Showing 99001 words to 102000 words out of 175193 words

Chapter 34 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

545

wahalar duniya ba, ba mutuwa nake tsoro ba amma azabar da Rashida zata cigaba da ganamin kafin ?arshen numfashi na shine Abinda nake gudu da tsoro.

Kamo hannunta Nasir yayi yana cewa

"Haba Maryam, ban sanki da haka bafa, idan baki zauna anan ba to a ina zaki zauna? Nifa ban taSa siyan wani gida na ajiye ba saboda wataran, gwarama filaye akwai su kashi kashi harda wanda na manta, dan haka dan Allah kiyi ha?uri ki kwantar da hankalin ki Insha Allah sabuwar Rashida ce zata dawo ba tsohuwar daba.

Da sauri Maryam ta kwace hannunta daga cikin nasa ta ?ara fashewa da kuka tace

"Wallahi ban yarda ba kuma wallahi bazan taSa yarda ba na zauna da Rashida akaro na biyu, idan kuwa ka dage sai mun zauna billahillazi idan na haWa kayana daura zan tafi kuma wallahi idan na baka baya bazan ?ara waiwayar kaba har abada, idan yaso idan na haifi Wan cikina na aiko maka dashi Rashidan ta shayar maka dashi.

Tana gama faWin hakan tatashi dakyar saboda girman cikinta ta shige Wakinta tana zuba shasshe?a.

Bin bayanta Nasir yayi da kallo yana kuma hasaso gaskiyar lamarin Maryam daya gani a cikin idanunta, wanda yaga da gaske take zata iya yin komai a wan nan karan dan yasan ha?urinta yakai geji.

Kwana biyu Maryam da kuma Nasir suna ta ?addama har dai wataran ya dawo gidan yaga bata nan, hankalin sa a tashe ya kira wayarta babu fargaba ko tsoro ta sanar dashi tana tasha zata tafi gidan su sai kuma wataran idan sunada rabon ganawa.

Sosai Nasir yaji babu daWi dan wallahi yanason Maryam sosai bama zai taSa tunanin rasa taba, dan haka tun a wayar yayi mata albishirin zai cenza mata gida ta tsaya karta shiga motar zai zo ya sameta sai su tattauna, wan nan dalilin ya hana Maryam tafiya ta tsaya ta jirashi san nan ya ?araso ya Wauki gungume men akwatinta ya saka a boot san nan ya buWe mata gidan gaba ta shiga.

A wan nan kwanakin da suka biyo baya ya nemi Ramadan akan ya sama mishi gida zai siya Wan nesa dashi yadda Rashida bazata ta kura masa ba, kasancewar a zoo road gidan nasa yake cikin gandun albasa sai Ramadan ya sama masa gida acen me dile ta sabuwar gandu inda nan Win ma ba hayaniya ne dashi ba, duka dai unguwan nin ba wani nisa ne dasu ba kuma yayi haka ne saboda karshi Nasir Win yayi nisa da duka iyalin nasa.

A lokacin da Nasir yayi wa Maryam bazata akan gidan rasa inda zata saka kanta tayi saboda murna dan haka sai kawai ta ?an?ameshi ta saka kuka tana furta kalmar godiya kamar zatayi masa sujjada.

Ri?eta yayi a jikinsa san nan yafara zagayawa da ita cikin gidan tana gani da kuma kayayyakin daya zuba mata.

Gidan flat ne dai-dai zaman mace Waya da parking spice na mota baifi biyu ba, sai Waki Waya a tsakar gidan da banWakin sa a ciki saboda ba?i , sai kuma falo babba mai ventilation da Wakuna biyu a ciki ko wanne da banWakin sa, sai kichen mai Wan girma.

Gado biyu Nasir ya sakawa Maryam sai kuma Wakin tsakar gida wanda iya katifa ya saka, sai kuma falo dayaji kujeru da labulaye masu tsantsar kyau wanda duk Abinda aka saka a gidan zaSin tane.

Kasa magana Maryam tayi sai hawaye a lokacin da take kallon kantar kichen Win da kuma kayan kichen na alfarma wanda duk sabbine aka zuba mata harda sabon cooker gas.

Tsugunna wa Maryam tafara ?o?arin yi domin ta rasa wace irin godiya zatai masa shiyasa taso ta tsugunna akan gwiwowinta domin ta jaddada godiyar ta amma Nasir ya dakatar da ita ta hanyar haWata da jikinsa yana raWa mata wata kalma a kunneta wacce ta sakata tsananin jin kunyar sa harta Soye fuskarta a cikin ?irjinsa tana Wan sakin dariya ?asa ?asa.

A wan nan ranar Maryam tatare daman bata da komai a gidan Rashida sai akwatin kayanta, bataje da tsinkeba haka ba Wauko tsinke ba sai akwatinta.

Washegari da sassafe kuwa Nasir yafita tare da saka Companyn S.D.K furnitures sukazo har gida suka kwashe kayan gidan Rashida suka fita dasu san nan suka zuba musu sabbi dal duk a cikin Wan ?an?anin lokaci.

Kuma a ranar Nasir ya Wauki motar Wiban kaya ya shiga tashi motar yatafi rogo dasu domin yakaiwa ?an uwansa tunda babu Abinda sukayi suma sababine basu shekara biyu dayin kayan ba, dan haka bazai siyar ba gwara ya bawa ?an uwansa tunda shi ba gwanin sai da abubuwan sa bane gwara ya bayar kyauta.

Daga ya zulai har zuwa Jamila babu wacce bata samu kaya na nagani na faWa ba suda yaransu, da yakema azumi ya kusa daman ya cika motarsa da kayan da yake kai musu ana gobe azumi kawai ya tafar musu dashi, wan nan rana ba iya ma?otan su lanta ba har taya na bayansu da gabansu babu wanda basan Abin arzu?in da Nasir yayiwa ?an uwansa ba dan har su alkairin sai da ya shafe su dan turamen ?ananun atamfofi ya rarraba wa ?an ?auyen saboda daman ya saba.

Kuka sosai zulai da Jamila sukai tayi suna faWin wan nan aure na Maryam ya zamar musu Alkairi tunda gashi daga aurenta zuwa yanzu bazasu iya irga sau nawa yayan nasu yazo ya ziyarce su da abin Alkairi ba, kuma sukace insha Allah suna nan zuwa kanon ranar salla suzo suyi musu barka da salla.

Da Nasir yazo tafiya ne yace kulu ?ar gidan zulai ta haWa kayanta su tafi tare dan ta dunga kamawa Maryam ai yukan gida tunda cikinta yafara nauyi kuma ga azumi za'a shiga.

Da yawa zulai ta haWa mata kayanta tunda daman ta gama makaranta san nan am fasa aurenta da za'ayi bayan salla, shiyasa zulai taji daWin tafiyar ta ko ta rage damuwar datake ciki saboda fasawar bikinta.

Da yadawo ya sanar da Maryam Abinda yayi haka taita murna tana nuna jin daWin ta kamar ?an uwanta yayiwa alkairin, haka taji daWin ganin kulu dan har kwalla taitayi ta rasa inda zata sakata dan murna.

*****

Ajiyar zuciya Nasir yayi yana lalubo wayarsa ya danna kiran Maryam dan yanzu Muryar ta kawai yakeson ji ko zuciyar sa zata washe daga disashewar da Rashida tai mata.

Bugu Waya biyu ta Waga tanajan hailala a ranta dan daga barci ya tasheta.

Amincin Allah ya tabbata a gareka ya muftahul khair.

murmushi Nasir shima yace.

Amincin Allah ya tabbata a gareki ya hurul ain.

Dariya suka saka gaba Wayan su sai Maryam tace

"Ina kabaro auntyn tawa ka kirani waya a wan nan tsohon daren?

Murmushi yayi har yana bayyana a kunnenta yace

"Karki damu auntyn ki tana barci a Waki, ni kuma na tashi ne naji babu Abinda nakeson ji kamar Muryar ki, ya babyna? Ina kuma kulu?

?an murmushi Maryam tayi a ranta tace

"Kamar gaske, sai kuma a fili tace

Ai kuwa mungode sosai Allah ya?ara girma, amma dan Allah ka kwanta kayi barci dan kasami tashi sawur da wuri.

Addu'a yayi mata sosai san nan ya ajiye wayar tare da tashi ya Wauro alwala dan yayi nafila kafin lokacin sahur.

*Rashida*

Sai tara na safe tatashi daga barci tana mi?a, Waga labulen Wakinta tayi taga haske ya gauraye ko ina, cikin takaici ta juya ta kalli a gogo taga ?arfe tara na safe gashi ko sahur batayi ba, yanzu haka zatayi azumi Wure? Tsaki tayi tana ayyanawa a ranta wallahi baza iya azumi Wure ba tunda ai a addini babu tsauwalawa.

Koda tayi salla tafito wurga ido ta dungayi tana sha'awar falon sosai amma a cikin ranta tana ba?in cikin barin Maryam gidan da kuma hanyar da zata shawo kan Nasir idan ma bazai dawo da Maryam Win ba yakaita gidan nata kona minti biyar ne tayi Abinda yakaita ta tafi.

Tana tsaye taji buWe ?ofar Wakin Nasir, juyowa tayi suka haWa ido sai taga fuskar sa a Waure ba kamar yadda ta sanshi ba, kasa daurewa tayi ta isa gabansa tare da Wan rissinawa tace.

"Ina kwana baban Halima.

Murya babu wani amo sosai ya amsa da lafiya ?alau kin tashi lafiya

Da lafiya Rashida ta amsa san nan tatashi tana masa murmushi tare da karSar jakar hannunsa, Nasir yaWan ji daWin yanayin data nuna masa shiyasa shima yaWan saki fuskar tasa dan daman can shi bashi da ri?o.

Har ?asa ta rakashi tana masa addu'a kamar babu komai a ranta kuma a hakan kawai daurewa takeyi, sai data tabbatar da cewar yatafi san nan tadawo gidan tana nufar Wakin su halima dan yau asabar ce kuma Waya ga azumi.

Har wajen ?arfe sha Waya tana zaune, tatashi ta zauna ta kwanta saboda yunwa, rasa inda zata saka kanta tayi taji daWi da sauri tatashi ta shige kichen tare da haWo ruwan tea mai kauri zata sha, har takai baki tai saurin cewa

"Allah ka gani ni Rashida inada ulcer kuma wallahi bazan iya kai wan nan azumin ba.

Take ta fara shan shayin nata har ta gama san nan ta zari wayarta tana dannawa ?awarta hanan matar Ramadan kira.

Bugu Waya biyu ta amsa suka gaisa san nan hanan tace

"?awata kwana biyu? Shikkenan tunda Nasir ya?ara Aure kika watsar dani.

Da sauri Rashida tace

"Dalla malama saurara min, ba wan nan maganar na kiraki muyi ba, inace sanda yayi auren harda gudunmawar mijinki? San nan ko sau Waya kin taSa kirana kin min jaje ko kuwa kin tako gidan nan domin kwantar min da hankali? Amma shine ina kiranki zaki fara min wani su baWaWun zance, dan haka dan Allah ki saurara ki nutsu muyi magana.

Kinsan Nasir ya Wauke Maryam daga gidan nan wai ya raba mana gida, kuma fafur nayi nayi dashi yakaini naga gidan ya?i, nasan cewar Ramadan baya Soye miki komai kamar yadda Nasir baya Soyewa Ramadan komai, nasan da saka hannun Ramadan a siyen gidan da Maryam take, haka nasan kema kin san gidan, shiyasa na kiraki na tambaye ki, dan Allah kinsan wani abu makamancin haka?

*Hanan*

?aga kai tayi kamar Rashida na kallonta tace

"Eh na sani

Da sauri Rashida ta gyara zama tace

"Yauwa ?awata, ai nasan kinsan komai daman, dan girman Allah sonake ki taimaka min saboda amintar dake tsakanin mu.

Ido hanan ta Waga tana kallon ?ofa tace

"Dame zan taimaka miki ?awata? Ni kuma insha Allah muddin na sani zan taimaka miki.

*KUTSE*

*PAGE 43*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Ramadan*

Da sauri ya karSi wayar hannun hanan ya kashe tare da jefa mata harara yana zama.

Cikin kaushin murya yace

"Ke yanzu idan aka baki kuWi akace ki sanar da Rashida inda Maryam take sai ki sanar da ita? Ko kuwa kin manta halin dataso jefasu a ciki watannin baya? Kin manta babbaka su tasoyi da ransu akan kishinta na banza? Amma shine saboda kwakwalwar ki tana kallon gusur zaki fara bata bayani ko? Gaskiya kin bani mamaki hanan, wato kenan nan gaba dake za'a haWu a cutar da baiwar Allahr da rayuwar Rashidan ma bata dameta ba?

Sai ya Wan zamo daga kan kujerar ya ?an?ance idanuwa yace.

"Zan shata miki layi na ?arshe tsakanin ki da Rashida, na rantse da Allah duk ranar da bakinki ya kuskure kika sanar da Rashida inda Maryam take wallahi hanan wan nan ranar sai ta zame miki mafi muni a rayuwar auren mu, san nan ina gargaWar ki daki fita harkar Rashida tunda batajin tsoron Allah haWi da sanin ciwon kai, kuma tuntuni na baki umar nin ki goge number ta daga wayar ki amma kin?i ko? Tohnm shikkenan, karki goge dan Allah ki barta.

*Hanan*

Da sauri ta saki murmushi tace

"An gama ranka ya daWe, yadda kace haka za'ayi wallahi, ina neman afuwa.

Batare da Ramadan ya kalleta ba yatashi yana ce mata ga kaya cen ya kawo tatashi ta ware ko wanne ta adana, da sauri ta mi?e tana masa adawo lafiya ganin ya zari mukullin motar sa zai kuma fita.

Ledar ta duba taga kaya ne na amfanin girki dana gida, Waukar duk wani abu tayi da tasan zai iya lalacewa ta saka a pridge san nan ta ware na gida da amfanin yau da kullum ta a danashi inda take sakawa.

*Rashida*

Tana cikin sauraren hanan dan tayi mata bayani game da gidan Maryam kawai sai ji tayi an kashe wayar, kallon wayar tayi tana mamakin yadda akayi ta mutu tunda dai tasan tanada kati, ?ara gwada kiran tayi sai taji kuma wayar a kashe, kanta ne ya kulle game dajin wayar hanan a kashe, zuciyar tace ta shiga yi mata wasi-wasi kawai sai ta basar da abin ta ayyana ko cajin hanan Winne ya ?are amma zuwa jimawa zata sake gwadawa.

A wajen ta shikin giWe ta kwanta nan da nan kuwa barci yayi awon gaba da ita wanda ba itace ta farka ba sai wajen biyar saura na yamma.

Da sauri ta mi?e tana kallon a gogon a ranta tana ta shiga Uku san nan ta mi?e ta wuce banWaki, ruwa ta sake watsawa dan zafi takeji san nan tayi alwala ta fito ta sallaci azahar da kuma la'asar, tana idarwa ta shafa fatiha tunda daman addu'a ba damunta tayiba ta mi?e tana tunanin Abinda zata Wora mai sau?i na shan ruwa.

Tana shiga kichen Win ta buWe pridge, kaza tafaracin karo da ita, da sauri ta Wauko ta fara aikinta dan daman ta saba duk azumi da farfesun kazar da soyayyan dankali suke shan ruwa, ya zamar mata wajibi tayi su san nan daga bisani ta haWa da wani abin, dan a rana duk azumi Rashida ta kanyi kalar abincin shan ruwa kamar shida, dan ko batayi shida ba takanyi ?o?ari tayi abu kala huWu dan wajen girki tabbas Rashida bada ganan ba.

*Maryam*

Wan nan azumin ba ?aramin wahala yabata ba, amma haka ta daure duk da Nasir yanata fama da ita akan ta sauke tunda Allah yayi mata uzuri da sassauci, amma fafur ta?i tace itafa bazata sha ko Waya ba insha Allah.

Ganin irin yanayin da Maryam Win takeci yasa Nasir yafasa fita kasuwar ma gaba Waya ya zauna a gidan nata yanata faman gadinta dayi mata sannu, dan ko salla tatashi zatayi sai yace tayi azaune amma sai ta?i, sai da yaga anyi la'asar san nan yatashi yacewa Maryam zaije gida bayan shan ruwa zai dawo.

Maryam taji daWin hakan domin yadda Nasir ya kasa ya tsare tasan idan tatashi tace zatayi aiki to tabbas hanata zaiyi yace bazatayi ba, shiyasa yana fita ta mi?e da kyar tashiga kichen Win domin ganin Abinda kulu takeyi a ciki data shiga, tana shiga kuwa ta tarar ta dafa musu shayi tana fere dankali, sannu tayiwa kulu san nan tafara Waukar wu?a zata tayata kulu tayi saurin cewa

"Haba aunty, kibari nayi mana, karkisa naga kamar kim raina ?o?arina dan Allah, murmushi Maryam tayiwa kulu tace

"Ba haka bane kulu, na riga na saba da aiki ne shiyasa nakejin jikina namin ciwo idan banyi ba, amma kiyi ha?uri kinji bara na taimaka miki da wasu abubuwan.

*****

Sai bayan shan ruwa ruwan jiki yafara tsattsafo wa san nan Nasir ya mi?e domin fita Masallaci dan yasamu sallar asham, fama yayi tayi da Rashida akan tazo suje tace ita dai tagaji wallahi dan duk jikinta babu daWi, kuma ba wani abinne ya saka mata ciwon jikin ba sai damuwar rashin samun wayar hanan da tayi tun rana har yanzu.

KafaWa Nasir ya Waga yace

"Ai shikkenan, ku kuzo muje su Halima, tashi sukayi baki Waya suna murna da tsalle dan daman suna ?aunar zuwa ita kuma maman su sai tace wai yara ne basu isa wan nan sallar ba.

Mukullin mota Nasir ya Wauka yace

"Tohnm shikkenan babu damuwa bara mu muje.

Tana ganin ya Wauki mukulli tayi saurin tashi tana cewa.

Da alama idan an idar da sallar asham Win akwai inda zakaje dan haka bara kawai naje sallar daga nan sai muje inda zakaje tare dan bazan yadda nayi zaman shiru ba ni kaWai.

Gaba Nasir yayi yana cewa kitawo muje to karki Sata mana lokaci.

Da sauri tayi Waki tare da zaro hijabin ta ta saka suka fice tare da rufe gidan, ba wani nisa ne da masallacin ba dan masallacin Bashir tofa nan gandu suke zuwa sallar, da ?afa ma ake zuwa dan zagaye ne bamai nisa ba.

Ita dai Rashida ba wani sallar tayiba dan raka'a huWu akayi da ita ta nemi waje ta zauna ta Wau wayarta tana chat da Amina.

*Amina*

Cikin mamaki take cewa

"Kiyi ha?uri Rashida dan zan Wana zagin mijinki gaskiya, amma wan nan Nasir kwai Wan iska wallahi, yanzu saboda yanason wargaza mana shiri shikkenan sai ya Wauki yarinyar cen ya canza mata gida? Gaskiya abu baiyi daWi ba, amma shawarar dazan baki ko, ki danne zuciyar ki ki lallaSa shi har ya kaiki gidan nata, mudai ba burin mu ta tsallake magani ba? Ai idan zaki jema kiyi mata shatara ta arzu?i ki kai mata idan yaso saiki faki ido ki bar baWa mata maganin ku tawo, tana tsallakewa ba shikkenan ba?

Sticker dariya dajin daWi Rashida ta turawa Amina san nan tace

"Bani da kamarki ?awata, shiyasa a koda yaushe bana iya wani tunani na kaina sai da tunanin ki, kedai na gode, kuma kin sanme? Wallahi gidan yafi daWi da babu Shegiyar nan, dagani sai mijina da ?a?ana, amma takaicin rashin nasarar bar baWa maganin nan shine Abinda yake cizar min zuciya ta wallahi nakejin daman bai canza mata gidan ba, amma nan gaba kaWan nasan zan samu nasara insha Allah.

Hira sukai tayi wanda basu suka ajiye wayaba sai da Rashida taji an idar da salla san nan ta ajiye wayar ta mi?e, mamakin saurin gama sallar takeyi dan taga anyi sauri sosai, amma data fara sallar sai taga sallar tana tsawo shiyasa taji bazata iya ba ta zauna.

Ba wani waje Nasir yajeba sai kawai ya zagaya dasu super market suka Wanyi siyayya, duk da cewar babu Abinda basu dashi amma ya gwammace ya kashe ko nawa ne da dai yaje gidan Maryam da Rashida, a hanya Rashida taita mitar daman ba unguwa zasuje ba ya WaWWagota daga gida?

Murmushi kawai Nasir yayi yace

"To ba gashi na samu ladan ki na ibada ba?

Kawar dakai Rashida tayi tana jin haushin Nasir har a cikin ranta.

Shi kuwa Nasir dariya yayi aransa yana tunanin halin Rashida, har ga Allah yayi niyar zuwa gidan Maryam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login