Showing 15001 words to 18000 words out of 175193 words

Chapter 6 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

538

take ba gaskiya bane, a ganina keda na kutso mata ta k'arfin tsiya da kuma ha'intarta Insha Allah watarana zatayi Alfahari dake san nan zata k'aryatao kanta da kanta na cewar ba kowane kutse ne me zama tashin hankali da rikicewar rayuwa ba ta dalilin ki, na dad'e ina miki kallon mai hankali da nutsuwa, na dad'e ina miki kallon saliha mai biyayya ashe ba haka bane.

Maryam

Da sauri ta d'aga hannu tana girgiza wa Alamar ba haka bane tana kuka sosai dan kukan ma bazai barta ta kuma wata magana ba.

Amma duk da haka tanason ta magantu tanason yazama tayi magana domin ta kare kanta kota samu sassauci awajen mutumin datake da yak'inin shine zai tallafi rayuwar ta yabata kulawa san nan ya zamar mata majin gina alokacin datake buk'atar taimako.

Dan haka da sauri ta bud'e bakinta da yayi mata mugun nauyi tace "Dan.....dan....Allah ka.

D'aga mata hannu Nasir yayi tare da saka d'an yatsansa ya saka akan bakinsa yace "shiiiiii" banason wata magana kibar wajen nan kawai malama.

Yana gama fad'ar haka ya wuce ciki yabata waje.

Ita kuwa Maryam durkushe wa tayi ta zauna akan wata kujera dake farfajiyar wajen tana k'ara fashewa da kuka tare da tallafe kanta dake mata ciwo takejin kamar zai fad'i k'asa.

Bayan kwana biyu

Nasir

Zaune yake akan kujerar likita yana k'ara jaddada masa bayanin sa da cewar

"Taya za'ayi ace har zuwa yanzu bata farfad'o ba? Kaifa kace zata farfad'o nan da 'yan a wanni, anawa lissafin yaufa kimanin kwana biyu kenan tana kwance ko motsi batayi bare na fara saka ran farfad'o warta, gaskiya wan nan Abin baiyi min ba idan bazaku iyaba gwara ku bamu sallama mu nufi wani asibitin inda zamu dace acen.

" Wani k'ayataccen murmushi likitan yayi san nan yafara magana cikin salo na kwantar da hankali yace "kayi hak'uri Alhaji Nasir, duk Abinda kake tunani bawai haka bane, Rashida tana lafiya kuma da yar dar Allah zata farka nan bada jimawa ba, munayin aiki tuk'uru koda yaushe akan ta dan musamu muga samun lafiyar ta cikin k'ank'anin lokaci, dan haka dan Allah kayi hak'uri ka kwantar da hankalin ka.

Da wan nan kalaman likita ya samo kan Nasir domin ya kwantar da hankalin sa zuciyar sa kuma ta nutsu waje d'aya ta daina tsalle tsalle.

Wata ajiyar zuciya Nasir ya saki yace "tohm shikkenan babu damuwa, ina fatan Allah yasa naji alkairi.

Da Amin likitan ya amsa yana k'ara bashi kalaman kwantar da hankali.

Koda Nasir yagama da likita fitowa yayi yana shawagi, kamar ya bud'e d'akin da Rashida ke ciki ya shiga sai kuma ya fasa, ba komai yasa ya fasaba sai don sanin Maryam na d'akin ta kasa ta tsare tana kula da Rashida kamar ba itace musabbabin faruwar komai ba.

Maryam ta zama kamar wata mayya kuma marar zuciya dan duk wulak'ancin da Nasir ke mata akan rashin lafiyar Rashida? ta shanye ta kauda kai tana tabinsa da kuma yiwa Rashida addu'ar samun lafiya dan su kansu yaranta su Halima suna tsananin buk'atar ta dan komai yagama lalacewa a gidan.

Tsaki Nasir yaja ya nemi wata kujera daga bayan d'akin da rashida ke ciki ya zauna yayi kasak'e kamar wani dolo yana jiran tsammani.

********

A cikin d'akin asibitin kuwa shiru ne ya mamaye ko ina, amma ga hasken da fitilar d'akin ta haskaka, kuma ga sanyin A.C mai kauyi dake fita yana mamaye lungu da sak'on dake cikin d'akin.

Sannu a hankali Rashida tafara motsi da hannayenta san nan daga bisani kuma tafara jujjuya kanta tare dason bud'e idanunta da sukayi mata nauyi takejin kamar an d'inke mata su da zare da allura, da kyar Rashida ta iya k'arfin halin bud'e idanunta ta zubasu akan fankar dake juyawa a saman silin, tabbas jikinta da kuma duka gabban jikinta sun bud'e sosai amma zuciyar bata bud'e ba dan a kuntace take, saboda duk wani abu daya kasance da takaitaccen lafazi kafin suma ya dawo mata sannu a hankali kamar busawar K'aho daga nesa.

Da sauri Rashida ta mike zaune tana furta kalmar "Nasir.

Wan nan lafazin datayi amfani dashi yasa Maryam dake cen kan kujera ta ankara da farfad'owar Rashida a wan nan lokacin, da sauri Maryam ta mik'e ta nufi wajen gadon bakinta a washe tace.

"Alhamdulillahi, kin farka maman Halima? Sannu Allah yabaki lafiya ya tsare gaba.

Da sauri Rashida ta kalli Maryam zuciyar ta na bugawa a dai-dai lokacin data tuna lafazin Maryam a kunneta da cewar

" _Ni matar Nasir ce ba_k'anwar sa bace._

Tuna wan nan lafazin yasa Rashida saurin kauda kai daga kallon Maryam hawaye na zarya daga cikin idanunta.

Da sauri itama Maryam ta maida kwallar ta tace

"Ban san dame zan faraba maman Halima, dan Allah ina neman yafiyar ki gafar ceni.

Kallon ta Rashida tayi a karo na biyu san nan ta kuma juyar da kanta gefe dan sam batasan ganin Maryam d'in ko jin muryar ta.

Amma duk da haka sai ta tsinci kanta dayin magana murya cen k'asa cikin rauni tace

" _Kuma kinason na_ _yarda dake Maryam?_

Da sauri maryam ta sunkuyar dakanta tanajin nadama da Kuma kunya na mamayeta.

A cikin zuciyar Rashida kuwa ba gafara ko neman yafiya take tunani ba tana tunanin fansa ne amma irin fansar da baza'a iya hangota a cikin idanuba, kuma baza'a iya jin karar ta da kunnuwa ba.

Dai-dai shigowar Nasir kunnuwan sa suka jiyo masa magan ganun Rashida wanda suka k'ona zuciyar sa suka dugun zuma kunyar sa.

Murmushin takaici Rashida tayi tace

" _Nasir ya yau dareni,_ _ke kuma kika_ _biye masa kika yarda da yaudar._ _tafad'a a hankali cikin sanyin murya._

Da sauri Maryam ta fashe da kuka ta girgiza kai Alamar ba haka bane.

Kyalkyale wa da dariyar takaici Rashida tayi tana kallon nasir wanda yayi tsamo tsamo dashi kamar mage tafad'a ruwan sanyi tace

"Inason ku duka kugane cewar nafi k'arfin kuka a yanzu, kuma inason kusani ba duk Abinda mutum yayi bane yake tafiya a banza ba.

Dan haka, dan Allah, dan annabin Rahama ku samamin salama, karku dameni ku jefa zuciya ta cikin ciwon dazai zama ajalina, banason ganinku dukan ku, yana da kyau kubarni naji da Abu guda d'aya.

Kuma Nasir nagodewa Allah da yazamana daka kawo maryam ban karb'eta hannu bibbiyu ba da ciwon sai yafi min haka yawa.

"Cikin muryar kuka Maryam tak'ara cewa ki gafar ceni maman Halima.

Dubanta Rashida tayi idanunta cike da gajiya da ciwo, d'auke kanta tayi daga kallon Maryam tace.

"Daman zuciya ta bata bani ba, san nan daga baya nafara gane wasu abubuwan marassa fasaltawa amma yanzu ne na tabbatar da komai da kukayi min.

San nan maganata ta karshe a gareku itace "kufita ku bani waje dan banson ganinku ko kad'an, kufita nace, tafad'a tana nuna musu hanyar fita.

Nasir wanda ya sank'ame ya daskare a wajen ya kasa motsawa sai san nan ne yayi k'arfin halin yin motsi tare da takowa zai nufo wajen gadon.

Rashida na ganin haka tayi saurin zamewa ta kwanta akan gadon tare da Jan bargo ta lullub'e jikinta har zuwa kanta.

Kallon juna Nasir da kuma Maryam dake kuka sukayi, sai yanzu ne Nasir ya kula da ramar da Maryam tayi akan wan nan lamarin, shidaman ramarsa tafito muraren amma Abinda yafi bashi mamaki shine ramar Maryam d'in wanda baiga huruminta a cikin rashin lafiyar Rashida ba.

Ai daman Abinda takeso ne tasamu, burinta ta tona musu asiri ta rikita rayuwar gidan sa, kuma gashi dai Allah yabata nasara hak'onta ya cimma ruwa banda kuma gulma meye na rama?

Tunda Rashida ta fad'i suka shiga tashin hankali wan nan ne karo na farko dayaji d'an tausayin Maryam, wan nan kukan datake yawanyi harya kod'ar mata da idanunta, hakan yasa tausayin ta yakuma tsirga masa har bai san sanda ya nufi gareta ba tare da rungume ta a cikin jikinsa yana shafa bayanta ba Alamar rarrashi.

Tun fara takunsa Rashida tajiyo hakan yasa tad'an lek'o da kanta domin ganin fita yayi ko kuma wajen ta ya iso, har ga Allah dataga yatako gaban gadon nata ta zata wajenta zai nufo ya yaye bargon ya rarrasheta yabata hak'uri, amma babban tashin hankalin dataci karo dashi shine na isa wajen Maryam da Nasir d'in yayi har ya rungume ta a jikinsa yana kuma shafata a gaban ta kuma akan idanun ta yasa ta kwala wani uban ihun dayasa Nasir yayi saurin sakin Maryam tare da hankad'a ta gefe ya isa gaban gadon Rashida wanda tashin hankali yasa bargon ya yaye ya rik'eta yana kiran sunanta.

Duka take kai masa tako ina tanajin wucin zafin da zuciyar ta take fitarwa.

Shigowar likitoci d'akin ne yabawa Nasir damar matsawa daga jikin Rashida yana share hawaye tare dajan hannun maryam suka fita, akan idanunta Nasir ya rik'e hannun maryam suka fita hakan yasa ta kuma kurma ihu tana fusge fusge tanason sauka daga gadon amma likitocin suka hana faruwar hakan

*KUTSE*

*PAGE 9*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


Dakyar likitoci suka samu kan Rashida fizge fizgen da take yalafa sakamakon Allurar da suka zuzzur kud'a mata ta barci, nan da nan kuwa barci ya d'auketa a take dan bata kuma ko shurawa ba, amma ko kafin tatafi barcin sai da wasu a zababbun hawaye masu K'una suka gangaro daga idanunta suka sauka kan kuncinta.

Sai da suka tabbatar ta samu nutsuwa san nan suka fita tare da rufe mata k'ofar d'akin suna fatan samun lafiyar ta idan ta dawo hayyacin ta.

*Maryam*

Suna tafe a mota tana kuka wiwi tana tunanin anya zaman aurenta da Nasir abune kuwa mai yuwa? Taya zata zauna tana kallon yadda yakeson matarsa kamar ransa ga gudun duk wani Abinda da zai tab'ata, daman haka maza masu mata biyun suke? Toma ita ba wan nan ba, wai meyasa tun farkon fari yasan bazai iya zama da mata biyu ba ya amince da aurenta? San nan ma meyasa bai fara zuwa yayiwa Rashida bayanin Abinda yasameshi na aurenta da aka bashi ba san nan ya koma ya d'auko ta? Meyasa kansa ya kulle har yayi tunanin ya munafurci matarsa mai sonsa da k'aunar sa da Kuma tarin kishinsa agareta?

Sanin bata damai bata wan nan amsar yasa taja w??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ata shasshek'ar kuka mai k'arfi har sai da Nasir ya juyo ya kalleta tukunna cikin fad'a yace

"Wai bazaki dakata dayimin kukan banzan nan a cikin motar nan ba? Karfa ki manta duk wan nan Abinda ke faruwa kece sanadin faruwar sa, to akanme zaki dameni? Ni wallahi ma daga yau bazaki sake zuwa asibitin nan ba, gwara ki zauna a gida ki kula da yara dan zaman ki acen babu Abinda yake haifarwa sai tarin wata damuwar, yanzu fisabilillahi da ace ba akusa dake Rashida ta farko ba wallahi da ciwonta bai kuma ta azzara ba dan haka wallahi har tadawo gida bazan bari ta kuma tozali dake ba.

*Maryam*

Kamar zatayi shiru ta cigaba da jajantawa kanta shiga wan nan hurumi na mata da miji da tayi sai kuma ta kasa dan haka cikin dashash shiyar murya tace

"Yanzu ya Nasir duk k'ok'arin da nayi na kula da Rashida tsawon sati d'aya a asibitin nan banyi gwaninta ba? Kullum kusheni kakeyi da d'oramin laifin lalurarta? Menayi maka da zafi haka? Meyasa bazaka dubeni da idanun rahama ka tausaya min kodan rashin wani nawa akusa dani kajani a jiki? Shikkenan saboda Rashida ta samu lalura shikkenan motsi d'aya sai kafara min fad'a da hayaniyar nice sila?wai menene nayi muku da zafi haka ne? Me yasa kasan baka da k'arfi Had'i da jarumtar rik'on mata biyu ka karb'i aurena wai? Nidai gaskiya wan nan Abin ya isheni, ya kamata komai ya tsaya haka.

*Nasir*

Cikin tsawa da dakatar da tuk'in da yake yacewa Maryam

"Zakiyi min shiru kosai ranki ya b'aci? Koda na karb'i aurenki kinji na furta kalmar soyayya a agareki? Kinji nace inason zama dake har abada kuma na had'aki matsayi da Rashida? To tsaya kiji, baki da wan nan matsayin a wajena Maryam, bance bazan soki ba amma a yanzu dai ki tsaya a iya matsayinki, kin san cewar kai kanki inda ban kaiki ba shine Abinda yajawo duk matsalar da muke ciki yanzu, da kinyi hak'uri kin bari na samu dai-dai to da matata na kwantar da hankalin ta nabita ta siyasa yadda zata fahimceni a duk lokacin dana sanar mata ke matata ce da duk hakan bata faruba, yanzu gashi kinzo kin shiga tsakanina da matata shiyasa kullum kalmar Rashida itace d'aya ta batasan kutse, ashe ita tasan me take ganowa kanta shiyasa ta tsani wani ya kusanci iyalinta, wallahi tallahi badan inajin kunyar yayanki da kuma baban kiba billahillazi da daga nan gida zan maida ki muga Abinda hali zaiyi dan saina tabbatar da Rashida tasamu lafiya ta nutsu hankalin ta ya kwanta san nan zan waiwayoki.

*Maryam*

Cikin tashin hankalin daya fara sark'e mata numfashi ta tsinci kanta wanda gaba d'aya tama fara rasa wane irin tunani zatayi kuma duk da Nasir yagama fayyace mata wacece ita a gareshi, tabbas zamanta da Nasir ba abune mai yuwuba dan haka dole ta samu mafitar rayuwa tunkan bak'in cikin su ya tasamma kashe ta ko saka mata ciwon zuwa da hauhawar jini.

Shiru ne mai nauyi yabiyo bayan magan ganun da Nasir yagama gwab'awa Maryam, dan haka tana ganin ya nisa ya tada mota tare da fara tafiya a hasale tace.

"Dakata.

Da sauri Nasir yataka birki yana mata kallon mamaki ranshi b'ace yace "me zakiyi?

Itama cikin d'aga murya tace "saukeni zakayi.

Tsaki Nasir yaja zai cigaba da tafiya ta danne hannunsa tace.

"Wallahi wallahi sai na sauka daga motar nan, ka saukeni nace.

Banza yayi mata kamar bai jitaba ya fizge hannunsa yacigaba da tafiya, aikuwa a take ta kwalla k'ara tace.

"Ka saukeni.

Cigaba da tafiya Nasir yayi sai kawai ta fara k'ok'arin bud'e motar bayan yana tafiya da niyar ta sauka.

*Nasir*

Cikin karaji yacewa maryam.

"Wai bakida hankali ne? Me kikeyi hakane?

Itama Maryam cikin masifa tace masa.

Hankalin kenan, dan wallahi muddin baka saukeni ba wallahi ko gudun fanfalak'i zakayi wanda bama mutab'a hasashen ya yakeba wallahi saina b'alle murfin motar nan na sauka.

Ganin da gaske Maryam take zatayi masa hauka yasa ya gangara gefen titi tare da tsayar da motar, Maryam naganin ya tsayar da motar tayi saurin b'alle murfin motar tafice tare da figar jakarta tana share hawaye ta fara tafiya.

Shima Nasir a zafafe yaja motarsa ya figeta da bala'in gudu yabar wajen ko waiwaiyen Maryam baiyi ba.

Anan bakin hanya Maryam ta tsaya taci uban kukanta san nan tafara tunanin mafitar rayuwar ta, sai a san nan zuciyar ta take gaya mata shin data sauka a wan nan yammacin inane zataje? Kuma ina zata dosa da tarin matsalarta? Batasan kowaba a wan nan garin idan ba gidan Nasir ba, kenan cen zata koma?

Girgiza kai tayi tace "innaaa, bazan koma gidan ya Nasir ba, bazan iya komawa ba , bayason ganina da k'aunar na rab'esa, mai yasa bazanyi hak'uri nayi nesa dashi ba? Tana cikin wan nan tunanin ta tuna gidan k'awarta "samira.

K'awarta ce tun suna yara suka tashi tare, itama aurene yakawota garin kano amma kowa da kowa nata yanacen daura, sam ta manta da ita, koda Nasir ya aurota ya kawo ta kano ta manta da samiran a kanon take hakan yasa bata taba tunanin nemanta domin suyi zumunci ba.

Da sauri Maryam ta ciro wayarta ta fara laluben neman wayar samira, inda Allah yabata sa'a kuwa bugu uku tayi mata samiran ta d'au wayar.

Da sallama samira ta fara san nan tafara cewa

"Gaskiya k'awata bakida mutunci wallahi, ashe kinyi aure a kano amma baki nemeniba? Badan naje gida wancen satin nakejin labari ba da sai dai kawai naji labarin har kin haihu ko kuma mu had'u a hanya, ai shikkenan nagode sosai.

Duk bar kwancin Maryam amma a wan nan lokacin bar kwancin bazai samu ba, hakan yasa magan ganun samiran suka kuma tunzura zuciyar ta sai kawai ta fashe da kuka.

Da sauri samira tace " subhanallahi, Maryam, menene? Meya faru? Kina ina haka?

Kuka kawai maryam keyi kuma cikin kukan take ce mata ita batasan inda take bama, ajiyar zuciya samira tayi tace "dakata a inda kike inason yanzun nan ki samu napep ki bashi wayar muyi magana da juna.

Cikin sa'a kuwa mai napep yazo wucewa da yake wajen akwai wadatar ababen hawa, da sauri ta tsaidashi tare da mik'a masa wayar, kamar bazai karb'a ba dan gudun a cutar dashi sai kuma yaga yanayin ta na sanyi kuma tace masa "Dan Allah ka karb'a kwatancen inda zaka kaini za'ayi maka.

Duk da jikinsa ya d'anyi sanyi amma haka ya karb'i wayar hannunsa na rawa tare da bissimillah, yana karawa a kunne samira tace "dan Allah malam goron dutse zaka kawota wajen gidan mai, da sauri yace to yana mik'awa Maryam wayar, karb'a tayi tana shiga napep d'in yaja suka fara tafiya.

Mintina kamar talatin sai gashi yakawota goron dutse gidan mai, koda ta kuma kiran samira a waya sai ga samira tafito daga gidan dake kallon gidan man tana bugawa Maryam murmushi Had'i firgicin dayake bayyane a kan fuskarta.

Dubu guda samira tabawa mai napep d'in tana masa godiyar taimakon da yayiwa 'yar uwarta.

Koda suka shiga cikin gidan a dai-dai falon Maryam ta cake tare da fashewa da wani kukan ta rungume samiran tsam a cikin jikinta, kai daga ganin kukan da Maryam keyi kai kasan cewar Abinda ke damunta ba k'aramin abu bane, abune mai nauyi kodan yadda takejin jikinta yana kakkarwa tare da d'aukar zafi a lokaci guda.

*Samira*

Bata hana Maryam kuka ba san nan batayi gangancin rarrashin taba, dan duk wanda kaga yana irin wan nan kukan to tabbas da akwai tabo mai zafi wanda yake cike a zuciyar sa, kuma wan nan kukan shine ke kankare dukkan wani tabo dake neman zamowa gyanbo a cikin zuciya, shiyasa tabarta tayi mai isarta, sai dataga tsayuwar ta dameta har kafafunta sun fara alamar tsami san nan ta d'agata daga cikin jikinta taja hannunta suka shiga cikin falon, zaunar da ita tayi tare da cire mata hijabin jikinta domin ta samu iska ta shigeta sosai ko zata samu sauk'in tururin dake fita jikinta.

Da yake samira girki take a lokacin kuma ta saka sanwar miya shiyasa koda taji zuwan Maryam sai takashe gas d'in baki d'aya tafita tawo da ita, shine yanzu ta koma ta kunna gas d'in domin miyar ta karasa ta kasheta baki d'aya.

*****

*Nasir*

Gudu yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login