Showing 6001 words to 9000 words out of 175193 words

Chapter 3 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

528

ko?

Taya zan kawo yarinya gidan nan ki dunga wulak'anta ta Alhalin nace miki k'anwata ce, to ko kare nakawo gidan nan idan har kina sona da mutuntani ai kamata yayi ki karramashi ballata mutum, mutum mace kamar Maryam mai kawaici, tunda tazo gidan nan kinga wani hali nata dabai miki ba?

Amma ke tunda tazo gidan nan kink'i kula da ita kink'i bata masauki kin ki sakar mata, wan nan wane irin rashin tunani ne, idan nayi magana kice kinaso na kina kishina, haka akeyin kishi? Ai kishi bai kamata ga wani bak'oba, sai ki bare idan Abin kishin yazo sai kiyi, dan haka kibari kawai nasha ruwana, k'ark'ari nasha wahala ko kuma yayi ajalina, sai yayi saurin fuzge hannunsa yana kai ruwan bakinshi.

Da sauri Rashida ta kwace ruwan daga hannunsa tare da wullarwa ta rungume shi tana fashewa da kuka, shima hannu yasa ya rungumetan yana shafa gadon bayanta.

*****

Wan nan shine farkon fara sakewa da kuma watayawa da maryam ta samu a wan nan gida, kuma wan nan shine farkon tarin matsaltsalun dazasu wargaza gidan da kuma mayar dashi wani fukai mai cike da wawakeken rami daya ginu a cikin zuciyar nasir, wanda daya san hakan zata faru kota kasance kuma akan macen daya bawa amana yabawa soyayya da duka zuciyar sa dabai tab'a kuskuren bawa Rashida duka zuciyar sa data yarda da kasantuwar Maryam acikin gidansa ba.

******

" A zaune suke baki d'ayan su suna kallo suna hira da dariya Abin sha'awa, Rashida ta kalli Maryam fuskarta da murmushi tace "Maryam jeki d'aukowa sadiya jakar makarantar tak'arasa homework d'in ta, da to Maryam ta amsa ta mike ta shige d'akin su Halima tana neman jekar makarantar tata, ta duba ko ina bata ganta ba hakan yasa tafito tace

"Banga jakar taki ba sadiya, a ina kika ajiye? Murgud'a mata baki sadiya tayi tace "nima ai ban ganta ba kije ki kuma dubawa, tsawa Nasir yadakawa sadiya yace.

"Bance kidainawa babba rashin kunya ba? Da sauri sadiya ta matsa kusa da Rashida tace mamana, kallon Nasir Rashida tayi da irin katakurawa yarinya ta tace "tunda tace bata gantaba ba shikkenan nan ba, menene Kuma na hantarar?

K'in magana Nasir yayi saboda baisan mai zaice ba dan Rashida tana shayar dashi ruwan mamaki akan yaransu, kallon Maryam yayi da kallon kina hak'uri yace.

"Muje muga ina ta saka jakar, kema idan naganta saina cuwad'a miki jikin ki, da sauri Maryam ta shige tana murmushi shima ya rufa mata baya.

Suna shiga Nasir ya rik'o hannun Maryam tare da nanata a cikin jikinsa ya rungume ta tsam, mutsu-mutsu Maryam tafara tanason kwace jikinta amma yak'i bata wan nan damar, ganin haka yasa ta bud'e baki zata kwala masa ihu yayi saurin toshe bakinsa danata yana sakar mata sumba mai tayar da tsikar jiki.

Jikin Maryam ne yafara rawa kamar mazari tanason kwace kanta Amma tanajin wani magana d'isu na fusgarta zuwa gareshi.

Jin bugun k'ofar d'akin da akeyi yasa futsari yafara kufcewa Maryam suna daga tsaye, da sauri Nasir ya saki Maryam saboda shima bugun ya kid'imashi yayi saurin juyawa tare da d'an ture maryam gefe ya bud'e d'akin a hankali kansa a k'asa.

Ganin Halima ne yasa yasaki wata zazzafar ajiyar zuciya yace

"Halima"

Bakinta washe tace "wai anga jakar a d'akin mama.

Ina maman naku? Nasir yafad'a a d'an tsorace.

Kallon bayanta tayi tace " ta shiga d'akin ta salla shine tace nazo na gaya maka.

Wata ajiyar zuciya Nasir ya sauke, bama shi kad'ai ba hattaya Maryam sai da ta zubar da kwallar jin dad'in kub'uta.

Shafa kan Halima Nasir yayi yace "to maza jeki taya sadiya homework d'in bara nima nayi sallar.

Yana juyowa yaga Maryam na kakkarwa kamar an tsunduma ta a cikin ruwan sanyi, da sauri ya kamata tare da jinginar da ita ajikin bango yafara shasshafata, har lokacin jikinta bai bar rawaba hakama Nasir baibar shafata ba, sai da ya latseta san ransa ya bar mata wasu tabbuna masu wuyar goguwa a cikin kwakwalwa da gangar jiki.


Sosai Maryam kejin kunyar Nasir tun satin baya daya lallatseta a d'akin su Halima, Abin yak'i barin kanta haka kuma take yawan jin gangar jikinta nason ta kuma jin Nasir a cikin jikinta yana mata wan nan Abin, shiyasa muddin yana waje da wuya kaganta a zaune, ko gaishe zatayi takan tsinci kanta da kasa koda kallon fsukarsa ne ballantana cikin idanuwan sa.

Yauma kamar wancen karan haka Nasir yaso shan mintinsa da Maryam batare da Rashida ta ankara ba, amma sai hakan bai faruba, domin Maryam tana tsaye wajen igiya tana shanya kayan su Halima data wanke Nasir ya risketa a wajen, da sauri ya kamota yana shinshina wuyanta ita kuma tayi saurin zillewa zata gudu, ruwan dake tsiyaya ajikin kayan shine yasa santsi ya kwasheta tatafi luuuu zata fad'i, da sauri Nasir yayi kanta zai kamota Rashida wacce zuwanta wajen kenan tayi sauri rik'e hannunsa bai samu Nasarar rik'e Maryam ba har sai data fad'i.

Wata iriyar k'ara ta saka wacce ta nusar dasu cewar ta fad'i d'in, da sauri sukayo kanta suna kiran sunanta suna kallon hannunta data rik'e tana runtse idanu Alamar ta samu matsala a jikinsa, da sauri Nasir yakai hannu zai rik'e hannun nata Rashida tayi saurin rik'e hannun tana wurga masa wani mugun kallo mai tattare da ma'anoni kala kala.

***

Sannu sannun da Rashida keta zabgawa Maryam yana k'ara k'ular da ita, akan idanunta fa tafad'i saboda son zuciyar ta wai kar mijinta ya tab'ata, wan nan wane irin kishine mai kuntar da notukan Kai? Sannu, Rashida tak'ara fad'a tana kallon yadda Maryam ke matsar hawayen gyaran targad'en dataji.

Ita kanta tasan cewar bata kyauta ba, kuma har a ranta taji bata kyautaba akan Abinda tayi wa Maryam d'in, amma ya zatayi? Ta yaya zata canza kanta da zuciyar ta dake bijiro da rashin kirki da rashin imani a duk sanda taga wata na k'ok'arin yi mata kutse a wajen mijinta.

A ganinta ko zatayiwa kowa banda Maryam, Maryam yarinya mai biyayya da sanin yakamata, tunda suka samu dai-dai to take mata biyayya iya yinta da kuma gudun fushinta, bata k'aunar wani Abinda zai tab'a ranta musamman akan yaranta, Eh! Tabbas tasan cewar sadiya bata kyautatawa Maryam,.tanayi mata rashin kunya ta hantareta ta gwaleta idan zata yi mata Abu.

Amma saboda ita mai kawaici ce dasanin ya kamata bata ko d'aga kai ta kalla, bazata manta ba akwai wata rana da sadiya ke wasa da wuta tana dad'e da leda, tayi yafi sau nawa tana samun sa'a a wan nan karan sai aka samu akasi, tana d'od'ano wutar ledar na tsiyaya zata zuba akan k'afar sadiyan, da sauri Maryam dake wajen tana kallon yadda take k'iriniya tana mata maganar ta bari tayi saurin saka tata k'afar ledar ta d'isa akan k'afar, tasan da zafi kuma itama Maryam d'in taji zafi amma haka ta daurewa ciwon har sai daya warke tana jin rad'ad'insa.

Cikin d'an tausayawa Maryam da Kuma d'an rusunar da zuciya Rashida taji sai kawai ta tsinci kanta dacewa Maryam.

"Kiyi hak'uri Maryam"

D'aga kai Maryam tayi tana murmushin yak'e tace "akan me fa?

D'an runtse ido Rashida tayi ta bud'e tace " akan wan nan Abin kuma akan komai ma.

Girgiza kai Maryam tayi tana murmushin gefen baki tace "babu komai ai tsautsayi ne.

Da sauri Rashida ta mike ta shige d'akinta tana jin wani nauyi nason ya danne zuciyar ta, nauyi ne takeji kamar najin haushin Maryam ko kuma na tausayinta ne ita dai takasa ganewa.

Maryam na ganin Rashida tatashi tabawa hawayen dake shirin zubar mata taketa dannewa damar zuba, haka tabawa hawayen dama yayi ta zuba kamar an b'ula pure water duk yajik'a mata gaban riga.

Sai datayi mai isarta san nan ta gode ta kuma godewa Allah dayasa rayuwar aurenta tafara da k'alubale masu tarin yawa irin haka, kanta ta d'aga sama tana kallon silin tare da fad'awa tunanin rayuwar ta har zuwa aurenta da Nasir yayi.


PLEASE COMMENTS AND SHARE.
KUTSE

PAGE 5

NA

MOM HANEEF

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Wai waye

Wai waye yakasance babban adone a cikin kowacce irin tafiya,
A cikin rayuwar ko wane bawa, akwai k'addara mai kyau ko akasinta da aka rubuta tun farkon zane tafaru dashi, haka wasu akasin da wahalhalun dasuke faruwa damu ko Shirin faruwa damu da munsan suna zuwa da zamu nemi tsari mai nisa tsakanin mu da faruwar su, haka da munsan suna zuwa da bazamuyi kuskuren da zata fad'a kanmu har tashafi makusantan mu wad'anda basuji ba basu ganiba a duk nisan tafiya.


Ni maryam haifaffiyar 'yar daura ce, nice 'ya ta biyu a wajen mahaifiya ta da kuma mahaifina, ina da yaya namiji wanda shine farkon had'uwata da Nasir, Nasir abokin yaya nane wanda tun tasowata tare na sansu kuma nake ganinsu, tunda iyayena suka haifi yayana jafar basu k'ara samun haihuwa ba har shekaru masu d'an nisa sukaja san nan Allah ya basu kyautata.

Na taso naga iyayen Nasir da kuma iyayena suna zumunci sosai a tsakanin su, takai takawo wata rana wajen kwana baya rabasu har lokacin dana daina ganinsa, na daina ganin Nasir ne sanadiyar ya koma kano domin karatun gaba da secondary wanda zamansa ya koma gidan abokin babansa.

Rayuwa ta tataso cikin sa'a da nasara, Allah yayi min wata baiwa ta farin jini wacce a duk sa'anina da muka taso babu wacce tasamu wan nan Alfarmar sai ni, idan aka kace soyayya ko farin jini ba ana nufin soyayyar samari kota maza kawai ba, ta had'a da soyayyar mutane 'yan uwa da malamai da kuma iyayen kansu, to tabbas Allah yabani wan nan farin jinin, kuma wan nan Alfarmar farin jinin ta samo a saline da irin halayyata wacce ake dan gantata data gari kamar yadda mahaifiya ta itama ta samu wan nan shaidar.

Allah ya azurtani da hak'uri, biyayya, kawaici, nutsuwa da kuma maida sharri izuwa alkairi da kyautatawa, ni kaina nasan a kwai abubuwa da yawa wanda saboda kawaici na suke zama cutarwa a gareni, amma hakan bai fiya damuwata ba na kanyi murmushi na juya baya da addu'a'oin Allah ya zab'a mafi alkairi a gareni.

****

Yau ranar juma'a kuma yau ce rana ta karshe wacce zan gama zana jarrabawar makarantar 'yan mata ta secondry, tunkan na k'arasa makarantar manema sukayi ta bazowa da sunan soyayya a gareni, wan nan dalilin yasa mahaifina yabani umarnin na fidda wanda nakeso domin ina gama makaranta aurar dani zaiyi.

Banyi musu ba na fidda guda d'aya wanda yafi kwanta min a rai, wan nan dalilin kuma shine ya hassala sauran masoyana daban zab'ab'a sukayi mummunar kalma a kaina.

Farkon fara matsaltsalun rayuwata kenan.

Ina fitowa daga makaranta nida k'awayena sunata tsokanata akan nice wacce za'a fara aurarwa nan da wata d'aya, farin cikine fal raina wanda nakejin kamar nafisu sa'ar rayuwa tunda zanyi aure after candy ba kuma dan inada fariya a zuciyata ba.

Muna tafe muna hira mukaci karo da yayana jafar yana tawowa domin ya d'aukeni dan dama munyi maganar zai d'auko ni yau Albarkacin candy danayi.

Ina shiga motar sa one dor naji muryar ya Nasir yana cewa

"Iyeeeh, ashe k'anwar tawa ta zama y'an mata.

Murmushi nayi ina gaidashi ya amsa da fara'a san nan muka fara tafiya, hannunsa ya saka ya karb'i takardar hannuna yana cewa "muga paper d'in exam d'in taku, mik'a masa nayi ina tunanin sauk'in kai irin na ya Nasir a gareni, sai da yagama karantawa san nan ya mik'omin Had'i da fad'in Allah yabada sa'a ya kawo babban sakamakon cigaba da karatu.

Da Amin na amsa shi kuma ya jafar yace "yo ai ta gama samun babban sakamonta, 'yar candy marriage cefa, aurenta wata d'aya ya rage a daura shi.

Murmushi naga ya Nasir yayi yace "kai Masha Allah, Ashe k'anwar tawa bata da nauyin jini, to Allah ya nuna mana lokacin.

Da Amin ya jafar ya amsa ni kuma na amsa a zuciyata ta san nan mukaci gaba da tafiya.

Rana bata k'arya

Yau takama asabar d'in daza'a d'aura arena, kuma yaune ranar daban iya manta taba a rayuwa ta saboda mummunar k'addarar data fad'awa masoyina wanda baifi minti goma a d'aura mana ba aure.

Shiru-shiru waliyan ango sa bayyana amma basu bayyana ba, haka akai ta kiran wayoyin su amma maganar d'aya ce idan an kira basa d'auka, wan nan Abin tashin hankali da yawa yake, gashi an tara mutane kowa so yake a d'aura auren ya juya nashi wuri.

Ya jafar na zaune yaji wayarsa na ringing, da sauri ya d'aga ganin babban yayan ango.

"Hello, Hello, yaketa fad'i amma saboda hayaniyar mutane bata barin shi yaji Abinda yake cewa, fitowa ya jafar yayi daga masallacin yana k'ara kiran hello san nan daga d'aya b'arin ya Jiyo hayaniya kamar ma harda koke koke.

Tun kafin ma yace kanzil tuni yayan ango dayaci kuka ya k'oshi yace.

"Jafar daman na kiraka ne na sanar maka Allah yayiwa sa'adu rasuwa yanzun nan, saboda haka a dakatar da d'aurin auren nan.

Mutuwar tsaye ya jafar yayi yana tunanin tashin hankalin dazan shiga idan wan nan magana ta riski kunnuwa na, bashida da yadda ya iya a haka ya koma masallacin ya sanar da baban mu shi kuma yasanar da liman akafara shelar rasuwar sa'adu angon Maryam, cikin tashin hankali kowa ya mimimke aka fara fita ana tafiya gidan su sa'adu.

Koda zancen mutuwar sa'adu yazo kunnena yanke jiki nayi na fad'i a sume wanda bani na farfad'o ba sai da nayi kwana biyu a gadon asibiti.

Nasha takaici nasha bak'in ciki haka nasha Alhinin mutuwar sa'adu dan kamar nima na bishi haka nakeji, da addu'a'r ta wakkali da banbakin iyayena da yayana mai sona hankalina yafara dawowa jikina har na fara iya cin abinci batare danaji d'acin saba ko rashin d'and'anon sa.

Komai yayi farko zaiyi karshe.

Wan nan ce ta faru dani bayan d'aukar watanni masu yawa da rasuwar sa'aduna, na samu dan gana sosai wanda har wasu mazan suka fara kawo caffa gareni domin aurena, haka wan nan karan ma nafitar da wanda nakeso batare da tunanin komaiba domin ya kwanta min arai sosai, shi kuma tunda aka saka ranar bikina dashi ya fara tsuromin da zantukan banza dason yatab'a jikina amma nak'i bashi damar hakan, bazan mantaba har akwai wata rana dayace zanje na gaida yayarsa yakaini wani gidan maza da sunan na bashi kaina yayi lalata dani.

A wan nan ranar ina komawa gida na tubure na burkicewa iyayena da cewar ni bazan aureshi ba domin badan Allah yake sona ba, babu irin lallab'anin da ba'ayi ba amma nakafe kai da fata ni bazan aureshi ba.

Bansan dai ya akayiba mai ya faru sai gashi ya aiko amsar kayan aurensa gidan mu, inason garba dan haka naji duk duniya tayi min d'aci amma na saka a raina cewar wan nan itace k'addara ta, shima garba da kyar na manta dashi a yayin da wani yafito min daniyar zai aureni.

Mutum kirkine usman hakan yasa tamu tazo d'aya dashi dan kwata kwata bamu fiye samun sab'ani dashi ba.

Haka shima aka saka ranata dashi har alokacin aure yazo aka fara Shirin biki gadan gadan, anyi komai na Al-adar bahaushe yayin da d'aurin aure ya rage kawai na zama mallakin Usman.

Ranar d'aurin aure.

Sai da aka tara jama'a mak'il san nan Usman ya aiko da cewar wai ya fasa aurena, k'urace ta tashi sosai akaita d'auki babu dad'i san nan k'urar fasa aurena ta lafa.

Wan nan karan ma nasha kuka kamar raina zaifita san nan na jawo wayata dake ta k'ara ana kira wacce ban kulataba sai yanzu na fara dubawa.

Wata gun dumemiyar fad'uwar gabace ta ziyarci k'irjina a lokacin danaga sunan garba ya fito b'aro-b'aro akan screen d'in, cikin mamaki nace

"Garba kuma?

Ban goge number garbaba dan har ga Allah ina son garba shiyasa na adana number sa saboda in dunga gani ina karantawa inajin dad'i.

Hannuna na rawa na d'aga wayar na saka a hansfree dan bazan iya karata a kunnena ba domin banida nutsuwar rik'eta

Garba

Wata mahaukaciyar dariya ya saka harda kyakyawa tawa yana cewa

"Maryam kenan, ke a zatonki kuma a tunanin ki zakici amanata kici bulus? To bara kiji, tun ranar da kika bujirewa aurena ni kuma naci alwashin saina tar watsa rayuwar ki naga bakin cikin da zaki k'unsa a duniyar ki, daman Usman banaki bane nawane.

Nine na turo usman saboda yashiga rayuwar ki ya lalata zuciyar ki san nan ya gudu ya barki, nine na shirya komai Maryam, da soyayyar da kawo komai na aure nine na shirya shi, haka nine nake da wuk'a da nama na d'aurin auren ki da usman kuma na yanka naman har jini yayi tsartuwa, kuma wallahi ki sani, muddin ina raye wallahi bazan tab'a barin kiyi aure ba har abada tunda kika yaudareni, dan haka kijirani a episode na gaba, bye-bye.

Yana fad'in hakan ya datse wayar batare daya bani daman cin mutuncin sa koyi masa Allah ya isa ba, atake wani zazzafan zazzab'i yayi awon gaba dani saboda furgici da tashin hankalin da garba ya tsunduma ni yanzun nan.

Nasir

Cikin bacin rai yake cewa

"Amma dai wan nan anyi tsinannen yaro, gaskiya lamarin rayuwar samarin bana yana bani tsoro da tafiyar da duka nutsuwa ta, gaskiya usman ya cuci yarinyar nan haka ya zalunce ta wallahi Allah bazai barsa ba, san nan k'arin Abin bak'in cikin wai wan nan gungumemen shaid'anin ne ya turosa domin ya zubawa maryam guba a zuciyar ta, wallahi badan kun hanani ba wallahi dasai na makasa a kotu baba, wan nan rashin mutunci ne da rashin imani ai.

Kai baban ya sunkuyar yana kumajin babu dad'i a cikin ransa game da rayuwar auren maryam yake wakana, shikam yana ganin kamar Maryam bata da rabon aure aduniyar nan, ga mahaifiyar ta tana ta fama darashin lafiyar kansar nono wacce ciwon yayi tsamari har tana kwance a gadon asibiti.

Ita kanta Maryam d'in wata damuwar ta k'ara rufta mata akan wata yana tunanin kar yayi biyu babu wato yayi ba 'yar babu uwar, dan haka da sauri ya kalli ya jafar yace.

"Jafar, wanene ni a wajenka?

Da d'an mamaki jafar ya kalli baban yana neman Abinda yafaru yayi masa wan nan tambayar amma duk da haka sai yace "mahaifina nane Kai.

Gyad'a kai baba yayi san nan yace "idan na baka umarni zakabi?

Da sauri ya jafar ya d'aga kai yana cewa "ko wuta kace na fad'a zan fad'a baba.

Kallon sa baba ya mayar kan Nasir tare da rik'e hannunsa yace

"Nasir, wanene kai a wajena?

Sai da Nasir yad'an muskuta tare da gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login