Showing 132001 words to 135000 words out of 175193 words

Chapter 45 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

521

sameta ba.

*Bayan sati biyu*

Kamar a mafarki wayar Rashida tafara ringing tana Wagawa sai taga sunan maman mu na reto a jikin screen Win wayar, da sauri ta rarumi wayar har wayar na kusan faWuwa tayi sauri ta Waga tana maman mu Lafiya najiki shiru?

Dariya maman mu tayi tace

"Kinga gamu nan nida yayanku munzo garin kano muna tashar kuka ina zamuce a kawo mu? Wata ?arar jin daWi Rashida tayi tana tashi tsaye tace bara nazo na Wauko ku, duk da tun karayar nan da tayi bata kuma yin tu?iba amma tasan zata iya tunda ta samu sau?i, kafin kace me Rashida tatashi zata fita zita ta biyo bayanta tana cewa zata bita.

Kai Rashida ta girgiza tace

"Babu inda zaki bini malama, akwai miya a cikin fridge ki Wauko ki Wumama ta san nan kiyi sauri ki dafa musu taliya ko makaroni kafin na Wauko, har tayi gaba ta dawo tace

"Ke jinan, akwai dafaffen soSo shima a fridge ki Wauko ki Wiba ki haWa musu soSo dan nasan idan ban faWa miki ba hankalin da kike dashi bazai baki cewar kiyi Winba.

Zita ba'a sonta ba ta koma gidan tana ?un?uni dan tafara gajiya da gadarar da Rashida take mata kamar wata mai aikinta.

Mintina kaWan sai ga Rashida ta dawo da maman mu da kuma Babban wansu zita sunata zuba ?auyenci, ganin gidan da Rashida take rayuwa ba ?aramin gigita tunanin maman mu yayi ba, duk da gidan mahaifin Rashidan yayi talatin Win wan nan amma tsaruwar sa irin na turawa ne, baki maman mu ta saki tace

"Allah yabaki gida kamar wan nan ko wanda yafi wan nan zita.

Da Amin suka amsa harda Rashida wacce bata fahimci ba?in ciki ya saka maman mu faWar wan nan maganar ba.

Ai kuwa maman mu ta karkace tacewa Rashida

"Wai zita bata da saurayi a garin nan ne? Ya kamata fa ace tafara kamo wuyan samarin garin nan masu son fara da kyakkyawar mace, kuma zita ta haWa komai da komai da samarin garin nan sukeso ga gashi har Wuwawu wai me suke nemane?

Murmushi Rashida tayi tace

"Banda abin maman mu ai zita karatu zatayi, guda nawa zitan takene da ake mata maganar aure?

Baki maman mu ta kama tace "taratu kuma? A'a gaskiya, tana samun miji ki aurar da ita tayi karatun a gidan mijinta.

Cigum Win bakinta Rashida ta cire tace "maman mu ina zita taga saurayin? Kingan mufa tun da muka dawo muna gida babu inda muke fita. Ta ?arasa zancen da damuwa fal ranta.

Cikin jin haushi lafazin Rashida maman mu tace "amma gaskiya anyi ?ar ba?in ciki Rashida, yanzu saboda ke Allah ya rufa miki asiri shine ita zita kike mata ba?in cikin samu? Mai makon da kuka dawo ki Wauketa ku dunga fita yawon sha?awata har ta samu wani mai kuWin acen shine zaki dun kumemin ?ar a gida kamar dafarfiyar awara?

Kai Rashida ta girgiza tace "ba haka bane ba maman mu, dan bakisan Abinda Ya sameni bane da bakiyi wan nan zancen ba, nan Rashida ta kwashe duk Abinda akayi mata a gidansu ta faWawa maman mu da yayansu wanda keta huci kamar zai kai duka.

Cikin hassala da Sacin rai maman mu tace

"Ita Hajjan ce ta saka akayi miki wan nan cin mutuncin? A lallai babu ?aunar ki a zukatan Mutanen nan ko Waya Rashida? Toke wane mataki kika Wauka?

Shiru Rashida tayi batace komai ba sai share hawaye san nan tace

"Ni babu matakin dana Wauka maman mu, jinake Nasir zai Wauki mataki amma shiru kikeji saboda yanzu batani yakeyi ba.

Tashi tsaye maman mu tayi tana huci tana cewa "taso maza ki kaimu gidan hajjan, dan wallahi yau idan banci mutuncin matar nan ba bazan iya barci ba, billahillazi yau sai tasan kema kinada gata, sai ta kalli Wanta tace "kaiiii, taso muje mufar musu idan yaso ayi uwar watsi kowa ya kama gabansa.

Tashi yayi suka fara tafiya dan ita Rashida bataji komai ba dan a yanzu idan akwai wanda ta?i jini idan a????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  ka Wauke Maryam da ?a?anta tosu hajja ne, musamman ya Aliyu wanda takejin da zata samu dama wallahi shine wanda zata fara aikawa lahira Saboda tsanar datayi masa.

Suna tafe maman mu na SaSatu da masifa har suka kusa ?arasawa gidan, har sun kusa kaiwa maman mu ta kalli Rashida yace

"Ince ko kin karSi dukiyar ki daga hannun su? Kai Rashida ta girgiza tace "A'a. Cikin masifa maman mu tace

"To uban me kikeyi da baki karSa ba? Ko kuwa so kike kibar musu su cinye tunda dai sun fiddake daga cikin zuri'arsu? To wallahi basu isa ba, na rantse da Allah kafin mubar garin nan sai mun tattara komai mun karSa tunda ai kowa da nasa, nifa bazan zuba ido su kasheki da ba?in ciki ba, gwara su tattara su baki ha??inki idan yaso ayi uwar watsin baki Waya, shi kuma Nasir ki barni dashi dan ubansa, bari mugama wan nan ya?in na gurin waccen makirar hajjan san nan na waiwayo kansa.

Ko minti biyar ba'ayi ba suka ?araso gidan hajja wanda suna shiga gidan gaban Rashida ya faWi saboda ganin motar ya Aliyu a fake shaidar yana cikin gidan.

Ganin sun fito Rashida ta kasa fitowa sai da kyar san nan tana wani baya-baya yasa maman mu ta finciko hannunta tace.

"Uwarwa kike jin tsoro kike baya -baya? Cikin ?ar fargaba Rashida tace

"Daman naga kamar ya Aliyu yana cikin gidan ne shiyasa, dan Allah maman mu ko zamu tafi gobe madawo?

Cikin Waga murya maman mu tace "bantan uba, saboda kinga dodon ki shiyasaka zaki bamu kunya? To baki isa ba, yau Aliyu ko tsirenki zaiyi wallahi sai mun shiga gidan nan kuma mun aiwatar da Abinda ya kawo mu.

Suna tafe a cikin gidan maman mu tana ikon Allah, wan nan gida kamar kullum ?ara ?erashi akeyi, kigafa babu Abinda yayi wallahi, ga tulin arzu?i, ke kiga motoci kamar ka sata ka gudu, oh! rayuwa, bayan fa mutuwar Rashida babu yadda banyi ba yayar ku tazo gidan nan ta fara aiki koda da rainon kine ko Allah yasa babanki ya aureta ya sama miki uwa amma shegiyar matar nan hajja ta hana, gashi nan a yawon banza da zubar da mutunci akayi ajalinta ko auren batayi ba, kai wallahi Allah ya isa tsakanina da wan nan matar. Ta ?arasa tana share hawaye da fatar majina.

Ita dai Rashida batace komai ba sai rarraba idanu da rawar kyarma da take dan tasan yau Allah ne kaWai zai iya kwatar ranta a wajen ya Aliyu, dan tasan duka na musamman zai mata tunda ta kawo mutane har gidan su aci mutuncin mahaifiyar sa.

*Maryam*

A wan nan watannin da Nasir yayi da dawowa suka fara keSawa tafara jin canji a cikin jikinta, jitake kamar tanada shigar ciki amma ta kasa gasgatawa saboda tunda ta warke bata taSayin period ba , hakan ya tabbatar mata ba ciki ne da itaba dan su kansu yaran guda nawa suke da zata yi musu ?ani ko ?anwa?

Kamar yadda taso yau taje gidan samira kuma suna zaune suna hira tare da tuna Abinda ya wuce, tsaki samira tayi tace.

"Wai dan Allah ya Nasir bazai saki wacce annobar ba? Wallahi na tsani shegiya, banason ko tuna sunanta.

Murmushi Maryam tayi tana lumshe idanuwa dan tasan ko giyar wake Nasir yasha bazai iya sakin Rashida ba dan taga Alamar hakan, amma sai ta waske maganar tace

"Ni wallahi bama nason yasaketa samira, badan komai ba kodan yaran dake tsakanin su da ita, kuma kinsan shifa so babu ruwan sa da munin hali ko kyawun hali, san nan ni a kullum fatana shine Allah yasa Rashida ta shiryu ta gane Allah Waya ne bashi dana biyu ya dawo da ita mu zauna Lafiya babu cuta babu cutarwa.

Sakin baki samira tayi kamar yawu zai zubo tana harar Maryam tace

"Wai ke Maryam kinada hankali kuwa? Anya wan nan shemarwar da Rashida tayi miki bata shafi tunanin kiba? Yo banda haka da bakinki kike fatan wan nan iftila'in ta dawo muku gida? Gaskiya Maryam baki da hankali, toko ni daba wani abune ya haWani da ita ba wallahi bana fatan ko a hanya mu haWu da ita ballantana zama waje Waya, kuma bari kiji infaWa miki, muddin kina nunawa Nasir wai kina tausayin Rashida kodan ?a?a ko kuma makamancin haka kina nan sai dai kiji ya dawo da ita ta cigaba da mulkinta akanku san ranta, kuma kibar ganin aikinta na Saci wallahi wan nan karan idan tadawo da hannun ta zata kasheki a Wauki gawarki, dan kaWan daga cikin aikinta kenan.

Kuma su yaran da kike zance, bata bar miki ba? I, nace tana sane da yaran ta watsar dasu ta Wauki miji suka shiga yawon duniya, wallahi ki rufawa kanki asiri Maryam ki kuma rufamana dan idan ke baki san ciwon kanki ba mu mun sani.

"Ta tabbata Maryam ciki gareta domin tana faWawa samira yanayin da takeji tace yasin ciki ne da ita kuma bara ta gwada mata tagani, ana gwadawa kuwa sai ga ciki raWo raWo ya fito alamar ma yaWan kwana biyu, kallon Maryam samira tayi tace

"Kodan wan nan da waWan nan kirufawa kanki asiri kibar zancen wan nan wawiyar Rashidan marar tsoron Allah, samira ta faWa tana nunawa Maryam cikin jikinta da kuma ?an biyu daketa wasa da yaron samira.

*KUTSE*

*PAGE 57*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Ya Aliyu*

Ya zata zuwan nasu Rashida na mutunci ne shiyasa bai tanka musu ba ya cigaba cin apple Winsa yana danne danne a waya, dan koda suka shigo kallo Waya yayi musu ya Wauke kai sai da Rashida ta gaidashi ne ma san nan ya Waga mata hannu batare daya kalleta ba, su maman mu kuwa ko arzu?in kallon su baiyi ba bare ya gaida su, rumi rumi suka gaisa da hajja da kuma Rashida dan ko kaWan hajja bata nunawa Rashida Sacin ran Abinda tayi ba sai ma camata datai ya jikin nata tace da sau?i.

*Maman mu*

Kallon wula?anci tayiwa hajja tana gyara zama tace.

"Yo ai jinake idan kikaga Rashida ko kika ganmu bazaki ganemu ba, amma abin mamaki sai gashi kin fahimce mu kuma kin gane Rashida.

Hisunul Muslim Win dake hannun hajja tana karantawa ta ajiye tare da cire glass Win idanunta ta kuma kallon maman mu tace.

"To ai kiyi ha?uri baiwar Allah na baku wajen zama ne kawai Saboda fuskar Rashida, amma ku kuwa ban sanku ba bare na ganeku.

Cikin fushi da Waga murya maman mu tace "ai bazanyi mamaki ba kam idan kikace baki sanni ba Hajja, A, bazanyi shakkun ?aryata sanina da kikayi ba, to taya ma zakice kin sanni tunda kin kashe ?ar uwata san nan kinyi kane kane da ?ar Waya data haifa kuma kinsa ?a?anki sunyi bake bake da dukiyar ta, ai bazaki gane ne niba.

Ajiye apple Win hannunsa ya Aliyu yayi tare da juyowa yana kallon maman mu da fuskar sa wacce bata ko sauya yanayin fushi yace.

"Ke dalla malama daga ina? Ko kuwa haukar dangin naku har takai ku kwaso ?afa kuce zaku zo har gida kuci mutuncin masu mutunci?

Kai maman mu ta Waga ta kalli ya Aliyu kafin tatashi tsaye tana Waura mayafinta a ?ugu tace.

Daga gani kaine Aliyu futsararre, kai waye dazaka sakamin baki a cikin Al-amurana? Ko kuwa dakai nake magana? Inace da uwarka nake Magana bada wani ba?

A hasale ya Aliyu yayi kanta yana huci dan ya tsani matar tun a ganin farko san nan ta tsaya a gabansa tana masa magana gatsal kamar ?anwar babarsa.

Da sauri hajja tace "Aliyu, kallonta yayi da magiyar ya barta ya koya musu hankali sai kawai hajja ta Wauke kai tace "nemi waje ka zauna kuma banason ?arajin muryar ka a wajen nan.

Cikin ladabi ya Aliyu ya zauna amma zuciyar sa da gangar jikinsa mazari kawai suke dan kaWan yake jira ya far musu, daman ita Rashida ta kasa kwakwaran motsi hasalima bayan kujera ta shige take le?en Abinda ke faruwa.

Nuna ya Aliyu maman mu tayi da yatsa tace "ai da kin barsa ya gwada ?ashin nasa akaina yaga kozaici riba, itama Rashida badan komai yaci galaba akanta ba Saboda ba dahuwar ?ashin mu bace, amma kasani kayi na farko kayi na ?arshen taSa min ?a, wallahi tallahi idan ka kuma kuskuren taSata to faWan nawa ne bana kowa ba, anan zaka gane faWa da aljan babu riba ?ila ka shiga hankalin ka.

Shiru ya Aliyu yayi bai kulataba saboda duka idanun hajja akansa yake taga kozai saSawa umarnin ta ya tanka mata shiyasa yayi shiru .

Wani babban Abinda ya saka Aliyu mazari shine, kawai wai sai yayan su zita ya tashi yana kallon ya Aliyu da murmushi ganin ya?i magana a nufinsa zai ci galaba a kansa yace.

Ka kiyayi buzaye Aliyu, bamu da daWi haka bamu da imani a wani lokacin, dan haka ka buWe kunenka kaji da kyau, kodai ka faWawa wan nan azzalumar uwar taku...ya faWa yana nuna Hajja.

Wani kukan kura ya Aliyu yayi tare da sakarwa yayansu naushi a baki wanda daman tuni ya dun?ule hannun sai yanzu ya samu damar aiki dashi, kwalar rigarsa ya Aliyu ya dam?a tare dayi masa wata iriyar azzalumar sha?a kuma ya kafe shi da idanun sa masu kama dayaci bala'i yafara jijjiga wuyansa yana cewa.

"Maimaita Abinda ka faWa yanzun nan.

Kacaniyar kwace kansa yayansu yafara yana zazzare ido dan sha?ar da Aliyu yayi masa kamar bata mutum ba, maman mu ganin za'a kashe mata Wa yasa ta kwarara wani ihu tana faWin ta shiga uku ta SalSalce azo a taimaketa.

Ita kanta hajja tashi tayi tana ri?e Aliyu tana faman ya sake shi amma fafur ya?i sakinsa dan Aliyu so yake ya kaishi lahira a rufe babin su Rashida, ita kuwa maman mu ganin ya Aliyu ya?i sakin Wanta haka ta daddage ta kafa masa cizo a hannunsa ta dunga gartsawa amma ya Aliyu ko gezau baiyi ba, da gayaji da cizon data ke masa haka yasa hannu ya shemeta gefe ta faWi wanwar akan glass Win dake tsakiyar Wakin goshinta ya datse, ita kuwa Rashida ta kasa kataSus domin dataga bala'i yayi bala'i sai tafara sakin futsari a tsaye tana rawar kyarma kamar mai farfaWiya.

A guje hajja tafita tana kwalawa hadiman gidan kira da suzo su taimaka musu, ganin ba ji zasuyi ba takuma keta da gudu tayi wajen bell tafara danna ?a rarrawa wacce ta jawo hankalin masu aikin suka garzayo wajen hajja.

Amma inaaaaahhhh kafin sukai ga ?arasawa tuni ya Aliyu ya sumar da yayansu ya watsashi gefe guda kusa da uwarsa da jini ke tsiyaya a goshinta.

Wani irin muzurai ya Aliyu ya shigayi wanda duk wanda ya shigo ya haWa ido dashi baya kuma kuskuren ?arasowa wajensa sai dai subi bango su sulale, sai da ya Aliyu yagama mai da numfashi san nan ya kalli Rashida wacce numfashinta ya kusa Waukewa yayi mata wani kyakkyawan gargaWi san nan ya fice daga falon duk da kiran da hajja take kwala masa.

Su yayan mu anji maza dan koda aka kaishi asibiti sai da ya daWe bai farfaWo ba san nan yadawo hayyacin sa, ita kuwa maman mu kukan da take ya wuce misali dan batayi tsammanin irin wan nan Wibar albarkar na Aliyu ba, a gaban uwarshi zai nemi kashe mata Wa? A gaban uwarshi zai bugeta tafaWi taji ciwo har haka? Lallai ya zamar mata wajibi ta Wauki kwakwaran mataki a kansa koda a hukumance ne, dan wallahi bazata bar garin nan batare data tattara dukiyar Rashida tatafi da ita ba, goshin ta ta taSa wanda ke nannaWe da bandage tace, Allah ya isa tsakanin mu dakai, kuma wallahi zakaga gatan mu, Insha Allah sai Rashida ta zamar muku ciwon ido.

Kwanan su maman mu uku da zuwa gidan Rashida maman mu ta kuma Sallo wata masifar, fita tayi tana tambayar inda zata samu kotu domin takai ?arar su Aliyu, wani mai shago ta samu take bashi labarin ?arya nan yace mata ai ba'a zuwa kotu sama taka sai an dan gana da police station san nan za'a turasu kotu.

Maman mu dai bata baro waje ba sai da ta tabbatar an kaita police station ta shigar da ?arar su hajja da ya Aliyu san nan tatawo gida.

*Rashida*

Cikin tashin hankali take kallon maman mu tace

"Haba maman mu dan Allah, taya zakiyi min haka? Sai ta fashe da kuka tace "ya zakije kiyi abu batare dakin sanar dani ba? Kinsan suwaye kikai ?ara kuwa? Gaskiya maman mu baki kyauta min ba.

Kallon rashin wayau maman mu takebin Rashida dashi san nan ta kwaSe baki tace

"Yau kijini da yarinya marar wayau, banda shashanci ina tsaye kan ?afafuna danna samo miki ?ancin ki amma ke kina gwasalewa? To wallahi Rashida baki isa ba, dole ne mu samowa kanmu ?anci a wajen wan nan mai ?arfin kamar hukuma, dan wallahi sai yasan ya taSani ni amabuwa.

Cikin kuka Rashida ta girgiza kai tace "baki san wanene ya Aliyu ba maman mu, yadda kika san hukumar haka yake da ?arfi, kuma wallahi yadda yake da ?arfi hakafa yake a hukumancen, nidai gaskiya maman mu kin cuceni wallahi, yanzu ya zanyi dasu hajja ne? Gaba Waya shikkenan ni Rayuwa ta a babun ba Wulahu zata ?are?

Haka zan dauwa ma babu miji san nan ?an uwan nawa ma zamu rabu dasu? Kina ganin fa ko yarana har zuwa yanzu ban sakasu a cikin idanuna, shekara Wayafa rabona dana gansu, nidai ina cikin shiga uku wallahi.

Baki maman mu ta kwabe tana shan lemo tace "ke Rashida, ki sanifa saika rasa wani abin san nan zaka samu wani bin, dan haka wallahi ina nan akan ?afafuna sai mun shiga kotun nan da waWan nan azzaluman mutanen, ai ba wani abin zamu nema ba, ha??inki na dukiyar ki kawai zasu bamu, san nan daga bisani mu nemi ha??in cin zarafin dasu Aliyu sukayi mana, shi kuma wancen ja'irin yaron ki barni dashi, Nasir ba, wallahi sai ya gwammace ?ida da karatu idan ya shiga hannuna.

Kai Rashida ta murgina tana tunanin halin da zata shiga idan aka yiwa su hajja wan nan cin zarafin, cikin fushi tatashi tana shigewa Waki dan tarin ba?in ciki.

Kallon maman mu yayansu yayi yace

"Kinga maman mu, ki janye kai mutanen nan kotun nan, ki bari da kaina zanyi maganin abin.

Hararar sa maman mu tayi tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login