Showing 102001 words to 105000 words out of 175193 words

Chapter 35 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

537

idan suka fito daga masallaci, amma jin Rashida tace zata bisu kuma yasan da wujja tayi hakan dan a tunanin ta gidan Maryam zaije shi kuma sai ya?i zuwa yayi zagaye dasu.

Sai bayan Nasir ya sauke su ya tabbatar sun shige gida san nan ya zauna a mota ya kira Maryam, ha?uri yabata akan rashin zuwansa saboda gajiyar da yayi da kuma nauyin jiki amma insha Allah a gobe zai zo da wuri dan ya ganta.

Murmushi Maryam tayi cikin jin daWin maganar sa tace

"Babu komai, Allah yakai mu goben, dan nima na kwanta saboda nawa jikin ciwo yake min nima.

Dariya Nasir ya saka yana yi mata kiss ta wayar yace

"Kice munyi anko.

Sai da ya gama wayar san nan ya shiga da motar gidan yana jin kewar Maryam na rufe duka ilahirin jikin sa.

Yana shiga falon ya tarar babu kowa alamar kowa ya tafi makwancin sa, bai damuba shima yayi Wakin sa danya saka a cikin ransa bazai ?ara neman Rashida da wani abinba tunda ta?iyin hankali duk kuwa da irin kewarta da sha'awar ta dake damunsa.

Addu'a yayi ya kwanta dan bayason yana kaiwa dare da azumi baiyi barci ba saboda sallar dare da kuma sahur.

Sai misalin ?arfe sha Waya na dare san nan Rashida ta nufo Wakin Nasir, tasha wanka ta saka wata ?aramar riga iyakarta mazaune gata sharara dan ana ganin komai na jikinta, ranta ne ya Wan sosar mata ganin nasir kwance yana barci dan daga gani ma ya daWe da kwanciyar, jitai kamar ta juya ta koma amma tuna zatayi asarar maganin data saka kuma ta shafa na shafawar sai kawai ta daure zuciyar ta ta ?arasa gadon tana kwanciya kusa dashi.

*Washegari*

Binta kawai Nasir yake da kallo yana mamakin irin warin daya ji na fita a gaban Rashida da kuma jikinta, shifa yana cikin wata lukutar masifar da tsamoshi sai dai Allah, tunani yakeyi me ya saka Rashida wari? Gashi gaba Waya baiji wani WanWanon taba kamar yadda yakeji da, salam haka ta koma masa kamar dai wacce ta warke daga Cuta, gabansa ne yafaWi daya tuna irin dagwalo da kuma ?uraje dasuka fito mata a gabanta watannin baya, a take yabawa ransa cewar wan nan cutar datayi ne ya haddasa mata rashin WanWano wari da kuma bushewa.

Ita kuma Rashida tana ganin yadda Nasir ke binta da kallo duk inda tayi sai Abin ya dungayi mata daWi a ranta har take ganin lallai maganin data matsa a jikinta kuma ta shafa shine yayi mata aiki har Nasir yake binta da kallo, murmushi tayi masa a sanda take kallonsa tare da Waga masa gira tace

"Ya ne?

Shima murmushin yayi mata yace

"Babu komai

Tashi yayi tare da Waukar jakarsa zai fita sai tai saurin cewa

"Ina kuma zaka?

Cikin mamaki yace

"Ina zanje kuma? Zanje kasuwa ne mana.

?ata fuska tayi tace

"Ban yarda dakai ba baban Halima, kace dai gurin ?anwata zakaje ka ganta, sai kuma taWan saki rai tace

"Hakan ma yayi dai-dai, dan Allah idan kaje kace ina gaidata da jiki.

?aga kai Nasir yayi yace

"Zataji san nan yafara tafiya, da sauri Rashida ta ?araso kusa dashi tana manna masa kiss tare da karSar jakar tace muje na rakaka.

Gaba tayi Nasir yabita a baya yana ganin yadda Rashida ke juya mazaunai, a gefe guda kuma yana tunanin rashin jin warin dabaiyi ba yanzu a jikinta, saSanin jiya da warin ya isheshi sai da ya dunga toshe hanci.

*Maryam*

Tanajin ?arar zura mukulli a jikin ?ofar gate Win tayi saurin mi?ewa duk da nauyin jikinta tayi waje bakinta a washe tana jiran shigowar sa, yana kuwa shigowa ta ?arasa garesa tare da faWawa jikinsa tana masa sannu da zuwa

Kanta Nasir ya dafa yanajin wata sassanyar nutsuwa na shigarsa da ganinta lafiya dan rashin zuwansa jiya ya sosa ransa.

?ar hira suka taSa take tambayar kozai fita yace

"Eh.

sai tace to ya sauke kulu gidan samira zata karSo mata sa?o.

Tasan itace da girki shiyasa koda kulu ta dawo kichen suka shiga suka fara hada hadar Wora girkin shar ruwa, wajen shida sun kammala komai har wanka sunyi sun zauna suna lazumi tare da jiran lokacin shan ruwa, ba'a daWe ba kuwa sai ga Nasir ya dawo a gajiye shima, wanka ya faWa yana fitowa a kafara kiran magariba.

*Rashidan*

Tun tana zuba idon dawowar Nasir har tafara tunanin Abinda ya tsayar dashi gashi har an sha ruwa, ta kasa cin komai sai ruwan shayi data haWa tanata zaman jiran sa amma shiru, salla tatashi tayi san nan zuciyar ta ta raya mata data kira Nasir taji menene matsalar dahar yanzu bai dawo ba.

Kusan sau Uku tana kira san nan Nasir ya Waga da sallama Wauke a bakin sa, daga cen Sangaren Rashida tayi gyaran murya tare da cewa.

"Naga shiru baka dawo ba ka gayan shan ruwanka na jiranka shine nace bara na kirawo ka koka biya wani wajenne?

Maryam Nasir ya kalla tare da fara irge da hannunsa yaga dai tabbas yayi kwana biyu gidan Rashida yau kwanan gidan Maryam ne, sai kawai yayi dariya yace

"Hala dai lissafin ya kufce miki ko maman halima? Inace yau gidan ?anwar ki nake shiyasa dana taso daga kasuwa nayo gidan ta, zuwa Anjima amma zanzo mu gaisa ai.

Cikin Sacin rai duk da tana dannewa tace

"Okay, to bama sai kazo ba ai, ka zauna ka huta.

Batare da Nasir yaja zancen da tsawoba shima yace.

"Yauwa Nagode maman halima, sai da safen, yana faWar haka ya kashe wayar baki Wayanta yana cewa a ransa.

"Na canza Rashida, badai a nufinki gatse kika min ba? Zaki ga Wanyen kai.

*Rashida* .

Wani kuka ne ya kufce mata tai saurin wullar da wayar tana kallon tulin abincin data girka duk dan saboda shi, ashe daman Nasir bazai iya bata sati guda su cancare ba tunda tayi watanni a gida? Watanta nawa a gida? Batare da Maryam Win tabar su ba? Amma saboda zuciyar sa bata gareta shine zai tafi gidan Maryam daga kwana biyu? Ita aiji take ko bata nema ba shi mai ?ara mata kwana ne kamar na sati ko sati biyu tunda ai an shiga ha??inta, tashi tayi daga wajen tana tan kwaSe kofin sayin dake gabanta ya Sare.

Ni kwa nace "oho dai>?7? @&?ki zubar kuma ki gayara tunda babu mai gyara miki=??=??=??

?aki ta shige tana bugo ?ofar da ?arfi tana kiran sunan Maryam a haukace kamar wacce takeyi d aradu.

Daga halima har sauda ma sai suka kasa cin abincin suka zubawa ?ofar maman tasu ido suna tunanin Abinda akayi wa maman su take kuka.

*KUTSE*

*PAGE 44*

*MOM HANEEF*

Lamarin duniya

Kwanci tashi babu wahala yau gashi muna saura kwana uku a kama ?aramar salla, haka zatazo itama ta wuce kamar yadda aka kama azumi shima yake shirin shuWewa.

*Rashida*

Cikin damuwa take kallon tulin uban kayan miyan dake gabanta a zube, cefane ne kala kala sai a binda aka manta ba'a siyo ba duk na shirin abincin salla da za'ayi, kallon tulin kajin dake gefe Rashida ta kuma ranta na Saci da ba?in ciki ta kalli yaron da Nasir ya aiko tace

"Kace yace na raba na bayar ka kaiwa Maryam?

Kai Wan aiken ya Waga yana mamakin irin dugun zumar da yaga tayi yace

"Haka yace na faWa miki.

Kujera ?ar tsugunno ta samu ta zauna san nan tafara bubbuWe kayan miyan tana duba abubuwan dake ciki.

Ledar hannunsa ta karSa tana tsaki tafara buWewa tana zuba kayan miya a ciki, ajiye wa tayi tare da kar Sar wata ledar ta kuma zuzzuba sauran abubuwan, san nan ta mike tsam tace

"Ka Wiba gasu nan.

Cikin mamaki yaron yake kallon ?ullukan da Rashida tayiwa Maryam, amma saboda ya gaskata sai yace wan nan ?ullukan ma?ota za'a mi?awa sadaka?

Harararsa Rashida tayi tace "Ah almajirai za'a bawa ba ma?otaba, ince waccen yace a Wibawa ka kai mata? To ai natan ne.

?aya bayan Waya yaron ya dunga Waga ledar yana ajiyewa yana faWin humm umm, humm umm.

Duka uban lodin kayan miyan nan wai Wan wan nan za'a zubawa Maryam kamar ba matar gida ba, gaba Waya kayan miyan data zuba mata baifi na Wari biyar ba, san nan ga agushi amma shi bama ta zuba mata ba, bayan haka kabewar ma gutsurowa tayi ta wulla ma a ledar taWan yafa mata alayyahu, wani abin ba?in cikin ma kajin daya kawo guda ashirin ne da????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? n shiya tsaya a wajen aka gama gyarawa san nan ya Wauko ya tawo amma saboda son zuciya guda Waya ta saka mata sa iuban kai da ?afa data loda mata kusan guda sha biyar.

Kai yaron ya gaWa tare da tattare kayan yana cewa gaskiya matar nan bata da mutunci wallahi.

Da sauri Rashida ta juyo tana matsowa kusa dashi tace

"Me kace?

?an baya yaja yana ya?e ganin ta hayayya?o masa yace, daman canai kinada adalci ranki shi daWe.

Tsaki Rashida tayi tana wucewa a ranta tana ayyana wallahi a yau dai ko Nasir ya?i koya so sai taga inane gidan shegiyar yarinyar nan dan wallahi bazata bari ta haifi cikin jikinta ba dan ko menene zata iya yi akan hakan.

Rashidan na ganin yaron ya fice itama tai saurin zarar mayafi ta yafa tare da saka facemask ta fice tana sauri dan kar yayi mata nisa, Wan sahu tatare tace drop tare da nuna masa a dai-dai ta sahun da yaron ke ciki akan yabishi har inda zaije, babu musu mai Wan sahu ya amince tare dafara falla gudu dan karma tace baya sauri sun Sace musu ta?i ta bashi ha??insa.

Cikin mamaki Rashidan take kallon layin gidan Maryam wanda manya manyan gidaje ne a layin dan za a iya cewar gidan Maryam ma shine ?arami a jerin gidajen.

Da sauri ta isa gaban yaron tana dariya ?asa ?asa tana cewa.

"Kayi ha?uri karka ga na biyo ka.

Da sauri yaron ya matsa baya yana mamakin ganin Rashida, matar daya bari a gida ita ce tsaye a gabansa haka? Shin kodai aljanna ce? Anya kuwa babu wani abin? Yakewa kansa tambayar zuciyar sa fal tsoron Rashida dan tashayar dashi mamaki.

Ganin da Rashida tayi ya cika da mamaki sai kawai tace

"Ka daina mamaki kaji? Daman tukuici ne ban baka ba shi yasa na biyoka na baka saboda karka yi tunanin matar oga marowaciya ce.

?an sakin ya?e yaron yayi yanajin kamar futsari zai kufce masa a wondo dan haka sai yayi saurin mi?a hannu ya karSi kuWin tare da sake mata ledojin yana juyawa yafara tafiya yana cewa

"Dan Allah ki mi?a mata yanzu zan dawo, yafara tafiya yana wai wayar Rashida wacce tuni tayi bugu kuma aka buWe mata gidan ta shiga.

Shi kuwa yaro a sanda zai kuma waiwayo wa yaga Rashida sai yaga wayam bata nan, take futsarin dayake ri?ewa ya kufce masa yafara tsiyaya ai kuwa bai tsaya jiran komai ba ya kwasa a guje yafara gudu yana yararar futsari.

*Maryam*

Wata irin dokawa ?irjinta yayi a sanda taji murya kamar ta Rashida a tsakar gidan tana kiran sunanta, kasa motsawa tayi dan daman tana zaune ne ga azumin yau yana bala'in wujijjigata tare da kwalata, kamar ta karya shi ma haka ta dungaji amma daga baya sai wahalar taWan saketa bayan tayi barcin wahala ta farka, shiyasa ta kasa wani yun?uri.

Shigowar kulu falon kenan taga Maryam na ?o?arin tashi tana cewa

"Wacece?

Hawaye kulu ta share tana zama tace

"Matar kawu Nasir ce tazo.

Gaban Maryam ne ya faWi take tafara addu'ar kariya daga sharrinta dan tasan banza batakai zomo kasuwa dole akwai sharrin daya kawo ta ta ?ulla tatafi.

Hakan yasa ta kasa tashi sai ma dafa cinyan kulu tayi wacce ke kuka tace

"Wai me akayi miki ne kulu?

Cikin Muryar kuka kulu tace ba matar kawu bace, dan tayi bugu na buWe mata shine na gaisheta ta?i amsawa san nan nace ta kawo kayan dana ganta dasu na shigar mata dasu shine ta dakamin tsawa wai kar Na sake na saka ?azamin hannuna nace zan taSata idan ba haka ba sai ta wula?anta ni, harda cewa wai nida uwata kwaWayayyu wanda basu iya ?auyan cinsu ba.

Cikin bacin rai Maryam tayi ?okarin tatashi tana kiyi ha?uri kulu itama ai a salin ta ?auyen ne to dan ta zagi ?auye ma har ribar me zataci? Bari naje naji da wacce tazo dan tabbas nasan Alkairi bazai kawo Rashida gidan nan ba.

Saboda Sacin rai ma sam Maryam ta manta bata Wauki hijabin data saba sakawa ba idan zata fita, haka tafita tsakar gidan da zungureren cikinta tana jan ?afa da kyar, duk da dukan tara taran da ?irjinta keyi da ganin Rashidan datayi bai hanata Wauko murmushi ta sanya akan fuskarta ba tana cewa

"Sannu da zuwa maman halima, ki shigo ciki mana.

Kai Rashida ta girgiza cikin ba?in cikin ganin cikin Maryam kuma wai Nasir ne yayi cikin, idanunta har ciccikowa sukayi da hawaye amma sai tayi saurin mayar dasu dan kar ta fallasa kanta, itama murmushin tayi har hakwaranta suna bayyana dan farin cikin ganin maryam ta tsallake bar baWen maganin da tayi mata tace.

"iKon Allah, Allah mai iko ashe kinyi nauyi haka? Badan nazo na ganiba kenan da sai dai muji haihuwa ko?.

Ita dai Maryam yake kawai takeyi musamman yadda taji marar ta ta wani soka Wan cikinta ya wani hautsine ya gicciye yayi gefe Waya ya dun?ule gashi ta kasa Waga koda ?afarta ce.

Dakyar ta iya cewa Rashida

"Uhummm, ki shigo mana kya tsaya daga nan.

Baki Rashida ta Wan kwaSe tace

"Daman bazama zanyi ba ai, sa?one ban samu mai kawo miki ba shine na tawo da kaina na kawo miki, gashi nan inji mijinki, ta ?arasa faWa tana ajiye ledojin dake hannun ta daWi fal ranta na ganin canjin da Maryam ta samu a lokaci guda.

Harta juya zata buWe gida ta fice taji Maryam ta saki salati mai haWe da ?ara tana washh Allahna tare da ri?e Kwankwaso tana cije leSSe, da sauri Rashida ta ?araso kusa da ita tana faWin menene? dai-dai fitowar kulu tana kiran sunan aunty Lafiya?

Hannun ta Maryam ta fuzge daga na Rashida tana kallonta da jajayen idanunta wanda suka kaWa sukayi ja kamar gauta cikin ?arfi tace

"Cikani, muguwa azzaluma, wallahi duk Abinda kikazo min dashi sai dai ya koma kanki, sai Maryam ta kalli kulu tace

"Kulu yi sauri ki Wauko min wayata na kira ya Nasir jinake kamar zan mutu.

Da sauri kulu ta juya hankali a tashe tana kuka tayi falo.

Rashida kuwa ganin maryam na mur ?ususu sai kawai ta juya a guje ta fice daman bata sallami mai Wan sahu ba ta waWa ciki tace malam tayar ka zuga muje.

Tayar war kuwa yayi yafara shara gudu dan yadda Rashida take azalzalar sa daya bada wuta abin har mamaki yake bashi kamar ba mace ba.

Maryam kuwa tun tana iya buWe baki tana salati har tagaza domin yadda takejin marar ta na ?ullewa da sokawa da karta kamar zata tafi bar zahu.

*Nasir*

Cikin ?an?anin lokaci ya har gitse domin kwata kwata bayason wani Abinda zai samu Maryam ballatana cikin jikinta, sharara gudu kawai yake yi duk da cikowar da gari ke dashi saboda hada hadar zuwan ?aramar salla, da taimakon Allah yaje gida kuma yana zuwa baiyi wata wata ba ya sungumi Maryam ya zura a mota sai asibiti.

Abin da ya ?ara tsorata Nasir bai wuce sanda ya Wauko Maryam Win ba sai yaga zanin jikinta ya Saci da jini Alamar jinine yake zuba a jikin ta.

Emergency aka shiga da Maryam domin bata taimakon gaggawa dan sosai take ciwo ga Alamar zubar jini a jikinta.

Safa da marwa kawai Nasir keyi domin yama rasa wane tunani zaiyi dan gaba Waya kansa ya gama kullewa.

*Rashida*

Wani razanan nen ihu ta saka tare da sumewa a lokacin da Wan sahun nasu yayi wata irin sufa ya kife akan titi take kuwa wata tirela tayo kansu zata take su.

*****

Duban irin ciwukan da Rashida taji Nasir keyi yana mamakin Abinda ya fitar da ita batare data nemi izininsa ba, ?ara Waga kai yayi ya kalli Rashida wacce wuyanta yake Waure da abin Waure wuya idan wuya ya taSu, ga wani ?aton bandage da'aka zagaye mata kai dashi Saboda ?aton ciwon dake goshin ta.

So yake yayi mata tambayar ina taje da har zatayi hatsari a kirasa a faWa masa? Amma nauyin ciwon da Maryam tayi ya danne zuciyar sa har yake ganin ciwon Rashida bama komai bane bare ya zauna bibiya tunda koma menene ya sameta ai ita tajawa kanta, dan haka sai kawai ya juya ya fita yana Waukar wayar sa domin kiran Maryam.

Wayar bata daWe tana ringing ba sai kawai kulu ta Waga da sallama.

Ina Maryam Win? Nasir ya tambaya bayan amsa sallamar kulu, kallon Maryam tayi wacce ke kwance tana barci hankali kwance kamar ba itace ke ciwo ba.

"Barci takeyi, kulu ta faWa tana ?ara manna wayar a kunnenta, ajiyar zuciya Nasir yayi yace

"Kin tabbata? ?aga kai kulu tayi kamar Nasir na kallonta tace

"Da gaske nake kawu barci takeyi.

Kashe wayar Nasir yayi yana fita daga asibitin yana ayyanawa a ransa babu Abinda zaiwa Rashida tunda bashi ne ya aiketa ba, bazai zauna a sha ruwa yana zaune asibiti ba, Dole ne yaje gida yasha ruwa koda zai dawo asibitin.

Abin ba?in cikin da Nasir ya tarar a gidan daya koma ma jiyayi daman a bakin titi ya zauna yasha ruwansa a wajen mai shayi ko kuma yaje gidan Maryam yasha ruwansa.

Su Halima ya gani zaune a ?ofar gida ta Wora sauda akan cinyarta tana rarrashinta, daga gani an san sun sha kuka, kuma daga ganinsu sun sha ba?ar yunwa tunda tun uku na rana ake tashin su daga islamiyya amma gashi har ?arfe shida da wani abin suna ?ofar gida a zaune, cikin Sacin rai ya ?arasa inda suke yana tambayar su me sukeyi a wajen a zaune?

FaWawa kansa sukayi suna sakin kuka tare da cewa tun rana suke zaune suna jiran mamansu bata dawo ba har yanzu, numfashin Sacin rai Nasir ya sauke a ransa yake cewa

" tun rana Rashida tafita kenan? Hnmmm.

Wani bunsurun wari ne yaji yana dokar hancinsa, a take kuwa ya kalli su Halima dan daga cikin jikinsu warin yake fitowa, Wan toshe hancinsa yayi yace

"Ku warin meye wan nan nakeji?

Kallon sauda Halima tayi tace

"Kashi sauda tayi a wando Abba.

?anja baya Nasir yayi yace

"Kashi a wando kuma sauda?

Shasshe?ar kuka sauda tafara tanason magana amma wani kukan ya kwace mata .

Sai Halima ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login