi sanyi kuma fuskar sa babu walwala, hakan yasa ta takaita da duka rawar jikin data dashi ta zauna kusa dashi tace.

"Waye yarasu? Kodai wani Abin na damunka ne?

Har ga Allah Abinda Nasir keji a cikin ransa yayi masa yawa, yanason ya furtawa wani koda zai samu salama a cikin zuciyar sa san nan ya samu mafita, baiyi tunanin komai ba kawai yace.

"Maryam ce, mahaifin Maryam ne yarasu d'azu, san nan ita kanta Maryam d'in itace da muwata, dan ban san...

Jin fad'uwar kofin glass d'in hannun Rashida yasa Nasir yayi saurin d'agawa ya kalleta, sai ya ganta tsaye maimakon da datake a zaune tana sakin huci ga jini na zuba a hannunta ashe cup d'in dake hannunta tafara matsewa a hannunta daya ambaci sunan Maryam, har sai daya tsaga mata hannu san nan ta sakeshi ya fad'i kasa tare da k'arasa ragar gajewa.

*KUTSE*

? ? *PAGE 12*

? ? ? ? ?? *NA*

? ? *MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Hannunta nad'e cikin bandage ga waya kare a kunnen ta tana kuka wiwi tana cewa.

"Saboda tsabagen bai damu dani ba yaya, shine zai kaWa kai yatafi garinsu wajen wancen dangin jarabar wai babanta ya mutu, toni ina ruwana da mutuwar babanta? Tun jiya daman daya dawo naga bashi da wata nutsuwa ko kad'an, kuma saboda muna furci shine ya b'oye min, badan ma Allah ya matsi bakinsa ya fad'a ba da sai dai naji alak'a mai k'arfi tsakanin sa da Maryam d'in.

Daga cen b'angaren yaya karimatu cikin fad'a take cewa.

"Ai kece babbar shashashar data bada goyon baya, wai yaushe kika koma hakane Rashida? Sanin da nayi miki acen da bakya wasa da duk wani Abu daya shafi mijinki, towai tayama kikayi saken da har Nasir ya iya kallon wata mace da sunan yanaso har ya aurota? Kuma banda lusara ce ke a lokacin da asirin su ya tonu mai ya hanaki ki nutsu ki samo hankalin ki kiyi duk Abinda kika san zai saketa a take? Amma saboda hauka sai ki zauna kifara tumami a k'asa kamar wata akuya har ki kwanta a asibiti wai saboda kishiya? Ai wallahi kishin naki ya zama na banza Rashida, kuma wallahi wan nan labarin ma da kike bani wallahi sawa yakeyi inajin haushin ki.

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke tace

"Ba haka bane yaya, abinne yazo min a bazata, bantab'a zata Nasir zai iyayi min irin wan nan cin amanar ba sai yanzu, kuma sai yanzu nake k'ara fahimtar maganar da kike gaya mana na duk wanda ya maida namiji uba zai mutu maraya, yaya, da Nasir bayason yaga koda canji a cikin fuskata, ko motsi nayi idan bai masa dai-dai da yadda yakeso ba yanzu zai rikice, Amma yaya wai ni yau Nasir yake k'ok'arin juyawa baya saboda wata halittar 'ya mace, ta k'arasa tana fashewa da kuka.

Tsaki yaya karimatu taja saboda haushi kawai ta kashe wayarta, sai bayan kamar minti biyu haka san nan Rashida taga text daga ya karimatun

"Banda lokacin sauraren wan nan lusarancin naki, dan haka zanzo Anjima mu fuskanci matsalar tare, dan idan na barki hauka kawai zakiyi tayi harki shashance a haka batare da sanin kema mace bace.

Koda Rashida ta karanta text d'in ya karimatun kawai sai ta k'ara fashewa da kuka saboda tunanin cewar ashema Nasir ya daina yi mata kallon mace, sai ta tambayi zuciyar ta da cewar "to kallon me yake min?

*Nasir*

Tunda ya shiga garin daura ya cake a waje d'aya ya kasa gaba kuma yakasa baya, tunanin labarin dazai bawa Mansur akan Maryam kawai yake sak'awa da warware wa, wata zuciyar shawara take bashi kawai yafad'a masa gaskiya, a yayin da wata zuciyar tasa kuma tana gargad'ar shi akan kada ya soma, yadai k'ara dan jirkintawa zuwa wani lokacin, Amma yanzu dai yasan k'aryar daya sharawa Mansur akan Maryam don kar yafara harbo jirgin sa.

Gumin dake tsattsafo masa yashare sanda ya kuma tunawa da maganar abokinsa mai tracking.

"Wallahi Nasir babu yadda za'a yi a iya tracking wayar nan Alhalin tana kashe, tun d'azu muke maganar nan dakai, gashi yanzu wajen awa d'aya kenan muna Abu d'aya, wayar akashe take ,hak'uri fa kawai zakayi mu bari a kwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login