Showing 168001 words to 171000 words out of 175193 words

Chapter 57 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

556

"ina jinka.

?ar Soyayyar ajiyar zuciya ya sauke san nan yace

"Wai Maryam bakisan Abinda Ya samu Rashida bane? Kai ta Waga tace masa nasani mana. Naji a wajen ?a?anta kaima kayi min text ka faWamun.

Amma kinsan da haka baki taSa cewa ko dawasa zakije ki dubata ba bare kice min ya jikinta.

"Murmushin ya?e Maryam tayi tace "ni zance maka yajin waccen matar? Nice zanje na dubata? To idan ma mafarki kakeyi ka daina, dan wallahi Allah bazan taSa zuwa na duba Rashida ba, kai ko mutuwa tayi bazance Allah yaji?anta ba, ato.

Kallon mamaki kawai da taurin zuciyar da Maryam ta koya Nasir yake binta dashi, wai ya akayi Maryam ta kangare zuciyar ta haka? Yarinya mai ladabi da biyayya da tausayi amma yau itace ta zama haka? Hummm umm jan, ya faWa a cikin zuciyar sa, sai kuma ya Wan Waure fuska san nan yace "ai duk Abinda kikayi wa Rashida domin Allah zakiyi mata badan halinta ba, kuma koda jinyarta kikaje ai baki faWi ba Maryam, naga dai ?ar uwarki musulma ce, kuma bayan haka dukan ku mata nane.

Gajiya da wan nan surutan nashi Maryam tayi dan haka sai ta kalleshi tace "kagama maganar taka? ?aga kai Nasir yayi alamar Eh! Sai Maryam ta gyara zama san nan tace "ka buWe baki kasanar dani Abinda zanyi koda zan iya taimakawa.

Sai a san nan Nasir yaji wani Wan sanyi a ransa san nan yace "dan Allah Rashida inason kije kiyi jinyar Rashida saboda babu kowa a wajenta, idan yaso sai zita ta dunga kula miki da yaranki.

Cikin mamaki Maryam ta buWe baki tace "amma dai da wasa kake ko? Girgiza kai Nasir yayi yace da gaske nake, sai kawai Maryam ta she?e da dariya harda hawaye tace "zita zan bawa yarana? Wato na batasu ta kashe minsu ko? San nan nice zanje nayi jinyar matarka? Sai ta hade rai ta zare mai ido tace "to wallahi baka isa ba, na rantse da Allah ko duk duniya babu mai jinyar Rashida idan naje nayi jinyarta Allah ya tsinemin, ai wallahi ko dagani sai Rashida muka rage a duniya sai dai ta mutu akan naje nayi jinyarta.

Cikin Sacin rai Maryam tace "wai kai Nasir ka manta da Abinda Rashida tayi min ne? Tun farkon zuwana gidan nan tafara ganamin azaba da magan ganu da kuma asiri, ko ka manta ita ce daga haihuwata ta kwantar dani ?asa sai danayi shekara ina jinya? Ko kuwa ka manta ita ce wacce ta gusar maka da hankali kabarmu katafi wajenta kusan shekara? Zalunci wane iri ne batayi min ba? Babu Abinda batayi min ba sai Abinda na manta, to idan maye yaci ya manta uwar Wa bazata manta ba, dan haka ka rabu dani naji da Abinda ke damuna Nasir.

A hasale da magan ganun Maryam Nasir ya tashi ya daka mata tsawa yace "Maryam, ya isheki haka, koma menene Rashida tayi miki aiya wuce ko? Amma saboda mugun halinki na ri?o shine bazaki manta ba? Itama Maryam mi?ewa tayi har tana huci tace.

Bazan manta ba Nasir, idan kai Rashida ta gama dakai ni bata gama daniba, kuma bazanje jinyar tataba wallahi, ko darajar sannu bazata samu a wajena ba bare dunbiya, duk hukuncin da zaka Wauka ka daWe baka Wauka ba, san nan banda ma kwakwalwar wasu mazan kallon Arewa takeyi har kaine da bakinka zakace naje jinyar waccen azzalumar bayan duk Abinda tamin? To ai karka manta koda ta kwantar dani uwar data haifeni ce da kuma yayarka suka yi jinyata har ta shekara Waya, dan haka sai kaje ka Wauko yayar taka da kuma kai kuje kuyi jinyarta, amma karka manta Rashida azzaluma ce kuma mai kisa dan itace ta kashe min kulu.

Tana kaiwa nan a magan ganun ta saka hannu tare da Waukar jug Win lemon data ajiye masa ta rotsashi da ?asa kafin daga baya ta bangaje shi ta wuce tana sakin kuka mai Waci dacin rai.

Baki da hanci Nasir ya buWe yana kallon Maryam har ta gama shigewa Waki tana kuka, bai san ma bakinsa a wangale yake ba sai da yaji sauro wuf ya shige bakin sa ya zarce masa ma?ogaro, tari da kakari ya shigayi wanda har hakan sai da tazame masa kwarewa, ai kuwa nan yayi ta fama da sar?ewar numfashi, ?arshe dai sai da yayi amai san nan yasamu salama.

A wan nan rana sam Nasir kasa runtsawa yayi, juyi kawai yake yana mamakin halin da da Maryam ta koyo da banata ba da kuma maimaituwar magan ganun ta da nazarin su. Ah, yasan gaskiya ne duk Abinda Maryam ta faWa akan Rashida, to yaya zaiyi? matarsa cefa, idan bai tsaya kai da fata wajen lafiyar ta ya kula da itaba to me zaiyi, da ?an uwanta har ?an uwansa kowa ya gujeta, kowa ya juya mat baya baya sonta, a yanzu bata da kowa sai shi sai yaranta, to idan bai kula da ita ba waye zai kula da ita?.

Kuma koma menene Maryam ta faWa shi yasan halin Rashida saboda shekarun da suka Wauka, duk wani muguntarta ta kishi akan Maryam bazata iya kisan kaiba, dan haka shi bai yarda Rashida ta kashe kulu ba, kuma kowaye zai cigaba da Wora mata sharri zaiyi maganin sa.

Rashin makamar da Nasir zai ri?e yasa yaje tsohuwar unguwar su yatawo da baba gaje, baba gaje wata dattijuwa ce da mijinta ya rasu Nasir yake taimaka musu, ita ce tayi jinyar Rashida badan Rashidan taso ba.

Yauma haka Rashida ta wuni tana koke koken ciwon ?afa da kuma kai, duk allurai an mata amma abin kamar turi, hannun Nasir ta kama tana cewa "dan Allah Nasir kaje ka gayawa hajja halin danake ciki, ta taimaka min tazo ta ganni koda bazatayi jinyata ba, ina cikin shiga ukun daban san ranar fitarta ba Nasir, jinake kamar ana daddatsa min ?ashin cinyata da kuma ?afata, hajja da ?an uwana nakeson gani kozasu ro?ar min Allah ya bani lafiya.

Girgiza kai Nasir yayi yana ri?e hannun Rashida yana mai tausaya mata yace "kiyi ha?uri da wan nan kukan Rashida, Insha Allah zaki samu lafiya, yanzu dai kizo ki kwanta ki huta. Matse hannun Nasir Rashida tayi saboda azabar data kuma soka mata tace "banyiwa hajja daidai ba ita da ?an uwana, ha?i?a na kasance mai butulci a garesu, dan Allah ka nemomin su na ro?i yafiyar su dan ban saniba kobazan tashi ba.

Wata murya taji ta gilma a kunnenta tace "tun yanzu kin fara tunanin mutuwa Rashida? Ai tukunna dai, dan wan nan kaWan kika fara gani akan kala-kala na a zabun da duniya ta tanadar miki.

Da sauri Rashida ta kalli inda taji wata iska tana wucewa tana shiga kunnenta tace "nasir zan haukace fa, ka rike min wan nan iskar zata hura min kai, wayyo kaina, ta ?arasa tana kwalla ?ara, juye juye Nasir ya fara yi yana son ganin Abinda Rashida kewa ihu amma sam bai ganiba, haka dai taita kurma ihu har sai da likita ya shigo ya danna mata allura san nan barci yayi gaba da ita.

Tun daga ranar da Nasir da Maryam sukayi sa'insa dashi bai ?ara ganinta ba, kafin yadawo ta ajiye masa abincin sa tayi shigewarta Waki, haka bazata fitoba sai ya fita, shima daman bala'in haushinta yakeji shiyasa ko abincin nata bayaci, musamman da yaga kusan sati kenan da sanar dasu ya zulai akan rashin lafiyar Rashida suka ce Allah ya sawa?e basu ?ara bi takansa ba, babu waya babu zuwa dubiya, kuma yasaka a ransa yana da ya?inin Maryam ce ta zugasu tare da hure musu kunne, shiyasa gaba Waya yake ganin gwara ya tattara su yayi jinyar Rashida tunda babu mai taimakon sa.

Sukuwa su hajja yasan sarai bazasu saurari Rashida ba, dan yanada ya?inin cewar Saboda rashidan ne yasa suka tattara komai nasu sukayi hadaya da gidansu wajen gina masallaci da makaranta suka koma garin Abuja da zama baki Wayansu, dan wani estate suka gina wanda dukansu suke rayuwa a cikin sa ko wanne da gidansa na alfarma, hattaya nusaiba autar hajja data tashi aure a cikin estate Win hajja tabawa mijinta gida suke zaune.

*KUTSE*

*PAGE 73*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Hajja*

Kallon ikon Allah kawai take a wajen Rashida, dan gaske a lokacin da ya Aminu yake sanar da ita Rashidan babu Lafiya tsawon watanni biyu kenan batayi tunanin ciwon Rashidan yakai haka ba, banda ma Allah yasa tayi hangen nesa da kuma tursasawar nusaiba ba wacce taketa damunta harda kukanta na don Allah suje suga aunty Rashidan da hajja batayi niyar zuwa ba, badan komai ba saboda gaba Waya ta cire Rashida daga iyalanta ta rungumi wanda Allah ya azurtata dasu kuma Alhamdulillahi suna raye tana jin daWin su.

A jirgi suka tawo baki Wayansu banda ya Aliyu wanda ma shi baya ?asar kusan satinsa biyu kenan a ?asar Egypt wajen wani kasuwancin su, hakan yasa daga hajja sai ya Aminu sai kuma nusaiba akazo dubiya, ajiyar zuciya hajja ta sauke tana ?ara kallon ?afar Rashidan wacce tayi wani irin kumburi ta fita daga hayyacinta tace

"Yanzu Rashida daga karaya shine ?afar nan ta koma haka? GyaWa kai Rashida tayi tana hawaye tace "Eh hajja, karayar kuma a cinya ne amma abin mamaki sai wani ?urji ?ato ya fito min a kasan galalin ?afata, shine fa ya fashe yaketa ruwa, kuma mun koma asibitin suka ce wai kansar ?aface ta kamani, ta ?arasa tana kuka wiwi, kama hannun ta hajja tayi tace "kinga Rashida ki daina kukan nan, ko wanne bawa ai da irin ?addarar ko? Dan haka kiyi shiru Allah zai baki lafiya kinji? ?aga kai Rashida tayi tana cewa "yanzu hajja shikkenan mutuwa zanyi? Wai me yasa lokaci Waya rayuwa takeson tayi min atishawar tsaki ne? Me nayi ne wai? A kul hajja ta faWa tana rufe bakin Rashida san nan tace "bakiji nace miki ?addarar kice a haka ba? Dan haka kiyi ha?uri ki rungumi ?addara, kuma zaki samu sau?i Insha Allahu.

Kai Rashida ta Waga tana kallon hajja tace "amma hajja anan zaki zauna kafin ku tafi ko? Girgiza kai hajja tayi tace "ya zan zauna a gidan surukai Rashida? Muna da namu gidan dan haka cen zan koma na zauna kafin nan da kwana biyu mu koma abuja kuma. Cikin raunanniyar murya Rashida tace "hajja naje neman ku akace ai ginin masallaci da makaranta za'ayi a gidan namu, ko kunsai wani ne? Murmushi hajja tayi tace "Eh an sadaukar dashi ne ga Abban ku Rashida, da nufin Allah yakai masa ladan kabarin sa, jinjina kai Rashida tayi tana cewa "Allah ya jikansa yasa ya huta, ta faWa tana tunanin tata uwar da bama santa ba kuma bata taSa ganinta ba sai a hoto, ajiyar zuciya Rashida ta sauke a sanda hajja ta dafa kanta tace Allah yabaki lafiya Rashida, kafin daga bisani suka tafi.

Tun a hanya nusaiba take kuka saboda ganin Rashida bai mata daWi ba, haka nan taji kamar banzatarwar da sukayi da itane ya kuma jefata a wan nan yanayin, dan haka sai kawai ta kalli hajja tace "hajja haka kawai muka banzatar da Rashida, koma menene tayi mana ai kamata yayi muyi ha?uri mu cigaba da rungumar ta har Allah yasa ta dawo hayyacin ta, amma dubifa yadda ta koma, ta rame ta lalace duk tayi ba?i kamar ba ita ce wacce farinta yake kusa kashe idon mutum ba, yanzu dan Allah hajja da nice a wan nan yanayin ya zakiji?

Tsawa ya Aminu ya dakawa nusaiba yace "dalla malama rufe mana baki, meyasa baki da tunani ne? Ko kuwa kinfi hajjan son Rashidan? Aiki san Abinda hajja tayiwa Rashida ko uwar da takawo Rashida duniya iyakar Abinda zatayi mata kenan, wane irin hali ne hajja bata shiga akan Rashida ba? Wace irin jawowa ajiki da shawara ne hajja batayi wa Rashida ba, hasalima ita Rashida ita ce ta nuna bata bu?atar mu cikin rayuwar ta shiyasa muka fita, kuma san nan ai ke shaidace na irin halin da hajja ta shiga a lokacin da muka bar Rashida muka koma abuja, hajja har asibiti ta kwanta saboda yadda jininta yahau dan damuwa, dan haka wallahi ki rufe bakinki anan wajen, kuma duk sanda kika ?ara yin makamancin yar wan nan maganar wallahi sai ranki yayi bala'in Saci, ke badan ma muna duba Abba ba wallahi bazamu kuma bi takan Rashida ba har abada.

Jin yadda ya Aminu ya hayyako wa nusaiba yasa tayi gum da bakinta tana sakin shashshe?ar kuka, tasan duk Abinda Ya Aminu ya faWa gaskiya ce, to amma ai da sai suyi ha?uri su juyar da Abinda tai musu na sharri zuwa Alkairi tunda sunsha yin haka akaro na babu adadi.

Ita kam hajja shiru tayi musu gaba Wayansu dan ita wan nan matsalar ma ta rasa a Sarin da zata sakata ta bata suna.

*Maryam*

Tana zaune tanashan fura cikin nishaWi ita da ?an biyun ta wanda ta zuba musu a ?an ?ananun kofuna, bawani sha suke ba sai wasannin su da sukeyi da ita duk sun Sata jikinsu, sallamar Nasir ce taWan saka Maryam ta jiyo tana satar kallon sa, gabanta ya zagayo ya zauna akan kujerar dake facing Winta yace "ina abincina? Ban dafaba, Maryam ta faWa tana zu?ar furarta, kamarya baki dafa ba? Nasiru yafaWa yanayin fushi naWan hawa kansa, saboda banice da girki ba koka manta ne? Rufe ido Nasir yayi tare da sakin huci yace "saboda bakece da girki ba sai ki?i bani abinci? Wai wan nan wane irin hali ne? Naga Dako ba kyece da girkin ba bani abincin kikeyi, Ajiye kofin furar maryam tayi tace "kaga ya Nasir da da yanzu fa ba Waya bace, kuma dai na faWa maka banyi girki ba dan haka kagama munashan fura, dan Allah ka samamin Lafiya, nifa banason shiga hurumin da banawa ba, saboda haka dan Allah karka sakani a cikin tsaka mai wahala bayan nasamu na fito da kyar.

Ajiyar zuciya Nasir yayi ya mi?e batare da yace mata komai ba ya fice daga wajen Maryam jikinsa a saSule, wajen Rashida ya nufa yana kallon yadda tayi furkai furkai tana kuka wiwi tana cewa zita ta taimaka mata takira mata Nasir, itama zitan kuka takeyi tana kallon tsutsar dake dun?ulewa tana faWowa ?asa daga ramin ?afarta, da gudu Nasir ya ?araso wajen Rashida yana tsugunnawa da faWin menene? Hannu na rawa zita tafara nuna masa ramin ?afarta wanda ya jagwule yana tsutsotsi, cike da tashin hankali Nasir yace "innalillahi, menene wan nan? Badai tsutsa ?afar tafara ba? Kuka Rashida ta kuma fasawa tana kallon Nasir tana "ka taimaka min Nasir mutuwa zanyi, tsugunnawa Nasir yayi a wajen yana toshe hanci saboda wani wari mai tsayawa a ma?ogaro ya bugo hancin sa yace "innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, wai ?afarki ce ta koma haka? Maza tashi ki saka mata mayafinta mutafi asibiti, Nasir yafaWa yana kallon zita wacce hawaye yayi kace -kace akan fuskarta.

*Bayan kwana biyu*

Rashida rungume da hannun hajja tana kuka tana cewa "banason a yanke min ?afa hajja, hajja idan aka yanke min ?afa ya zanyi da raina kenan? Waye zai cigaba da kula da Nasir bayan banida ?afa? Na shiga ukuna hajja, ajiyar zuciya hajja ta sauke tana share hawayen tausayin Rashidan tace "baza'a yanke miki ?afa ba Rashida kiyi ha?uri Insha Allah zamu san abinyi.

Sai bayan sun koma gida san nan hajja ta kalli nusaiba tace "ya zama dole muyi wani abu akan Rashida, dan tabbas hannun ka baya ruSewa ka yanke kayar, yanzu kiramin Aminu kice yazo inason ganinsa. ya aliyu na zuwa hajja ta faWa masa Abinda takeso ayi akan Rashida.

Jinjina kai ya Aminu yayi yace "yanzu hajja abin har yakai haka? Amma abin baiyi daWi ba sam, amma kuma hajja ai idan har za'akai Rashida Saudiyya ganin likita dole fa sai antafi damai kula da ita? Yanzu wanenene zai kula da ita? Kinsan kuma sai antafi da mijinta ko? Kafin hajja takai ga magana nusaiba tace "to hajja wai duk da wane kuWin za'ayi wan nan jigilar? Kinsan fa ya Rashida bata dako asi a wajen mu tunda ta turo dangin mamanta sun karSa mata dukiyar ta.

Ajiyar zuciya ya Aminu ya sauke yace "tana da kuWi a hannun mu ai musaba, ba duka muka basu ba, mun rage wasu abin saboda nan gaba, kuma kuWin suna hannuna, sauran kuWin hayar gidan ta da shagunanta kuma suna hannun Aliyu, kinga kenan da ha??inta za'ayi mata komai, dan zan mata bayani ma, da wan nan shawarar suka rabu kowa na mata fatan samun sau?i.

A Sangaren Rashida kuwa tana cen tana tunanin tashin hankalin da take ciki, sam bazata iya bari a yanke mata ?afaba, dan haka washegari da sassafe da zita tazo Rashida tace mata maza taje wajen wan nan malamin ta gaya masa halin da take ciki ya taimake ta yayi mata aiki ta samu lafiya kar a yanke mata ?afa. Zita na zuwa ta zayyanewa malam Abinda Rashida ta aikota dashi, jijina kai yayi tare buga ?asa yace "kinga, ki faWa mata zamuyi aiki kuma zata samu sau?i kinji, san nan ungo wan nan maganin idan kikaje ki barbaWa mata a jikin ?afar da kuma ramin ?afar, kunayin wan nan zancen aiki yasha ruwa kenan.

Koda zita ta dawo da maganin sai Rashida tabata umarnin data barbaWa matan kamar yadda malam yace "ai kuwa tayi dana sanin barbaWen nan, domin a ranar Rashida batayi barci ba, haka ta cika asibitin da koke koke da ihun azaba, kafin da safe kuwa ?afa tayi wani irin ruri mai ban tsoro, san nan tayi wani laSa laSa kamar zata fashe dan har tafara tsattsagewa, wan nan yasa ko awa biyu kyakkyawa ba'ayi ba bayan saka hannun Nasir aka fille ?afar Rashida wacce aka wulla duniyar barci

Sai bayan wasu awowi da basu san nan Rashida ta farfaWo, dakyar ta iya buWe idonta saboda wani irin kafirin nauyi da sukayi mata, sai data tabbatar ta fahimci inda take san nan ta tuna Abinda yafaru da ita, da sauri ta kalli ?afarta ta ganta nade da farin bandage, sai tayi saurin matsawa baya tana kallon dungulmin ?afar tata tana zare ido ta kalli su hajja tace "menene wan nan? Hajja ina ?afata? Meya sameni?

Dafa kafaWarta hajja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login