Showing 108001 words to 111000 words out of 175193 words

Chapter 37 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

546

bin umarnin ?ofofin gidan kafin su buWe masa yaga Hajja.

*Hajja*

Tana zaune kan dadduma tana lazumi kawai taga ya Aminu ya faWo mata, da sauri ta saki carbin tana salati tare da ?o?arin mi?ewa tana tambayar Lafiya zaizo a ?arshen daren nan?

Kwantar wa da hajja hankali ya Aminu yayi san nan ya faWa mata Abinda ke tafe dashi, ba ?aramin furgici hajja ta shiga ba dajin wai za'a cirewa Rashida mahaifa, ?arshe ma kuka ta fashe dashi dan itakam yarinyar tabata tausayi, sai da tagama kukanta san nan ta lallashi kanta da taimakon lallashin ya Aminu tayi shiru.

"Aje a saka hannun, Allah yasa ayi cikin nasara, indai cirewar shine zai bata mafitar samun Lafiya kawai a saka hannun acire, ka tashi kaje ayi gaggawa kamar yadda suka faWa kada a Sata lokaci azo a samu Matsala.

Hannu na rawa Nasir ya maka hannun sa akan takardar cirewar mahaifar matarsa masoyiyar sa, har hawaye sai da yayi a lokacin da aka fito da Rashida kuma aka bashi mahaifar tata akan cewar yaje ya samu guri ya binne.

A cikin asibitin Nasir da kuma ya Aminu suka kwana, da sassafe kuwa ya Aminu ya tafi shi kuma Nasir bai tafiba sai daya ga zuwan hajja da nusaiba san nan yayi musu sallama da cewar zaije ya dawo.

*Maryam*

Cikin tashin hankali ta dafe ?irji tana nanata innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, wan nan wace irin jarrabawa ce? Cire mahaifa fa? Rashidan? Kawai sai ta saka kuka domin ta kasa daurewa ta ri?e zuciyar ta.

Sai da Nasir ya rarrashi Maryam san nan yatashi domin yaje yayi wanka yaji daWin jikinsa kafin ya koma asibitin.

Fita ita ma Maryam tayi tana Wan aike aikace-aikacen ta tana Wan cije cije tunani fal ranta dan ji take har sokawa marar ta keyi ma, kasa cigaba tayi da yin aikin tayi kawai sai ta ajiye aikin tafita zuwa Wakinta domin tayi waya.

Samira takira take bata labarin zuwan da Rashida tayi gidan ta bar baWa mata magani dan ta mutu, gashi muguntar data ?unso ta koma kanta har takai ga cire mata mahaifa.

Allah shi?ara samira tayi domin tuntuni daman ta dawo daga rakiyar wan nan jakar matar acewar ta.

*Maryam*

Sakin wayar tayi a lokacin dataji ?arar buWewar banWakin Wakin nata, wa zata gani? Nasir ne ya fito ransa a bala'in haWe kamar fuskar sa zatayi aman wuta Saboda yadda tayi jawur, cikin Sacin rai ya wullar da tawul Win dake jikinsa yayo kan Maryam gadan gadan yana bala'in Abinda yasa bata sanar dashi zuwan da Rashida tayi gidan ba, kuma wanene ma ya rakota gidan har da zatazo?

Kuka Maryam ta saka dan har ga Allah batasan cewar Nasir na cikin banWakin ba, jitake dayace zaije yayi wanka data fito Wakinsa yatafi wankan ashe a Wakin nata yakeyi, dan haka kawai sai ta saka kuka mai sauti ta dur ?ushe a wajen.

Shi kuwa Nasir fitarsa yayi ya zari kaya ya saka yabar gidan saboda Sacin rai, yana fita bai zame ko ina ba sai gidan Rashida wanda tunda ya kwaso su Halima suka tawo bai ?ara zuwa koda ?ofar gidan ba.

?akin Rashida ya shiga ya fara binciken sa?o da loko na Wakin domin sam zuciyar sa ma bata yarda da Rashida bata bin malamai ba saboda shi, har banWaki sai da ya luluba baiga komai ba, kichen ya shiga yafara dube dube, anan ya tarar da wata drower wacce ba kowa ma zaice akwai taba sai wanda yasan kichen Win sosai, aciki yaga tarin magungunan asiran da Rashida ke musu, filla filla yayi da kowanne san nan ya karanta na karantawa, kusan ciwo zuciyar sa tafara saboda tsoron Rashida da tashin hankalin daya faWa ciki ai kuwa baiyi wata wata ba ya tattara asiran baki Waya yayi musu fitsari san nan ya gangama wuta a tsakar gidan ya ?ona komai.

Ko minti Waya kasa tsayawa yayi ya ?ara a cikin gidan dan gani yake kamar wani abin zai sameshi idan ya ?ara minti Waya a cikin gidan , har da gudun sa sanda yabar gidan ya shiga mota ya figeta yayi kasuwa asibitin dabai koma ba kenan.

Nasiru bai ?ara yiwa Maryam maganar ba sai dai kawai yana kallonta da tausayawa ganin yadda Rashida taso ganin bayanta kuma bata samun nasara ba, shiyasa ko zama sukayi ita dashi suna hira sai ya kamo hannunta yace

"kidunga tsawaita addu'a idan kinayi kinji? Ita dai Maryam sai dai ta Waga kai dan bazai iya yi mata wan nan bayanin ba.

Shiyasa shi kuma Nasir yayi zuciya ya?i komawa asibin domin rashin imanin Rashida yakai intihar da bazai iya Wauka ba dan ko bai saketa ba wajibi ne manya su shiga tsakaninsu a wan nan karan kuma ba'iya hajja ba harda mazan family Win su.

Ko ranar idin da yaje Maryam ce ta takura masa akan sai taje ta dubata kuma suma yaran suna bu?atar su ganta, wan nan dalilin kaWai shi ne ya maidashi asibitin amma da yayi al?awarin ko kayan ciki za'a cirewa Rashida bazai sake zuwaba bama mahaifa ba.

Shine duk da haka ya kuma ?o?arin dannewa yazo amma yayarta take faWa masa magan ganu san ranta.

*KUTSE*

*PAGE 46*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Rayuwa juyi juyi wai kwaWo ya faWa ruwan zafi.

*Amina*

Kallon Rashida take cikin takaici tace, ke yanzu kenan saboda Wan wan nan Abinda yafaru dake zakice kin naWe hannu kin zuba musu idanuwa suna cin karansu babu babbaka a kanki kenan? To ai shikkenan, seme dan ancire miki mahaifa? Yaran guda biyu basu isheki ba? To in hakane ni kuma nace me? Ko kuwa kin manta ni banta Sa haihuwa ba kuma san nan ban daina rayuwa ba? Ke wataran mafa rashin ?a?an Alkairi ne a wajenka, ki godewa Allah tunda kin samu.

Kai Rashida ta gyaWa tace bazaki gane ba Amina, yara biyu fa kawai na haifa da nasir, har yau ban fidda rai zan ajiye masa magaji ba, sai gashi wan nan mummunar ?addar ko nace masifar ta sameni, wallahi da nasan haka wan nan maganin yake da hatsari billahi da bazan soma zuwa na sakawa Maryam ba, kinaji fa malam yace ?arfin addu'ar tane yasa maganin baiyi mata illa ba, shi kuma ?a'idar shaiWanun sane idan yayi aiki bai isa wajen wanda kayiwa ba sai dai ya dawo kan wanda ya tura shi , dan haka gaskiya na cutu wallahi, gashi duk kishin da nake zan bar maryam ta haifawa Nasir yara, waya san me zata haifa? Na mijine ko mace, kuma wayasan iya yaran da zata haifar masa.

Sai ta mi?e tsaye tana cewa

"Never, wallahi tallahi bazan bari wan nan lamarin yafaru ba, innaaa, ina zaune wata cen banza tazo taci gajiyar arzu?in da uba nane yayi silar samuwar sa?

Tashi itama Amina tayi tare da dafata tace

"Me zakiyi Rashida, kinsan dai a yanzu baki da wata mahaifa a cikin ki bare kice.

Jikinta Rashida ta fusge daga dafawar da Amina tayi mata tace

"Wallahi zan Wauki matakin da bazai yiwa kowa daWi ba, na rantse da Allah daga wan nan cikin bazan sake bari Maryam tayi wani cikin ba, kuma na rantse da girman Allah bata isa takaini ?a?a ba, san nan shima wan nan Win bazan bari yazo duniya a kirasa da sunan Wan mijina kuma Wan uba a wajen yarana ba, ke koda zata haifeshi wallahi zanyi ?okari wajen hanata ta haifi namiji a cikin gidan dan nice ya dace na ajiye masa magaji ba Maryam????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ba.

*Hajja*

Cikin kiWina ta shigo Wakin Rashida jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankalin magan ganun Rashida, ashe Rashida bata da hankali? Ashe har bokaye takebi bata saniba? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una

Hannu hajja ta saka ta kwashe Rashida da mari mai tsananin zafi, da sauri Rashida tafe kuncinta hawaye na zuba mata saboda zafin marin, kafin takai ga wani motsin kirki ya Aminu ya ?ara sauke mata wani marin.

Ihu Rashida ta saka tana buga ?afa tare da sulalewa ta zauna a ?asa tana kuka sosai.

Cikin karaji hajja tafara magana tana share hawaye tace.

Ashe Rashida baki da hankali? Ashe ke azzaluma ce wacce bata san Allah da ?udurar saba? Ashe ke Allah bai isa ya jarrabeki ba? Sai ta jinjina kai tana dariyar takaici tace.

"Gaskiyar hausawa da suke cewa butulci sai Wan butulci, dan ubanki ke ba'a aure aka auri uwar ki harta haifeki? Ko kuwa kin manta cewar kema ?ar ubar ce? Tunda kika taso a hannuna kin taSa fuskantar wani matsala dani ko yara na wanda zasu nuna cewar ke ?ar ubansu ce? duk fa Abinda kikeyi ina sane dake kuma a tafin hannuna kikeyinsa, yanzu rashin imanin naki har yakai kice zaki hana mace haihuwa? Har dai bazan yi mamaki ba Rashida, keda kika kusan kisan kai saboda rashin imanin ki ai babu Abinda bazaki iya aikatawa ba.

Daman jiyan nan mijinki yaje min da ?orafin irin jifa da kuma son rabashi da matarsa da kikeyi, dan da cayayi ma sai yaje gaban magabatanki da kyar yayanki Aminu ya lallaSa shi mukace zamuyiwa tufkar hanci, a zatona ma wallahi wan nan isharar da Allah ya nuna miki zaki nutsu kiyi hankali ki rungumi ?adarar data faWo miki, amma sai naji kamar ma rashin imanin naki ?aruwa yayi, to wallahi bara kiji na faWa miki Rashida, tunda ke kin zama ?ar kanki ba'a isa a faWa miki kiji ba wallahi nikam na cire hannuna daga kanki, tunda faWan da muke miki gani kikeyi ma tsanar ki mukayi to saboda haka mun rabu dake.

Cikin Sacin rai ya Aminu ya kalleta yace

"Tunda kin zaSi waWan nan ?an iskan ?awayen wanda sukafi miki kowa sai kije kici gaba da rayuwa dasu, sai kuma ya kalli Amina cikin Sacin rai yace

"Zoki fita daga gidan nan dan uwarki, ko gidan uban kine kona uwarki? To wallahi duk sanda na ?arajin kinzo gidan nan ko kin haWu da Rashida wallahi saina ci mutuncin ki, shashashar banza marar imani.

*Amina*

Rai ta haWe tana kallon ya Aminu sama da ?asa irin kallon rainin nan, sai kuma ta buWe baki tare da cewar.

To saime idan ka hanani mu'amala da ?anwar ka? Naga dai ita Rashidan ita ce take nane min, san nan duk inda nake rakata muje ai ba dole nake mata ko najata da ?arfi ba, da ?afarta take zuwa, hasalima ita ce take bu?atar dana taimaka mata, kuma har kayi ha?ilo akan Rashida Alhalin ba ?aunarta kuke ba Saboda ba uwar ku Waya ba.

Rawa jikin ya Aminu ya hauyi saboda magan ganun Amina, ai bansan sanda ya daka wani uban tsalle ya nufi gabanta ba ya Wauke fuskarta da mari, kafin takai ga Wagowa Nasir ya kuma sauketa mata biyu zafafa domin a lokacin da Amina take yiwa ya Aminu rashin kunya a san nan ya shigo gidan dan haka yaji duk Abinda take faWa, da sauri gaba Waya suka kalli Nasir ita kuma Rashida tayi sauri mi?ewa daga tsugunon da tayi tana zare ido.

Hannu Nasir ya Waga tare da niyar kuma saukewa Amina wani marin ya Aminu yayi saurin tare shi yace.

"Kayi ha?uri Nasir, munyiwa tufkar hanci ai, idan ita ?ar halak ce bazata sake neman Rashida ba har abada, idan kuma uwarta a yawon ta zubar ta sameta sai ta kuma nemanta.

Ji nasir yake kamar ya Salle ?asusuwan wuyan Amina saboda Sacin rai, dan haka sai yayi saurin nuna mata hanyar ?ofa yace

"Zoki fitar min daga gida tunda bana ubanki bane, kuma karki ?ara takowa cikin gidan nan, idan kuma ba haka ba wallahi sai na makaki a kotu .

Kuka Amina ta saka tana mai kallon Rashida itama wacce take zubar da hawaye tana kallon ta, da gudu Amina ta fita tana gudu da Waukar alwashin wallahi bazata bar Rashida ba har sai ta halakar da ita kamar yadda ta halaka wajen neman asiri a wajen malamai har suka shafa mata ?anjamau.

Su hajja ma tafiya sukayi suka bar Rashida da kuma Nasir bayan ya Aminu ya ?ara babbawa Nasir ha?uri.

Shima Nasir Win ba zama yayi ba tafiyar sa kasuwa yayi domin daman ba zaman ne ya kawo shiba, yazo ne ya Wauki wasu takardu a Wakinsa sai ya wuce, amma ganin su hajja yasa ya tsaya.

*****

Tana zaune zaman daSaro akan tsakiyar gado tanata kuka kamar hawayenta zasu ?are, komai ya dagule mata ya cakuWe mata, komai ya ?are mata yanzu bata san ina zata nufa kota daso ba, daman can tasan babu ?auna tsakanin ta dasu hajja tunda kullum faWin su itama ?ar kutse ce uwarta amanar hajja taci ta auri babanta alhalin ba itace ta sakata ba, gashi saboda tsana ma yanzu sunce sun zare hannun su daga kanta saboda bata da gata, shi kansa mijin da takeji dashi take alfahari dashi ya tsaneta ya juya mata baya, itama Aminar dake taimakon ta gashi sun rabata da ita saboda rashin ?auna, so suke ?unci ya kasheta su daina ganinta saboda basa kaunarta.

Kuma abin takaicin duk wan nan jarrabawar bata sameta ba sai da nasir ya auro Maryam ta shiga cikin rayuwar su, tayato zata taSa son Maryam? Ai ita da samun soyayyar ta har abada wallahi.

Ajiyar zuciya taja mai nauyi tana kallon yadda Wakin nata yake a har gitse, duk zaman da tayi a acikin asibiti babu wanda ya taimaka ya gyara mata Wakinta kafin ta dawo, san nan gashi yau tsawon kwanaki bakwai da sallamar ta babu wanda ya kuma zuwa ya taimaka mata bare suyi gyaran gidan, ita kanta ya karimatu ma kwana uku ta ?ara mata tayi tafiyar ta har yau bata ?ara dawowa ba sai dai ta kirata a waya, gashi shima Nasir Win ba zuwa yakeyi ba yayi mata yaji saboda yana fishi da ita, ?arin ba?in cikin ma yadda nasir ya Wauke yaranta daga gabanta ya kaisu cen gidan.

To wallahi dole ya dawo mata da yaranta, gashi sun korin mata aminyar ta wacce ke ?aunarta da ?aunar farin cikin ta.

Hawaye ta share tace a fili.

Duk duniya babu mai ?aunata a garin nan, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suke cewa dan gin uwa sunfi na uba ?aunar jininsu, dan haka ya zama dole tayiwa a gadez tsinkaye ko zata samu mafitar matsalarta acen, kuma tayi al?awarin indai su hajjane da iyalanta ta barsu har abada koda me zai sameta bazata ?ara neman su ba.

Washegari da sassafe Rashida ta haWa kayanta duk da jikinta bai gama dawowa normal ba haka ta shiga jirgi domin zuwa ?asar Nijar cikin garin agadez batare data sanar kowa ba, dan tayi niya kuma babu wanda ya isa ya hanata hanata.

*****

*Maryam*

Safa kawai takeyi da marwa saboda yadda takejin ciwon mara da baya, ta rasa meke mata daWi gashi Wazu dataje fitsari sai taga wani yellow Win ruwa na Wiga a jikinta kaWan kaWan, wayarta ta Wauko tare da kiran wayar Nasir dan yakawo mata Wauki, saboda tun tana iya Waga kafarta tayi tafiya har Abin ya gagareta ta daina iya Waga kafar, ga wani azababben ciwon baya mai wahalar fassaruwa dake danda?ar Kwankwasonta kamar an dagargaza mata shi.

Dauriya iya dauriya Maryam tayi amma abin yafara so ya gagareta, addu'a kawai take da salati da sallallami, ga Abinda yake ?ara dugun zumata shine irin kukan da kulu ke kanta tanayi da kiran ta shiga Uku.

Ana cikin haka Nasir ya durfafo gidan tare da shiga Wakin Maryam dan yaga halin da take ciki, yana shiga Wakin yazaro ido saboda ganin yadda take malalar da jini da wani ruwa kamar an kunna famfo, cikin azama ya sungume ta yayi waje da ita ya zura a mota, harya fara tafiya yaga fitowar kulu tafito da gudu da akwatin Maryam na haihuwa tana rufe gidan da mukulli.

Tsayawa yayi kulu ta shiga ya figi motar sai cikin asibiti, suna shiga akayi saurin karSar Maryam tare da shigar da ita lebour room.

To Maryam mukan muna daga gefe munata yaki da addu'ar sauka Lafiya=?O?
*KUTSE*

*PAGE 47*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Mamar mu*

Kallon Rashida take da fuska irinta ta yaro kyau take bata ?arko san nan ta gyara Waurin Wan kwalinta tace.

Rashida kenan, wato ai ita bari ba shegiya bace da ubanta, san nan duk wanda yabar gida ai gida ya barshi, kina tunanin acen garin naku a kwai wanda zai ?aunace ki kamar yadda zamu ?aunace ki? Ai wan nan matar ba ?aramar azzaluma bace Rashida, ita wane irin kishine batayi da uwarki ba? Saboda tsananin kishin tafa itace ta kashe uwarki datazo haihuwar ki, tanaji tana gani Saboda rashin tsoron Allah Hajja ta murWe mata wuya har sai data bar duniya, kuma Saboda tsananin makirci ta hanamu ke tace zata ri?eki tsakani da Allah, kuma wallahi nasan ba banza ta ri?eki ba, ta ri?ekine saboda tana tunanin dukiyar da zaki gada idan baban ku ya mutu, kuma ga maganata ta dawo kan hanya dan nadaWe ina faWa, yanzu da uban naki ya mutu ina dukiyar taki?

*Rashida*

Numfashi ta sauke tare da cewa

"Tana wajen yaya Aminu.

A haf, ai kinji ba, ai idan abin na Allah ne da sai a baki kayarki da kikayi Aure tunda ai duk macen da akayiwa aure shikkenan ta mallaki hankalin kanta, amma saboda zalinci suka rike, hnmmm amma babu komai Rashida, ai daman ki shiyar uwa babu yadda za'ayi taso Wan daba nataba, ninasan hajja bata ?aunar ki kamar yadda take faWan uwarki ta mata kutse cikin gida, kinga kuwa ai dole taji daWin kutsowar da kishiyar ki tayi miki, amma karki damu kin riga ai kin kawo kuka gidan mutuwa, ina faWa miki maganar nan, indai ina raye wallahi bazaki sake kukan wani maraici ba Rashida.

Hawaye Rashida ta share tana mai tsananin jin kaunar maman mu kamar yadda yaranta suke faWa mata a ranta, dan sai takeji kamar mahaifiyar tace a gabanta suke tattaunawa, dan maman mu tana bala'in kama da babar Rashida.

*****

*mai duma*

Shafa kan Rashida yayi yace

"Zillah yasa miki albarka, yana rufe bakinsa sai ga wani ba?in haya?i na fita daga kan Rashida yana bajewa a cikin iska, ba ?aramin tsorata Rashida tayiba ita kuwa maman mu bataji komai ba dan ta riga ta saba da aikin mai duma tun iyaye da kakanni.

Wasu irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login