Showing 87001 words to 90000 words out of 175193 words

Chapter 30 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

544

mutuwar zaune, gabanta ya isa har numfashin sa na canja yanayi yace

"Me baban mu yayi miki? Shiru Rashida tayi ta?i magana ko motsi kamar an dasata a wajen.

Wata irin tsawa Nasir ya dakawa Rashida yana cewa mai baban su yayi mata?

*Rashida*

Tunda Nasir ya fito ya ri?e Maryam taji tsigar jikinta tashi jijiyoyin zuciyar ta sun tsinke, ya fito ya ganta a zaune matarsa tana marinta harda niyar naushi amma shine maimakon ya nufo gareta sai yayi kan maryam yana rarrashinta? Wani ?aton ba?in cikine ya dasar mata a zuciyar ta shiyasa tayi mutuwar zaune dan koda Nasir ya matso wajenta yana mata magana batajin Abinda yake cewa wa sam.

Shi kuma Nasir ganin Rashida ta kafeshi da ido ta?i bashi amsa yasa ya nufota gadan gadan domin yabata hukunci.

Shi bai kula da ?afar Rashida ba a wajen wacce ta mi?e ta domin tatashi ai kuwa ya take ?afar sai jin kukuwar ihu yayi kamar zata mutu, kuma a take ta saki futsarin daya matseta a zaunen, gurin da take kallo ya kalla sai yaga ashe ?afarta ya take mata sai ya matsa baya yanajin ba daWi a ransa amma madadin yabata ha?uri ya rarrasheta sai kawai ya juya ya koma kan maryam wacce har lokacin kuka takeyi ya ri?e kafaWarta tare da fara tafiya da ita yanajin ransa na suya da kukan da Maryam Win takeyi.

?akinsa yafara tafiya da ita domin yayi aniyar kwana da Maryam ayu kuma bayajin akwai Abinda zai hana shi.

Ita kuwa Rashida tana ganin Nasir ya ri?e kafaWar maryam yayi hanyar Wakin sa da ita tayi saurin zabura ta mi?e kamar bamai ciwo ba, kamar ba itace Wazu ta kasa tashi tayi tafiya ba.

Sam basu lura sun an kara ba sai ganin Rashida sukayi a tsaye a gabansu tana haki da nishi kamar Mayun waciyar zakanya tace.

"Heeehhh, azzalumai annamimai muna fukai, wato saboda rashin adalci shine zaka yimin satar kwana ko Nasir? To ta Allah ba takuba wallahi, billahillazi kuma babu ?aton daya isa ya shigar da wata Wakinsa muddin ina numfashi a wajen nan, karka manta fa yau kwanan ne, ko kuwa kana nufin irin yadda kayi min kwacen kwana danaje gida yauma haka zakayi min?

Yaufa kusan watana Waya ba tare dakai ba baban Halima, san nan na dawo yau ka Wauki wata wai zaku shige Waki, to wallahi baka isa ba, nima inada bu?atar mijina.

Kallon kallon mamaki akayi a tsakanin Nasir da kuma Maryam kafin daga bisani su she?e da dariya, dariya sukaita kyakyatawa Nasir harda nuna Rashida da yatsa yanayi mata kallon sama da ?asa.

Cikin ba?in ciki Rashida tafara nuna kanta da hannu tana hawaye tana cewa

"Ni kukewa dariya Nasir? Dariya fa? Ni? Menene a jikina da yake baku dariya? Ta ?arasa cikin sigar abin tausayi tana russunar dakai.

"Saboda idan kina bu?atata dame zaki biya bu?atar Rashida? Nasir ya faWa yana nunata da hannu, to bara kiji, a wan nan yanayin da kike ciki babu amfanin da zakiyi min Rashida, yanzu dai kiyi ha?uri da koma menene yake damunki ki lallaSa ki kula da kanki harki warke Rashida, sai ya ri?e hannun maryam yace

"Muje zumata, har naji zuciya ta ta wanke da Sacin ran dana samu kaina da wan nan abin dariyar da yayarki tayi, itama Maryam Win dariya tayi tace nima haka hubbyna.

Rashidan na tsaye su Nasir suka wuce suka barta tanajan majina saboda kukan da take yi, juyawa tayi cikin zafi ta nufi kichen ta zagaya baya ta Wauko robar fetur da a shana ta fito zuciyar ta na azalzalar ta da dolane ta zazzagawa Wakin Nasir fetur ta cinna masa wuta su babbake su mutu daga shi har Maryam Win, dan wan nan cin zarafin da sukayi mata ha?i?a sun cancanci su karSi hukuncin mutuwa.

*KUTSE*

*PAGE 37*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Kana ganin fuskarta kasan ta daku ba ?aramar da kuwa ba dan tasha marin da bazata iya wassafa kalarsa ko yawansa ba, hawaye ne kawai ke zuba akan fuskarta wani nabin wani dan batasan ma yana zuba ba danjin fuskar tata takeyi kamar takamu da faralayis.

*Hajja*

Cikin Sacin rai take kallon ya Aliyu wanda ya haWe girar sama data ?asa yakejin kamar ya kama wuyan Rashida ya murWe matashi dan gab take da tona musu asiri da Sata musu suna, dan yana ganin data Sata sunan kyakkyawar zuri'ar su gwara ya kasance bata numfashi a duniya.

"Yanzu me kayi kenan? Aliyu daka kasheta yanzu dame zakace min kacewa sauran ?an uwanta da sauran mutane? Wallahi baka kyauta min ba aliyu, jibi yadda kamai da fuskar yarinya kamar bata tataba, san nan dan Allah tunda kake a rayuwa an taSa yi maka irin wannan dukan kaida kake namiji?

*Ya Aliyu*

Numfashi mai zafi ya sauke yana hararar Rashida yafara magana cikin zafi kamar zai kai duka.

"Yanzu hajja matakin dana Wauka akan wan nan da?i?iyar yarinyar wacce kwakwalwar ta bata haskaka mata sai dai ta nuna mata duhu shine yayi tsauri? To wallahi hajja nayi mata da sau?i, dan data jawo mana abin faWa da gori da shaguSe a gari wallahi gwara ta mutu kowa ya huta, taya saboda batada nutsuwa da hankali ace ta zuba fetur a cikin Waki tace zata kunna a shana? Yanzu hajja da Allah bai kaini gidan ba da tuni sai dai aji mummunan labari marar daWi a family Win mu, saboda me yarinyar nan zata hana mana zaman lafiya da kwanciyar hankali? Shikkenan duk sanda akaji fitina daga ita ne, wallahi tallahi kaWan nayi mata Hajja, kuma Allah yabaki lafiya, inanan zan waiwayoki dan uwarki, duk wan nan rashin hankali da rashin mutuncin wallahi sai na sauke miki shi yafaWa yana tashi zaiyi kanta yana kai mata harbi da ?afa.

Da sauri Rashida taja Wuwawu tayi baya tana kwala ihu hajja ta ri?eta dan karta fama ciwon ?afarta.

Kwafa ya Aliyu yaja wanda yaji jikinsa yafara mazari hannunsa na rawa yanason maimaita wa Rashida Wan banzan dukan da yayi mata jiya, ganin haka yasa kawai ya kuma jan kwafa yayi waje ya Aminu na kiransa amma yayi banza dashi baiko juyo ya kalleshi ba.

*Ya Aminu*

Ido ya tsurawa Rashida cike da mamaki yake cewa

"Gaskiya kin bani mamaki Rashida, kuma wallahi abinki ya wuce iyaka har yaushe zakiyi tunanin yin kisan kai saboda baki da hankali? An faWa miki cewar kishi hauka ne wai? Ko kuwa an faWa miki mu shashashaine da zamu biye miki kina dabbancin da bazamu Wauki mataki akanki ba? To wallahi Aliyu ma ya miki da sau?i dan da ace mahaukatan suna kanshi billahillazi sai ya SaSSalla miki ?afafu idan yaso ki zauna gaba Waya kiyita jinya har illa masha Allah, idan yaso sai kibar mijin naki wata ta mallakeshi baki Waya.

San nan ya juya ya kalli hajja yace

Wai hajja Aliyu bai faWa miki Abinda yafaru har Aliyu yayi mata wan nan dukan?

Jijjiga kai hajja tayi tare da cire tagumin data rafka tace

"Ni bai faWamin ba Aminu, kawai dai yace sunje gidan dubiya ne suka tarar da Wanyan aikin dataso tayi na tashin gobara a cikin gidan, dana nemi yayi min ?arin bayani sai ya cemin wai ranshi a Sace yake bazai iya cewa komai ba, shine yatafi bayan ya watsar min da ita a falo jiya, sai yau kuma dayazo ai a gabanka yagama faWanshi yatafi batare daya kuma maganar ba.

Ajiyar zuciya ya Aminu ya sauke yace

"To hajja bari kiji.

Kinsan Aliyu baya gari suna dubai hutu shida yara, ajiyan fa suka dawo, yanacen amma hankalin sa yana nan, burinsa kawai yazo yaga jikin nata, kuma kinsan daman matarsa ?awarta ce sosai shine daga airport ta takura ta matsa masa akan sai taje ta ganta da jiki, suna shiga gidan fa suka haura sama sunata sallama amma babu wanda ya amsa, Abin mamaki suna shiga falon suka ga Rashida da robar fetur tana zazzagawa a Wakin Nasir zata kunna wuta tana kuka tana cewa sai ta kashe su baki Waya ta huta.

Shine fa Aliyu ya hana faruwar hakan ta hanyar buge hannunta cikin Sacin rai kuma yayi mata wan nan dukan, shi Nasir da matar tasa ma basu saniba kukan Rashida da hayaniyar Aliyu ce tasa suka tashi suka fito sukaga Abinda yake faruwa, ita matar tasama Saboda kiWima yanke jiki tayi ta faWi a sume.

Yanzu hajja badan Aliyu yajeba damai zai faru? Yanzu ita dan ubanta bazata iya control Win kanta da zuciyar taba a duk sanda suka faWa mata ba dai-dai ba? To wallahi tallahi zakici uban ki nima na daina Waga miki ?afa.

*Hajja*

"Hawaye ta share tace

"Ke yanzu Rashida bazakiyi hankali ba? Yanzu tsananin kishin naki har yakai kiyi tunanin Waukar rai? To ki iya tunawa Allah kaWai ne yake da hurumin Waukar rai ba mutum ba, kuma wallahi Rashida duk ranar da kika kuma yin ?urin cutar da kishiyar ki wallahi sai ranki yayi mummunan Saci, kin bani mamaki, ashe shiyasa kika dage bazaki biyoni gidaba saboda akwai wani mugun ?ulli a cikin ranki ko? To kisani wallahi mutuncin kanki kike zubarwa a wajen mijinki, yanzu wan nan abin da kikayi wallahi nasan Nasir dakyar zai iya cigaba da zama dake Rashida, shashasha marar tunani, nikam bara malam lawal ya dawo yayi miki ru?iyya dan ina kyautata zaton akwai aljanun dake juya kwakwalwar ki.

*Rashida*

Ita dai kuka kwai takeyi ganin kowa ya?i bin bayanta har ya Aminu wanda take fakewa a bayan sa take Abinda takeso yanzu shima yayi fushi da ita, wai ita waye zai fahimce ta? Wanene zai fuskanci halin ?unci da ba?in cikin da take ciki?

Nasir nefa yaci amanar ta yayi aure a Soye batare data saniba, kuma san nan tayi ha?uri ta cigaba da zama dashi, duk ba'aga ?o?arin taba san nan yanzu ta Wauki ba?in cikin fifita Maryam da Nasir yake yi? Wallahi basu isa ba baki Wayansu, idan yanzu Allah yakawo mai cetar su nan gaba zatayi musu talalar da babu wanda ya isa ya cecesu a wajenta.

?o?arin tashi takeyi nusaiba tazo ta tashe ta dakyar dan idan tayi ?asa da fuskarta ma jitake kamar zata faWo saboda nauyin datayi mata, da taimakon nusaiba suka shiga Waki tana Wingisawa da ri?e fuskarta da hannu bibbiyu.

Bin bayanta hajja tayi tana tausayawa halin Rashida wanda tanada tabbacin dole idan bata canza ba watarana wan nan halin nata zai kaita ya barota, ta daWe tana yiwa Rashida addu'a da kuma jin daWin nononta da tasha, dan gani takeyi daba nononta tasha ba na Rashida uwarta tasha da Abinda Rashida zatayi sai yafi haka tasani, amma bazatayi ?asa a gwiwa ba zata cigaba da yiwa Rashida addu'ar shiriya ko Allah zai tsamota daga halakar dakanta da takeso tayi.

*Maryam*

Tana lulluSe jikin Nasir tayi lamo abin tausayi tanata sauke ajiyar zuciya mai nauyi kuma akai akai, tunani take yanzu tsanar da Rashida tayi mata har takai tayi tunanin kasheta? abin tashin hankalin ma ba ita kaWai zata kashe ba harda mijinsu wanda tsanar datake mata ta shafesa.

Tana ganin barin rayuwar Nasir a wan nan takin gaskiya shi yafi mata saboda bazata iya zuba idanuwa tana ganin yarasa rayuwar sa saboda ita ba, tana son Nasir da ?aunarsa amma tabbas barinta gidansa ya zamar mata dolen wajibi muddin tanason ta kufutar dashi daga sharrin Rashida.

*Nasir*

Akai kai yake shafa kan Maryam wacce jikinta yaWau zafi sosai tun daga suman da tayi jiya da daddare, kansa ya juya ya kalli ya ransa waWanda suketa shirin komawa makaranta gobe Monday idan Allah yakaimu, baisan ya zasuyi da shiri ba tunda jarababbiyar uwarsu bata nan san nan maryam tana kwance babu Lafiya, tunani ma yakeyi kamar gobe idan jikin nata baiyi sau?i ba ya kaita asibiti, dan yau Win ma itace ta dage bazataje ba sai dai ya kaita daura, kuma a ranta ta ?uduri aniyar muddin tatafi daura to har abada bazata ?ara waiwayar Nasir ba.

*Bayan kwana biyu*

Malam lawal ya dawo kuma yazo ganin jikin Rashida wacce yanacen amma mugun aikin datayi yana tambayar sa sakamakon maganin addu'ar daya bata, tunda sukaje garin nan bashi da nutsuwar zuciya, kullum a cikin furgicin jinnin dake tsorata shi yakeyi, har fito masa jinnin yayi a zahiri da suffar tsofaffi ya sanar dashi shine mai tafiyar da tsarin Rashida a yanzu, shi kuma yana neman ya tujeshi ta ?arfin tsiya, saboda haka ya cire hannunsa daga taimakon ta dan jifa tayiwa Abokiyar zamanta bai kamata ba ita kuma yakoma kanta.

Ranar malam lawal kasa barci yayi shiyasa ya tattaro baki Waya yadawo gida batare daya gama wancen aikin da yaje yiba.

Kuma a yau ne ya ziyarci gidan hajja domin kawo ?arshen komai da komai.

Kallon Rashida ya dungayi wacce muraren ga jifane daya dawo kanta, wani ya sauka wani kuma yana kewaye da ita yana niyar sauka, bata da ibada da tanada ibada da tuni na jikinta daya sauka ma ya barta bare wanda bai ?araso ba.

Girgiza kai malam lawal yayi tare da farawa Rashida tofi kan ?afarta wanda suka fara hayewa saboda sihirin dake caccakarta, ga wani duhu da yake gani yana kewaye da gefen kwakwalwar ta wanda idan ba'ayi da gaske ba zai iya zautata.

Tunda malam lawal yafara mata tofi tafara ihu ?afarta tafara futar da wani ba?in haya?i mai kauri, san nan nan da nan ta kwanta tafara birgima tana bawa malam lawal ha?uri akan yabarta .

?afar malam lawal ya dam?a yana jijjigawa yana tofa addu'a har sai da Rashida ta suma, wani abin mamaki sai ga ?afar ta sace ?urajen sun Sace baki Waya sunyi sumul kamar basu taSa fitowa ba.

Hamdala su hajja suka dungayi wa Allah kafin daga bisani Rashida ta farfaWo tan sakin haki da ajiyar zuciya.

*Malam lawal*

"Sallama yayi gaba Waya mutanen falon suka amsa harda ya Aliyu wanda yake cin Waci kamar zai amayar da ma?ogaron sa.

"Amm daman Abinda nakeson na faWa muku game da ciwon Rashida shine.

A zahirin gaskiya Rashida itace wacce ta jawo wa kanta wan nan ciwon ba wani ba, nasan a ranku zaku dunga tunanin ko wanine ko kuma Abokiyar zamanta itace silar ciwon nata, amma duk ba haka bane, wan nan ciwon nata ya samo asali ne ta hanyar ita Rashidan da tayiwa Abokiyar zamanta jifa mummuna domin tahaukatata kota rabata da duniyar ma baki Waya, to inda Allah ya taimaki ita Abokiyar zaman nata yarinya ce mai tsananin ri?o da addini da kusanci da Allah, shiyasa koda tasha?i haya?in datai mata baiyi tasiri akanta ba, tadai shiga mawuyacin hali wanda badan akwai tsari a jikinta ba wallahi idan tafita tabar gida har abada baza'a kuma jin Wuriyar taba.

To bayan ta galabaita sai asirin ya saketa, shine yana sakinta ya dawo kan Rashida dan daman ?ai?ayi ne koma kan mashe?iya.

*Rashida*

Kuka ta fashe dashi tana kallon hajja da ya Aliyu wanda yafara futar da haya?i ta bakinsa da hancinsa, tanajan majina da shasshe?a tace

"Wallahi tallahi ba haka bane hajja, wallahi ni banyiwa Maryam asiri ba na rantse da girman Allah, dan Allah hajja karku yarda da wan nan maganar.

*Ya Aminu*

Cikin Sacin rai ya zamo daga kan kujerar da yake zaune ya zabge fuskarta da zazzafan marin da sai dayasa ta hantsula, a fusace yatashi tsaye yana nuna Rashida da hannunsa yace

"?arya malam zai miki ne? Wacece ke da har zai rasa wazaiwa ?arya sai ke? Tashi daga nan wajen kafin na murWe miki wuya dan ubanki, Shegiya mai fuskar munafukai kina tafe da wuya kamar mari?ar lema.

Da gudu Rashida tatashi tana kuka wiwi zata shige, da sauri ya Aliyu yakawo ?afa zai shemeta hajja tayi saurin tareshi dan idan ya kafta masa wan nan ?afar tasa to tanada ya?inin Salla mata Kwankwaso zaiyi dan dukansa ba irin dukan ko wanne bil-adama bane.

Itama Rashida da gudun bala'i ta ?arasa shigewa Waki tana ihu tana cewa

"Wayyo Allahna kaine gata na a duniya, bani da kowa sai kai dan kowa ya tsaneni.

*KUTSE*

*PAGE 38*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*Maryam*

Jikinta ya?i domin tun ranar da Rashida taso ?onasu ta faWi take fama da ciwon kai da zazzaSi mai zafi har rana irin tayau wacce ta kasance sati guda kenan da faruwar lamarin, gashi duk yadda Nasir yayi akan ta yarda ya kaita asibiti ta?i yarda saboda ita ji take da Allah zai Wauki rayuwar ta akan halin da take ciki datafi farin ciki da hakan.

Yau ma suna zaune akan kafet tayi fulo da cinyar sa sunashan kayan fruit sai kawai ta Wauki gwanda guda Waya ta saka a baki tare da taunawa, ai tun kafin takai ga haWiyewa wani marayan amai mai saka zafin ma?ogaro ya tawo mata a guje, da gudun itama tatashi tayi Waki tanajin wani irin tashin zuciya wanda bata taSa tsammanin akwai irinsa ba a duniya, banWaki ta shige tafara kelayashi kamar zata kwararo da kayan cikinta har ta hanci haka ta dunga zuboshi yana tafiyar mata ?wa?walwa.

*Nasir*

Daman maryam natashi yayi saurin bin bayanta yana kiran sunanta har suka shiga bayin tare, ganin aman ya?i tsayawa domin tun tana aman abincin da dakyar take iya cinsa har tadawo tana aman ruwa zalla mai yalo yalo, ganin taja numfashi ta mi?e alamar ta gama yasa yaWan matsa baya domin yabata hanya yanata jera mata sannu, ai kuwa tana Wan fara tafiya tayi taga taga zata faWi saboda jirin dake Waukar ta Nasir yayi saurin ri?eta a jikinsa yana subhanallahi, Maryam, Maryam.

Ganin tayi sanyi baki Waya ga jikinta babu kwari yasa ya zura rigarsa akan vest Win dake jikinsa ya ru?ota har ?asa ya sakata a mota suka nufi asibiti tunda su Halima suna makaranta.

*Bayan awa biyu*

Bayan gwaje-gwajen da likita yayiwa Maryam anan take ya gane tanada shigar ciki har na wata uku, koda ya faWawa Nasir kasa magana yayi saboda mamakin daya ishi rayuwar sa, abin yazo masa a bazata shiyasa ya shiga shock yana tunanin Abinda yasa Maryam ta?i sanar dashi zancen cikinta har tsawon wata Uku, murmushi yayi ya karSi takar dar yana dubawa yana hasashen irin murnar da Maryam zatayi idan taji wannan labarin abin Alkairin.

*Maryam*

Kwantar da ita akayi domin a Wanyi mata treatment na Wan wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login