Showing 45001 words to 48000 words out of 175193 words

Chapter 16 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

572

ga Allah taso ace Nasir yaci wan nan abincin data girka, amma maimakon taji ba?in ciki kawai sai tayi murmushi tace

"Allah ya kaika lafiya ya dawo dakai lafiya ya Nasir, da yake tagama kawo komai ta ajiye kawai cine ya rage, sai tayi zamanta a wajen tana jiran Rashida ta fito su karya, kusan mintinan Maryam talatin a zaune tana jiran Rashida, gashi wata yunwa takeji na kwakwular cikinta, kuma batasan tafara cin abincin Rashida tafito taga ta mata ba dai-dai ba.

Shawarar da zuciyar ta take bata na ta Kwankwasawa Rashidan ?ofar tace mata ita take jira, dan zai iyuwa batasan ita take jira Winba, Kwankwasa wa biyu Maryam tayi ?ofar Rashida sai gashi ta buWe.

Kallon rainin hankali rashida takebin Maryam dashi, gashi sai wani yatsina fuska takeyi kamar taga kashi saboda wula?anci, duk da Maryam bataji daWin irin kallon da Rashida tayi mata ba amma sai tace a ranta ?ila bataji daWin bugun data mata bane kotana wani abin, dan haka sai Maryam tayi saurin sadda kanta ?asa tace.

"Kiyi ha?'uri maman halima, daman canai bara na faWa miki nagama haWa abincin ke nake jira muci kada yayi sanyi.

Kallon sama da ?asa Rashida tayiwa Maryam san nan tace ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?

"keda Allah dakata min, wai meyasa kika fiya shisshigewa mutane ne, kuma kinga alamar yunwa atare dani? Ko kuwa an faWa miki zan iya cin jagwal gwalon kine? To banaci, kuma kece mayunwa ciyar abinci ai tunda babu a house, dan haka kije ki cinye jagwal gwalon naki ki cika cikin ki ko kyayi Waurayar ciki kafin a saba dacin daWi, sai ta saka hannunta ta hankaWeta baya tana cewa

"Ni matsa kibani waje na wuce kada ki Sata min lokaci domin ke bakida da darajar dazan saurareki, aikin banza aikin hofi wahalalliya kutsattsiya maiyin maso wani.

Tana ?arasa faWar hakan ta zura mukullin hannunta ta rufe ?ofarta san nan ta baWe Maryam da ?amshin turarenta ta ja mata tsaki tare da tofar mata da yawu tace

"?azama kawai. San nan ta wuce abinta ko waiwayar Maryam batayi ba.

*Maryam*

Kusan suman tsaye tayi Saboda jin magan ganun da Rashida ta jefeta dasu, da kyar ta iya motsawa tabi bayan Rashida da kallo tana tunanin kodai rashida nada aljanune bata saniba, idan ba mai hawa da saukar iska ba, ita bata taSa ganin inda mutum yake canzawa haka lokaci Waya ba kamar wahainiya idan ba Rashida ba, da kyar ta iya dafa bango ta jingina da bangon saboda yadda takejin jiri yana neman yasar da ita, sai datayi wajen minti biyar a haka san nan ta iya daddafawa ta isa wajen dining domin ta samu ta sakawa cikinta wani abun ko zai daina zugin da yake mata.

Koda ta zauna kan dining Win kasa cin abincin tayi sai kaWan data saka a cikin ta ta daka uban tagumi tana tunanin halaye irin na Rashida, a ranta take cewa

"Wai matar nan me takeso da nine? Kodai daman shigo shigo babu zurfi tayi min saboda na yarda da taci amanata? Hawaye ta share tanajin kaWaici na lulluSeta a lokaci ?alilan.

Haka tagaji da zama akan dining Win sai tatashi ta nufi Wakin su Halima ta kwanta tanajin kamar ta zura da gudu saboda tsoron gidan da take ji.

Ta rasa me zatayi ya Webe mata kewa, kawai sai ta Wauki wayarta ta kira samira domin su gaisa suji muryar juna, samira na Wagawa Maryam ta saki ajiyar zuciya tace

"?awata tsoro nakeji.

Da sauri samira ta sauko daga kan gadon data ke kwance tace

"Tsoro kuma Maryam, tsoron wa? Tsoron rashidan ko Nasir Win?

Idanu Maryam ta lumshe san nan ta kuma buWewa tace

"Tsoron gidan nakeji samira, babu kowa a gidan nan duka sun fita.

Sun fita kuma? To ina suka je? Samira ta tambayeta tana mamaki.

Da Wan sauti kaWan Maryam tace

"ya Nasir yatafi bichi Waurin Aure, su Halima suna gidan kakar su, ita kuma maman halima tatafi gidan yayarta, ni kaWai suka bari a gidan.

Murmushi samira tayi tace "to banda a binki Maryam ai haka rayuwar mace ta gada, ai gwara kema kinada da ?an tayin hira, zuwa jimawa zasu dawo gidan Insha Allah, ni kuwa ina zaune ni kaWai kamar mayya dan haka kinsan kiran nan nawa da kikayi kin Webe min kewa?

Murmushi Maryam tayi tace "nima kin Webe min kewa.

Sai samira tace "to faWa min, ya ake ciki a cikin gidan? Da fatan dai komai yayi normal ko? Kuna shiri sosai da Rashida?

Cikin raha Maryam tace "samiraaah, wan nan tambayoyin fa? Ajiyar zuciya samira ta sauke tace "na damu ne Maryam, nadamu kwarai da gaske domin na ganki cikin walwala da farin ciki.

Insha Allah zanji daWin zama dasu baki Waya samira, Maryam ta faWa wani kuka yanason kufce mata, sosai kukan ya tunkaro mata ma?ogaro yana neman fitowa, sanin zai iya fitowa koda yaushe yasa Maryam tayi saurin katse wayar data keyi da samira dan kar kukanta ya tona mata asirin halin da take ciki.

Kuka sosai Maryam taci tana tausayawa kanta kishi da Rashida har wani barci yafara fuzgarta.

*****

*Rashida*

Tana fita gidan ya karimatu ta nufa tanajin ?unci sosai a cikin zuciyar ta, sallamar mai napep Win Rashida tayi tanajin takaicin rashin gyaran motarta da har yanzu rashin nutsuwar zuciya ya hanata batai ba.

Tana shiga gidan ta tarar da mijinta dan ko fita baiyi ba, babban Abinda yabawa Rashida mamaki bai wuce ganin ya karimatu ta zauna daram a ?asan ?afar mijinta tana Sare masa a yaba tana bashi cikin ladabi ba, daman ladabin gidan aure sunnar gidan su ce amma ita ya karimatu ta daWe rabonta da Wabba?a wan nan suna, dan madadin ace itace takewa miji biyayya to shine yake mata biyayya iya iyawar sa dan kar ya Sata mata rai.

Sai da suka gaisa da Rashida san nan tashiga Wayan falon wanda yake mallakin ya karimatu ne datake zama dan ta jirata, zaman jiran wajen minti Ashirin tayi san nan ya karimatu ta tawo tana Wan Wingisa ?afarta.

Dariya Rashida ta saki tace "ai dole kiyi Wingishi yaya, ganinki fa nayi kina dur ?ushe kina Sare a yaba.

Hararar wasa ya karimatu tayiwa rashida tace "ai biyayyar dole ne a wajena Rashida muddin inason gamawa da Mijina da hajja kuma da duniya lafiya, dan gaskiya lamarin duniyar nan yafara bani tsoro Rashida.

A kai kaice Rashida ta kalli ya karimatu tana mai gyara zama tace

"ban ganeba wai anyi yamma da kare ya karimatu? Saranda cikin gaggawa haka? Kodai wani abin tashin hankalin kika gani ya tsorata ki?

Kai ya karimatu ta girgiza tace ko Waya Rashida, kawai dai na tuba ne da dukkan Abinda nakeyi, kuma wallahi nayi nadamar Abinda naitawa Salisu ada, nifa yanzu ma indai yasamu wata matar da yakeso wallahi ya kawo nayi al?awarin da kuWina zan masa auren.

Wata guWa Rashida ta saki ta Sacin rai tace

"ya karimatu dai, bakya rabo da abin dariya wallahi, Ni duk ba wan nan ba dan wallahi nagaji dajin magan ganun nan saboda sosa min rai suke yi, daman labari nazo baki kuma san nan na karSi sa?ona ki rattabamin bayanin yadda zanyi dasu na wuce gida.

Murmushi ya karimatu tayi tace

"Rashida kenan, to ina jinki.

" Duka abubuwan da suka faru Rashida ta kwashe ta sanar da ya karimatu, amma madadin taji ya karimatun ta Wau zafi kamar da sai taji a kasin haka, dan kallonta ya karimatu tayi cikin murmushi tace.

"Amma baki taSa burgeni a rayuwa ta kamar yau ba Rashida, haka yakamata mace ta gari ta kasance a cikin gidanta, kuma ni shawarar dazan baki a matsayina na ?ar uwar ki shine.

"Kinga Nasir na ?aunar ki, kuma wallahi muddin kika bari wan nan capacity Win naki ya sauka daga kansa da idanunsa kin kaWe har ganyen ki, dan haka ki kula, ki ri?e mijinki da mutunci san nan ki ri?e kishiyar ki amana, muddun kikayi haka zakiga kyakkyawan sakamako.

*Rashida*

Saboda yadda takejin Sacin ran magan ganun ya karimatu sai taji idanunta ma har wani yaji suke fitarwa kamar an baWa mata bar kono, ga numfashinta dake sama yana ?asa yana fita da zafi zafi kamar wacce zazzaSin mashasshara ya lafke.

Kallon ya karimatu tayi tace

"yanzu dai ina sa?ona? Girgiza kai ya karimatu tayi tace "ban kar So ba, saboda na tuba nayi nadama wallahi, nayiwa Allah al?awarin bazan sake aikata aikin saSo irin wannan ba, san nan kuma bazan kai kowa dan yasaSa masaba, saboda haka kema ina shawar tarki daki zubar da makamanki ki rungumi shawarar dana baki dan itace hanyar tsira.

"Mi?ewa Rashida tayi ta zari jakarta tace "haka ne kam, Nagode da shawarar ki ya karimatu, ha?i?a sai yau na ?ara tabbatar da cewar ni marainiya ce, kuma bani da wani ishasshen gata saina Allah dana dangin mahaifiya ta, saboda nasan cewar da autace take cikin halin danake ciki da dukkan yadda zakiyi sai kin taimake ta iya ?arfin ki da kuma aljihun ki , amma saboda ni ?ar ubace shiyasa kikayi min haka,Saboda haka Nagode.


Fuuuuu, Rashida ta fice daga falon ya karimatu duk kuwa da kiran datake mata bata waiwayo ba domin tuni hawaye ya wanke mata fuska dan har wani hazo hazo take gani a cikin idanunta

*Nasir*

Tunda suka dawo garin yaji babu inda yake da muradun yazo sai gida domin yayi tozali da matansa, musamman salihar matarsa wacce yanayinta yake bala'in burgesa, bai santa ?a mace ba amma yana fatan koda ya santa ?a mace ta kasance mai kunya kamar yadda take a yanzu

Yana zuwa gidan yaji shiru kamar babu motsin mai rai, Wakinsa yafara le?awa san nan ya rufe ya le?a na Rashida, babu kowa a ciki sai ya nufi Wakin su Halima dan yana kyautata zataon cewar Maryam tana ciki.

Yana buWe War kuwa ya ganta a kan gadon daga ita sai Waurin ?irji tana barci, gaba Waya zanin nata ya yaye ilaihirin jikinta duk a waje, wani irin yarr Nasir yaji tsikar jikinsa tatashi tare dajin wani Abin yana War suwa a zuciyar sa game da Maryam Win.

Zuciyar sace taita zugashi akan ya Wauketa cak yakai Wakinsa Saboda yaji daWin gudanar da ?ar bar ha??insa a nutse a wajen Maryam Win, dan haka sai ya Wauketa cak a hannunsa yana murmushi tare dajin mugun sha'awar kasancewa da ita.

*Maryam*

Bada niya ta kwanta haka ba, kuma tabbas datasan Nasir zai dawo a wan nan lokacin bazata soma ma cire kayan jikinta ba, bayan tagama kukanta sai kawai taji kayan jikin nata sun mata nauyi suma, hakan yasa ta cire su saboda tabar nauyin zuciyar kaWai ya dameta banda na kaya, shine fa tacire rigar taja zanin rigar sama ko Iska tafi ratsa jikinta, tana kwance tana wan nan sa?ar zucin sai ga wani nannuyan barci ya tafi da ita, wanda bata farkaba sai dataji an Wauketa kamar wata yarinya anyi sama da ita.

A furgice ta farka tana mutsu mutsu tana kallon fuskar Nasir, zuciyar tace ta buga da?arfi Saboda wani kyataccen annuri dake zuba a cikin idanun da Nasir ya kafeta dashi, ita tama manta babu kaya a jikinta, shiyasa ta saki jikinta itama takama kallon Nasir Win da idanunta wanda suka kaWa sukayi ja Saboda barcin data sha.

*Rashida*

Cikin Sacin rai ta shigo gidan, tana ganin motar Nasir gabanta yayi mummunan faWuwa da har sai da taji ?irjinta ya motsa saboda tuna Maryam Win itama tana cikin gidan, da gudu ta haye sama har tana haWa step bibbiyu tana hayewa, tana shiga falon ta rusa wani uban ihu tare da wullar da jakarta ta zube a wajen kamar matacciya, ba komai ya haddasa mata wan nan shiga shock Win ba illah ganin Maryam a hannun Nasir tsaye sun kafe idanu akan juna suna murmushi, gashi Maryam Win daga ita sai pant da brezia.


Su Nasir kuwa ?arar ihun da Rashida ta rafka ne ya dawo dasu hayyacin su, wani salati Nasir ya zuba ganin Rashida ta faWi a wajen sai ji kuke timmm Nasir ya wullar da Maryam yayi kan Rashida a kiWime yana kiran sunanta, ita kuwa Maryam jin Nasir ya ti?ar da ita Wuwawun ta ya runtuma da ?asa shine yasa ta cije leSe ta saka hannu zata sosa tajita babu kaya, sai a san nan ta tuna Waurin zaninta datai kenan ya yaye ko kuwa Nasir ne ya yaye mata har Rashida ta ganta a haka, wani irin tashin hankali ne mai haWe da kunya ya dirar mata lokaci Waya, ai kuwa da gudu ta mi?e ta runtuma da gudun bala'i danta manta zugin Wuwawun nata ta banka ?ofar, hayewa kan gadon tayi tanajin daman mafarki takeyi kuma kamar kowa yana kallonta, shiyasa har da rarumo bargo ta lulluSe jikinta baki Waya.


*KUTSE*

*PAGE 20*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Nasir*

Cikin kiWima ya isa wajen Rashida yana kiran sunanta tare da jijjiga ta amm ta?i koda motsa hannunta, gashi dai yaga alamar ba suma tayi ba kuma ba mutuwa tayi ba danga idanunta nan tana wurgasu tare da rarrabasu kamar Sera a buta, ganin haka yasa Nasir ya tashi da saurin gaske ya buWe fridge tare ta Wauko gorar ruwan sanyi ya nufota dashi kuma biyi wata wata ba ya Salle murfin tare da tsiyaya mata ruwan.

*Rashidan*

Wata ajiyar zuciya taja mai ?arfin gaske jin ruwan sanyi a cikin jikinta, da sauri ta kalli Nasir tare da fashewa da kuka ta rungume shi tace

"Banason ta Nasir, banason ka haWa jiki da wata mace idan baniba a duniya, dan girman Allah Nasir ka sallami yarinyar nan ta koma gidan su ni kuma wallahi zan maka duk Abinda kakeso, san nan wallahi zan mallaka maka komai dana mallaka a duniyar nan indai zaka barni dakai ni kaWai mu zauna mu samu farin ciki, zama da wan nan yarinyar bazai kawomin farin ciki a cikin gidan nan ba, dan Allah ka taimakawa rayuwar duniya ta.

Sai ta ?ara ?an?ameshi tana shasshekar kuka.

*Nasir*

Tabbas lamarin Rashida yana matu?ar bashi tsoro a rayuwar sa, shifa bai san haka lamarin kishin Rashida yake ba sai yanzu, yasan dai tana da kishi amma baiyi zatan irin nata kishin kenan ba, dan shi yana ganin wan nan ya wuce kishi sai dai a kirashi da mahaukacin kishi, gaskiya idan har haka masu mata masu kishi irin na Rashida suke fuskantar matsala to lallai suna cikin iftila'i kamar yadda yake ciki yanzu, kuma tabbas ya kamata yafara tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro tun da wuri, kuma tabbas yafara lankwasa ?arfe tun da zafi zafinsa kafin ya huce a rasa yadda za'a yi dashi.

Hakan yasa ya raba jikinsa dana Rashida da ?arfi yaja da baya yana hucin Sacin rai badan ran nashi a Sace yake ba, dan idan za'a tona zuciyar sama shi wallahi tausayin Rashidan yakeji ma, amma sai ya maze dan yayi rantsuwa da al?awarin zama da maryam kuma ya gwada musu a dalci har ?arshen numfashin su.

*Rashida*

Ganin Nasir ya rabata da jikinsa ya mi?e yana haki sai hankalinta ya kuma tashi, dan haka itama sai ta mi?e da zafin gaske ta isa gareshi tana kuka tace

"Dan girman Allah karka juyamin baya masoyi, idan ka juyan baya bansan ya zanyi da rayuwa ta ba.

Jiyowa Nasir yayi ranshi a haWe yana kallon Rashida cikin kaushin murya yace

"Ba nufina na juya baya a gareki ba Rashida, bana fatan ranar dazanyi butulci a soyayyar ki, amma abubuwan da kikeyi sunyi yawa, haba, sai kace a kanki aka fara kishiya? Ko kuwa kece ta ?arshen wacce za'a yi wa kishiya a rayuwar nan, duk kinbi kin tashi hankalin ki kamar wadda akace biyu za'a rabani.

To bara kiji, billahillazi tun wuri gwara kidawo hankalin ki da nutsuwar ki, idan kuwa ba hakaba wallahi kece zaki wahala a banza dan bazan taSa rabuwa da Maryam ba Insha Allah, kamar yadda bana fatan rabuwa dake sai dai mutuwa to itama bana fatan na rabu da ita sai dai mutuwa, dan haka Rashida ki dawo hankalin ki, ya ?arasa maganar da karsashi a cikin zuciyar sa.

Wani saranda a tsaye Rashida tayi Saboda tsabagen mamakin Nasir, itace yau yake furtawa wan nan banzayen kalaman? CaSSijan, ashe kuwa an kusa ayi ruwa da feshin wuta, dan wallahi wan nan kalaman nasa dai-dai suke da jefa rayuwar Maryam dama tashi rayuwar a jalala.

Da sauri kuma ta dawo hayyacin ta lokacin dataga Nasir Win ya gewaye ta yayi hanyar Wakin su Halima yana kiran sunan Maryam, da gudu Rashida ta ?arasa tare da ri?e rigarsa tana kuka tana cewa "dan manzan Allah ka rabu da ita, kada kashiga Wakin nan Nasir, jinake kamar zan haWiyi zuciya ta saboda ku, ka taimakawa Rayuwa ta data yarana.

Cikin fusata Nasir ya fuzge rigar tasa yana buga Wakin su Haliman yana kiran sunan Maryam.

*Maryam*

Tana kwance a lulluSe da bargo tana rawar sanyin magan ganun da tajiyo su Rashida sunayi, a ranta take cewa "kenan Rashida bata karSe ni ba daman taje har inda nake tayi min roman baka? A gaskiya mutanen sun ha ince ni, bazan yafe mataba ta cutar da zuciya ta, tana wan nan tunanin taji bugun ?ofar Nasir yana kiran sunan ta, da sauri ta yaye bargon tare da saukowa ta rarumi rigarta ta saka ta maida Waurin zaninta tare da Waure Wankwalinta.

Ba nufinta ta buWe masaba, sai dai ta mayar da kayanta ne saboda gudun kota kwana, kuma ta ?udure a ranta ita da Nasir ko Rashida su ganta suyi ido huWu da ita sai an kwana biyu, dan haka sai ta mi?e ta shige banWaki dan ta Waura alwalar la'asar da akayi tana barci, koda ta fito ta daWe tanajin bugun ?ofar Nasir da kuma kiran sunanta da yakeyi amma tayi masa banza kamar bataji ba.

*Nasir*

Cikin hucin zafi ya jiyo ya kafe Rashida da ido, itama kallon sa take irin kallon Allah zai sakamin Win nan, bai saurareta ba ya juya yabar falon duk da kiran sunan sa da takeyi, ?arshe ma sauka ?asa yayi ya Wauki motar sa yayi fitarsa.

Yana fita Rashida tayi wajen Wakin su Haliman ta fara bugawa da ?arfi tana kiran.

" Wallahi Maryam sai naga bayanki, ke baki isa ki haWa jiki da mijina na barki ki huta ba, na rantse da girman Allah sai ya sakeki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login