Showing 3001 words to 6000 words out of 175193 words

Chapter 2 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

529

gida batare daka saka ta amarya a k'arshe ba, a koda yaushe idan kana son fasamin kai ai ba haka kake cemin ba, naga CA kake min

"Uwar gida kuma amarya ta ta har abada" ko kuwa yau kana kyashin fad'amun hakan saboda kada nayi farin ciki? Nifa shiyasa banason kowa ya rab'eni kona awa biyu ne, yanzu gashi nan saboda ganin yarinyar nan yau d'aya tana gilmawa a cikin gidan nan har ka fara sha'awar ganin mata biyu a tare dakai, sai ta saka kuka tana cewa.

Kabar ganin inason ka Nasir, billahillazi duk ranar daka kuskura ka kutsa wata cikin zuciyar ka har ta samu matsugunni bare har kayi gangancin kawo ta gidanka a matsayin matar ka wallahi sai ka ga masifa da bala'in dabaka tab'a tunanin akwai su a cikin rayuwar duniya ba, wallahi Nasir duk ranar daka had'ani da wata sai kayi kukan jini, kuma ka sani, bazan tab'a kallon soyayya ko zaman lafiya ba, wallahi tallahi sai na rikitaka, sai na gigita tunanin ka, wa billahillazi saina saka kafita daga hayyacin ka.

Duka kuma wan nan magan ganun da takeyi rawa jikinta kawai yakeyi idanunta suna zubar da hawayen ba'kin cikin maganar da take, hannu Nasir ya kai zai rik'eta dan tunda yake bai taba ganin ta shiga d'imuwa da tashin hankali irin wan nan ba, da sauri ta fusge hannunta tanayin gaba tare da banke k'ofar falon nasu san nan taja hannunsa suka shige uwar d'aka suka bar Maryam yashe afalo tana barci ga sauro da zafin bala'i duk ya addabeta.

Washe gari

PLEASE COMMENTS AND SHARE
KUTSE

Na
? ?
? Mom Haneef

? ?? Page 3

Washegari

Tun tsakar asuba Maryam ta mik'e ta fara waige waigen neman band'akin gidan dan taji ana kiran sallar asuba, tabbas bata samu barci mai dad'i kuma mai yawaba, sauro da bala'in zafin da suka takura mata ne ya hanata katab'us a rayuwar barcin nata, kuma Abin mamaki sai yanzu ne yake neman d'auketa a gigice, barcin takeji sosai, amma hakan bazai shagaltar da ita daga ibadar asubar data sababa, bazata bari shed'an yayi galaba akanta ba a dai-dai wan nan lokacin datake da yak'inin ubangijin ta na kiranta data bauta masa kuma ta kwashi roman da yake bawa bayin sa su kurb'a a wan nan lokacin ba.

Duka falon babu band'aki, hakan yasa tatashi tad'an bud'e k'ofar falon a hankali tafita zuwa tsakar gidan, wai gawa ta k'arayi sai taga wata k'ofa a rufe mai nuni da ita ce ke b'an tacciya a cikin tsakar gidan, da sauri ta k'arasa ta bud'e, nan taci sa'a kuwa band'akin ne, har d'an gudu sai da tahad'a dashi saboda mugun fitsarin daya cika mata mara ya kuma tokareta ya hanata sukuni.

Koda tagama fitsarin da sauri ta d'auro alwalar tafito tana haskawa da wayarta domin tagano hanya, wata iriyar mummunar fad'uwar gaba ce ta daki zuciyar ta a dai-dai sanda taga inuwar mutum yana tsaye yana kallon ta gashi bak'i bata iya ganin kayan jikinsa sai dai fararen idanun sa da suka k'ureta da kallo, cikin firgici ta matsa baya da sauri tace

"A'uzubillahi minashshai d'anirajim, sai ta k'ara haske halittar dake gabanta, wata sassayan ajiyar zuciya ta sauke ganin Rashida tsaye tasha bak'ar doguwar rigar barci ta daddafe k'ofar falon tana wurga mata wani kallo, kafin ma takai ga magana sai kawai Rashida ta saki tsaki tare da juyawa ta koma falon, bin bayanta Maryam tayi tana tunanin Abinda ta biyota yi a wan nan lokacin.

Abin mamaki baya k'arewa, maimakon Rashida ta d'aura alwala tayi sallah kawai sai ta koma kan gadon ta nad'e tana kallon Nasir wanda yayi d'ai-d'ai yana barci kamar gawa, wani k'ayataccen murmushi ta saki a karo na babu adadi tana tunanin tuni ta samo hanyar dazata hana shak'uwa tsakanin sa da Maryam dan tasan Abinda yakeso kenan.

Tun jiya bayan sun gama dramar nan da Nasir tayi zuciya ta kwanta, batayi niyar bashi shayin dayake kwad'ayin shaba kullum da dare shiyasa tayi kwanciyar ta, ya riga ya zamar masa jiki idan bai sha shayin na nan ba sai yaji har barci ma bazai iya ba, shiyasa koda yaga ta juya masa baya yamayar da abin wasa yafara tab'ata yana cewa

"Maman Halima shayin fa? Banza tayi masa kamar bataji shi ba har sai daya fara mata magiyar dan Allah tabashi shayin yasha, hakan yasa tatashi tana zumb'ura tafito falon domin shiga kichen, taga Maryam sarai kuma taga irin uban gumin dake tsassafo mata, hakan bai dameta ba kawai ta wuce kichen tana k'ananun magan ganu a cikin ranta, har ta d'ebo shayin tai saurin komawa ta d'auko wani sachet d'in maganin barci wanda yake saka nannauyan barci idan kashashi, a k'a idar maganin rabi ake b'alla asha, amma saboda muguntar Rashida uku ta b'alle ta zuba masa a ciki, sai da ta tabbatar ya narke san nan takai masa yafara sha.

Nasir

Wani irin test shayin yayi masa a bakinsa kamar ba shayin Rashida mai d'and'a non dad'in data saba bashiba, kallon idanta yayi ya zaro harshe waje dan harshen nashi ya daure yace "maman Halima amma wan nan shayin ba irin wancen bane?

Batare data kalleshi ba tace "to wane iri ne?

K'ara kallon cikin kofin Nasir yayi yace "gaskiya baiyi dad'i ba sam, wani irin k'amshi da kuma d'aci d'aci naji yanayi.

Bata kalleshi ba har yanzu tace "to idan bazaka shaba basai ka ajiye ba.

Ganin taji haushi yace "Allah yabaki hak'uri, ai kuwa yayi dad'i.

Banza tayi masa tacigaba dashafa turarenta ta kwanta, shima Nasir anan wajen ya b'ingire kamar k'aramin yaro barci yayi garan bawul dashi, sai data tabbatar barcin nasa yayi nisa sosai san nan ta taso ta gyara masa k'afafun sa wanda ya wancakalar dasu cen gefe guda tana masa dariya.

A fili tace "ai wallahi maganin ka kenan na dare a cikin gidan nan, babu wanda ya isa yakawo min iskanci wallahi, nasan cewar daban zuba maka maganin barcin nan ba wallahi da fakar idona zakayi, dan wuyarta kaga nayi barci zaka tashi ka salallab'a kaje gurin waccen shegiyar yarinyar data kutso min rana d'aya kace zaka kaita d'aki ta kwanta kamar yadda kayiwa yaranka.

Wan nan tunanin datayi na Abinda tayi masa yasa tace.

"wallahi ko sallar asubar ma ka daina tashi tunda naga waccen yarinyar itama jahar ku d'aya.

"Ita kuwa Maryam sallar ta tayi cikin jin dad'i da nishad'i san nan ta zazzago da addu'a'oin data saba kuma tanada yak'inin Allah ya amsa mata.

Har azkar sai datayi san nan garin yafara haske kad'an, kamar ta koma ta kwanta dan barci ne sosai akanta, wani tunani tayi kawai sai ta mik'e tafara tattare kayan falon tana kimtsaawa, batasan inda ake kai ko wanne ba shiyasa ta jibgesu waje d'aya ta ajiye, tana gama share falon tayi kichen danta duba, lodin wanke wanken data gani yasa ta fito tsakar gidan dasu dan tayi.

Magana taji abayanta Rashida na cewa "ke! Ke! Ke! Ya haka? Na sakaki wani abinne? Kona ce miki ina son taimako ne? To bari kiji dan Allah ki fita daga sabgata nifa banason shisshigi Maryam, dan haka ki tsaya a matsayar ki kinjini ko?

Jiki a sab'ule Maryam ta ajiye kayan wanke wanken san nan tad'an tsugunna tace " maman Halima ina kwana?

"Lafiya" Rashida ta amsa a takaici tana d'auke kanta daga kallon Maryam tana tunanin rashin zuciya irin tata ta shanye disgi.

Itama maryam d'in barin gurin tayi tare da komawa falon ta takure waje d'aya a jikin kujera.

Barci ne ya kwasheta a wajen sai hayaniyar yaranne suka tadata da shirin su na tafiya makaranta, da sauri ta bud'e idonta tana kallon su gwanin sha'awa yadda sukayi kyau a cikin uniform d'in nan, ta kalmi taga sadiya na kiciniyar sakawa sai tayi saurin mik'ewa ta isa wajen tana cewa.

"Zo nasaka miki, da sauri sadiya ta matsa baya tana kwace k'afarta tana cewa "banaso, ni ki rabu dani, ta giftata ta wuce, d'an murmushin yake, tayi san nan ta kalli halima tace "zona taimaka miki halima, da sauri itama haliman ta matsa tace

"Ki barshi nagode Aunty"

Tashi Maryam tayi tana bin inda taga Halima nabi da kallo, Rashida ce a tsaye tasha kunu tana k'are mata kallo, D'an rissinawa maryam tayi jikinta a mace tace "barka da fitowa maman Halima.

D'auke Kai Rashida tayi tana kama kunnen Halima suka shiga d'aki tanai musu fad'a.

Wata dariyar takaici Maryam tayi tana tunanin irin zaman da zatayi a cikin gidan muddin asirinta na itama matar Nasir ce ya bayyana.

Nasir

Idonsa fal bacci ya fito domin yakai su Halima makaranta, ta babban falon yazo wucewa ya tarar dasu Halima suna karyawa kamar yadda suka saba kafin su tafi makarantar, zama yayi akan d'aya daga cikin kujerar yana kallon Maryam wacce kanta ke k'asa da carbi a hannunta tana lazumi, murmushi yayi yanajin dad'i a ransa yadda take da ibada kamar bak'aramar yarinya ba, dududu Shekarunta bazasu wuce sha takwas ba amma Allah ya azurtata da ibada da kuma hankalin manya, wan nan dalilin yana d'aya daga cikin Abinda yasa ya aureta dan haka yana sonta kuma yana k'aunar zama da ita, amma kuma ta yaya?

Shin zaiyu su zauna inuwa d'aya da Rashida mai kishin mutuwa?

Yana wan nan tunanin ne yaji muryar Maryam tana cewa

"Abban Halima ina kwana?

Da sauri ya amsa yana kallon b'arin da Rashida ke zaune wacce ta k'ureshi da ido, saurin tashi yayi yafara yiwa su Halima magana akan suyi sauri kada su makara.

Maryam na ganin sun tashi itama tayi saurin mik'ewa tace "Dan Allah zan biku Abban Halima, da sauri ya juya ya kalli Rashida wacce ke sak'alawa sadiya jakarta, jin Abinda Maryam tace shine yasa ta d'ago tana kallonsu da mamaki.

Tun kafin Nasir yabata amsa Rashida tace "ina zaki bisu? Idan kin bisu mai zakiyi a makarantar?

Kasa amsawa Maryam tayi sai k'asa da kanta datayi tana cewa a ranta.

"Zan bisu, dole ne na bisu kodan furta Abinda ke k'asan zuciya ta zuwa ga Nasir, inada magana da mijina dole ne na bishi domin mu tattauna.

Maganar da taji Nasir yayi yasa maryam ta d'ago dakai inda taji yana cewa.

"Haba Rashida, menene idan tabimun? Nan da makarantar su Halima? Minti nawane munje mun dawo? Ina ganin tanason ganin makarantar ne shiyasa takeson bin mu, kinsan wanda ba d'an gari ba idan yazo gari burin sa yafita yad'an zaga.

Cikin b'acin rai Rashida tace "yanzu akan wan nan yarinyar kakeson mu fara ja'inja dakai? Abinda bamu tab'a yiba? To ai shikkenan, nidai nace bazata jeba ta zauna a gida dan akwai aikin dazan sakata.

Ran Maryam yafara b'aci, tanada hak'uri da kawaici, amma fa da alama Rashida zata kaita bango da wuri, kawai sai ta tsinci kanta da kallon Rashida tace

"Inason zuwa maman Halima, kuma zanje, ai yanzu zamu dawo, rik'e hannun sadiya tayi duk da ta fusge, bataji komai ba tayi gaba abinta tare da zura takalman ta ta fice waje.

Rashida

Da kallo ta bisu baki d'ayan su cikin mamakin maganar Maryam, tsintar kanta tayi da cewar "kan uba, lallaima wan nan yarinyar, daga kutsowa cikin gida zata fara sakin jiki? Kai kuma ka d'auki kafa yawa sillen kara ka rufa mata baya kaida yarana?.

Kuje kudawo wallahi sai yarinyar nan tabar gidan nan, bazan d'auki iya shegeba, haka bazanzo nayi rik'on dazan yi nadama ba.

Maryam

Hawaye take sharewa lokaci zuwa lokaci, tama rasa dame zata kira wan nan auren nasu, shiyasa ta dage tayi Abinda tayi saboda ta biyoshi taji tarti biyar magana daga bakinsa.

Nasir

Ya rasa me zaicewa Maryam wacce take jikinsa tana kuka a cikin motar, k'ara shafa kanta yayi zuciyar sa damfare da tausayin ta yace

"Wallahi Maryam ina sonki sosai, kuma banzatar dake danayi badan baki da mahimmaci a wajena bane,ina tsara komai yadda zai tafi dai-dai batare da tashin hankali ba, da yardar Allah zan samo mana mafita.

Maryam

Zuciyar ta babu dad'i ta tashi daga jikin Nasir ta kalleshi cikin ido tace "meyasa bakason ka sanar da matarka nid'in matarka ce? Saboda me kake mata b'oyo akan Abinda ya zama halalinka kane daga tasakar ubangiji? Kenan ka d'auko nine saboda na zama baiwa kasasshiya acikin gidanka? Me yasa ma ka d'auko ni ka aureni Alhalin kasan cewar matarsa tafi k'arfin ka kuma ita take juya komai na gidan harda kaima?

Nasir

Bakinta ya rufe yana cewa "ban d'auki amanarki ba har sai dana na tabbatar da zan iya, zan iya fuskantar komai ciki harda canzawar zaman takewar gidana wanda bana fata, hawaye ne ya cika kurmin idanun sa yace

"Bana tsoron Rashida maryam, haka bata juya lamarina zuwa wani Abin daban, duk Abinda kika gani yana tafiyane da fahimtar juna da kuma soyayya da yarda, amma zan dage zan daure wajen karya zuciyar ta na gabatar mata dake amatsayin Abokiyar rayuwar ta.

Sai kuma yakama hannun Maryam yace " dan Allah Maryam kiyi hak'uri, nima banzata al-amarin zaizo min a hakaba, amma zan d'auki mataki, amma dan girman Allah Maryam Alfarma d'aya nakeso kiyi min, inason ki cigaba da zama a matsayin k'anwata, da yardar Allah zan san abinyi kafin Abin yayi nisa.

Kallonsa Maryam tayi tace "kenan kana tunanin a falon zan cigaba da rayuwa? San nan haka zan kasance cikin razana da k'unci? Yaufa kwata kwata kwana na d'aya da zuwa gidanka amma na fara ganin wasu halaye na matarka wanda muddin akace a haka za'a zauna bazata kaimu hanyar da zamu zauna lafiya ba, saboda haka, "nidai gaskiya ina ganin cewar ka maidani gida in yaso duk lokacin daka saita al-amura sai kaje ka d'auko ni kadawo Dani, amma ka sani kuma ka rik'e a ranka.

"Ina sonka yaya Nasir, ina kuma son kasancewa tare dakai har k'arshen rayuwa ta.

Rungume ta Nasir yayi yanajin k'aunarta har cikin zuciyar sa.

Kiran wayarsa da Rashida tayi ne yadawo dashi nutsuwar sa, da sauri ya zaro wayar yanajan dogon numfashi, kasa d'aga wayar yayi sai kawai yatada motar tare da figar ta suka bar wajen.

PLEASE COMMENTS AND SHARE.
KUTSE

Page 4

Na

Mom Haneef

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Rashida

Tana zaune akan dining ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana jijjigawa cike da takaici, babban bak'in cikinta bin da Maryam tayi masa, san nan Abu na biyu dad'ewar da sukayi da suka tafi, bazata jureba, bazata iya zuba idanuwa tana kallon Maryam tana shisshigewa Nasir ba, amma wata zuciyar tana gaya mata k'anwar sace fa, ko zaiyi soyayya da wata ai bada k'anwar Saba, sai kuma ta mik'e tafara jijjiga tana cewa "dan k'anwar sace ai ba muharramar sa baceba, da aure a tsakanin su, safa da marwa ta farayi kamar ta zura takalman ta ta bisu haka takeji a ranta.

Yunwa ce take kwakwalar cikinta, gashi tasaba ci?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dasha tare da mijinta Abin k'aunar ta, taya zata fara karyawa ita d'aya?

Wani tunani na b'arin zuciyar ta kenan, d'ayan b'arin kuma yace mata "kici abincin ki kirabu dashi, duk sanda suka dawo daga gantalin nasu yaci nashi.

Shayi tafara zubawa tanasha a zafafe dan ita kad'ai tasan halin da zuciyar ta take ciki, bata shan shayi da zafi sai ya d'an huce, amma wai yau sai ta tsinci kanta dashan shayin mai bala'in zafi, batajin zafinsa saboda Abin datakeji a ranta yafi shayin zafi, ita kanta tasan da adane tasha wan nan shayin da sai ya k'ona mata harshe, kuma wani bala'in sau uku tana kwarewa saboda zancen zucin datake.

Da sauri ta ajiye kofin shayin a dai-dai sanda taji harm d'in motar Nasir, tashi tayi tana huci tafita harabar gidan, basu da mai gadi, tunawa da hakan datai shiyasa taci burki a dai-dai bakin gate d'in, kamar ta bud'e masa sai kawai ta fasa ta koma ciki.

Nasir

Sosai yake harm dan a tunaninsa ko Rashidan barci take duk da yasan a wan nan lokacin tana da himar ta salla mesa ne, ganin bata da niyar fitowa ta bud'e masa yasa ya bud'e motar daniyar fita ya bud'e, da sauri Maryam ta bud'e tata k'ofar itama ta fito, saurin k'arasawa jikin gate d'in tayi tana cewa

"Bara na bud'e maka na samu lada.

Murmushi Nasir yayi yace "to nagode Allah yayi miki Albarka.

Maryam ce ta bud'e masa k'ofar ya shigo da motar, sai da ya gyara parking san nan yafito suka jera domin shiga cikin gidan.

Maryam

turus ta tsaya ganin Rashida ta shak'i kwalarta tace "gidan ubanwa kika ja min mijina kuka kai har yanzu batare da kun dawoba? Rau rau Maryam tayi da ido tare da tsugunnawa tace "dan Allah kiyi hak'uri maman Halima, wallahi tawowa mukeyi babu inda mukaje.

Har Rashida ta bud'e baki zatayi magana Nasir yace.

"Kinga dakata maman Halima, babu inda mukaje fa, dan Allah ki saketa, banason tashin hankalin nan.

Harara Rashida ta watsawa Nasir tace "to idan ba wani wajen kukaje ba ina kukaje?

Numfashi Nasir yaja yace "babu inda mukaje Rashida, ina sauke ya ran nan mukataho, tafiya muke bamuje ko inaba.

Cikin jin haushin maganar sa Rashida tace "dayake da taya kuke tafiya bada motaba ai dole kucemin tafiya kukeyi, Hnmm, wallahi baban Halima banason b'acin raina yafara tasiri akan Abinda ban shirya masa ba.

Sai kuma tasaki Maryam tace "wuce kibamu waje kike sissink'e kai kamar munafuka.

Wucewa Maryam tayi tanajin fad'uwar gaba dan itafa gaskiya lamarin Rashida yafara bata tsoro, mace sai hauka akan an rab'i mijinta, waifa duk wan nan Abin datakeyi amatsayin anyi mutsu kutse a cikin iyalanta batare data amince ba, to duk ranar da kwai yafasu cewar ita matar Nasir ce ya zatayi?

Nasir

Kan dining d'in ya zauna yana zubawa Rashida ido wacce taketa jijjiga kai cikin jin haushi tana kwafa, gaba d'aya abincin yafita daga cikin ransa, bayajin zai iya karyawa ma saboda b'acin ran da Rashida ta k'unsa masa da safen nan, dan haka kawai sai ya tashi yanajan kujerar yafice daga wajen, da kallo Rashida tabishi tana mamakin sa natashin da yayi baici abincin ba.

D'aki ya shige tabishi tana kiran sunan sa, k'in amsa mata yayi kawai ya bud'e k'aramin pridge d'inshi ya d'auki ruwa zai Sha, da sauri Rashida ta rik'e ruwan tace.

"Karka bawa kanka matsala mijina, bai kamata kasha ruwa ba batare daka sakawa cikinka ruwan zafiba.

Hannunsa Nasir ya fizge yace "babu ruwanki da Abinda zai sameni Rashida, koma menene zai sameni ai ba damuwar ki bane tunda dai bakya k'aunar farin cikina, danayi magana kice wai "kutse, komai an miki kutse, wato ke duk bak'on dazanyi a gidan nan kike kira kutse, amma inda bak'o nakine shine bak'o

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login