Showing 105001 words to 108000 words out of 175193 words

Chapter 36 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

576

tace

"Kashin ne ya matseta sosai Abba shine mun rasa inda zatayi, kuma nace mata mushiga gidan maman sadik amma ta?i shine tayi a wondo tun Wazu ?uda ke bin mu kamar masai.

Kai Nasir ya jijjiga haushin Rashida na ?ara ya Wuwa a ransa san nan ya nufi gidan ya buWe da nashi mukullin suka shiga, suna shiga kuwa Nasir yayi turus a tsaye ganin kayan daya bayar aka kawo tun wajen safe sune a yashe a tsakar gida ko arzu?in kaisu sama basu ciba bare suci arzu?in gyarawa.

Wani tu?u?in ba?in ciki ne ke tasowa Nasir wanda har yakejin jirin Sacin rai na neman ya dashi, bango Ya dafe yana kallon Halima yace

"Kuje sama ki tayata ta wanke jikinta kuzo, wacewa su Halima sukayi suna karantar Sacin ran dake kan fuskar Abban nasu.

Haka koda suka shiga ban Wakin sauda tace

"Kinga na Satawa Abba rai saboda nayi kashi a wando ko? Ki faWa masa matsata yayi ai, dan Allah yayi ha?uri bazan ?araba.

Kai Halima ta girgiza tace

"Ba kece kika Sata masa rai ba sauda, inaga dai mama ce ta Sata ransa tunda kinga ta daWe a unguwar data tafi har dare bata dawo ba.

Shi kuwa Nasir ganin ba?in ciki na neman Waukewar numfashin sa yasa yaita addu'a kala kala har ya samu Sacin ran nasa yaWan rage ya dunga jin nauyin ?irjin nasa yana raguwa.

Kayan yafara tattarewa yana lodawa a bayan Boot Win motarsa, tass ya kwashe komai ya rufe san nan ya haura sama wajen su Halima dan yaga Abinda suke shukawa.

Koda ya hau saman ya tarar da yaran sunyi wanka sun janza kaya sunata ?amshin turare, kumatun sauda yaja yana mata ya?en dole yace

"Ja'ira mai kashin wando.

Dariya Halima ta saka tana cewa Wallahi kuma Abba bakaji wari ba kamar tanacin mushe.

Shima dariyar yayi wacce batakai zuci ba yace

"Kuzo muje gidan Aunty ku musha ruwa a cen.

Suna sauka ?asa sauda na tambayar sa ina mamansu take? ?in kulata yayi har sai daya rufe ko ina na gidan suka fice yana ce mata taje unguwa ta dawo.

*Maryam*

Suna zaune da kulu suna kallo bayan kulu ta gama shan ruwa dan ita Maryam tuni azuminta ya karye saboda jinin data zubar da kuma abincin da aka bata acen asibiti taci, wani film Win indiyar hausa suke kallo a tumbin giwa sai dariya take gwanin sha'awa kamar ba itace Wazu ciwo yaso kaiwa lahira ba.

Shigowar su Halima yasa Maryam tayi saurin tashi tana dariya da murnar ganinsu dan ta daWe bata gansu ba, rungumar su tayi a jikinta baki Waya tana ce musu

"Welcome da yaranta.

Da sauri sauda ta saki Maryam tana tsalle tana cewa

"Yeee aunty kin kusa haihuwar mana baby? Yeeeh zanyi partyn suna aunty, wata ?awata ma da mamanta ta haihu sai da ta gayyace mu partyn suna amma mama ta hanamu zuwa, ta ?arasa tana Sata rai kamar yanzu abin yake faruwa.

Zauna wa Maryam tayi akan kujera tana shafa kansu tace

"Ai kuwa ina kawo muku baby da kaina zan haWa muku partyn sunan nan, ku dai kuyi min addu'ar Allah yasa na kawo muku baby lafiya kunji?

?aga kai sukayi suna murna sosai kamar a lokacin akace musu zata haihu.

Kallon cikin nata Maryam tayi tana ?ara addu'a da godiyar Ubangiji da tsarewar da yake mata a duk sanda Rashida ta jefa mata ?ullinta.

Ita tasan Allah ne kawai ya tseratar da ita ba wani ba, dan da sukaje a sibitin nan a jigace har ta fiddarai da cigaba da rayuwar duniya sai kuma daga baya Allah yasa ciwon yalafa mata.

Duk gwaje gwajen da akayi mata a asibitin sun ga babu wani dake damunta sai suka ce wai kawai juyi ne da wasu masu cikin sukeyi a watanni takwas sai ayi zaton haihuwa ce, jinin kuma data fara zubarwa juyin Wanne daya karci mararta yayi sanadiyar zubar jinin amma babu komai.

Wani abin mamakin hajaran majaran Nasir yakai Maryam asibiti amma sai gashi da ?afarta ta fito har suna hira da dariya dashi a hanyar su ta zuwa gida.

*****

Ajiyar zuciya Maryam taja tana kallon Nasir da ya shigo wani wurjanjan dashi kamar an koroshi yana cewa kulu ta bashi shayi.

Da sauri Maryam tatashi tana cewa kulu ta zauna ita zata bashi dan sam yau Win nan ma sai taji gaba Waya ta daina jin nauyin cikin da nauyin jikinta, kichen ta nufa tana mamakin yanayin data ganshi a ciki kamar ma ranshi a Sace yake, komai da komai sai data haWa masa nashan ruwa harda farfesun kazar data rage mata a cikin fridge, dan kayan da Rashida ta kawo mata ?in taSasu tayi ta bawa kulu tace takaiwa cen wani gida dake bayan layinsu wanda basu da hali ace suyi miya, kuma a take ta gargaWi kulu akan karta soma gayawa Nasir cewar Rashida tazo gidan dan gudun fitina.

Dan Maryam ta kuma tsorata da lamarin Rashida da kulu tace mata taga an bar baWa magani a ?asa, kum da tasaka ruwa tana wankewa haka taga yana kumfa tare da fitar da haya?i kamar ana ?ona wani abu.

Abincin ta kawo masa ya Wanci domin a gaskiya Sacin ran dake ?asan zuciyar sa bazai iya barin sa yaci wani abin kirki ba, yana gamaci ya shige Wakinsa ya watsa ruwa tare dayin salla ya kwanta.

Harya kwanta sai ya tuna ashe akwai kaya a cikin mota sai kawai ya mi?e yatafi ya Webo.

Kayan ya Webo ya ajiye a kichen san nan yacewa Maryam akwai aiki ya kawo ta faWawa kulu.

*Rashida*

Ganin Nasir ya fice yabarta sai ta shiga damuwa, gashi tun tana irga sa kannni da mintinan fitar shi harta fara irga a wanni, cikin sanyi jiki ta kalli likita ganin har takwas ta wuce tace masa kawai ya sallameta ta wuce tunda mijin nata bai dawo ba.

kallonta yayi yace

" Amma hajiya zaki iya tafiya kuwa? Naga akwai tar gaWe a hannunki da yatsanki na ?afa.

Jijjiga kai Rashida tayi tace karka damu idan aka samomin abin hawa zanje gida lafiy....wata ?ara rashida ta saki tana dafe mararta tana mur?ususun a zaba, kamar zata mutu haka takeji shiyasa ta kama wata nurse dake tsaye kusa da ita tana bata taimakon gaggawa.

Guda gudan jinine yaketa zuba yake SulSula daga jikin Rashida kamar wacce ake kwararosa da roba, ihun azaba kawai Rashida keyi tana ?a??afe-?a??afe kamar wacce ake zarewa rai.

*KUTSE*

*PAGE 45*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Tana kishingiWe tana hawaye, wayasan hawayen me yake yi? Hawayen Sacin rai ne da ba?in ciki ko kuwa hawayen halin data jefa kanta a ciki ne?

Ita dai ta sani.

Kallon ta ya karimatu tayi tace

"Kinsan Allah muddin baki daina duk wani abinda kike ba to ina tabbatar miki wataran sai kinyi kukan jini saboda nadama, dan haka ina tunanin zuwa yanzu ya kamata ki zubar da makaman ya?inki tunda kinyi kinyi kinga babu nasara sai ki ha?ura, ince yanzu kin bani labarin irin jifan da kike wa Maryam? YataSa cinta? Bai taSa cinta ba kuma gashi duk sanda kikayi mata sai abin ya dawo kanki, mafi munin abin ma na yanzu dayafi na koyaushe zafi da ciwo, wai dan Allah duk ba'a kan namiji kike wan nan ha?ilon ba? Toga shinan shi Nasir Win da kike wan nan abin saboda dashi ya manta dake, so nawa yazo asibitin nan tunda kika kwanta?

Idan ba Satan lissafi nayi ba tun ranar idi da yazo da yara da ita kishiyar taki dubaki har yau uku ga salla bai ?ara takowa yazo ko yayi miki waya ba, to yakamata kiyi tunani kisan halin da kike ciki kuma kisan ciwon kanki, dan Rashida sanin kanki ne duk bala'in biye - biyen malaman ki baki kaini ba, kuma tunda nakeyi ban taSa faWuwa ?asa ba kin sani, amma gashi yanzu na daina bin kowa na ri?e Allah mai kowa da komai

Dan haka tun dake kin gwaggwada baki samu riba ba kiyi ha?uri ki dakata, ke macace Rashida, kinsan fa yadda zakiyi da mijinki ki mallake zuciyar sa tun kafin wata tazo miki, amma da yake kin bada dama yanzu gashi nan sai Abinda Maryam tacewa mijin naki yakeyi.

Hannun ya karimatu Rashida ta dam?e a nata tanajin tafasa da ?una suna huhhuda cikin aikin da kayi mata.

Ba komai yasa take kuka ba illa ganin yadda Nasir yayi shagulatin San garo da ita kamar ba Rashidan saba? Kamar ba ita ce Rashidan da yake yawan faWin idan babu ita sai rijiya ba, wai ita Rashida ita ce yau take ?unsar ba?in ciki da takaici akan Nasir saboda ya?ara Aure, hnmmm, namiji, namiji buhun ?ai?aiyi duk wanda raSesa sai yayi susa, taso ace sanda aka kawo mata labarin Abinda Ya sameta ta mutu dan bataga amfanin rayuwar taba, amma data tuna wani lamari sai taji tana da bu?atar ta rayu, badan komai ba sai dan ta Wauki fansa akan Maryam wacce duk ita ce sila da kuma sanadin rasa mahaifarta da tayi.

Wani kuka ta kuma ke cacewa dashi tana bubbuge bubbugen ?afa da hannunta tana kwala ihun wallahi bazata yarda ba wallahi sai an dawo mata da mahaifarta ko zata rasa ranta kuma sai taga bayan Maryam.

Ana haka ne sai ga Nasir yayi sallama shida likita suna magana, da sauri likita yafara neman ri?eta tunda akwai c.s a jikinta zata iya famawa ta maida musu aiki baya ita kuma ta jawo kanta Wanyen aiki, da kyar da siWin goshi aka samu bubbugen da take ya lafa sakamakon allurar barcin da likita ya soka mata tare da zu?e mata ruwan a cikin jikinta.

Kuka sosai ya karimatu takeyi saboda ganin halin da ?anwar tata take ciki, bala'in haushin Nasir takeji danji take kamar ta sha?eshi ya sume tunda duk halin da Rashida ta shiga a sanadiyar sane, kwata kwata bai damu da rayuwar taba, dan da yadamu da ita to babu yadda za'ayi ya banzatar da ita har tsawon kwana biyar a asibiti amma sau Waya yazo, dan haka shiyasa koda ya juya tare da Wan rissinawa ya gaidata Wauke kai tayi tare dayi masa banza tace.

Karka kuskura ka ?ara buWe baki kace zaka gaisheni, dan maganar ka ma ?ara ?onamin rai takeyi, ai daman Rashida ita kaWaice take sonka kuma take damuwa dakai, gashi a sanadin haka har take neman rasa tata rayuwar, dan haka dalla tashi kafita ka bani waje, ko daman kaine ka kawota asibitin?

*Nasir*

Kansa a ?asa yakejin duka irin magan ganun da ya karimatu take jifansa dashi, babbar yaya ce a gare shi dan haka bazai iya kallon cikin idonta ma tana faWan ba bare har takai gaya saka mata baki, dan haka sai daya bari ta gama ya Wago yaWan kalleta yace.

"Ayi ha?uri yaya, Allah yabata lafiya, ni bara na wuce idan ta farko zan kirata a waya.

Wani irin kallo ya karimatu tabi Nasir dashi tace

"Waya kuma? Waya fa? Amma gaskiya bansan baka da mutunci kuma baka damu da rayuwar Rashida ba sai yau, amma babu komai ina son kuma ka tuna kai ubane, kuma ?a?a mata gareka, dan haka kaje Allah yatashe mu lafiya.

Ran Nasir yaWan sosu da take cewa wai ?a?a mata garesa? Ai baya fatan ?a?an sa su Wauko banzan hali irin na Rashida duk da dai itace uwar su, madadin ya nuna mata Sacin ransa sai kawai ya buWe ?ofar ya fita yana jin jikinsa na ?ara nauyi da halin da yaga Rashida.

Yana fita gida ya nufa domin cikinsa banda kiran curoma babu Abinda yake yi, daman ya sani ya faWa a ransa yana buWe kulolin da yagani a kan dining, Maryam ya kalla wacce ke jifansa da murmushi tana niyar tashi yayi saurin ?arasowa ya dafa kafaWarta yace ta zauna zai zubawa kansa yaci, Maryam na kallon sa har gama ci dan a jikinta takejin akwai Abinda yake damun zuciyar sa kodan yanayin da gangar jikinsa take nunawa.

Bata tanka masa ba har sai daya shiga banWaki yayi wanka ya fito ya shirya barci san nan tace masa

"Naga kamar kana cikin damuwa ko? Meke faruwa? Ko jikin maman su halima ne?

Girgiza kai Nasir yayi yace

"A'a kawai dai inajin Wan ciwon kai ne da zazzaSi, ita kuma jikinta da sau?i dan dagacen nake, kuma har naje na tawoma barci takeyi.

?aga kai Maryam tayi tana jinjina ?udura irin ta Ubangiji san nan tace

"Allah ya?ara mata lafiya.

Da Amin Nasir ya amsa san nan yajata jikinsa domin suyi barci.

Maryam tana kwance ne kawai amma tunanin halin da Rashida ke ciki yana saka ta kasa sukuni, bataso haka ba, a rayuwa babu macen da zataso ace tana rayuwa kuma babu mahaifa bayan hakan ita ba babbar mace ba bare tace daman ta haifa da yawa sun isheta, hawaye Maryam ta share tanawa Rashida addu'ar Allah yaba ikon cinye jarrabawar da Allah ya Wora mata, hardai ai itace silar Abinda Ya sameta, daman hausawa suna cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere domin baka saniba ko kai zaka rufta ciki, to gashi ita dai Rashida ta ginashi da zurfi kuma ?arshe itace ta afka ciki.

*Waiwaye*

Irin jinin da Rashida ta dunga zubarwa guda guda ne ya tsorata likitoci, gashi duk wata hanya da zasubi wajen ganin jinin ya tsaya amma sam abin yaci tura, dan haka take suka shiga da ita binciken gaggawa a nan sukaga cewar mahaifar tace ta ruSe shine taketa zubda jini, kuma sunga cewar muddin ba'ayi saurin cire mahaifar tataba to tabbas jininta ne zai ?are ta mutu.

Babu wani dake a wajen Rashida a asibitin gashi sun mata Allurar barci amma duk da haka jinin kuma SulSula yakeyi, hakan yasa likitan yanemi wayarta domin ya duba number daya dace a kira, ai kuwa cikin sa'a daya duba number sai yaga number an saka my One.

Da sauri likita ya danna kiran dan babu password akan wayar tata, haka yayita kiran wayar ba'a Waga ba, ha?ura yayi ya ajiye yana mamakin wan nan wane irin miji ne wanda bai damu da rayuwar matarsa ba, ganin ya kuma kira ya?i Wagawa kawai sai ya kwafi number tasa akan wayar sa, bai kirasa a lokacin ba sai da yabada ?an muntuna san nan yakira Nasir Win.

Ringing Waya biyu Nasir ya Waga wayar da magagin barci a cikin muryar sa yace

"Salamu alaikum.

Cikin rashin jin daWi likitan yace

"Wa'alaikassalam, san nan yatafi maganar kai tsaye yace

"Daman matarka Rashida ce take cikin wani mawuyacin hali, nine likitan da nake dubata, dan haka tana da bu?atar a saka hannu nan take za'ayi mata emergency tiyata.

A kwance Nasir yake amma sai da ya mike tare da zaro ido yace

"Emergency tiyata kuma? Akan me? Ban fahimta ba kayi min bayani likita.

"Yin bayani a waya bazai yiwu ba Alhaji, akwai bu?atar kazo kafin nan da minti Ashirin idan ba haka ba zaka iya rasata.

?it likitan ya kashe wayar dan baiga amfanin cigaba da tattaunawa da Nasir ba alhalin ya faWa masa dalilin kiran nasa.

A wajen Nasir kuwa da azama ya mi?e yana zura jallabiya ya zari mukullin mota ya fita, ta kichen yabi domin acen ne yaji motsi da kuma ?ar magana ?asa ?asa alamar akwai mutane a ciki.

Su Maryam yagani sunata faman aikin suyar kaji duka gidan ya Wumame da ?amshi, murmushi yayi duk da baya hayyacin sa yace

"Haba Maryam, kidunga hutawa fa, ?arfe har wajen Waya na dare kina tsaye alhalin kinsan bakida da lafiya.

Itama Maryam Win murmushi tayi tana Wan tallafe ?asan cikinta da taji Wan cikin ta yayo ?asa ya tokare mata mara yana sokawa, sai data Wanji ya koma dai-dai san nan tace

"Naji sau?i fa yaya, kuma wan nan aikin ai yayiwa kulu yawa dole sai na saka hannu ga kuma gyaran kayan miya duka dana sauran aikin ai kaga kuwa dole na tayata muyi tare.

GyaWa kai Nasir yayi yace

"Gaskiya ne ?ar aljanna, amma idan kuka gama suyar kajin ku bar aikin haka ku kwanta kwa ?arasa da safe in Allah yakaimu.

?an takawa gaba Maryam tayi tana buWe deep prezer Winta tace le?o ka gani, ai mun gama komai suyar kajince kawai ta rage.

Cikin jin daWin ganin Maryam ta gyare kayan miyan ta markaWe ta dafe su ta saka a cikin fridge ya kalleta yana dariyar yace

"Allah yayi miki albarka Maryam, nagode miki da komai ma na alkairin da kike min, Allah ya saukeki lafiya kinji matata, ya ?arasa tare dayi mata kiss a goshi yana shafa cikinta, da sauri ta kalli inda kulu take sai taga bamasu take kallo ba hankalinta yatafi kan kajin dake cikin mai tana kwashewa saboda sun soyu.

Juyawa yayi zai fita san nan yace

"Rashida babu Lafiya an kaita asibiti Maryam, wai naje ana bu?atata da gaggawa shine zan tafi.

Da sauri Maryam ta kalleshi tana cewa

"Subhanallahi, tun yaushe? Allah yabata lafiya yasa kaffara ne, dan Allah ka gaisheta kuma kayi tuki a sannu saboda dare, Allah yakaika lafiya ya dawo dakai lafiya.

Da Amin ya amsa yana fita yanajin yadda nauyin ?irjinsa ke raguwa saboda addu'ar da Maryam tayi masa.

Yana isa asibitin likita ya zayyane masa halin da Rashida ke ciki da kuma bu?atar da ake nema a wajensa ta saka hannu, takardar yake kallo kamar mai koyo karatu dan kansa baki Waya a Waure yake.

Cire mahaifa? A dalilin me? Yaushe har Rashida tayi fama da ciwon da mahaifar ta zata lalace bai saniba? Sai kuma ya girgiza kai yace.

A'a toko dai hatsarin da tayine ya daki mahifar ta samu matsala? Ganin babu mai bashi amsa ya nemi waje ya zauna ya zurafafa a cikin tunani, taya zai saka hannu a cirewa Rashida mahaifa? Akan me? Sai ya kuma girgiza kai yana Wauko wayarsa a cikin aljihun sa ya kira ya Aminu dan koma menene bazaiyi shi kaWai ba yana bu?atar mai Worashi akan hanya.

*****

*Ya Aminu*

Yana tafe yana tunanin Abinda ya samu Rashida a tsohon daren nan har da mijinta zai kirashi, runtse ido yayi yana addu'ar Allah yasa koma menene yazo musu da sau?i.

Shi kansa ya Aminu da likitan ya gama zayyana masa jawaban sai ya buga ta gumi yana tunanin bazai yarda a haWa kai dashi a saka hannu a cirewa Rashida mahaifa ba, sai ya mike yacewa su Nasir yana zuwa.

Direct gidan hajja ya nufa yanata tunani, bai damu da daren dake kuma tsalawa ba kawai ya danna kai cikin gidan yana mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login