Showing 72001 words to 75000 words out of 175193 words

Chapter 25 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

561

tabbas tasan a ibadar su akwai gyara, shikansa karatun Alkur'anin ba wani kwarewa sukayi ba, gashi daman makarantar islamiyyar ta bokon su sukeyi bawani fahimtar karatun suke sosai ba tunda kwakwalwa ba hutu take samuba tunda anyini sur a makaranta, to babu hutu mana, da safe an shiga karatun boko an tashi da azahar, ana idar da sallar azahar kuma akaci abinci sai kuma a shiga islamiyya, ita dai gaskiya zata saka Nasir ya cire su daga islamiyyar a dawo dasu ta cikin unguwa wacce ake shiga ?arfe huWu, ai ko banza yaro ya huta, tunda idan yaro ya taso ?arfe biyu zaiyi hutun awaya Waya san nan yatafi ta islamiyya, wan nan shine ?udurin Maryam.

ko uwarsu Rashida zata yarda? Zadai mugani.

Karatun nasu taji taga duk akwai gyara a cikin sa, shiyasa ta saka musu awa Waya kullum da asuba zasuyi karatun kafin a koma makarantar.

Wan nan Abin da Maryam tayi yayi bala'in farantawa Nasir rai har yakejin muddin Rashida bazata zauna da Maryam lafiya ba to wallahi tsaf zai iya rabuwa da ita duk da yana sonta dan a ganin sa Maryam tafiye masa amfani fiye da Rashida.

*****

*Rashida*

Ta Wau wayarta ta kamo number Nasir yafi sau a ?irga, tanason ta kirasa ta bashi ha?uri, amma rashin sanin yadda zai Wauki lamarin yasa sai ta fasa, kumama daWin da Wawa batason ta zubar da mutuncinta da ?imarta a wajensa, ?ilama sai ya gayawa waccen jakar yace tana bikon sa, sai kawai takuma sakin tsaki tayar da wayar ta fice daga Wakin tana tunanin yadda zata tunkari hajja da zancen bata ha?uri.

Dan taga hajja tayi fushi sosai da ita, kuma ita ma daga baya bayan ta nutsu taga bai dace ace tayiwa hajja rashin Wa'a irin haka ba.

A wan nan sati na ukun tana shirin shiga sati na huWu a gidan duk safiyar Allah zataje ta gaida hajja, tana amsawa amma a dake kuma ko kallon ta batayi bare taga alamar canjin ?aryar data Worawa kanta wanda zai wahalar da ita, dan dakyar Rashida take iya danne azabarbiyar zuciyar ta tana tana pretending na ?arya Win.

A gaban Wakin hajja Rashida ta tsaya tana wasi wasin ta shiga kota juya, amma zuciyar ta sai tunkuWa ta takeyi akan ta shigan dan shigar tata shine zai sama mata masalaha.

A hankali kuwa ta hankaWa ?ofar ta shige da sallama a bakinta, a cen inda hajja ke sallah Rashida ta hangota tana azukar dan lokaci an idar da sallar la'asar, ?arasawa Rashida tayi kusa da hajja ta zaune acen gefenta tare da lankwashe ?afafu ta zauna kanta a ?asa.

*Hajja*

Kallo Waya tayiwa Rashida ta maida kanta akan littafin azkar Win ta cigaba dayi, hajja Allah yayita itama da ibada sosai, shiyasa koda babar Rashida tayi mata asirin barin gidan kasacin galaba tayi a wajen hajjan sai dai dole ta komawa Abban su Rashidan shi kuma asirin ya kama shi.

Shiyasa idan hajja tana zaune tana ibada kowaye zaizo wajenta sai dai ya jira ta dan bazata taSa tashi daga wajen ba sai ta kammala ibadar ta.

Hakan yasa sai da Rashida tayi zaman wajen awa Waya dan koda Hajja tagama azkar Win sai da taja carbin ta tayi lazuminta tagama tayi addu'a san nan ta shafa ta kalli Rashida wacce ta sake takejin kamar tatashi tatafi idan hajjan ta gama ta dawo, amma sai kawai ta daure dan hajjan ta kuma tabbatar da cewar Rashidan ta fara canzawa daga halinta na tsiya.

*Hajja*

Kallon Rashidan tayi tana mata addu'ar Allah ya shiryar da ita.

Rashida kuwa tana ganin hajja ta kalleta sai ta fashe da kuka ta matso zata faWa jikin hajjan.

Da sauri hajja ta dakatar da ita ta hanyar Waga mata hannu tace

"Tashi kifita, kifitar min aWaki ko ranki yai matu?ar Saci Rashida.

Hannu Rashida ta aza aka tana mai kurma ihun tashiga uku ta lalace ina zata saka kanta hajja tana fushi da ita.

Tsaki hajja tayi tare dayin bissimillah ta mi?e tana niyar fita itama Rashida ta mi?e tana kuka ta nufi hajja.

?afar hajja Rashida ta rike tana cewa.

"Dan girman Allah hajja kiyi ha?uri ki yafemin, dan manzan Allah kiyi min aikin gafara wallahi na tuba hajja.

Idan baki yafemin ba hajja zuciya ta zata iya bugawa saboda tashin hankali, dan Allah hajja ki yafemin kona samu haske a cikin rayuwar duniya ta.

Ganin jikin hajja ya fara sanyi yasa Rashida takuma ?an?ame hajja tana kuma cewa

"Ki yafemin Hajja, bani da kowa bani da komai sai ke a cikin Duniya, kece uwata kece ubana kece gatana hajja, dan girman Allah hajja ki yafemin karna cigaba da lalacewa, wallahi hajja bazan ?araba.

Ajiyar zuciya hajja tayi tare da juyowa ta tsugunna ta kamo kafaWar Rashida tace

"Ina sonki Rashida kamar yadda nake ?aunar ?a?an dana haifa da cikina, haifarki ne kawai banyi ba Rashida amma nonona kikasha kika ginu har kika rayu, ban taSai miki kallon banice na tsugunna na haifeki ba Rashida, amma da banason ki Rashida wallahi da bazan kar Seki ba har na shayar dake, dazan bawa dangin babar ki ke su tafi dake cen garin ku su raineki Rashida, amma ke ?atace dan haka yasa na hanasu na ri?eki kamar wacce nayi ba?uda na haifa nake jinki Rashida.

"Na yafe miki Rashida kuma Allah ya yafe mana baki Waya, kedai ki kasance yarinya ta gari a cikin al-umma Rashida domin ba'a cewa mutum gaskiyar sa ta ?are sai dai ace ?aryar sa ta ?are Rashida, dan haka kije Wakinki ki huta nima inason hutune dan kaina ciwo yakeyi min.

A take Rashida taita godiya kuma ta rikice da ciwon kan hajja, nan take kuwa ta shiga haWa mata magun guna dan tasha kota samu sau?i.

Zama hajja tayi akan Waya daga cikin kujerun Wakin tana kallon yadda Rashida take rawar jiki, sai da Rashida ta kawo mata magun gunan san nan ta tsugunna tacewa hajja Allah ya?ara afuwa.

?aga kai kawai hajja tayi san nan Rashida tafice tare da rufe mata ?ofar Wakin.

*Hajja*

Kwantar da kanta tayi asaman kujerar tana sauke numfashi, ha?i?a Rashida abin tausayi ce, yarinyar batayi sa'ar uwar data haifeta ba, kuma har ga Allah ta Wauki Rashida ne ta shayar da ita dan batason ta Wauko halayar iyayenta dan zasu cutar da ita muddin taba data suka tafi da ita agadez, tasan yarinyar zata taso cikin jahilci da matsin talauci domin iyayen Rashida marigayiya basu da komai mugayen fa?irai ne, tasan kuma komai zasu kaiwa Rashida na kuWi ko jin daWi bazasu bata ba dan gaba Wayansu san zuciya ne dasu, daWin da Wawa ma batasan irin rayuwar da Rashida zatayi a hannun su ba, batason taga rayuwar ta ta tozarta kota jirkita tasha banban data ?an uwanta shiyasa ta dage sai data karSe ta.

A lokacin data biye magan ganun ?an uwan Rashida marigayiya da kuma zagin tsamar naman da suka dungayi mata da zuciya zatayi ta wulla musu ?ar su kuma ta yanke duka wata ala?a a tsakanin su tunda daman bawai zaman daWi sukayi da uwarta ba balle tace zata dunga tuna Alkairin ta.

Amma haka ta daure ta Waura Wamara ta hanasu Rashida dan ko ranar da zasu tafi garin nasu bayan an share makokin Rashidan sai da sukayi faWa da yayar Rashidan, haka ta dunga zaginta da buzanci tana han?arowa wai zata daketa, sai da kyar ?an uwansu maza suka hanata suka turata a mota suka bar gidan.

Kuma ko bayan nan sai da yayar tata ta kuma da wowa gidan, amma wan nan karen ba zuwa tayi ta karSi Rashida ba, tazo ne da fuskar salihai san nan tatawo da wata budurwar ?ar ta mai bala'in kyau tamkar aljanna, wai dan Allah ta zauna a gidan ta runga tayata aiki da kula da Rashida, a wan nan lokacin ran hajja yayi matu?ar Saci.

Hakan yasa ta kalleta tace

"Ashe bakida hankali ban saniba? Wato ni zaki rainawa hankali ko? Kije ki dafo ki wanko ?arki da asiri da tsafi ki kawo min ita wai ta zauna a gidana ko? Daga nan sai kuma ku kuma zamewa ku aurawa mijina ita sai kuma ku samu kafar kasheni ku tattaro ku dawo gidana ku mulkemin gida ko? To baki isa ba, dan haka maza kitashi kifice min a gida keda wan nan aljanar ?ar taki tunkan na wula?anta ku.

Baran baran dai aka rabu suka tafi suna tsinewa hajja da buzanci dan ita ?ar tatama ko hausa bataji sai buzanci.

Shikkenan tun daga ranar babu wanda ya kuma zuwa a cikin ?an uwar babar Rashida domin ganinta ko wani Abin, amma bayan Rashida ta fara wayau Abban su na sakawa a kaita wajen su ta gansu su gaisa, duk da batasan waye suba sai data girma san nan ta fahimci komai.


*Rashida*

Tana shiga Waki ta daka tsalle tace

"Yess, na gama da matsalar hajja saura kai da matar ka Nasir.

Daman fushin hajja ne babbar matsala ta dan Nasir da kuma Rashida bata Waukesu matsayin matsala ba.

Sai kawai ta Waga waya ta turawa Amina Wan gajeren sa?o mai ?unshe da ma'anoni da yawa.

*****

Wasa wasa saida rashida kwashi tsawon sati shida a gida batare da Nasir ya waiwayeta ba, bazai ce ya manta da ita ba Saboda kodan yaranta dake gilmawa a gabansa dole ya tuna da uwarsu, amma har ga Allah yasan yanzu yadda yakejin Rashida ba kamar yadda yakejin ta da a cikin zuciyar sa bane, kuma a kullum idan ya tuna da Rashida zata dawo sai yaji gabansa ya faWi saboda yasan Rashida tana saka ?afa cikin gidan nan tofa tashin hankali da balbalin bala'i ya dawo, shiyasa ko yana ayyanawa yaje bikonta sai ya watsar da zancen dan bayason tashin hankali a sanda hankalin ya fara dulmiya da kwanciya.

Amma kuma dole ne yayi bikon Rashida kodan yaranta da yake tausaya musu rashin ta, kuma badan basajin daWin zama da Maryam ba tunda har taya sauda ma ta sauya ta canza halinta saboda jajircewar Maryam a cikin gidan.

Yau talata kuma yau ne Nasir Win yayi niyar yaje bikon Rashida kafin daga baya ya Wauki Maryam yakaita ta gaisa da hajjan, sai kawai wata zuciyar tasa tace masa

"Meyasa bazaka tafi da Maryam Win yau kuje bikon tare ba, itama Rashidan ai ita taje bikon Maryam sanda bata gidan, da wan nan ?udurin yatashi a ransa.

Koda suka gama karyawa yana shirin fita sai ya kalli Maryam wacce tayi fari sosai ga wasu kumatuka data ajiye, shi gaya canje canje kala kala a wajenta amma baiyi tunanin komai ba sai jin daWi da kwanciyar hankalin data samu, dan shi yasan ko nutsuwar da yake bata a gado ya isa yasa ta ajiye teSSa, dan ma dai ya lura Maryam bata da jikin ?iba sai dai ta murmure ta zama ita ba siririya ba kuma ita bamai ?iba ba.

Murmushi yayi yana zama kusa da ita tare da kamo hannunta yace.

Maryam akwai maganar da nakeso nayi dake, magana ce wacce kinsha yimin ita amma nake kauda kai saboda lokacin tattauna ta baiyi tukunna.

Dan haka yanzu da lokacin ta yayi zamu tattaunata.

Inason yau ki rakani gidan su Rashida muyi bikonta.

*Maryam*

Wani irin rarass taji ?irjinta ya buga a take kuma zuciyar ta tayi tsalle kamar zata fito ta bakinta, da sauri ta runtse idanunta tana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'una a cikin ranta, kallonsa kawai take bata ce komai ba har sai da tasamu nutsuwa san nan ta sauke a jiyar zuciya mai haWe da gajiya tace.

"Alhamdulillahi, ai hakan yana da kyau, san nan wan nan shine matakin daya kamata ka Wauka tun bata daWe da tafiya ba, naji daWin wan nan maganar Allah yasa kuma tadawo mana da Alkairi mai cike da yalwa.

Hannunta Nasir ya kuma ?an?amewa yace Amin zumata, san nan ya rungume ta a cikin jikinsa ganin ta saka kuka marar sauti.

Shafa bayanta ya dungayi yana kwantar mata da hankali domin yasan ba komai takewa kuka ba sai rahin kwanciyar hankalin dazai Sallo sabo a Cikin gidan da zarar Rashida ta dawo gidan, shi kansa zuciyar sa a cun kushe take da dawowar tata domin yasan tana dawowa zata azzaba masa masifa yadda zaiyi Wan uwa ya furgice duk inda yayi a dunga nunashi da leSe.


*KUTSE*

?? *PAGE 30*

? ?? *NA*

*MOM HANEEF*

? *ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Gabanta ne kawai yake faWuwa ganin Nasir ya tsaya a ?ofar wani taf keken gida yana buga harm, sai da wajen sakan biyar ta wuce san nan mai gadin ya le?o dan yaga waye, ai kuwa yana ganin motar Nasir ya buWe baki yana dariya dan yasan yau aljihun sa zai cika da ?an sulalla, yana buWewa Nasir ya danna hancin motar cikin gidan.

Ai Maryam batasan sanda ta kware ba sai uban tari data dunga tuttulawa ganin han gamemen gidan da suka shigo kuma wai gidan su Rashida ne, sannu Nasir da halima suka dunga yi mata ita kuwa sauda burinta kawai yayi parking ta afa cikin gidan wajen mamanta.

Maryam bata kuma sarewa ba sai da ta fara kalle kallen ?aya tattun abubuwan da bata taSa ganiba a gidan su Rashida, a ranta take cewa.

"Gaskiya ne, shiyasa Rashida take Wiga rashin mutunci da ciwa mutane mutunci ashe ?ar gidan ji?a??un masu kuWi ce haka, shiyasa take taka duk wanda takeso har mijin ma bata kyaleba.

Ita dai Maryam batasan anzo wajen shiga faloba sai da taji Nasir yana wa sauda magana akan ta daina gudun nan karta faWi, shine ta kalli inda saudan take, wata zabgegiyar ?ofar glass ce mai bala'in tsawo da faWi, kuma glass Win irin glass Win nan ne dako bindiga bata Sulashi bare hannu ya fasa duk kuwa da irin jibgar da za'ayi mata.

Ba iyaka ?ofar glass Win ba, duka ?ofofin gidan bullet proof ce.

Ganin Nasir ya saka hannu ya zuge ?ofar glass Win yasa Maryam ta saisaita nutsuwar ta dan karta shiga tana kalle kalle ta bada kanta.

Koda suka shiga faWeWen falon baki Maryam ta saki dan gaskiya bazatayi ?arya ba bata taSa ganin gida da irin wannan falon ba a rayuwar ta, bazatace bata ganin gidajen masu kuWi ba a gari amma a gaskiyar lamari bata taSa shiga gida irin wannan ba, shima kuma gidan Nasir da kyansa sosai amma wan nan yayi million Winshi a kyau da tsaruwa da girma, dan haka a ranta tace

"Wallahi sai na kalla gaskiya, dole na bawa idanuwa na ha??insu tunda sun gano sabon abu, kalle kallenta taitayi har taga sun dan gana da wata ?ofa itama ?atuwa zasu shiga.

Shima ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????falone babban gaske amma bai kai na farko girma ba, shima kuma koda suka shiga a cikin falon a kwai wasu ?ofofi guda huWu wacce bazata ce na meye ba bare ta faWesu, amma sai taga sun nufi ta ?arshe wacce ke cen Sarin dama, nan ma wata ?ofar suka tarar sai da Nasir ya saka hannu ya matsa wani abin acen ?eyar ?ofar yayi ?ararrawa, mamaki ne ya isheni dan idan ba sanin wajen da abin yake kaiba bazaka taSa cewar a kwai shi a wajen ba tunda babu tudun shi ko kaWan a wajen kawai dai danna wajen ake.

Muna tsaye inata mamakin da nasaki baki sai kawai naga ?ofa ita kaWai ta zuge kanta batare da wani ya kuma taSata ba, kallona Nasir yayi yana min murmushi sai yaja hannuna muka shiga falon.

Wallahi Saboda kayan alatun dana gani da muka shiga wan nan ?ofar sam sai na manta da wai wajen Rashida mukaje ji nake ma mafarki nakeyi, sai da muka wuce wasu corridor guda biyu san nan muka zo gaban wata ?ofa itama ta glass muka tsaya wajen Nasir ya saka hannu ya zuge san nan muka shiga.

Shima falone ?ato na musamman kamar yadda naga kayan dake cikinsa shima na musamman ne dan haka nayi tunanin a raina munzo ai nahin cikin gidan kenan.

*Rashida*

Tunda garin Allah ya waye take tsintar kanta da faWuwar gaba, batasan kota menene ba amma tabbas tasan tanada na saba da Nasir da yaranta tunda tun safen tunanin ta bai kau daga kansu ba, yau Win nan kwakkwaran abinci bata samu taciba saboda fargaba.

Wata iriyar wawar ajiyar zuciya Rashida ta saki a lokacin data hango sauda agaban Nasir shi kuma yana bayansu tsaye kansa a ?asa yana maida waya aljihun sa, wata iriyar rawar jiki ce ta kama ta sanda ta hango Maryam tsaye a bayan nasir tana rarraba idanuwa kamar Sera a buta , wani irin malolon Sakin cikine yafara taso mata tun daga cikinta har zuwa ma?ogaronta yafara mata wani irin ma?a?i da yaji yaji.

Ji tayi tamkar tatashi ta sha?i wuyan Maryam ta aikata lahira saboda yadda takejin tsananin tsanarta a cikin zuciyar ta jini da Sargonta, da sauri ta Waga kanta sama lokacin dataji wasu ruwan hawaye sun kwaronyo mata zasu zubo tayi saurin mai dasu tana ?i??ifta idanuwa.

?ara sowar su Nasir cikin falon yasa nusaiba autar hajja tayi saurin mi?ewa daga kan jurar da take zaune tana murmushi tare da kama hannun halima tana faWin welcome da mamana, ita kuwa sauda kan uwarta ta nufa da niyar ta hau jikinta amma tayi saurin tare ta tare da tashi tana murmushin ya?e ta isa gaban Maryam.

Tana isa wajen ta ta rungume ta tare da saka kuka mai sauti wanda hajja tayi saurin kallonta tana "A'a menene haka Rashida?

Lafiya kuwa?

Kuka sosai Rashida takeyi a jikin Maryam wacce tayi suman tsaye zuciyar ta take dokawa da ?arfin gaske dan makircin Rashida babu kalar da bata nuna mataba kuma tasanshi sai wanda ta halitto sabo, kuma tana ganin ko sabon ta halitto tana ganin ta zata gane Abinda take nufi.

Tsaye kowa yayi cirko cirko suna kallon dramar Rashida, shidai nasir da yake yasan wan nan Abinda Rashida take duk pretending ne sai kawai abin yake bashi dariya haWi da mamaki na makircin Rashida, amma hajja da nusaiba har ?a?anta wani tausayin ta yake tsirga musu sunajin koma menene yafaru kukan ya isa haka.

Ita kuwa Maryam Rashida na faWawa jikinta tayi saurin runtse ido tanajin kamar ta WoWana mata wutane a cikin jikinta, tayi iya dauriyar ta dan ta barta ta cigaba da rungumar ta Abin yaci tura dan ji take sosai zafin wutar Rashida take shiga jikinta, idanunta ta buWe wanda sukayi jajawur ta saka hannu da ?arfin gaske tare da SanSare Rashida daga jikinta san nan ta hankaWa ta baya tayi taga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login