Showing 9001 words to 12000 words out of 175193 words

Chapter 4 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

527

zamansa yace "aminin mahaifina nane kai baba, kuma uba mahaifi nake kallonka.

"D'aga kai baba yayi yace "inada alfarmar dazan rok'i Abu kayi min nasiru?

Duk da maganar tazo masa ababu zata san nan bai san menene Alfarmar dayake buk'ata a wajensa ba sai da yaji zuciyar sa ta tsinke.

Tsintar kansa yayi da d'aga kai Alamar Eh san nan yace "zanyi k'ok'ari iya yina naga na baka Abinda kakeso muddin bai sab'awa shari'a da addini ba.

Murmushi baba yayi yace "Allah yayi maka Albarka ya jikan gyatuminka aminina, dan Allah dan darajar annabi da Alkur'ani mai girma ka karb'i auren maryam, Maryam k'anwar kace halak malak, kuma Maryam babu inda zataje tayi zaman gidan aure hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa kamar gidanka, dan Allah Nasir, Ina maka umarni a matsayina na aminin mahaifinka ka karb'i auren maryam.

Wani irin gim gim dirim dirim Nasir yaji a cikin kansa da k'irjinsa wanda bazai iya fasaltawa bane ya duro masa lokaci d'aya, har wani zufa ce ta musamman ta dunga d'iga daga goshin sa jikinsa yana kakkarwa.

Me yasa baba zai masa haka? Meyasa baba zai zab'eshi domin ya aurawa Maryam shi Alhalin yasan yana da mata?

Bud'e baki Nasir yayi da kyar yace "am..am...da..da..Daman...nace dayake ita mai d'akin tawa.

Katse shi baba yayi da cewar.

"Na sani Nasir, nasan kana da matarka harda yara biyu, ai nine babanka kuma inada damar zab'a maka mace ta biyu a cikin rayuwar ka, kasan dai bazan tab'a cutar dakai bako?

Kai Nasir ya d'aga hankalin sa atashe yana tunanin taya zaiyiwa Rashida kishiyasa a zauna k'alau Alhalin yasan babu binda tafi tsana sai kishiya, kuma shi da kansa yayi mata alk'awarin bazai tab'a yi mata kishiyar ba.

Hannunsa da baba ya sakine yasashi d'an kallonsa yanajin karayar zuciya musamman da yaga baban ya saddakai hawaye yana d'iga daga idonsa zuwa kuncinsa, da sauri Nasir ya kamo hannun baban ya rik'e bata re da tunanin komai ba yace.

Ka saba rik'e hannuna tun ina k'ank'anin yaro baba, baka tab'a sakin hannuna da b'acin rai ko karayaba sai yau, yau dinma bazan bari ka saki hannuna batare da tarin yak'ini akaina da yarda ba baba, saboda haka na amince da auren Maryam baba.

Inason ka d'aura min aure da maryam yau na koma da ita gidana dan akwai abubuwa dayawa dana baro cen kuma suna nan suna jirana.

Wata iriyar ajiyar zuciya baba ya saki ta farin ciki ya kama hannun Nasir ya rik'e sosai yanajin sonshi da k'aunar sa kamar dai dansa jafar, kan Nasir ya dafa yace.

Nagode da taimakona Nasir, Allah yayi maka Albarka, Alhamdulillahi da maryam ta kasance a gidan aure na gari wanda zatayi farin ciki, nasan ko bayan raina Maryam bazatayi kukan rashina ba muddin tana k'ark'ashin inuwar auren ka.

*****

Wan nan aure da aka d'aura na maryam da kuma Nasir shine yabawa Rashida makama da kuma bugar k'irji tana fad'in an mata kutse a cikin iyalinta Alhalin kutsen datake fad'a a zahiri ne kawai take kallonsa dan babban kutsen da zata gani yana nan gaba.
KUTSE

? PAGE 6

NA

? ?? MOM HANEEF

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Nasir

Kallon Rashida yakeyi cikin takaicin dayake a bayyane akan fusakar sa, lallai idan ba fito mata yayi a mutum ba bazata gane annabi yafaku ba ta daina kawo masa rainin hankali akan Maryam.

Ido cikin ido yace "Rashida, babu inda Maryam zataje, anan zata zauna tayi jinyar hannunta, ko kuwa an gaya miki ni banida hankali da tunani? Taya zan d'auko yarinya lafiya kalau daga gidan iyayenta san nan yanzu saboda tsautsayi ya faru da ita kice wai na maidata gida tayi jinya idan ta warke sai tado? Wan nan wane irin abune wai?

Bansan mai Maryam tatare miki ba a cikin gidan nan, keba wanka kike mata, ba tsarkin kashi kona futsari kike mata ba, taya zaki bi ki tsangami yarinya tun zuwanta kink'i kibarta ta huta? Wai shin maryam akanki take zaunane?

Rashida

Tunda tafara maganar ya kamata Nasir ya maida Maryam gidansu tayi jinya idan ta warke ta dawo tafara ganin wani bayya nan nan b'acin rai shinfid'e akan fuskar sa, itafa bawai fa tanason abubuwan datakewa Maryam d'in neba, kawai tanajin a cikin zuciyar ta bata son Maryam d'in kuma da duka ruhinta, san nan wallahi batasan Abinda yasa duk sanda ta kalli Maryam d'in ba gabanta yake yawan yankewa yafad'i ba, shiyasa kawai taga gwara Maryam d'in tayi nisa dasu ko tasamu salamar zuciya gangar jikinta ta huta.

Idanun ta narai narai kamar zai kawo ruwa tace.

"Ba Abinda nake nufi kenan ba baban Halima, kawai dai inason na d'an samu hutune koda na mako biyu ne zuciya ta ta koma cikin nutsuwar ta dan Allah.

A fusace Nasir ya ajiye cokalin dake hannunsa ya mik'e yana cewa.

Babu inda Maryam zataje Rashida, zata zauna anan harta warke, san nan zatayi ta zama har illa masha Allahu a cikin gidan nan.

Wata iriyar mummunar fad'uwar gaba ce ta riski Rashida har sai data zauna saboda jin k'afafunta zasu gaza d'aukar ta tace

"Kasan kuwa Abinda kake fad'a baban Halima? Cafa kai zatai ta zama a cikin gidan nan har illa masha Allahu, kana nufin zaman kenan na dun-dun? Babu Abinda zai iya rabata da gidan nan kenan koda aurne?

Shima Nasir d'in gabansa ne yafad'i dajin wan nan kalmar data fito daga bakin Rashida wai aure, to ai Abinda bata saniba indai aure ne Rashida ta riga tagama d'aura shi, ta d'aura auren da babu yaji balle saki a cikin sa ya d'au wan nan alk'awarin, madadin Nasir yabata amsa sai kawai yafice daga d'akin dan tabbas bashida amsar bawa Rashida a halin yanzu.

Duk budurin dake faruwa a falon Rashidan Maryam najinsu domin basuyi maganar a hankali ba, shiyasa taketa zubar da hawaye tana kallon hannunta wanda ai rashidan ce silar faruwar had'arin data samu a hannunta.

Tashi tayi tashiga band'akin dake d'akinta domin ta d'aura alwalar walaha dan taga lokacin ta ya gabato, tana alwalar tana hawaye haka koda tazo sallar shima kuka taitayi tana rok'ar Allah daya kawo mata sauk'i, koda ta idar da sallar ma kwantar da kanta k'asan cinyoyinta tayi tana tunanin anya rayuwar aurenta zata yiwu a cikin gidan nan? Anya ma kuwa ita tanada sa'ar rayuwar auren agidan duniya? Kaiiii! Bata ga Alamar hakan ba, koma dai-dai menene tana rok'ar Allah ya kawo mata sauk'i a kowane yanayi.

Har akayi sallar azahar tana zaune tana wasik'ar jaki, ta sak'a wan nan ta kwance wan nan domin dai ta rasa makamar dazata rik'e ta zauna lafiya da Rashida tun asirin su bai tonuba a wajenta.

Wayarta ta d'auka ta kira baban ta wanda kwana biyu take yawan mafarkin sa a cikin barcinta.

Da sallama baba ya d'aga wayar yana karawa a kunnesa yace

"maryamu na.

Wani sanyi Maryam taji a cikin k'ir jinta dajin muryar baban nata, madadin ta amsa sai kawai ta saka kukan da batayi tsammanin saba, cikin kid'ima baba yafara tambayar ta da lafiya take kuka? Menene ya sameta? Kasa bashi amsa tayi sai data gama kukanta ya isheta, shima dayaga haka sai bai kumayi mata maganar ba yabarta taci kukan nata ya isheta san nan yace.

"Maryam" kwata kwata har yanzu ko sati biyu bakiyi da barin gabana ba, kinga kenan bazai yiwu ace har kin fara samun matsala a gidan aurenki wacce zata sakaki irin wan nan kukan mai ciwo ba, ko baki fad'a min Abinda ke damunki ba inason ki gayawa Allah, inason ki bud'e baki a fili ki gayawa Allah damuwar ki saboda baki da wani bayan shi duk duniyar nan, muma da kike ganin mu a kusa dake'yan rakiyar duniya ne Allah yabaki, dan haka inason ki sani Allah shine Allah, kuma Allah shine dahir bamu ba, nasanki da ibada da kuma addu'a'oi Maryam, to karki gaza, karki k'osa kicigaba da yinsu domin su kad'ai ne mataimaka a wajenki duniya da lahira.

Ire-iren? wan nan magan ganun baba yayita nanatawa Maryam har sai dayaji tana sakin ajiyar zuciya da sauke numfashi k'asa k'asa san nan yayi murmushi daga cen b'arin nasa har tana jiyo sautinsa yace.

"Nasanki maryam, ban mantaki ba ke jarumar macece mai cike da k'arfin zuciyar Imani, nasan zaki iya ai, shiyasa bani da haufi a duk inda na kaiki, kedai Allah yayi miki Albarka ya zaunar daku lafiya ya Kad'e muku dukkan fituntunun rayuwa.

Da Amin Maryam ta amsa tana share hawayen ta dad'i da dariyar farin ciki tace.

"Ina godiya mahaifin dayafi kowane mahafi a duniya, nagode dakayi silar kawoni duniya kuma nagode da kasancewar ka uba nagari a gareni, ina fatan Allah yasaka muku da alkairi kuma ya biyaku da gidan Aljannar Firdausi.

Dariyar farin ciki baba yayi ya amsa da Amin 'yata gari, Albarkar Allah ta lullub'e ki ta zagaya dukkanin zuri'ar ki.

Numfashi Maryam taja san nan tace.

"Baba ina wuni. Lafiya kalau Alhamdulillahi Maryam ya gidan da yaran gidan? Ina kuma mai gidan da yayar taki? Dafatan kuna lafiya dai ko?

Kai Maryam ta d'aga kamar tana gabanshi tace "lafiya kalau Alhamdulillahi muke baba, sai kuma ta kalli hannunta dake d'aure, kamar tagaya masa ta samu gocewar k'ashi kamar kuma karta fad'a, amma zuciyar ta tafi bata amanna data gaya masan saboda yarik'e cewar shine musabbabin kukanta, dan tasan halin baba sarai, wan nan kukan datayi a kunnensa zai ta nanata kansa ne a kwakwalwar sa ya hanasa sukuni har ya haifar masa da damuwa, shiyasa tayi saurin cewa.

"Na samu hatsari baba.

da sauri baba yace "subhanallahi, hatsari kuma Maryam? A garin yaya? iKon Allah, kinga kuma ko d'azu munyi waya damai gidan naki amma bai sanar dani ba, hatsari wane iri? Allah dai yasa ba babban hatsari bane.

Ka kwantar da hankalin ka baba, santsine ya kwasheni a band'aki na fad'i akan hannuna, da sauri baba yace

"shine kika karye?

Girgiza kai nayi kamar yana ganina nace "A'a baba, na samu gocewar k'ashine, shine nakira na fad'a maka, da sauri ya kuma cewa

"kina nufin Abinda ya sakaki kuka kenan?

Da sauri na d'aga kai kamar ina gabansa nace "haka ne babana.

Har acikin wayar inajin wata iriyar sanyayar ajiyar zuciya da baba ya saki ta samun nutsuwa, nima murmushi nayi dajin k'ullin daya zauna a k'irjin baba na kukan danayi ya fad'a.

Sai na tsinci kaina da cewar "ina kewar ka babana hakama ina kewar ummana.

Dariya baban yayi yace "muma haka Maryam, ki k'ara saka ummanki cikin addu'ar samun dace, rana itayau za'ayi mata aiki a cire mamanta guda d'aya.

Dayake nasan da zancen sai bai sakani cikin tashin hankali ba, sai dai ina yawan jin babu dad'i duk sanda na tuna cewar za'a cirewa ummana mamanta.

Haka dai mukayi sallama da babana yanata k'aramin nasiha da kuma shimin Albarka har nakashe wayar.

Maganar gaskiya naji wani nauyi dake tare da zuciya ta d'ari bisa tamanin ya zagwanye, tabbas iyaye rahamane koda baka fad'a musu damuwar kaba to ko zantawa kayi dasu kakan samu sassauci game da tarin damuwar datayi maka tsaye a mak'oshi.

Da k'arfin gwiwata natashi ta shige kichen domin d'ibar abincin da zanci dan yunwa sosai take kwakwalata, idan ban mantaba ko karin safe banyi ba kuma hakan yasamo asaline saboda tarin damuwar danake ciki, sai yanzu ne naji yunwar na neman kayar dani saboda farin cikin dana samu a wajen baba na.

Koda na duba kichen sai banga abincin ba, haka naita bud'e bud'en fulasai amma banga komai ba, kuma gashi da dukkan alamu anyi girki a cikin gidan, haka yasa na jawo k'afata na dawo wajen dining domin na duba, nan ma babu komai a kai sai cokula da sugar su gishi wad'an da basa barin wajen.

Yunwa nakeji sosai kamar zan fad'i, a yadda nakeji bazan tab'a iya jiran sai na dafa abinci ba san nan naci, shiyasa na juya na koma kichen d'in na nufi wajen da ake a jiye kayan shayi domin na had'a, nasan ba'a rabo da ruwan zafi a flaks, shiyasa na zuba komai na nufi wajen flaks d'in domin na d'ebi ruwan zafin.

Ina kai hannuna kan flaks d'in ina ganin wani hannu akan nawa, juyawa nayi domin naga hannun dake kan nawa, rashida ce , tana b'ata rai da had'e rai kamar zata dakeni, murmushi nayi nace.

Sannu da fitowa maman Halima, kauda maganata tayi ta jefomin tambaya kamar haka.

"???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Me zakiyi?

Batare dana damu ba nace "zan had'a shayi nasha ne yunwa nakeji.

Wani kallon raini Rashida tayi min tace "ohooo" wato saboda almubazza ranci shine zaki had'a shayi da yamman nan kice zaki Sha? To bari kiji, niba haka na tsara rayuwar gidana ba, yana dakyau kibi tsarina tunda a haka kika tarar, ki sani duk wani Abinda ya danganci break fast ba'a yinsa da rana ko yamma a cikin gidan nan, yana d'aya daga cikin Abinda yasa banason ayi min kutse a cikin iyalina, badan komai ba sai dan irin wan nan, taya za'ayi ga abinci ga komai kice zaki sha shayi da yamman nan? Ai ba'a azumi kikayi ba bare kice zaki d'umama ciki karki sha ruwa ya k'ulle, dan haka ki ajiye min flaks kibar wajen nan.

Kasa magana nayi sai binta da ido kawai danakeyi dan ba k'aramin mamaki tabani ba, ni rashida zata tsaya a gabana tana min wasu magan ganu, kawai sai na ajiye flaks d'in na gewayeta zan wuce da cup d'in a hannuna, ko kunya bataji ba wai sai tace min, baki ajiye min cup dina ba malama.

Har zan fita na ajiye, san nan nace "na duba ko ina banga abincin ba, wani kallon banza ta watsa min tace "nayi girki amma ya k'are saboda nayi bak'i dan haka zaki iya dafawa ko kijira na dare ya sauka sai kici.

Banbi ta kanta ba na fice zuciya ta na daka kamar zata b'alle, Allah yasani ina tsananin hak'uri, amma wataran idan aka k'ure hak'uri na ban iya tashin hankali ba, abu na farko kenan da banason yafaru tsakanina da Rashida a wan nan zaman k'anwar na nasir wucin gadi, banason na fitowa da Rashida d'ayan site d'ina wanda ko iyayena suna tsoran birkicewa ta, na fison koma menene zai biyo bayan abubuwan datake min ya kasance lokacin na bayyana amatsayin matar mijinta ko kishiyar ta dan nasan Rashida bazata tab'a yadda ta daukeni a matsayin 'yar uwar taba.

Waje na nema na zauna akan d'aya daga cikin gujerun falon ina kallon yadda Rashida tayi bake bake a kichen tak'i gaba tak'i baya domin karna shiga kichen d'in na dafa wani Abin

Ganin ina neman rasa kuzarina baki d'aya yasa na mik'e na shiga wata k'ofa dake da rila a bene, a cikin gidan take amma idan ka lek'a kana ganin waje da abubuwan da akeyi.

Ina lek'awa naga wani almaji zai wuce, dayake akwai mai shayi agaban gidan namu sai nayi saurin ya fitoshi da muka had'a ido, da sauri ya tawo gidan zai shigo domin na aikeshi, ni kuma nima nai saurin barin wajen na shiga d'akin na zaro dubu biyu a kud'in da babana yabani nafito, inajin sallamar sa nayi saurin sakkowa nafito tsakar gidan muka had'u, kud'in nabashi nace yayi maza yasiyo min indomie da kwai shima a dafa masa, amma nasanar dashi afara dafamin ya kawo min.

Cikin k'an k'anin lokaci sai ga yaron ya dako sallama ya kawomin idomien, na kawo hannu zan karb'a kenan Rashida ta amsheta da hanzari tacewa yaron yaje.

Fita yaron yayi ya na waigena danba Rashida ba shi kansa yaga tsananin b'acin rai a cikin idona da fuskata, juyawa nayi na kalli Rashida tare da bud'e baki zanyi magana.

Da sauri ta d'ora d'an yatsanta akan bakinta tace min

"Shiiii" karki sake kicemin ta tafasa a wajen nan, ke yanzu saboda cin mutunci da tonan silili shine zaki fita siyan abincin da zakici saboda ki tonawa Nasir asiri a cikin unguwar nan? Tun da muka gina rayuwar mu ko sugar da bread bamu tab'a siyaba a cikin unguwar nan, sai ke? Saboda kawai kin kutso mana lokaci guda shine zaki wargaza mana rayuwa? To baki isa ba wallahi, saboda haka wan nan indomien da kika siya ta zama hara miyar ki.

Wata dariyar bakin ciki na saki ina mata kallon ta haukace, dakyar nake iya magana nace

" Me kike nufi data zana haramiya ta?

Kai Rashida ta jinjina tace "ina nufin bazaki ciba.

Murmushin kan leb'e nayi nace "kenan ke zakici?

"Girgiza kai tayi tana wani d'aga ledar tare da ya mutsa fuska tace "wan nan k'azantar zanci? Allah ya kiyaye.

Da kyar na bud'e baki nace "to tunda baci zakiyi ba kuma k'azanta ce dan Allah kibani naci k'azantar ni inaso haka.

Ido Rashida ta zaro min kamar wata 'yarta tace "idan nak'ifa?

K'irji na bala'in zafi yakeyi min dan ina da wata mahaukaciyar ulcer mai sani fitar hayyaci da sark'ewar numfashi.

Dakyar na tattaro yawun bakina dan har ya k'afe min nace

"Idan baki bani ba, wallahi zan kira ya Nasir na shaida masa Abinda kikayi min na hanani abinci a cikin gidan nan, san nan zan gaya masa naje na siya kin kwace kince bazan ciba.

kuma duk bayan wan nan.

"Yatsana manuni na nuna sama nace.

billahillazi la'ilaha illahuwa sai kin biya bashin wan nan Abinda kikayi min a cikin daren nan, sai na hanaki barci, na hanaki nutsuwa da jefa rayuwar ki cikin ko kanto.

Wan nan maganar dana shaidawa Rashida kuma taga babu Alamar wasa a fuskata gashi babban tashin hankalin ta danace zan gayawa Nasir bayan duk kashedin daya mata akaina da safe, gashi na fito mata da wasu magan ganun dako a sikili ta aunasu bataga Alamar sunyi kala data hankali ba a wajenta, dan yadda taga na canza mata lokaci guda ina zare ido da rik'e kirji da kuma yadda fuska ta ta canza lokaci guda yasa ta tsorata dan ji take Aljanu na tayar.

Da sauri Rashida ta d'aga ledar zata wullarmin ni kuma nayi saurin rik'ewa, tun kafin ta sakar min na figze nayi tafiyata nabarta a tsaye a wajen tana bina da kallo.

Ina shiga d'akina na zauna tare da saurin bud'e ledar na fara cin indomien hannu baka hannu kwarya kamar zan cinye 'yan yatsuna, sai lokacin na dawo hayyacina, ruwa na d'auka nasha mai yawa san nan na ajiye na fara tunanin Abinda yafaru tsakanina da rashida yanzu.

Wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ya ruftomin naji zuciya ta na neman bugawa, jin idan banyi kukaba zan iya loosing memory kawai saina fashe da wani k'ak'k'arfan kuka mai ya kusar zuciya.

PLEASE COMMENTS AND SHARE
KUTSE

? ? PAGE 7

NA
??
?? MOM HANEEF

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Bayan sati biyu

Abubuwan da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login