Showing 135001 words to 138000 words out of 175193 words

Chapter 46 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

531

gwasale shi tace "kai taficen, inace nan ri?o Waya wan nan shegen yaron yayi maka ka sume, shine zakace zakayi wani maganin su? Dalla ware, nifa inajin ma gida zaka koma gobe saboda zuwanka bashi da amfani.

Da sauri yayan su ya tari numfashin maman mu yace

"daman fa tarashi nakeyi kuma lokaci Waya zan dam?eshi, kai maman mu ta dungure masa tace, wallahi idan bakayi min shiru ba saina cire maka hakwara.

Shiru yayansu yayi tare da matsawa gefe yakame bakinsa yayi tsit dan yasan halin maman mu, Wan tama bata kyaleba indai akan son zuciyar tane.

*Washegari*

Tun safe maman mu take bugawa Rashida ?ofa akan ta buWe tazo ta raka mai kai sammaci gidan hajja dan yaje ya mi?a musu ta karda, cikin Sacin rai Rashida ta kalli maman mu tace

"Wai maman mu meyasa kike haka ne? Taya zaki dunga abu babu lissafi? Gaskiya nidai ki rabu da wani zuwa kotu ki rabu dasu.

Jingina da bango maman mu tayi tace

"Billahillazi sai an kai musu, ke bara kiji na faWa miki, wallahi ko za'ayi ya?in duniya na uku wallahi sai an kai takardar nan, dan haka kifito ki rakasu ko kiyi musu kwatance.

Tsaki Rashida tayi ta juya tanajin kamar ta sha?e maman mu ta buga ta da bango dan takaici, zama tayi akan kujerar Wakinta ta fashe da kuka, tunanin rashin dacewar Abinda maman mu takeson yi takeyi, taya zata bada goyon baya a maka waWan nan mutanen bayin Allah a kotu? Kamar hajja, ita wai zata kai hajja kotu? Da gudu Rashida ta mi?e ta fito falo dan jin wai maman mu ta tasa ?eyar mai kai ta karda zasu nufi gidan hajja dan kai sammaci.

*KUTSE*

*PGAE 58*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Ya Aminu*

Cikin Sacin ran ganin kukan hajja ya zamo daga kan kujerar da yake zaune tare da kamo hannunta yace.

Kiyi ha?uri ki daina kukan nan hajja, badai kotuba?suje kotun hajja, ai hujja a bayyane take, dan haka babu wani mahalu?in da zamu Wauki zunzurutun uwar dukiya mu bashi batare da tantance waba, musamman waWan nan jahilan mutanen wanda ba ilimine ya wadace suba.

Kai Ahmad Wan autan hajja a maza wanda tayi goyon su da Rashida ya girgiza yace

"Ni Abinda yake bani mamaki bai wuce yadda Rashida duk ta canza haka ba, nifa abin yazo min a wani iri, dan haka gaskiya inason ganin Rashida yaya.

Hararar sa ya Aliyu yayi wanda ya koma gefe yanacin Waci san nan yace "ai daman kai baka da zuciya a ?irjin ka Ahmad, kasan dai duk cikin nan babu wanda zaiyiwa Rashida sharri ko? Badai ka dawo ?asar ba, to ka zuba idanuwa kaga Abinda zai faru nan gaba, dan wataran sai ka rufe idanuwa kace Rashida ba jinin ka bace indai muna raye.

Hawaye hajja ta share ta fara magana cikin karaya tana cewa.

"Wai Rashida? Rashida ce zata kaini kotu dani da ?an uwanta? Lallai ne, daman ance Wan wani bazai taSa zama naka ba, ba gori zanwa Rashida ba amma nice duniyar ta baki Waya, dan haka babu komai watarana sai labari kuma shukar da mutum yayi watarana shine zai girba.

Ta kar dar ya Aliyu ya Wauka yana cewa

Aina faWa miki yarinyar nan ta fara haukacewa hajja, amma da nayi magana sai kice son raina nake faWa saboda bama jituwa, wallahi inada ya?inin kishin nan da yarinyar nan takeyi yafara taSa mata kwakwalwa, amma duk da haka kiyi ha?uri hajja muje kotun, ai shi al?ali ba mahaukaci bane, san nan ma gamu da kwararran lauya, yafaWa yana nuna Ahmad wanda ko sati baiyi da dawowa daga Egypt ba, ya gama karatun lauya kuma yana aiki acen, yanzu ma matar aure ya samu shiyasa ya dawo gida a gama shirin auren sai ya koma da matar sa.

Kai hajja ta girgiza tace "Allah ya sawa?e Aliyu, bazamu je kotuba, ai abin kunya ne ace mun tsaya Shari'a damu da ?ar mu a idanun duniya, sai ta kalli ya Aminu tace, inason ka basu nan da sati Waya su dawo, kai kuma a wan nan satin kayi ?o?ari ka tattaro dukiyar Rashida kaf Winta karka bar saura ka kawota gabana, inason ka tawo da takardun rabon gadon nan ayi komai a rubuce mu basu a wuce zancen da kuma tayar da zaune tsaye.

Kar kuma ran wani ya Saci a cikin ku da kar Sar wan nan dukiyar, domin kunsan kowa da tashi kuma kowa da abarshi yake tun ?aho, kuma yanzun ma da Rashida tace abata abarta ai dai-dai tayi, tunda daman ya dace abatan tunda tayi Aure, kuma ni ba kar Sar dukiyar ce tayi min ciwo ba, kotun da Rashida takai mu shine babban Abinda yayi min ciwo, ta ?arasa tana cije leSen bakinta na ?asa.

*Rashida*

A wan nan kwana Wayan nakai takar dar sammaci da akayiwa hajja sai data fita daga hayyacinta, badan komai ba saboda abin ya bala'in dukan zuciyar ta, itafa da maman mu tace zata Wauki mataki batayi tunanin wan nan Wanyen aikin zata yiba, gashi yanzu ta Sallo mata ruwan da tare zubar sa sai rabbul izzati, hawaye ta share tana kallon maman mu tace.

"Gaskiya maman mu zuwanki bai zamar min Alkairi danake tunani ba, ni nayi tunanin da kikazo abubuwa kikazo gyarawa ba Satawa ba, yanzu dan Allah da wane idanun kikeso na kalli su hajja nan gaba? Nifa hajja uwata ce kuma rabin rayuwata, duk da ba itace ta haifeni ba ai itace ta shayar dani dan haka da uwar data haifeni da kuma hajja duk Waya suke a wajena.

Saurin dokewa Rashida baki maman mu tayi tace

"Tuf-tuf, maza ki zubar da wan nan ba?in yawun mai wari na bakinki, banda ke mahaukaciya ce ta yaya zaki haWa uwar ki wacce ta mutu ta sanadiyyar haihuwar ki da wacce ta shayar dake? Anya Rashida zakiga Annabi kuwa? Uwarki ta mutu Saboda zuwanki duniya san nan ki haWata da wata mace? To wallahi na ari bakin Rashida uwarki nace Allah ya isa ban yafe miki ba wan nan kuskuren da kikayi, kuma banda taSewa ita uwar shayarwar har wata tsiyace? Ke barafa na faWa miki kiji, ita hajjan da kike fifitawa fiye dani na fita a wajen ki, ni yayar uwarki ce ita kuma kishiyar uwarki ce, kuma ma naga ita hajjan bada nononta ta shayar dake ba, inacen garin mu amma na baza ?an saka ido sun sanar dani da nonon akuya aka shayar dake, kuma ban musaba san nan ban karyata ba dan nasan hajja bason uwarki takeba dan haka kozaki mutu bazata iya baki nononta kishaba.

Shiru Rashida tayi tana nazarin magan ganun maman mu wanda tasan babu gaskiya ko Waya a cikin su sai tsagwaron son zuciya da kuma son dukiya.

Kai maman mu ta dungure wa Rashida wacce ta faWa tunani tace "kodai baki yadda da zance na bane naga kin tafi tunani? To idan ma kin yarda kanki, idan ma baki yarda ba kanki dan wallahi a zancena babu ?arya ko Waya, kumama idan kikace nayi ?aryar da uwarki Rashida kike bada niba.

HaSa Rashida ta tallafe tana nashiga uku nikam, wan nan wace irin masifa ce? Dan Allah maman mu yaushe zaki tafi?

"Ahayye nanaye, maman mu ta faWa tana tafa hannu wa tana kallon Rashida, san nan tace "zuwan nawa ne ya zamar miki bala'in? Hnmm, to wallahi bazan tafiba Rashida, idan kuwa kikaga nabar garin nan to dukiyar ki ta dawo hannun mu tukunna.

Tashi Rashida tayi fuuu ta wuce Waki tana tunanin mafitar da zata nema wajen hana zuwan kuWinta wajen maman mu dan tasan muddin kuWinta sukazo hannunta tofa sun gama babbakewa kenan kamar wutar kara.

Ita kuwa maman mu Rashida na shigewa Waki tace ", hnmmm, dani kike zancen Rashida, badai nice masifar ba? Zakiga masifa ganin idonki a lokacin da masifar ta tunkaro ki, ai wallahi tunda mai duma ya sanar dani babu aure a tsakanin zita da Nasiru wallahi kema sai na kassaraki, bari dai ki gani, ta faWa tare da tashi ta Wauko turaren haya?in damai duma yabata danta turarawa Rashida idan ta fara gaddama.

*****

*Nasir*

Yana tsaye a bayan Maryam yana tsokanar yadda take tura ciki tana tafiya, juyowa tayi tana kwaSe fuska tace

"Haba hubby na, menene haka wai? Maimakon ka dunga min sannu sai ka dunga kwaikwayo na? Nidai gaskiya kabari, ta faWa tana sakar masa Wan dukan wasa a ?irjinsa.

Kamo hannunta Nasir yayi yana dariyar tsokana yace

"Ai abinne yake bani nishaWi zumata, kinga girman wan nan cikin kuwa? Ciki Wan wata biyar amma kamar kin kusa haihuwa, anya kuwa bana ba ?an uku zaki haifo min ba? Ya ?arasa faWa yana mata cakulkuli.

Gan tsarewa Maryam tayi tana dariyar dole tana ya kyaleta bata so.

Suna cikin wan nan wasan ne saiga su hibba sun shigo da gudu itama ita da mahbub suna wasan Suya da kai ?arar juna, kamosu Nasir yayi yana dariya tare da Waukar su ya saka akan cinya yana wasa da bit Win da aka yiwa muhibba kitso dashi.

Kallonsa Maryam tayi tana murmushin ganinsu cikin nishaWi, shima kallon Maryam Win yayi yanajin sonta na kuma zagayawa ko ina kafin ya haWesu baki Waya ya rungume yace.

"Ina sonku da ?aunar ku irin sosai Win nan, ya ?arasa yana dafa cikin jikinta dan shima ya san anaji dashi.

Hawayen farin ciki ne da kuma tausayin kansu ya kamata tanaji a ranta daman su dauwa ma a cikin wan nan farin cikin har abadan batare da kutsen wata annoba ba a tsakanin su.

*Bayan sati Waya*

Da safe Rashida tatashi daga barci taji gidan tsit, batasan Abinda yafaru haka taji babu motsin kowa ba dan a iya saninta tun sanda maman mu sukazo gidan suka zamar mata tom and Jerry, domin kwata kwata basa barci kamar Sarayin dare, Wakin zita ta le?a ta ganta ta shagala tana barci kamar matacciya.

Juyawa Rashida tayi ta le?a Wakin da maman mu take taga wayan bata nan ita da kayan ta, da sauri ta sauka ?asa dan ganin yayan mu nan ma taga wayam baya nan babu kayansa, juyawa Rashida tayi batare da tunanin komai ya faWo mata a rai ba dan tasan dai ?alau suka kwanta tare kuma sai ta wayi gari taga basa nan? Saman ta koma tafara tashin zita tana tambayar ta inda su maman mu suke.

Ido zita ta fara mutsittsike wa tana mi?a da sakin Wan ?ara batare da salati ba, cikin Sacin rai Rashida ta daddage ta WaWawa zita duka a cinya cikin karaji tace "tashi dan ubanki.

A gigiece zita tashi tsaye tana sosa wajen tana rarraba idanuwa hagu da dama.

Tsaki Rashida ta saka tana ficewa daga Wakin dan daga ganin zita bazata bata Abinda takeso ba, tana fita falo ta nemi kujera ta zauna ta Wauki wayarta dan ta kira maman mu taji inda suka tafi da sanyin safiyar nan?

Kira wajen goma Rashida tayiwa su maman mu amma daga ita har yayan nasu wayar bata shiga, cikin Sacin rai Rashida ta shiga WhatsApp saboda taga Abinda duniya take ciki, ai kuwa tana buWe data sa?on ya Aliyu tafara cin karo dashi, da sauri ta buWe sa?on tana rarraba idanu dan ganin Abinda kardun daya turo mata suka ?unsa.

"Minti Waya, minti biyu minti uku.

Wata irin kururuwar ihu mai cike da tashin hankali Rashida ta zuba tana faWowa ?asa tare da aza hannu aka tana faWin ta shiga uku ta lalace, sai data Wauki sawon minti ashirin a zaunen tana rufzar kuka da juyayi san nan taga zaman bazai mata ba, shiyasa tatashi da sauri tare da zarar mayafinta ta fice daga gidan da gudu, da yake daga gidan nasu babu nisa da titi tana fitowa kuwa ta faWa a daidata sahun data tsayar.

*****

Suna zaune gaba Wayan su a falo suna jimanta Abinda yafaru a tsakanin su da Rashida, kwasam sai ga Rashida ta faWo falon tana kuka wiwi kamar an zaneta, hannu takai zata ri?e ?afar hajja ya Aliyu yayi saurin tan kaWe hannun yana cewa.

"Karki ?ara kuskuren taSa mana uwa tunda baki da haWi da ita? Ko kin santa ne? Da sauri Rashida ta kumayin kan hajja tana cewa

"Itace uwata, banida wacce tafita, dan Allah kuyi min ha?uri ku gafarce ni, cikin jin haushi ya Aliyu ya mi?e tsaye tare da kama damtsen Rashida ya tasheta tsaye, bata gama tantance wa ba ya Waga hannu tare da kwasheta da marin da sai data hantsila san nan yayi mata nuni tare da cewa da kakkaurar murya.

"Fita daga cikin gidan nan, ko kin mata baki da rabo kona sisi a cikin sa? ke, kinga, duk ranar dana ?ara ganinki a cikin gidan nan wallahi saina karya miki ?afafu, dan haka koma wace gulmar ce ta kawoki to bata samu ?ar Suwa, idan kuma ha??in da kika kai kotune na a karSa miki to ki duba wayarki mun tattara komai mun dan?awa dangin uwarki, fitaaaah, ya?ara Waga murya yana zazzare mata idanu.

?ara Rashida ta saka tana kallon ya Aliyu tana haki tana cewa

"Bazanje ko inaba ya Aliyu, sai dai ka kasheni, wallahi ina cikin gidan nan inji mayya a Wakin me jego, kuma wallahi zama daram abayan ku kamar doro, sai kuma ta sassauta hakin nata da kukan da takeyi kamar zata haWiyi zuciya tace.

Dan Allah ku tausaya min, ta faWa tana sulalewa ?asa tana ri?e ?afar hajja wacce ta haWe girar sama data ?asa ta kauda kai , dan duk Abinda akeyi a cikin falon bata kallesu ba, jin da hajja tayi zata fara kuka saboda kukan Rashida itama sai kawai ta fusge ?afarta daga hannun Rashida tatashi da sauri ta shige Wakinta tare da turo ?ofa ta saka mukulli.

Hajja na shiga Waki ta jingina da bayan ?ofa tana share hawayen dake zubar mata akan kuncinta tana cewa

"Allah ka gani, ya Allah ka yafe min , Allah karka kamani da ha??in wan nan marainiyar, nayi iya ?o?arina wajen ganin yarinyar nan ta zama ta gari kamar yadda sauran yarana suke, sai dai gashi ban samu nasara ba, ya Allah ka yafe min, hajja ta faWa tana sulalewa ?asa ta zauna.

A falon hajja kuwa ya Aliyu ne keta surfawa Rashida masifar idan bata fita ba zai SaSSalata, Rashida kuwa kafewa tayi a wajen tanata kukan tausayi tana kallon ya Aminu danya tausaya mata amma babban tashin hankalin ta maganar data fito daga bakin ya Aminu wadda yace.

"Kifita daga gidan Rashida, kuma karki ?ara waiwayowa baya domin muncireki daga cikin dangin mu, kuma cirewa tahar abada.

Girgiza kai Ahmad yayi yana niyar magana tare da tashi tsaye yayi wajen Rashida tausayi fal ranshi da kwantattun hawaye a idonsa.

"Me yasa kikayi mana haka Rashida? Ahmad ya faWa yana kallon ta, Me yasa? Basu san ya Aliyu ya tawo wajen su ba sai gani kawai sukayi yaWan han kaWe Ahmad yana kallon Rashida yana cewa

"Ya isa haka? Komai ya ?are, ya isa Madam Rashida, yana gama faWar haka ya dam?i hannunta tare da fita da ita daga falon har wajen far fajiyar gidan, yana zuwa kuma ya watsar da ita a wajen ya koma cikin gidan yana sakin ajiyar zuciyar sun yar da kwallon mangwaro sun huta da ?uda.
*KUTSE*

*PAGE 59*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maman mu*

Kallon tulin kuWin da tayo canjin su daga nera suka zama CFA tayi tana washe baki, tasan tunda suke kaf zuriyar su babu wani mahalu?in daya taSa ri?e irin wannan ma?udan kuWaWen idan ba Rashida ba, gashi mallakin Rashida ya zama nata, ita tana ganin barin ma agadez zasuyi su canza ?asar da zasu koma da zama dun-dun-dun, dan yadda taga wan nan kuWin soyayyar su ta shiga zuciyar ta tofa babu yadda za'ayi ta yadda ta rasasu koda zata rasa ranta a kan haka.

Kuma cigaba da irga su tayi tanajin nishadi da farin ciki a cikin ranta, ganin ta kasa iya cigaba da irga yasa ta tattara kuWaWen ta zubasu a cikin jakar da aka basu ita ta zuge tare dayin matashin kai da ita tana tunanin gari ko ?asar da zasu koma, amma a ranta tanajin basai ma sun koma wata ?asar ba, kawai zasu tattara ne ita da iyalanta su koma babban garin Niamey dake ?asar Niger dan su cigaba da rayuwa a can.

Kallon dillalin gidan maman mu tayi tace

"amma kai dai anyi Wan Sarauniya,duk girman wan nan gidan irin tayin da zakayi masa kenan? To tunda na fin ?arfi ne sai ka Wauka aka katafi dashi, Sarawon banza kawai, nifa daman badan wai bu?atar kuWi yasa zan sayar da gidan nan ba, zan sai dashi ne saboda bana bu?atar ?ara ganinsa dan ya lalace, amma tunda abin yazo dason zuciya kawai ka barshi zamu rufeshi ko muyi sadaka dashi.

Baki dillali ya kwaSe zuciyar sa cike dajin haushin maman mu da tace masa Wan Sarauniya, amma babu komai dama indai ba?ar magana ce sun saba jinta daga wajen mutane mabanbanta, dan haka sai kawai yayi tsaki yayi gaba yana cewa ita tasani idan ma babbaka masa wuta zatayi ai natane babu mai hanata.

Yayar zita wacce akoda yaushe take yawan bawa maman mu shawara ce ta kalli maman mu tace.

Amma gaskiya maman mu Abinda fa kikayi ha'inci ne, taya zaki gudowa da Rashida dukiya san nan kizo kifara shagare walle Winki da ita alhalin ita wacce ta mallakin kuWin bata saniba? Kuma san nan yanzu da zaki tattaro mu kice muzo mu koma Niamey to a ina kikeso mubar mazajen namu da ?a?ayen namu?

?an kwali maman mu ta turo gaba tana hararar yayar zita tace

"To ?ar ba?in ciki, ashe a masuyi maka ba?in ciki harda Wan daka haifa? Lallai duniya tazo ?arshe aradu, to bara kiji, wan nan kuWi da kikeji da gani gumi nane bana Rashida ba, tunda ita Rashida ma dukiyar bata dameta ba, kinga kenan tunkan ta mutu ta fara rabon gado domin da hannunta ta saka hannu a cewar ta mallaka min dukiyar ta, dan haka duk wani mai baki da kunu ma yaja bakinsa ya zu?e dan wallahi duk mai ba?in ciki sai dai ya mutu, san nan da kike cewa idan kin tafi dawa zaki bar mijinki? To bama sai kin tafiba, ki zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login