Showing 42001 words to 45000 words out of 175193 words

Chapter 15 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

564

Insha Allah zata basu mamaki, dan zata wanzar da farin ciki a tsakanin su, kuma wan nan kutsen da Rashida take cewar tamata Insha Allah zai zama sai tace gwara data kutso ba daman bata kutso ba.

Saurin kallon Rashida Maryam tayi a lokacin dataga tana goge mata hawaye tana mata murmushi dayi mata Alamar ta daina kuka, shima gogan Nasir da sauri ya taso daga inda ya zauna ya ?araso wajen dasu maryam ke zaune yayi joining dasu, Maryam suka saka a tsakiyar su suna mata murmushi tare da ?ara bata ?arfin gwiwar ta aminta dasu basuzo mata da wasa ba.

Ita kam Maryam tsam take a zaune takasa koda motsi ballantana takai ga kallon Nasir Win da yaketa sakar mata murmushi da le?a fuskarta wai shi lallai sai ta kalleshi ita kuwa ta?i.

Samira

Kallon mijinta tayi shima ya kalleta, idan suka ce ?ar dramar da aka gudanar a wajen nan bata birgesu ba sunyi ?arya, amma ita samira zuciyar ta cike take da wasi wasin wan nan lamarin shiyasa har yanzu ta kasa buWe zuciyar ta ta karSi Abinda rashida tayi, amma shi mijinta abin ?ayatar dashi yayi har yake ganin shikkenan matsalar maryam takau, daman Rashida itace mai matsalar kuma gashi da kanta ta kori matsalar ta zama tarihi.

*****

Samira

Kuka ta fashe dashi a lokacin da suka fito daga gidan Nasir bayan sun rako Maryam, itafa gaba Waya zuciyar ta ta?i karSar Abin da Rashida takeyi dan haka yazama dole ta dage damtse domin taya ?awarta addu'a da kuma ganin ta jajirce domin karSar ?ancinta a duk lokacin da abin Soye ya fito fili a wajen Rashida.

Kallonta mijinta yayi yana mamakin irin zuciya ta samira wacce bata Waukar abubuwa da sau?i, kamar ya shareta yabarta taita kukanta dan yasan a waWan nan watannin da Maryam tayi a gidanta bama sai an baka labarin irin sha?uwar su ba, amma sai yaga bazai iyaba dole ne ya rarrasheta yajawota jikinsa yaji menene kuma matsalar?

Hannunta ya ri?e guda Waya yana tu?i da Wayan, kallon sa samira tayi tana share hawaye shi kuma sai ya sakar mata murmushi, Wauke kai tayi daga kallonsa tayi facing windown motar tana kallon titi, bai damuba dan yasan samiran tasa akwai daru dan haka sai ya saki murmushi yace.

"Meya faru Madam? Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka tace "hankalina ya?i kwanciya doctor, sai nake ganin kamar Rashida kwantan Sauna tayiwa Nasir da kuma Maryam danta cutar da ita, nidai gaskiya a raina jinake kamar naje gida na faWawa umma da ya Mansur halin da Maryam take ciki, dan ajikina nakejin komawar Maryam gidan kamar bazai zamar mata alkairiba duba da yadda...

?aga mata hannu doctor yayi yace "haba Samira, ban sanki da hakaba, meyasa zaki sauya, na zaci har yanzu kina nan amace mai ?arfin zuciyar da babu wani abun dazai razanata ko yabata tsoro bare ya sakata shakku, ko kuwa zama da Maryam ya sanyaya miki zuciya? To bara kiji, itafa ?addarar bawa a rubuce take akan allon ?addarar sa, dan haka inason kisani duk wan nan abubuwan da suka faru da Maryam ?addarar tace.

Abu na gaba kuma danakeso ki ri?e shine, yana da kyau akoda yaushe bawa ya dunga kyautatawa Wan uwansa Musulmi zato, kiyiwa Rashida kyakkyawan zato san nan kibi ?ar uwarki maryam da addu'a, Insha Allah babu Abinda rashida ta Soye marar kyau a zuciyar ta game da maryam, da yardar Allah alkairin data ?unso shine zai cigaba da gudana a tsakanin su, dan haka kiyi ha?uri ki share hawayen kinji may hibba.

Murmushi samira tayi tanajin son mijinta na?ara nun kuwa a zuciyar ta saboda bayason yaga damuwar ta ko kaWan, shima mayar mata da murmushin yayi dan yaji daWin yadda ta karSi shawarar sa, hakan yasa ya zugeta suka tafi wajen shan ice-cream dan ya sanyaya mata kwa?oshi, suna tafe yana tsokanarta da idan suka siya gida zasu tafi dashi dan sai ya Wumama a oven zata sha, saboda kar sanyi yafara kama babynsa tun yanzu, dan daman samiran tanada ciki na wata uku a cikin jikinta.

Maryam

Tsuru tayi akan kujera tana sauraren yadda gidan ya Wau shiru da kuma dakon fitowar mutanen gidan, amma shiru basu fitoba dan tun shigar su gidan Rashida ta wuce Wakinta bayan tamata sai da safe, shi kuma Nasir Win sai yabi bayan Rashidan yana cewa Maryam Win yana zuwa, shine fa shiru shiru har wajen minti talatin basu fito ba kamar an aiki bawa garin su.

Sai data kuma jimawa taga dai basu da niyar fitowa san nan ta mi?e tare da buWe Wakin su Halima ta shiga dan tayi sallar shafa'i da wuturi dan tagaji dazaman jiran Nasir yafito ya sanar da ita Wakin dazata zauna.

Rashida

Kuka sosai take rafza wanda har Nasir yarasa ta yadda zai kuma Sullo mata domin ya rarrasheta, shikansa yasan ya taro March Win da mutuwar sa zai Wauki wasu kwanaki masu yawa, ganin yana neman ya dameta yasa tatashi daga rubda cikin datayi ta buWe banWaki tare da shigewa ta rufe ?ofar, tana shiga ban Wakin ta jingina bayanta da bango tanata kuka wanda har sautinsa ana jiyowa a cikin Wakin, ita Nasir zaiwa haka? Nasir Wintane yake cewa muddin bataje bikon matar saba sai ya sanarwa da hajja? Batayi tunani ba haka batayi tsammanin cewar Nasir zai so wata bayan ita koya fifita wata akanta ba, kuma wallahi tayi rantsuwa da girman Allah bazata bar cin amanar da sukayi mata yatafi a banza ba, tayi ?udirin Waukar fansa a ranta tun ranar data farfaWo daga gadon asibiti, tofa wan nan Waukar fansar tana nan babu Abinda Ya canza sai ma ?udurin jefa Maryam abala'in dazata gwammace kiWa da karatu akan kutsen datayi mata a cikin al-amuranta, dan wallahi tayi al?awarin wan nan kukun farin cikin dataga Maryam nayi wallahi tallahi sai ya zamar mata kukan jinin da bazai taSa ?arewa ba a rayuwar ta sai ranar futar numfashinta muddin suna tare.

Nasir

Jin kukan rashidan ya?i ?arewa yasa ya tashi yafara bubbuga ?ofar a hankali saboda kada yajawo hankalin mutanen dake gidan yana kiran sunanta.

"Rashida, Rashida, Rashida, dan Allah ki buWe ?ofar nan Rashida, kiyi ha?uri ki saurareni, yakamata kifito mu nemi mafitar dazata Sulle damu, shiru Rashida tayi ta?i koda motsin kirki sai kukan data keyi jefi jefi.

Maganar Nasir Win mugun ?ona mata rai takeyi sai takejin kamar ta buWe ta sha?e masa wuya har sai taga baya numfashi, amma madadin tunaninta sai ta Wauki robar hypo dake ajiye a banWakin ta daddage ta buga ajikin madubin dake banWakin take kuwa ya tarwatse.

Da sauri Nasir ya kuma zabura yana dukan ?ofar yana cewa "kibari fa Rashida, dan Allah ki saurara karki jiywa kanki ciwo, haba Rashida kina abu kamar ba musulma ba? Yafa kamata ?idauki wan nan auren nawa a matsayin ?addara, san nan yana da kyau ki cikawa Maryam al?awarin da kika Wauka na kulawa damu baki Waya da bamu farin ciki mai Worewa.

Shiru Rashida tayi kamar dai waccce bata banWakin, ganin haka Nasir yasa yajawo jikinsa ya fito yana tunanin a mai Maryam zata Waukeshi, wani ikon Allahn kuma koda yafito sai yaga Maryam Win bata inda yabarta, Wakinsa ya buWe ya le?a ko tana ciki sai yaga bata nan, ?arasawa cikin Wakin nasa yayi ya buWe banWaki ya shiga domin ya watsa ruwa, yana kunna famfo sai shaya ta fara tsiyaya a akansa ko kaya bai cire ba, da sauri ya kashe shayar yama fasa wan kan baki Waya ya fito daga Wakin.

juyowa yayi ya nufi Wakin su Halima ya buWe, yasan su Halima basa nan domin Wazu dazasu fita Rashida ta saka drivern gidan hajja yazo ya Wauke su wai zasuyi kwana biyu.

Yana le?awa ya hango Halima a kwance akan dadduma tana jan carbi da alamar salla tayi, takowa Wakin yayi yana kallon agogo yaga sha biyu saura, baiji daWi ba a zuciyar sa domin tun wajen shaWaya yana wajen Rashida sai yanzu ya fito, kawai tunanin kallon da zatayi masa yayi sai kawai ya shafa ?eya yana kallon yadda tatashi a nutse tana gyaran zamanta.

A kan gadon su Halima ya zauna tare da ri?o hannunta, wani abu Maryam taji mai kama dajin haushinsa ne ko kishi bata saniba, domin kallon datayi masa sau Waya ta gane cewar jikinsa a ji?e yake da alamar sai da yagama da matarsa san nan yayi wanka san nan yazo mata danya nuna mata Rashida itace matar so ba ita ba, dan haka kawai sai takasa Wagowa ta kalleshi saboda hawayen daya taru a idanuwan ta, kuma komai ta tuna oho! Sai tayi saurin cewa a ranta

"A'uzubillahi, toma menene idan yaje wajen matarsa, ai ita har yau batasan matsayar ta a cikin gidan ba, kuma san nan bata da girki a gidan ballantana tace cin amanar ta yaje yayi, saboda ta kuma kauda zancen sai tayi saurin mayar da kwallar idanunta ta Wago tana masa murmushi, shima murmushin yayi mata yace

"Salla kikayi? ?aga kai Maryam tayi tana kuma dakewa tace "ina wuni? Lafiya ?alau Alhamdulillahi ya faWa yana faWaWa fara'arsa, sai kuma ya sauko tare da facing Winta yace.

"Maryam. ?agowa Maryam tayi ta kalleshi san nan tamaida kanta batare datace komai ba, ganin haka sai yayi murmushi yace "kunyar ki tana Waya daga cikin Abinda yasa kika shiga zuciya ta, dan haka dan Allah komai rintsi karki bari wan nan kunyar tabar idanuwan ki, san nan inason wan nan nutsuwar taki Maryam, ke inason komai naki wallahi, dan haka wallahi kema Maryam ina sonki. YafaWa tare da rungume ta tsam a cikin jikinsa yanajin sonta na ?ara shiga zuciyar sa.

Sai da yaga kamar tagaji da ri?on da yayi mata dan gashi nan tanata mutsu mutsu san nan yayi murmushi tare da sakinta yace

"Kiyi ha?'uri Maryam, karki ga ban baki Wakin da zaki zauna ba, bamu da safayar Waki a saman nan, amma muna dashi a ?asa saboda ba?in kwana idan zasu zo, kuma gaskiya banason na barki a ?asan dan bazanji daWi ba ace mu muna sama ke kuma kina ?asa hankalina bazai kwanta ba, shiyasa nakeso kiyi ha?uri mubari muga zuwa gobe nayi tunanin inda zaki zauna, amma kafin nan kiyi ha?uri ki kwana anan Wakin nasu Halima zuwa kwana biyu mugani tunda basa nan sunje hutu, ni kuma nan da kwana biyun Insha Allah zanyi ?o?ari naga na tanadar miki Wakin san nan na zuba miki komai da zaki bu?ata kama daga Kayan Wakin da komai Insha Allah, amma fa sai dai kiyi ha?uri ku haWa kichen keda rashida dan shi kaWaine a gidan.

Murmushi maryam tayi tanajin haushin Nasir daya fara mata tabo a cikin zuciyar ta yana washewa da kaWan da kaWan, tsintar kanta tayi da kallonsa tace "Nagode sosai, Allah yasaka da gidan aljanna, Nagode sosai da kulawar ka a gareni, kuma ina fatan Allah yabamu zaman lafiya.

Murmushin shima Nasir yayi yace " babu komai Maryam, aike ?anwata ce kuma matata, kinga kuwa duk Abinda zan miki ha??i nane nayi miki shi, sai ya saisaici kuncinta ya sakar mata kiss mai tsayawa a zuciyar masoyi san nan yatashi yace "gobe ina da Waurin aure, inason na fita da wuri Insha Allah.

Tashi tsaye itama Maryam tayi tana masa murmushi tace "to Allah yabamu alkairin sa kuma Allah ya nuna mana.

Sai daya kuma rungumar ta san nan ya buWe ?ofar ya fice yana kallon ?ofar Rashida wacce yana fitowa yaga an banketa da ?arfi, mamaki yayi nako Rashidan zata fitone ko kuma tafito taje kichen data ganshi tai saurin shigewa dan karya ya tsayar da ita.

Yana fita Maryam ta zauna a inda ya tashi tana murmushi tare suffanta yadda zasu yi zaman lafiya a cikin gidan muddin Rashida ta gama saukowa.

Rashida

Tunda taji Nasir yafito daga Wakinta itama ta salallaSa tafito dan taga inda zai nufa, tana fitowa kuwa taga ya shige Wakinsu Halima, bata raba Wayan biyu a wan nan Wakin Maryam take shiyasa ya shiga dan yaci amanar ta, tanata tsaye bakin ?ofar tata domin taga sanda zai fito daga Wakin amma sai taji shiru ya?i fitowa, cikin ba?in ciki da Sacin rai tatawo da azama domin ta buWe Wakin su Haliman taga Abinda sukeyi, harta kama handle Win ?ofar kawai sai taji yana furta mawa Maryam kalmar so, batasan jiri ya kwasheta ba sai dataga muraran zata daWi, da sauri takama kujerar dake jikin Wakin tayi saurin tsayuwa akan ?afafunta, hawaye ne kawai ke zarya akan kuncinta ga zuciyar ta dake zaSalSala kamar an anza tukunya akan murhu, duk magan ganun da sukayi a kunneta ya sauka, haka kawai taji bazata iya barin wajen ba batare data ?arasa jin magan ganun suba, har kiss Win da yayi mata sai dataji sautin fitarsa a kunnenta, jin zata rushe da kuka mai ?arfin gaske wanda ya tunkuWo zuciyar ta yasa tayi saurin barin wajen tana jan ?afafunta da takejin kamar an rarraWe mata su, wani gudu ta saka kuma ta faWa Wakinta ta banko ?ofar a dai-dai lokacin dataji nasir zai buWe ?ofar ya fito.

Tana banke ?ofar cikin tsananin ba?in ciki ta rarumi kwalbar turaren wuta dake cikin show glass ta jefawa mudubin Wakin take ya tawar watse ?asa.

*KUTSE*

*PAGE 19*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*Washegari*

Da sassafe Maryam tatashi ta fara ayyukan gidan kamar yadda tayi lokacin datazo gidan, nan da nan kuwa ta gama aikin cikin farin cikin da zuciyar ta take da walwala, tana gamawa tayi wanka tare da dawowa falon ta zauna, akai akai take kallon Wakin Nasir da Rashida tanajin kamar ta buga musu ta sanar dasu takwas ta kusa, amma batasan shiga hurumin su dan batasan meya zaunar dasu basu fito ba.

Ganin zaman jiran nasu duk Sata lokaci ne yasa tayi bissimillah tare da mi?ewa ta nufi kichen dan ta samar musu Abinda zasu karya dashi, duba inda kayan abincin suke taga suna da dankalin turawa, hakan yasa ta Wiba tafara ferewa domin ta soya musu, tana cikin ferewa ne taji taku kamar an shigo kichen Win, da sauri maryam ta juya domin taga waye yake takun shigowa kichen Win.

Rashida ta gani tsaye a bayanta idanunta jawur kamar gauta ga fuskarta duk ta kumbura kamar wacce akayi wa duka, da sauri Maryam ta ajiye wu?ar hannunta cikin kiWima ta isa gaban rashidan tana cewa

"Maman halima meya faru? Meya sameki?

*Rashida*

"?agawa Maryam hannu tayi da alamar ta kyaleta haka batasan magana, dan ita kaWai tasan Abinda ke sukarta a cikin ?ahon zuciyar ta, musamman yadda taga Maryam Win ta saka sabbin kaya tayiwa wan nan ba?ar fuskar tata kwalliya, ga wani ?amshi dake tashi a cikin jikinta kuma wai tazo kichen zatayi girki wai ita matar gida.

Kasa yiwa Maryam magana tayi Saboda takaici kawai sai ta giftata ta wuce tanajin kamar ta sha?eta.

Ganin ta wuce yasa Maryam tayi saurin isa gabanta tace

"Sannu maman halima, ina kwana? Ya jikin?

Kasa kallonta Rashida tayi dan takaici kawai sai ta jinjina mata kai dan idan tace zata buWe bakin tayi magana muna nan magan ganu ne zasu fito a cikin bakinta.

Ita kuma Maryam ganin rashidan ta kasa magana sai tayi zatan kodai ciwon fuskar ne ya hana Rashida yin magana ko kuma ciwon ya shafi bakinta, sai ta kuma saurin cewa

Maman halima ko akwai wani Abinda kikeso zakiyi? Idan akwai wani abin ki faWa min sai nayi miki.

Nan ma banza Rashida tayi mata sai fridge data buWe ta Wauki Apple guda biyu ta fita tana makawa Maryam harara.

Tana fita Maryam ta ri?e haSa tace "ikon Allah, to ita wan nan me akayi mata ne haka? Ko batada da lafiya ne? Tabbas batada lafiya dan jiya ?alau muka rabu da ita shine kuma yanzu ta ganta a haka.

Da wan nan tunanin Maryam ta koma bakin aikinta dan kar Nasir ya fito ya tarar ba'a haWa masa abin karyawa ba.

Abinda kuma Maryam bata saniba Nasir tun dayaje sallar asubahi bai dawo gidan ba ya wuce garin bichi domin halartar Waurin auren abokin sa shima zai ?ara mata.

Sauri sauri Maryam tayi ta kammala aikin itace harda su dama kunun gyaWa domin tasan Nasir na sonshi dan duk sanda yaje daura yana yawan cewa ta dama masa, shiyasa ta dama dan tasan inda yagani zaiyi farin ciki da hakan.

Jera komai Maryam tayi akan dining kamar yadda taga Rashida nayi, ita bama ta kula da Rashidan dake zaune tanacin Apple a hankali ba sai dataji ta she?e mata da dariya, da sauri Maryam Win ta Wago da kanta ta kalli inda Rashidan ke zaune.

*Rashida*

Tasan sarai Nasir baya nan dan akan idonta nasir Win ya fita, dan saboda Abinda yayi mata jiya hanata barci yayi dan kwana tayi bata iya runtsawa ba, kuma dai-dai zai fita taji yana waya yana cewa "kafito mu haWu a kwana, dan fa ni yanzu zanfita masallaci, kuma daga Masallacin bazan koma gidaba kwanar zanyo mu wuce.

Amma Abinda yabata mamaki da dariya shine

"yadda taga Maryam ta gwaggwafe tanata girkawa miji abinci danta birgeshi, kuma mugunta bazata barta ta faWa mata cewar mijin baya nan ba ta daina rawar ?afa, kuma babban Abinda yabawa Rashida dariya ma bai wuce yadda Maryam Win ta jera kayan abinci har tana sakin murmushi ba, batasan sai dai ta zauna taci kayanta dan ita bata isa ta girka abinci taciba.

Shine abin yabata dariya har ta she?e da dariyar mugunta tana mata gwalo, ganin Maryam Win zata juyo ta kalleta yasa Rashida tayi saurin Waukar wayarta ta kara a kunne tana cewa

"gaskiya bakya rabo da abin dariya yaya, tohnm shikkenan sai nazo yanzun nan zanyi wanka nazo mu tattauna.

Sai ta kuma she?ewa da dariyar ta kuma cewa

"hnmmm baki da dama yaya, kedai bari , ai abban su Haliman ne baya nan yatafi bichi tun asubahi dan haka kema kinsan dashi ne zai kawoni, amma yanzu zan tawo idan yaso idan yadawo saiya biyo ya Waukeni. Tana gama faWar haka tatashi tana wata wa?ar sha?iyanci ta shige Wakinta.

*Maryam*

Sak tayi a tsaye a wajen saboda jin magan ganun Rashida, a ranta take cewar au daman ya riga ya fita? Sai ta kalli kayan abincin tanajin babu daWi a cikin ranta dan har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login