Showing 144001 words to 147000 words out of 175193 words

Chapter 49 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

548

kawai ta ?ara mannewa a cikin jikinsa tana sakin huci mai sanyaya mata rai

Shi kuwa Nasir koda ya farka daga barcin nan yaga Rashida a kusa dashi da sauri ya mi?e yana tunanin Maryam, baiyi niyar kwana a gidan Rashida ba dan haka sai yayi saurin mi?ewa daga jikin Rashida yana mai mayar da kayansa ya fice daga Wakin, sai da yafita daga gidan san nan yayi tunanin yanzu dare ne da wuya idan zai samu abin hawa, ?arfe uku saura ake magana dan haka sai kawai yayi saurin dawowa ya Wauki motar Rashida yatafi da ita.

*KUTSE*

*PAGE 62*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Cikin mamaki take kallon motar wacce aka fakata a tsakiyar gidan ta tana tunanin wanda ya kawota, sai kawai ta koma ciki tana kallon Nasir wanda ya zurfafa a tunani tace

"Ranka ya daWe mota na gani a parking lot ta waye? Cikin ?ar kaWuwar zuciya Nasir yayi saurin cewa "ni..ni..nine nazo da ita jiyan, daman dazan fita ai banfita da Mota ba, shine da muka gama meeting Win a bokina yabani motarsa na tawo da ita saboda dare yayi. Ya ?arasa maganar yana rarraba idanu.

Girgiza kai kawai Maryam tayi ta Wauke kai daga kallon Nasir tana ayyana wan nan haWa gumin da yake yana rarraba idanu da Alamar akwai Abinda yake damunsa, amma tunda ya?i faWa mata shikkenan zata zuba masa idanu har lokacin da yaga ya dace ya sanar da ita.

Sai wajen ?arfe tara san nan Maryam ta gama haWa musu break fast Winsu, aikin ya Wanso yasha kanta tunda kulu mai tayata tana kwance batajin daWi , da kallo tabi Nasir da mamakin yadda ya kasa cin abincin sai juyasa da cokali yakeyi, Wan zama tayi a kusa dashi tare da ri?e hannayen sa tana kallonsa tace.

"Duk da banyi niyar tambayar ka akaro na biyu akan Abinda yake damunka ba amma bazan iya jure ganinka cikin wan nan halin ba, kuma duk da haka ya zama dole nasan damuwar ka tunda na zama Waya daga rabin jikinka, san nan tabbas damuwar ka tana tsunduma ni cikin wata sabuwar damuwar, dan haka don Allah ka sanar dani Abinda yake damunka ko masu mu kamo bakin zaren tare idan mai kamuwa ne, idan kuma wanda zamuyiwa addu'a ne sai mu taru mu mi?awa Allah lamarin mu, ta ?arasa faWa tana share kwallar data zubo mata daga kurmin idanun ta.

*Nasir*

Wani dumm yaji kansa ya masa da magan ganun Maryam, ha?i?a tausayin Maryam shine wanda ya?ara assasa ?aunar da yake mata, kuma yana tunanin bazai daina tausayinta ba tunda yasan ita macace mai Wumbin ha?uri, kuma yasan tana sonsa da ha?urin zama dashi, dan haka dole zai sanar da ita Abinda ke faruwa tun kafin lokaci yayi ta tafiya cutarwar da yayi mata ta ?ara nunkuwa, dan haka sai yaji shima hawayen dayake ta ?o?arin dannewa a ransa suna zubowa, da sauri Maryam ta ?ara ?an?ame hannunsa tana girgiza masa tana subhanallahi.

Yan????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
zu matsalar taka har takai ka zubar da hawaye akanta ranka ya daWe? Rasa Abinda zaice mata yayi sai kawai ya fashe da kuka mai sauti tare da rungume ta tsam ajikinsa yana furta kalma cikin karayar zuciya da nadama.

"Ki yafemin Maryam, don Allah karki barni ki taimaka ki duba lamarina, idan baki yafemin ba nasan bazan samu salama a rayuwa taba, ki yafe min don Allah.

Cikin jirkicewar tunani Maryam tafara tunanin Abinda yayi mata har yake kuka da magan ganun irin wannan, sai ta ri?eshi tana neman Wagashi daga jikinta saboda ya sakar mata nauyi tace "me kayi min da kake kuka haka ranka ya daWe, nifa babu Abinda kayimin, dan haka don Allah ka daina kukan nan sabodani kada ka jefani a cikin matsala awajen Allah.

?agatan yayi amma yana ri?e da hannunta yana cewa "nayi miki babban laifi wanda bansan dame zan fassara shiba Maryam, amma dan Allah kiyi min uzuri da kuma yafiya a duk sanda kikaji magan ganun dana kasa furta miki.

Maryam batasan meya faruba amma har ga Allah ta fara tsorata da magan ganun Nasir, dan haka sai jikinta yayi sanyi san nan kuma zuciyar ta ta shiga bugawa da ?arfi da ?arfi dan haka sai ta tsinci kanta da Wan sakin hannunsa kaWan saboda yadda jikinta yaWan fara Waukar rawa.

Kallonta Nasir yayi sai kawai ta Wan lumshe idanuwa da kuma sakar masa murmushi a lokaci guda tana cewa

"karkaji komai ranka ya daWe, ka sanar dani Abinda ya shige min duhu.

Sai da Nasir yayi gyaran murya san nan ya tsinci kansa dacewa Maryam

"Na mayar da Rashida Wakinta Maryam, ya ?arasa yana sunkuyar da kansa ?asa.

Duk da Maryam sai dataji zuciyar ta ta buga kamar an fasa ganga, ga shi kansa Wan cikinta saida ya zakuWa yayi tsalle tare da soko mararta wanda har sai data runtse idanunta amma hakan bai hanata Wan sako murmushin takaici ba cikin dakiya tace.

"Daman ka saketa ne?

?agowa Nasir yayi yana kallon Maryam dan sunkuyar dakan da yayi jira yake yaji ta inda zai fara jin ruwan bulalai a jikinsa, amma madadin hakan sai yaji tambayar da Maryam tayi masa wacce tabashi mamaki ta Waure masa kai.

Murmushin Maryam ta?ara sakar masa tana kuma tambayar sa daya saketa ne?

Girgiza kai Nasir yayi a kunyce yace "A'a.

Hannunsa Maryam ta kuma dam?ewa da ?arfi dan da taWan saki san nan tace

"Saboda kun sasanta da matarka wacce babu saki a tsakanin ku shine kake min wan nan kukan da magiyar? To daman meyasa bazaku sasanta ba? Ai Abinda yafaru ya rugada ya wuce sai dai muyi fatan Allah ya kiyaye gaba, dan haka karkaji komai ya Nasir, ni Maryam aure nakeyi a ?ar?ashin inuwar ka kuma aljanna ta nake nema a wajenka, dan haka kaga dole na cinye abubuwa da dama domin ?ara kusantani da aljanna, kuma ya zama dole awajena nayi maka biyayya kamar yadda Allah ya munarce ni, dan haka ka godewa Allah daka kakuma Waukar wani nauyin a kanka wanda zai maka tsani zuwa gidan aljanna kaima.

Saboda haka ina maku fatan alheri ya Nasir, tana faWin haka ta sauko ?asa tare da jingina da kujera dan tagaji da zaman kujerar ta zubawa waje Waya ido tana kallo.

Zamowa shima Nasir yayi yana mai kama hannun ta wanda taji kamar ya WoWana mata wuta yana tunanin maganar gidan dazai mata.

Kallonsa Maryam tayi tana zame hannunta a hankali tana masa murmushi yake, shima murmushin ya mayar mata yana cewa "sauran zancen nakeso nayi miki Maryam.

?aga kai Maryam tayi tana kallonsa cikin ?arfin hali don ita kaWai tasan halin da zuciyar ta take ciki da kuma suka da raWaWin da mararta take mata, dan haka dakyar ta daure tace " ina jinka ya Nasir.

Sai da yaWan rausayar dakai ?asa san nan yace "sabon gidana na Yahaya Gusau na kaita, san nan kiyi ha?uri dan Allah a part Winki na ajiye ta saboda ba'a ?arasa wancen part Win ba.

Kallon ba?in ciki da takaici Maryam tayiwa Nasir san nan daga bisani tace " yayi kyau hakan, sai kawai ta daddafe kujerar tatashi da kyar da niyar bar masa wajen dan batason ha?urin ta ya ?are ta karta masa rashin mutunci, taku Waya biyu Maryam tayi sai kawai wani wawan jiri ya Wauketa ai kuwa tatafi luuuu zata faWi akan cikin nata Nasir yayi saurin yin tsalle ya tarota tafaWa jikinsa a sume.

*Rashida*

Cikin mamaki take kallon Sarin da Nasir ya kwanta taga wayam baya nan, saukowa tayi daga kan gadon tare da zarar rigar barcinta ta mayar tafara takawa ta isa banWaki domin ta duba, baki ta saki ganin babu Alamar ruwa a banWakin ballatana tayi tunanin ya shiga ciki, rufewa tayi ta fito falon taga nan ma baya nan, bata tashi tsinkewa da lamarin ba sai data fito harabar gidan taga babu motarta a wajen, take gabanta ya faWi, kwafa tayi ta shige Wakin domin Wauko wayarta ta kirashi, haka taita kiransa wayar na ringing amma bai Waukaba, tunanin kodai kasuwa yatafi tafara tunda data duba agogo taga ?arfe sha Waya na safe, sai kawai ta nufi kichen domin ta samawa kanta Abinda zata saka a cikin ta domin yunwa tafara kwakwalar ?an hanjinta.

Sai da tagama shan tea da indomie san nan ta Wauko wayarta tana kiran Nasir akaro na biyu, wan nan ma kiran haka wayar ta ?araci ringing Winta bata Wagaba, cike dajin haushi ta tura masa text da

"Ina kaje ne?

Nan ma shiru babu amsa, ajiye wayar Rashida tayi tatashi domin ta watsa ruwa a cikin jikinta, sai da tayi wankan san nan ta tuna da zita wacce kecen gidan Amina takai mata domin ta runga tayata Wan aiyuka kafin ta warke dan tanajin jiki sosai, wayar ta kuma Wauka ta kira delu mai kawo musu ?an aiki danta kawo mata mai aiki.

Cikin jin daWi delu ta Wauki wayar tana faWin sannu da warhaka uwar Wakina.

A yatsine Rashida ta amsa tace mai aiki takeson ta kawo mata yau idan akwai a ?asa. Cikin farin ciki delu tace akwai guda biyu da bazawara da ?ar budurwa wacce za'a kawo mata? Tsaki Rashida tayi tace akawo mata kowacce amma wacce tafi tsabta a cikin su, da wan nan maganar wayar tasu ta ?are.

Tana ajiye wayar sai ga zita tana kiranta, da kamar bazata Waukaba dan haushin zita takeji saboda Abinda maman mu tayi mata, tunawa da zata tambayi jikin Amina yasa tayi saurin Waukar wayar tana cewa "Hello.

Kukan da Rashida taji zita nayi shine Abinda yasa tayi zumbur tatashi tana ke dalla lafiya zaki kashemin dodon kune? Zita bata daina kukan ba sai ma catayi dan Allah aunty Rashida ki taimaka kizo aunty Amina zata mutu.

Wani das Rashida taji ?irjinta ya bada, ai kuwa cikin karaji tacewa zita suna ina? Nan zita take sanar da ita suna ?ofar gidan Aminan Alhaji ya korosu.

Cikin tsananin Sacin rai Rashida tafita ta hau napep tunda Nasir ya Wauki motarta, suna tafe tana bala'in wallahi idonta idon Alhajin Amina saita gurza masa rashin mutunci , kuma wallahi ta samu dama sai ta ramawa Amina zalunci da wula?ancin da yake mata.

Ai kuwa Rashida na sauka a napep taga su zita a ?ofar gida, zita na tsaye tana kuka yayin da ita kuma Amina tana zaune jingine da bango tanata wata zabura da fuffuka kamar zata tashi sama, wani abin tashin hankalin ma ganin wani yalo yalon yawu yana dalala daga bakin Amina bayan bakin nata ya karkace gefe guda.

Da gudu Rashida ta ?arasa wajen Amina hannu aka a kiWime tana faWin

"Na shiga uku na lalace ni Rashida, mezan gani haka? Amina ta faWa tana dafata, menene ya sameki? Rashidan tafaWa tana Waga kan Amina dayake ?asa, itakam Amina batama san Abinda Rashida takeba domin sam bata cikin hayyacin ta.

Rashidan na tsaye tana kuka saiga Alhaji ya danno da hancin motarsa waje alamar fita zaiyi, ai da gudu Rashida ta falfala ta isa gaban motar tasa tare da dun?ule hannu ta daki motar tana masifa, duk da Alhaji baiji Abinda Rashida take cewa ba amma yasan rashin kunya ce take masa, shiyasa shi kuma ya fito a fusace fuskarsa babu alamun Rahama yace.

"Ke malama kinada hankali kuwa? Meyasa zaki dakarmin mota kina wasu magan ganu saboda bakida kunya? A hasale itama Rashida tayo kansa tace kai Malam dakata, niba Amina bace bare kace zaka wula?anta ni, kuma banda rashin mutunci da rashin imani kana ganinta cikin ciwo haka shine zaka wullota waje wato idan ta mutu ko ajikinka ko?

Tsayawa Alhaji yayi yana kallon rashin kunyar da Rashida take masa, shi babban Mutun ne wanda ake ganin mutuncinsa a ko ina shiyasa ya danne Sacin ransa yana kallon Rashida yace kingama?

Zaro masa ido Rashida tayi tace bangama ba azzalumi.

Cikin fushin daya ?ara tokare Alhaji ya Waga hannun tare da Wauke fuskar Rashida da mari, taga taga Rashida tayi zata zube domin ba ?aramin shigarta zafin marin yayi ba, kuma tun kafin ma ta Wago daga gigitar da tayi ya kuma saka hannu ya Wauke Waya kuncin nata da mari, baya Rashida tayi tana sakin ihu da kururwa tana faWin

"Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah kayi ha?uri wayyo fuskata danji take kamar an watsa mata garwashi ko kwalta akan fuskar tata, Alhaji bai saurareta ba ya kumayo kanta gadan gadan zai kuma marinta ta zube ?asa tana ihu, binta yayi ya saka ?afa yayi ball da ita yana faWin

"Dan ubanki inada kamarki uku a gidan miji, amma kizo kinamin rashin mutunci har ?ofar gida? Toko uwarki bata isaba bare ke, shashasha marar tunani, kuma ubanwa ne yabaki ikon ki fito daga gidan mijinki kizo zaki tayar min da hankali? Ai kuwa wallahi sai nayi miki lilis dan ubanki saboda ki komawa da mijinki shaidar kinfito yawon barbaWa a gari.

*KUTSE*

*PAGE 63*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Cikin kuka Rashida ke kallon jikinta da kuma jikin Amina tana zubawa Alhaji Allah ya isa, itafa batasan Alhaji mugun mugu bane sai yau, dan datasan yafi ?arfin iskancin ta babu Abinda zaisa ta tsayar dashi tayi masa rashin mutunci, ta riga ta saba da salihin mijinta Nasir, Nasir baya zagi bare duka, kullum tsakanin ta dashi lallaSawa ce tsakanin sa da ita, sai yau ta kuma ganewa maza suna suka tara kuma gaskiyar magana nata yafi na kowa.

Dole Amina ta jigata taji jiki indai haka Alhaji yake zagewa ya daketa tabbas tasan yawancin raine kawai yakai Amina yanzu, tsayuwar da napep Win yayi abakin asibitin da Rashida tace ya kawosu ne ya dawo da ita hayyacinta , da kyar suka tattagi Amina ita da zita suka shiga da ita cikin asibitin, suna zuwa aka tawo da gadon Waukar marassa lafiya aka Wauki Amina akai aka shiga da ita emergency, itama Rashida sa kawa tayi aka duba aka bata magani domin yadda takejin fuskarta na raWaWi kamar ana Waye mata fata, ga kanta dage ciwo kamar zai Salle saboda bala'i, tsaki tayi a lokacin da aka sanar da ita an bawa Amina gado su haWo kayan kwanciya saboda kula da ita, wayarta ta Wauko ta kira babar Aminar ta sanar da ita asibitin da suke san nan ta mayar da wayar jaka tana tunanin Nasir da halin da yake ciki.

*Nasir*

Yana zaune akan kujerar dake gaban gadon Maryam ya zuba mata idanuwa yana kallonta hawaye na tsiyaya a cikin idonsa, yasan Maryam macace mai tsananin ha?uri, kuma wallahi ko ayau ta rasu yasan sai tatafi da fushinsa san nan da ha??inta akansa kuma yasan Allah bazai barta ba, yanzu da ace baya nan ta faWi akan cikinta da shikkenan wata mummunar maganar akeyi ba wan nan ba, gaskiya ya shiga tashin hankalin da Wimauta, shi baima san a yanayin da yazoba dan har sai da likita ya saka wasu suka ri?e shi dan gaba Waya yayi Wimuwar tunanin sa, Aljihunsa ya yafara lalubawa yana neman wayarsa, shi baima saniba ko a gida yabar wayar ko kuma sace masa ita akayi a asibitin oho.

Le?owar da norse tayi ta kira Nasir da cewar likita yanason ganinsa yasa ya tashi yafita ita kuma norse Win ta zauna a wajen Maryam.

Goshi Nasir ya dafe yana faWin Allah ma ya kiyaye likita, Insha Allah hakan bazata faru ba, Waga kafaWa likita yayi yana cewa

"Ai sai ka kiyaye Allah zai kiyaye ka, nadai sanar dakai, Maryam ta kamu da mummunan hawan jini, kuma badan Allah yasa ajikinka ta faWi ba da yanzu wata maganar akeyi, amma idan aka kwantar da hankalin ta da kuma nutsar da zuciyar ta shine kaWai zai saka jininta ya dai-dai ta sosai, san nan munasa ran Insha Allah idan ta haihu zata iya rabuwa da hawan jinin, kaidai kawai ka kiyaye Abinda zai dunga tayar mata da hankali

Kai Nasir ya gyaWa yace Insha Allah, saida likita ya gama dashi san nan ya fito yana tafe yanajan ?afa kamar zai faWi saboda yadda kansa yayi masa wani gingirin gin.

Kamar ance masa ya kalli gefensa sai kawai ya Wora idonsa akan Rashida wacce fuskar ta tayi jajawur, abinka da fara tass kamar zabiya, shiyasa fuskar tayi Wau daja kamar an kwara mata ruwan zafi.

Da sauri yayi kanta yana Rashida, meya kawoki nan? Meya samu fuskar ki?

Da sauri Rashida tataso tana kallon damuwar dake fuskarsa tace "kaima Lafiya na ganga a asibiti? Menene yafaru dakai? Kai yaWan kawar yana huro iska daga bakinsa yace "ina tambayar ki kina tambaya ta? Meya faru?

?an raurau tayi da ido tace, nazo wanka ne ban saniba ashe ruwan yayi zafi da yawa na zuba a fuskata, kuma nata kiranka a waya baka Wauka bare kazo ka kawoni asibiti kuma gashi naga ka Wau motar shine na hawo a napep na tawo ganin likita.

Hannunta Nasir ya ri?e cikin tausayi yana mata sannu, katseshi tayi tana cewa shi mai yakawo shi asibitin?

Kallon Wakin da Maryam take yayi yace

"Maryam ce bata da lafiya shine na kawota asibiti, dammm, gaban Rashida ya faWi, da sauri tace "meya sameta? Dan zuciyar ta tafara zargin ciki ta samu take laulayi shine ya kawota ganin likita.

?an murmushi Nasir yasaka yace "wai sunce hawan jinine da ita. Lumshe idanuwa Rashida tayi tace

"Allah shi?ara, saura ciwon zuciya, da yake a hankali ?asa ?asa tayi maganar yadda Nasir bazai ji sosai ba, shi kuma sai yazata magana take baiji ba sai yace "me kikace?

?an ya?e tayi irin tanajin jiki tace "canai mushiga na dubata.

Gaba Nasir yayi Rashida tana biye dashi har suka shiga Wakin,turus Rashida tayi jikinta na rawa ganin Maryam a zaune jingine da gadon idonta a ruge ga turtsetsen cikin ta agaba hannunta akai ta dafe.

Da sauri Rashida ta ?arasa jikinta na mazari tace "Mam...mamr.....rayam. tare da dafa cikin Maryam Win.

Da sauri Maryam ta buWe idonta tana jan addu'a a cikin ranta jin gabanta yayi mummunar faWuwa har ?irjinta yana neman ruguzowa.

Tozalin da Maryam tayi da fuskar Rashida yasa tayi saurin saka hannu ta ture hannun Rashida wacce ta dafe cikinta tana daddanawa, sai Rashida ta Wago idonta sukayi ido huWu da Maryam takafeta da idanunta wanda suke jawur kuma suka ?an?ance.

?auke kai Maryam tayi ta mayar da kallonta kan Nasir wanda shima idonsa suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login