Showing 30001 words to 33000 words out of 175193 words

Chapter 11 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

569

ita gaskiyar al-amari ko zata san Annabi ya faku.

*Nasir*

"Turyan-turyan ya sanar da Rashida yadda akayi yayi auren nan san nan ya sanar da ita shiba son Maryam yakeyi ba, idan ta kwantar da hankalin ta Maryam d'in ma zata zamar mata kamar mai taya ta aikace aikace ce a cikin gidan.

*Rashida*

"Kukan datake ta had'iye wane yaketa zullo yakeson kwacewa ya fito fili, ta rasa yadda zata ta iya had'iye wan nan kukan saboda idanun hajja.

hajja mahaifiyar su ce, hajja macace wacce tayi gwagwar maya a rayuwar ta ta kumasha wahala a wasu wuraren, wan nan dalilin yasa ba komai ne yake bawa hajja tsoro ba, san nan ba komai ne yake raunana zuciyar ta ba, haka zalika hajja tsayayyar macece wacce ta san kanta kuma takafa mutuncin ta darajar ta da kuma shakkarta a wajen 'ya'yanta , bama 'ya'yanta ba hattaya 'ya'yan 'yan uwanta dana mak'ota su kansu suna kaffa kaffa da hajja saboda macace tsayayya wacce sam bata son raini san nan bata had'a hanya da rashin mutunci ba, haka zalika hajja bata da sonkai da kuma son nata, idan gaskiya ko a rashin gaskiya ya biyo takan ko wanene d'an ta daba d'an taba zata tantance ta bawa kowa gaskiyar sa ko rashin gaskiyar sa.

*Hajja*

Kallon Rashida tayi tace

"Ince ko kinji labarin auren mijinki, kuma wan nan labarin daya fad'a miki nima shine yagaya min, kuma da dukkanin alamu babu k'arya a cikin zancen sa, da ace ya baki labarin akasin yadda yabani to bazan tab'a yarda da Nasiru ba, Amma yadda ya wassafa min labarin nan haka ya wassafa miki babu K'ari kuma babu ragi, dan haka Abinda nake so dake

"Ya zamar miki dole ki karb'i auren mijinki da hannu bibbiyu, ki rik'e Abokiyar zamanki da gaskiya, karki yadda ki cutar da ita ko ki kasance mai son kai a cikin lamuran ki, kuma ki nutsu ki kama kanki banason shashanci da wauta, raina zaiyi matuk'ar baci har mu samu sab'ani dake muddin kikace zaki cigaba da tayar wa mijinki hankali da Abokiyar zamanki.

Dan haka kai Nasir ka d'auki matarka ku tafi, ke kuma zan cigaba da bibiyar lamarin ki, kinij na fad'a miki.

*Rashida*

"Ta danne kukan ta takure zuciyar ta iya inda zata iya, to a wan nan jallin bazata iya zuba ido tanaji tana gani hajja tayi mata hawan k'awara ba, shiyasa ta d'ora hannunta akai kamar wacce aka jefawa masifa san nan ta daddage ta rushe da wani kukan bak'in ciki mai cin rai.

Cikin kukan kuma ta fara magana tana cewa.

"Tsakani da Allah ba ayimin adalci ba hajja, taya zaije yayi aure batare dana saniba, a cikin gidan nan fa yace bazai tab'a min kishiya ba, wace irin soyayya ce ban nunawa Nasir ba? Amma ya rasa damai zai saka min sai da auren cin amana, ni wallahi tallahi bazan yarda ba, wallahi sai dai ya zab'a koni ko ita, dan wallahi hajja dana zauna da wan nan bak'ar yarinyar gwara na dawo gabanki na zauna.

*Hajja*

" A kid'ime ta zamo daga kan kujera ta zabgagawa Rashida mari, kafin ta dawo hayyacin ta ta kuma kifeta da wani Marin.

Cikin takaici hajja ta nuna Nasir tace.

"Daman irin wan nan d'ibar Albarkar take maka a cikin gida Nasir shine baka tab'a sanar dani ba? Yaushe kayi lalacewar dazaka zauna mace ta rainaka har haka? Kabani mamaki Nasir, tabbas kabani mamaki.

San nan ta koma kan Rashida tace

"Ashe haka kika lalace Rashida? Ashe haka zama da mutanen banza yasa kika lalata rayuwar ki? Haka kika bari d'aukar ziga da shashashan kalamai irin nasu wan nan 'yar suka dafar da zuciyar ki har kike gwadamin kin girma a gabana? Hunmm ummm jan, lallai Rashida, ai bansan nayi lalacewar dazaki zauna a gabana ina fad'a kina fad'a ba.

Kuma dan ubanki har da zaki dunga cewar sai dai Nasir ya zab'a koke ko waccen yarinyar dan ubanki ke ba'a a auren aka aure ki? Ko kuwa ba'a auren ubanki ya auro min kishiyar muka zauna tare? da ba'a k'arin auren za'a haifeki ne? To kishiga taitayin ki, wallahi tallahi muddin baki zauna lafiya a cikin gidanki ba ranki zaiyi mummunan b'aci rashida, shasha marar hankali.

Kai kuma Nasir maza maza kaje ka dawo da matarka ku zauna lafiya, shi aure ai lokaci ne dan haka Allah yabaku zaman lafiya.

"Tunda hajja tafara magana jikin Nasir da kuma Rashida yafara rawa, hajja macace mai hak'uri sosai, Amma idan ranta yab'aci tafi giyar mota birkicewa, wan nan yasa kafin aga fushinta ana dad'ewa, shiyasa gaba d'aya hankalin su yatashi domin shikansa Nasir yasan da hakan.

"Tsawar da hajja ta daka musu dacewar

"Kun zauna kun zuba min idanu, kutashi kubani waje kutafi gidan ku ku zauna lafiya.

Har rige rigen tashi suke tare dayi mata sallama suka fice suna waiwaye.

Har sun kusa fita hajja tace

"Ku biya gidan wan nan 'yar ku d'auko 'ya'yan ku kutafi dasu gida, dan yanzu tarbiyyar yara sai uwar su, kuje Allah ya had'a kawunan ku.

Sum sum suka fice Rashida na kuka sosai tare dajan hanci.

Suna k'arasawa gidan yaya karimatu sai ganin d'an yaya karimatun sukai a bakin gate dasu Halima yana jiransu, dan tunkan su k'araso hajja ta kira yaya karimatun ta zageta tas akan Abinda Rashida takeyi dan tasan da saka hannunta a ciki, kuma tace ta har had'awa su Halima kayansu suna zuwa ta mik'a musu basai sun shigoba.

Har kuka yaya karimatu tayi tana bawa hajja hak'uri, a ranta kuma tana ayyana yadda zata taya Rashida suci uban Maryam su hanawa Nasir zaman lafiya, shiyasa tun kafin ma sukai ga zuwa yaya karimatu ta had'o musu kayansu tare da korosu k'ofar gidan dan batason tayi ido biyu da Nasir ma.

*Hajja*

"Tunanin Abinda Rashida tayi taitayi a ranta, wani murmushin takaici hajja tayi tana tuna yadda tayi rayuwa a cikin gidan mijinta wanda da dukiyar ta data mahaifin ta yake tun k'aho, Amma zuwan uwar Rashidan yasa zaman su da komai yafara tab'ar b'arewa, har sai da Allah ya dubesu ya tsinketa daga cikin gidan, shine yanzu kuma 'yarta zatace wai anyi mata auren cin amana.

Hnmm, wai aure cin amana? Banda ma d'an Adam mai manta baya har akwai auren cin amanar da akayi wanda ya wuce na uwar Rashidan da Alhaji?

Wan nan fa shi ake cewa "makaho bayasan jarfa.

Daga nan tunanin shekara talatin da biyar baya ya kawo mata ziyara.

*****

*Hajja*

'yar asalin garin kano ce wadda mahaifin ta yake zaune a unguwar gyad'i gyad'i dake kwandila, mahaifin ta Alhaji kamalu hamshakin mai kud'ine kuma d'an siyasa ne wanda yaci harya ta dakai, ya kasance mutum mai d'umbin alkairi ga duk wanda ya rab'eshi, har ma wanda bai rab'eshi ba idan Allah yayi da rabonshi alkairin ya isar masa har inda yake, wan nan dalilin yasa yake da d'umbin masoya a cikin al-umma.

D'an kasuwa ne kuma uban gida mai yalwata wa yaran dake k'ark'ashin sa, haka akwai zai iya saka rana guda ya yaye yaran dake k'asan sa san nan kowanne ya mallaka masa shago a kasuwa kuma ya ya cika masa shagon da kaya yadda kaima zaka zama uban gidan kanka, da wan nan taimakon Alhaji kamalu ya bawa matasa da yawa aikin ki ya kori zaman banza a cikin matasa.

Wan nan yasa koda ya fito takarar d'an majalisa ya samu kuru'u ninkin ba ninki Abinda yake nema, domin kuwa alkairin sane ya dawo masa har yayi nasarar haurawa dashi matakin da yake nema.

A kwai wani yaronsa guda d'aya mai suna ballo, bello yarone mai amana ta gaske, kuma hakan yasa Alhaji kamalu ya kasa rabuwa dashi, daga bayama duka wasu ragamar kasuwar sai Alhaji kamalu ya sakar masa saboda rashin zama dayake samu da kuma tsantsan yardar da Alhaji kamalu yayi dashi.

" 'ya guda d'aya ce Alhaji kamalu ya mallaka a cikin duniyar nan mai suna Halima, sunan mahaifiyar sa ce shine dalilin daya saka ake kiranta da hajja, Alhaji kamalu yana tsananin san hajja tamkar ransa, kuma duk wanda yakeson ya soshi sai yaso hajja san nan soyayyar sa zata tabbata a cikin zuciyar Alhaji kamalu.

Koda hajja ta girma ta gama karatu takai munzalin aure haka manema sukaita kawo kansu gareta, shi kuma Alhaji kamalu duk cikin manemanta babu wanda hankalin sa ya kwanta dashi, domin duk mai zuwa wajenta yasan yana sonta ne domin dukiyar daya mallaka, hakan yasa yaji bazai iya bawa kowa aurenta ba face yaronsa na kasuwa wato Bello.

Dayake itama yarinya ce mai tsananin biyayya kuma mai son farin cikin babanta shiyasa koda yazo mata da zancen babu wani tababa ta amince kamar yadda shima bellon ya amince.

Ba wani lokaci mai tsawo aka sakaba aka d'aura auren da bidirn bikin bakin d'aya, Alhaji kamalu shine ya mallakawa bello k'aton gida kyauta yace su zauna, haka ya sake masa mota da dukkan sauran kayan more rayuwa.

Ba k'aramar soyayya aka gina a gidan bello da hajja ba, soyayya sosai sukasha suka Ka'ra samun shak'uwa da juna kamar ba auren da aka had'a ba, kuma cikin iKon Allah sai gashi basu shekara ba sai da hajja ta haife 'yarta mai suna karimatu, daga karimatu kuma sai Aminu, daga aminu ta haifi aliyu, daga aliyu ta haifi isyaku sai 'yar auta nusaiba , sai da ta haifi 'ya'yan ta biyar ringis a gidan.

Rashida ba 'yar data haifa da cikinta bace 'yar gidan Abokiyar zamanta ce Amma ta maidata kamar 'yar data tsugunna ta haifa, ita Abinda yake bata mamaki ma shine, yanayin yadda uwar Rashidan sukaci amanarta suka ha inceta sukayi aure batare da masaniyar taba sai daga baya.

****

Tana da mai aiki mai suna Rashida, Rashida kyakkyawar buzuwace wacce zaman fasalta yadda kyanta yakema b'ata baki ne, yanayin yadda hajja take zaune da Rashida kai bazakace mai aiki bace, budurwa ce wacce hajja ta d'auketa tamkar k'anwa a gareta, ya wancin ai yukan gidan ma ba ita kad'ai takeyi ba harda masu taya ta Amma mazane, sosai suka shak'u har tafara sanin wasu daga cikin surrukanta, hajja batada dawata aminiya face mahaifiyar ta, kuma tuni Allah yayiwa mahaifiyar ta rasuwa tun lokacin tana secondry school, wan nan yasa ta maida Rashida kamar 'yar uwarta ta jini.

Rana tsaka wataran Rashida tace zataje ganin gida, haka hajja ta had'a mata shatara ta arzuk'i tatafi da niyar bayan sati biyu zata dawo, ana haka bayan sati da tafiyar ta sai Bello tabo yace zaiyi tafiya India, kuma sai yayi uku tukunna zai dawo.

Muna waya da Rashida sosai kamar babu Abinda yake faruwa, sai daga baya nadaina jinta kwata kwata kuma idan nakira wayarta bana samu, haka dai na ha k'ura na zubawa sarautar Allah ido.

Ashe soyayya ce sosai tsakanin Bello tabo da kuma Rashida, kuma tafiyar datayi ashe tafiya tayi a daura aurenta dashi, shima tafiyar da yayi daura auren yaje, kuma bayan an d'aura daga baya ya d'auketa suka tafi Indian tare, acen suka ci amarcinsu har na tsawon sati biyu san nan suka dawo.

Sai da Alhaji Bello tabo ya dawo da kwana uku san nan hure ta dawo, nasha mamakin ganin yadda ta dawo kamar balarabiya kyanta yaci uban nada ga wani jijji dakai data dawo dashi, wataran har na kan tambeyeta Abinda ya canza ta ta dawo wata mai isa daji da Kai kamar bamai aikina ba, takanyi dariya wani sa'in tace

"Hajja kenan.

Ni kuma bana iya daina mamaki a duk sanda tacemin hajja saboda kwata kwata bata iya fad'in sunana, bawai da muwa nake saboda tacemin hajja ba, tunda kowa da kowa hajja yake cemin har kuwa da 'ya'yana.

Tabbas wasu mazan azzalumai ne kuma maciya amana ne, ban taba sanin dafin namiji yakai yakai mace kushewa ba sai a wan nan rana, ranar da duk sanda na tunata har yau da girmana sai naji kwalla ta zubo min.

A lokacin tsohon cikin isyaku ne a cikin jikina haihuwa ko yau ko gobe, ba kasafai nake iya wasu lamuran ba musamman ta fannin auratayya, dayake cikin nasa yayi girman da muke tunanin ko 'yan biyu ne a ciki, hakan yasa tunda cikin ya shiga wata tara sai dai Alhaji yayi min uzuri, a wan nan ranar kuma ina kwance a d'akina misalin k'arfe d'aya na dare naji ni kaina ina buk'atar mijina, shiryawa nayi tsaf da farin ciki d'auke a fuskata na nufi d'akin sa ina tunanin tabbas yau zan faranta masa rai na sani.

Sai dai me? Ina shiga falon nasa na fara jiyo muryoyi sama sama da wasu magan ganun daya dace ace ma'aurata ne kad'ai zasu shiga irin su a yayin mu'amala, bansan zan iya wasu abubuwan da tsohon cikin nan ba sai yanzu, dan da gudu na falfala tare da banka k'ofar d'akin nasa na shiga, me zan gani?

Suman tsaye nayi a yayin dana shiga dan Alhaji na gani shida Rashida mai aikina turmi da tab'arya suna aikata Abinda ma'aurata ne kad'ai Allah ya halattawa dasu aikata.

Sunyi nisa dan haka shiyasa basu ji shigata da kuma salatin danake zabgawa ba, ihun dana kwarara a lokacin danaji d'an cikina ya dannoni kamar zai fasa marata ya fito shine Abinda ya dawo dasu hayyacin su, sauran abin ma bana iya furtawa kona so yin tunanin sa a raina.

Bansan Abinda yafaru ba kuma, nidai na farka na ganni da baby na a kwance ko ina nawa namin ciwo, ashe nak'uda ce ta tasomin gadan gadan kuma nakasa haihuwa sai da akayi min tiyata a ciro d'an.

Abubuwan da suka faru daga baya masu yawa ne dan alokacin har babana sai da yayi fushi mai tsanani da Bello dan ban iya b'oye masa halin danake ciki ba saboda duk duniya bani da kamarsa, har korar sa babana yace zaiyi na hana Amma yayi fushin da kafin ya sakko sai da akayi da gaske kuma da saka hannuna.

Haka babana ya taramu baki d'aya dan yajin ba'asin Abinda yasa Bello yake neman mata a cikin gidana kuma yarasa wace zai nema sai mai aikina.

Kuka sosai Alhaji Bello yayi tare da neman yafiya ta da kuma fad'ar ai Rashida matar sace, anan ya warware mana komai yayin da nayi suman zaune, ban ankara ba kawai naji lema ta lullub'e ni ashe fustari nake ban saniba.

Dakyar na saita nutsuwa ta na fahimci babana a lokacin da yake cewa bai yadda dacin amana ba, dan haka sai dai Alhaji bello ya zab'i d'aya koni ko kuma Rashida, sosai Rashida take kuka itama tana nema yafiyata.

Sai danayi da gaske tare dakai zuciya ta nesa san nan na iya tattaro jarumta ta na furta na yafe musu san nan nacewa Baba na hak'ura ya zauna da ita dan Allah yayi matarsa ce, shikkenan daga wan nan lokacin fushin da babana yakeyi da Alhaji Bello ya kau aka cigaba daga inda aka tsaya.

Nima haka na bawa kaina hak'uri na rungumi Rashida mukaci gaba da zama amatsayin kishiyoyi, bawai banji zafin Abinda sukayi min bane, kawai dai nabarwa Allah komai musamman danaga Alhaji Bello har yanzu tatawa yakeyi ba wani damuwa da Rashidan yayi ba sosai, ita kuma wan nan Abin yasa Rashida take tsananin kishina, taita hauka, har Aljanun k'arya takeyi idan ta ganni da sabon Abu, kuna sai tasan yadda talalata min shi.

Nikam naga jarrabta ta kishi a wajen Rashida, dan har wataran sai datayi sanadin da Alhaji Bello ya juyan baya nida 'ya'yana ya tsanemu yafita sabgar mu har saki d'aya sai da yashiga tsakanin mu, kuma tunkan na rufe idda Allah yayiwa babana rasuwa a yayin daya barmin tarin dukiyar da tsayawa lissafin ta b'ata lokaci ne, a wan nan ranar da babana ya rasu a wan nan ranar Alhaji Bello tabo ya dawo dani, a wan nan lokacin kuma matar sa Rashida ta haifi kyakkyawar 'yarta mai kama da ita sak, a wan nan ranar kuma Allah yayi mata rasuwa dan ko kwana batayi da 'yarta a duniya d'aya ba.

Wan nan yasa ranar rad'in suna aka maidawa da 'yar sunanta watau Rashida, nice na shayar da ita daga haihuwar ta har yayenta, sai bayan na yayeta da kamar shekara biyar sai na samu cikin autata nabila.

Har gobe idan na kalli Rashida ina kallon mahaifiyar tane, kuma har yau idan na kalleta ina mata kallon wacce itada da uwarta suka kutso min cikin rayuwa ta da mijina da 'ya'yana har ta kusa tarwatsa min rayuwa.

Da banyi hak'uri ba dazan kai yanzu? Dabanyi hak'uri ba datuni ana nan an kafa tarihi akaina, tarihi za'a kafa wanda har bayan rasuwar mijina Alhaji Bello tabo dabai rufa shekara biyar ba datuni ana nan ata fad'ar mugun aikin danayiwa Rashida bayan ta auri mijina, baza'a duba cin amanar dataimin ba sai dai a duba irin zaluncin datamin

Inason Rashida har cikin raina, kuma ina mata kallon wacce na tsugunna na haifa ba 'yar kishiyaba, dan haka Insha Allah zanyi k'ok'ari wajen ganin ta daina wan nan mahaukacin kishin wanda babu tantama babarta ta gada, zanyi k'ok'ari naga bata cutar da matar mijinta ba wacce K'iri-k-iri nake kallon tsantsan k'iyayyar ta a cikin idanunta.

Koda hajja tagama wan nan tunanin sai kawai tashare hawaye tare datashi ta nufi cikin d'akinta kewar mijinta dason ganinsa na lullub'e zuciyar ta.

*KUTSE*

*PAGE 15*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


Tunda suka tawo har suka kusa zuwa gida motar tsit babu mai magana sai tashin fitar numfashi, sukan su yaran dake baya duk basajin dad'in zaman musamman yadda suke cike da farin cikin ganin Abban nasu wanda suka kwana biyu basu ganiba.

Ita dai Halima kasa cigaba da dauriya tayi tace

"Abba kwana biyu bamu ganka ba ina kaje?

Satar kallon Rashida nasir yayi san nan yayi yak'e wanda bai bayyanar da hakwaransa ba yace

"Nayi 'yar tafiya ne Halima, Amma gashi ai nadawo.

*Rashida*

Wani tsaki ta buga tare da juya masa k'eya tana zumb'ura baki tace.

"K'arya dai haramun ce, kafito fili kafad'awa yaranka gaskiyar yau darar da kayi min da kuma cin amanata da kukayi kaida waccen ballagazar.

*Nasir*

Ranshi babu dad'i ya kalli Rashida, kamar zaiyi magana sai kuma yafasa dan ranshi ya b'aci da magan ganun ta dan haka idan yace zai bud'i baki yayi magana bazai fad'i mai dad'i agareta ba, bayason su cigaba dasamun sab'ani da juna dan haka yasa yayi mata shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login