Showing 162001 words to 165000 words out of 175193 words

Chapter 55 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

542

nan tsananin dafin gubar dataci ne yasa duka jijiyoyin jinin jikinta suka tsittsinke hakan ne yayi sanadiyar mutuwar ta.

"Yiffff. Sukaji faWuwar Maryam ?asa domin jin labarin mutuwar kulu, da gudu suka nufi kanta anan likitan yagane suma tayi a take ya shiga bata taimakon gaggawa.

*KUTSE*

*PAGE 70*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*ya zulai*

Kallon gawar kulu tayi wacce suka gama wanketa suka haWa ta cikin likkafani tana hawaye tace

"Tunda na haifeki baki taSa saSamin ba hauwa, kece ?ar da kikafi soyuwa a raina gashi tun ba'a je ko ina ba Allah ya Wauke mini ke alhalin naci burin ganin yaranki, Allah sarki rayuwar duniya kana naka Allah na nashi, ha?i?a kin dace kuma ke ?an matan Aljanna ce kulu, Allah ya ji?anki yayi miki Rahama, biyayyar da kikayi min Allah ya sanya ta zama rahama a gareki hauwa, na yafe miki, ta ?arasa tana fashewa da kuka.

Ri?eta umma tayi tana girgiza kai tana dainayi mata kuka, a san nan ne Maryam tayi ?arfin halin kallon gawar kulu dake cikin makara tana ganin abin kamar a mafarki ne idan tatashi zataga ba haka ba, dafa kafaWarta umma tayi tace "ki daure kiyi mata addu'a Maryam, sai a San nan Maryam ta matsa gabda kanta tare da dafe kan nata da hannun dama tace.

"Allah ya ji?anki kulu, ha?i?a kinyi shahada wacce ba kowa Allah yabawa, sai ta ?ara sautin kukanta tana cewa "me kika yiwa wani? Me kika tsarewa wani? Me yasa za'a rabaki da rayuwar ki tun kina ?an?anuwar ki, wanene mai alhakin baki guba kikaci kulu? Me yasa za'a kashe min ke? Ta ?arasa tana kafa kanta a jikin gawar kulun tana kuka, gaba Waya Wakin jikin sune yayi sanyi suka shiga far gaba a sanda sukaji maryam na faWin wai guba aka ciyar da kulu, su basuji ba sai yanzu? Suna cikin wan nan kiWimar maza suka shigo domin tafiya da kulu gidanta na gaskiya bayan an mata salla.

Sai bayan an kai kulu an dawo mutane sun fara raguwa san nan ya zulai ta kalli Maryam tace "kamar Wazu naji kina zancen guba aka bawa kulu taci ta mutu ko? Cikin tashin hankali Maryam ta kalli ya zulai dan tun sanda ta farfaWo a asibiti Nasir ya gargaWe ta kuma ya ro?eta akan dan girman Allah ta rufe zancen nan karta sanarwa da kowa har a gama zaman makokin kulu san nan yayi bincike, ita batasan sanda ta faWaba dan bata cikin tunanin ta, dan haka sai kawai Maryam ta jijjiga kai tace "a'a ya zulai? A ina kikaji kuma? Cikin kallon tuhuma ya zulai tace "kece kika faWa Wazu Maryam, nasan ai kina da hankali bazaki faWi maganar daba dai-dai ba.

Jijjiga kai Maryam ta sakeyi tace "ba haka bane ya zulai gaskiya bansan yadda akayi na faWi hakan ba, hannunta Jamila ta rike tana kukan rashin kulu tace "dan Allah aunty Maryam kifaWa mana Abinda ya samu kulu, munsan dai lafiyar ta ?alau sai kawai zancen mutuwa mukaji, dan haka ko ya zulai ne ita kaWai kifaWawa gaskiya. ?ara jijjiga kai Maryam tayi tace "Jamila ba Abinda kuke tunani bane, karki manta mutum ma yana mutuwa daga kwanciyar barci, toshi kice menene? Ai ita mutuwa tana zuwa ne koda ciwo ko babu ciwo, dan haka don girman Allah ku barni da Abinda yake damuna, ta faWa tana tashi tabar wajen tare da shigewa Wakinta ta kwanta, koda ta kwanta Win ma kukan ta cigaba dayi mai sosa zuciya, tunani da hasashen kulu kawai Maryam keyi, me yasa za'a kashe mata ita? Wallahi ko kaffara bazata yiba tasan mutuwar kulu tanada ala?a da Rashida ne, dan haka batajin zata iya barin wan nan lamarin.

*Rashida*

Tana kwance akan kujera duk Abin duniya yabi ya dameta, ta rasa inda zata saka kanta taji sanyi da wan nan lamarin, kuma Abinda yake ?ara bata mamaki ganin yadda zita take sabgogin ta kamar yadda ta saba, babu alhini ko kaWan akan fuskarta bare ayi tunanin damuwa a cikin zuciyar ta, ?arewa ma waya ta Wauka tana chart Winta harda kyakyata dariya, juyawa tayi da sauri tanajin kamar motsi na tawowa Wakinta, jin babu kowa yasa ta lumshe idanuwa domin fargaban komai takeji, tun Wazu ta kasa fita wajen zaman makokin, domin ji takeyi kamar za'a fuskanci ita ce ta kashe kulu shiyasa takasa fita, kallon zita ta kumayi sai ta saki Soyayyen ajiyar zuciya tatashi tayi Wakinta danta runtsa saboda damuwa tayi mata yawa. Tana shiga Wakin ta kwanta tana kallon inda kulu ta faWi tana Aljanu Wazu, runtse idonta tayi tanajin gabanta na tsananin faWuwar dabai taSayi ba, da kyar ta samu wani wahalallan barci ya kwasheta.

*Kulu*

Sha?e wuyan Rashida tayi hawaye masu tururi suna tsiyaya daga idonta bakinta kuma wani ruwa mai kauri yana zuba tana cewa

"Me nayi miki zaki kasheni? Meyasa zaki sakani a cikin jahilcin ki? Kin rabani da rayuwa ta batare danayi miki laifin komai ba? Kin cuceni kin zalunce ni Rashida. Sai kuma ta saka Waya hannun nata ta tsokane idanun Rashida wanda sukayi kwala-kwala dasu, runtse idon Rashida tayi cikin azaba tana niyar yin magana amma takasa, dariya kulu ta kyalkyale dashi tace "kin shiga uku kin lalace Rashida, da yau rayuwar ki ta burkice kamar yadda kike gudu, daga yau ?alu bale da tashin hankali marar misaltuwa zai fara a gareki tunda kika rabani da rayuwa ta, kulu na gama faWar haka ta saki Rashida tare da dun?ule hannu ta buga mata a saitin zuciya san nan ta Sace, Sacewar kulu shine yayi dai-dai da tashin Rashida daga wan nan mummunan mafarkin tana kwalla ihuu mai sauti.

Da gudu ta sauko daga kan gadon Saboda ganin kamar ana buWe labulen Wakin nata, wani ihun ta ?ara kwalawa ganin an shigo Wakin, kunna fitilar da Nasir yayi shine yayi sular nutsuwar Rashida, jikinsa ta faWa tasaka wani ?a??arfan kuka tana faWin na shiga uku Nasir, baki shiga uku ba sai nan gaba Rashida, taji kamar muryar kulu na kururuwa a kunneta, ?ara shiga jikin Nasir tayi tana tsoro takeji don Allah su tafi Wakinsa.

Kwata kwata Nasir baya yanayin jin daWi ko kuma magana, dan haka sai kawai ya cireta daga jikinsa tare da ri?e hannunta suka shiga Wakin nasa ya rufo ?ofar, ban Waki ya wuce yayo alwala yazo yafara nafilar dare kamar yadda ya saba, daman ya tashi daga barci ne zaiyi alwalar ya jiyo ?arar Rashida shiyasa ya fito ya duba, dan haka koda ya tada sallar haka Rashida taita mutsu mutsu tana Wan firgita kaWan kamar wani abin na tsorata ta.

Sai da ya idar da raka'ar ?arshe ya kalleta yace "wai meke damunki ne ke? Hawaye ne suka zubo mata tana sunkuyar dakai tace "wallahi tsoron gidan nan nakeji baki Waya Nasir, ni ban saba ganin gawa ba, san nan banaso naji anyi mutuwa a kusa dani duk sai na shiga Wimuwa, haka da Abban mu ya rasu sai da nasha fama kafin na daina tsorata, kai Nasir ya gyaWa domin shi shaidane, saboda suna tare Abban nata ya rasu, san nan shima haka yasha fama da ita kafin ta nutsu ta dawo dai-dai, shiyasa koda ta faWi hakan bai musa mata ba saboda yasan gaskiya ne ta faWa, dan haka sai yace tatashi taje ta Wauro alwalar tayi salla zata daina jin tsoron, da kyar Rashida tatashi dan shima banWakin sai da ya rakata san nan ta samu tayi alwalar suka fito, sallar ma dakyar ta iya raka'a biyu san nan ta sulale a wajen ta kwanta dan ita bama zatace ga Abinda ta karanta a cikin sallar ba.

*Washegari*

A ranta takeji kamar taje ta samu ya zulai tayi musu gaisuwa dan tanajin tsoron a fara zarginta, dan haka da sassafe tatashi ta toya ?osai mai yawan gaske da kunu ta saka zita takai musu san nan daga baya tashiga bayan tayi wanka, a Warare ta zauna tana kallon yadda fuskar Maryam tayi ?ar fayau daga jiya zuwa yau, san nan ya zulai a zaune itama ta daka ta gumi tana kallon waje Waya, kai duk al-ummar falon ma suna cikin jimami da mutuwar kulu, gaisuwa tayi musu wasu suka amsa wasu kuma suka shareta, batasan meyasa ba kawai saita tsinci kanta da fashewa da kuka tana cewa

"Allah sarki kulu, Allah yagafarta miki, yarinyar tanamin biyayya kamar nice na haifeta shiyasa nake ?aunarta.

"Shi yasa ai kika kasa zuwa gurin rasuwar ta sai yau alhalin kina cikin gidan nan, Jamila ta faWa tana watsa mata kallon banza.

"Kuma tana dawowa daga Wakinta ko minti talatin ba'ayi ba tarasu ba, Maryam ta faWa itama tana maka mata harara.

Wani irin ?uuuuuu, zuuuuu, Rashida taji cikin ta yafara, kallon Maryam Win tayi tace "haba Maryam, wallahi ni bansan komai ba, me kike nufi ne? Da sauri zita ta zunguri ?afar Rashida don ganin tanason tayi Saran Satama, hakan yasa Rashida tayi saurin sauya kalaman ta tace "mutuwa ai ta Allah ce Maryam, kuma ko kulu na wajena ajalinta yazo zata faWi ta mutu, kuma wallahi Abinda yasa ban shigoba tunda akace kulu ta rasu na fara gudawa da zazzaSi, daman cen ni tsoron mutuwa da tsoron gawa nakeyi.

"Ai kuwa ki daina tsoron mutuwa Rashida, dan kema wataran mutuwar nan zakiyi tane, ya zulai ta faWa tana tashi daga wajen dan iskancin Rashida yafara cika mata ciki.

Mutuwa mai lasisi da tonon asiri ma kuwa, Maryam ta faWa tana ?ure Rashida da kallo, a wan nan ranar Rashida kasa sukuni tayi dan duk a tunaninta a sirinta ya tonu wajen iyayen kulu, dan a lokacin dasu Maryam suke yada mata maganar nan jitake wani futsari yafara kufce mata yana tsiyayo mata kaWan kaWan, haka koda ta koma wajen ta safa da marwa ta shigayi dan dole tanason ganin boka kafin asirinta yakai da gama tonuwa, wani abin takaicin ma tana zaune wajen la'asar sai ga yara sun kawo mata kular data zuba ?osai da kunun a ciki sukace wai gashi an gode, jitake idan ta buWe kular zataga komai ya ?are, amma ga mamakinta sai ga uban tulin ?osai da kuma lodin kunun datayi a cikin kular da alamu ma ko taSawa ba'ayi ba, abin ya sosa mata rai sai kawai tafara zubar da hawaye.

*Zita*

Kallon Rashida tayi tana kallon ta tace "wai ke aunty Rashida bazaki bar wan nan kukan haka ba? Nifa kukan naki yafara isata, ki iya tunawa fa duk mai rai mamaci ne, kuma naga ko Abban kima ya rasu amma kikayi ha?uri, dan Allah kiyi ha?uri komai ya wuce, kulun nan fa naga ba ?ar uwarku bace, babu Abinda ya haWaki da ita, to dai koni na mutu ina ganin iya Abinda zakiyi kenan.

Girgiza kai Rashida tayi tace "bazaki gane ba zita, kisan kaifa nayi, wallahi ina cikin masifa zita, jiya kusan kwana nayi ina mafarkin kulu zata kasheni, sai ta kamo hannun zita tace "zita dan Allah kitashi kije wajen bokan nan ya taimaka min kafin kwakwalwata tafara samun matsala.

Murmushi zita tayi tace "wallahi ya Rashida yanzu idan na fita sai afara munafurci ace mutuwar bata damemu ba, amma gaskiya a barshi zuwa a kwana biyu, idan yaso sai mu Wauki mataki, da wan nan maganar zita ta kwantarwa da Rashida hankali harta Wan samu sau?in Abinda takeji.

Yau akayi sadakar ukun kulu, kuma tun washegarin rasuwar da Rashida ta shiga bata ?ara shigaba sai yau ranar uku, shima tana shiga ta fita dan bata ganewa irin kallon da Maryam take mata ba.

Hawaye kawai Maryam ke saki babu ?a??autawa tana cewa " Allah yajikanki kulu, wallahi mutuwar kulu ta tsaye min a raina samira, nikam inajin harna mutu mutuwar kulu bazata gushe a cikin zuciyar taba.

Hannun ta samira ta ri?e tace "ki kwantar da hankalin ki kiyi ha?uri Maryam, mutuwa wajibi ce ga kowanne bawa kuma kowa ita yake jira Maryam, ina Tauhidin kine? Matse hannun ta Maryam tayi tace "samira ba ba?in cikin mutuwar kulu ke damuna ba, babban Abinda ke damun zuciya ta shine yadda Rashida ta ciyar da kulu guba har tayi sanadiyar mutuwar ta, cikin kiWima samira ta zame hannunta daga na na maryam tana dafe ?irji tace "kina nufin Rashida ce ta sakawa kulu guba taci ta mutu?

GyaWa kai Maryam tayi tace "tabbas haka ne samira, saboda tun safe kulu take gurin Rashida take mata bauta, daga nan Maryam ta kwashe labarin komai har dawowar da kulu tayi wajenta tana kwanciya ta rasu, daga Maryam har samira kuka kawai suke yi kamar zasu ?arar da hawayen su, ya Nasir yace karna faWawa kowa wan nan maganar samira, to maganar zungurar min zuciya ta take shiyasa nakejin idan ban furtawa wani ba zan iya samun matsalar zuciya, shiyasa na faWa miki.

"Harda nima,naji komai Maryam, ya zulai ta shigo Wakin tana matsar hawaye, ?asa ta sulale tana cewa "haba Maryam, meyasa bazaki faWan gaskiya ba? Menene yasa zaki Soye min don Allah? Daman Rashida ce ta sakawa kulu guba taci amma kika kasa sanar dani gaskiyar lamari? Umma wacce ta shigo yanzu ce ta dafa kafaWar ya zalai tace "uhummm, uhummm zulai, bazamu tabbatar da hakan ba saboda bamu da wata tsayayyen shaida, kuma koda kotu mukaje bamu da hujjar da zamu kawo, kinga kenan idan bamu iya kama Sarawo ba sai Sarawo yakama mu, dan haka mubi komai a sannu dan tsaf idan muka zafafa babu shaida Shari'a zata iya kamamu.

Cikin kuka Jamila wacce ya zulai ta gama faWa mata lamarin tace "ai umma babu bu?atar wata shaida dan wallahi ko kaffara bazan yiba Rashida ce tabawa kulu guba taci, kuma tabbas akwai Abinda take Soyewa, dan haka na rantse da Allah babu ma wani hukuma da zamu kaita da kanmu zamu kasheta dan wallahi Rashida bazata ?ara ko kwana Waya a cikin duniyar nan ba, ta faWa ta tashi cikin zafi tayi hanyar waje tana kwalawa wasu matasa kira wanda sukazo musu ta'aziiya daga rogo.

*KUTSE*

*PAGE 71*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Tana kwance kawai sai jitayi an rufeta da duka ta ko ina, a furgice tatashi tana sosa jikinta domin dukan ba?aramin shiga jikinta yai ba, ihu take tana tumami akan a taimaka mata za'a kasheta, babu wanda yabi ta kanta sai ma Jamila dake ?ara an giza waWan da suke dukanta tana

"Ku daketa dan ubanta, kuci mana uwarta, yau so nake itama sai ta ba?unci lahira, dan billahillazi jinin kulu bazai tafi a banza ba, idan ta saba cin zalin mutane to wallahi daga wan nan ta ?are dan bata da rayuwar da zata aikata sharri, Shegiya tsinanniya.

Ihu Rashida ta dunga zabgawa tana kuka tana cewa "wallahi bansan komai ba, dan girman Allah kuyi ha?uri, zargine kukeyi min me kulu tayi min dazan kasheta? Ai bada ita nake faWa ba, kuma ko Maryam da muke faWan da ita bazan iya kasheta ba, hannu wani a cikin samarin ya dun?ule ya dokawa Rashida a baki wanda sai da yayi sanadiyar Sallewar hakwaranta guda biyu, take kuwa bakinta ya haye yayi suntum kamar an jawo shi, saboda a zaba ma Rashida kasa cigaba tayi da kukan sai jijjiga kai domin ita tasan gashin da take karSa.

Ganin zasu kasheta ne yasa zita dake cen wani ya ri?eta tana kuka tace "me tayi muku ne? Dalla ku daina dukanta, idan ba haka ba wallahi duk kanku sai kunyi nadamar rayuwar ku, wata irin mahan gurSa wanda ke ri?e da ita ya sakar mata,Duk da haka bata daddara ba ta kuma kwala ihu ta gartsa masa cizo a hannunsa, ba ?aramin shigarsa cizon nan yayi ba saboda haka yasa ya jiyo da ita ya zabga mata mari mai bala'in zafi, san nan ya daddage ya wullar da ita gefe, tana tashi faWuwa kuwa ta faWa kan Centre table nan da nan goshinta ya datse jini ya Salle, ?arar azaba zita ta saki kafin daga bisani ta sume.

Ita ma Rashida yadda azabar duka yayi mata yawa yasa ta suma a wajen, domin duka ne suke mata irin dukan gardawan nan sun samu Sarawon daya addabi rayuwar su.

*Maryam*

Bata san me Jamila zatayi ba, amma ganin tayi harabar gidan tana kwalawa samarin nan kira yasa ta dawo a gigice tana neman wayarta domin ta kira Nasir ta sanar dashi Abinda yake shirin faruwa, bataga wayar ba shiyasa ta bazama nemanta, ita kuwa samira tana kallon yadda samarin suka tashi a hautsine suna huci saboda Jamila ta gaya musu bayanin Abinda ya faru, tana gani suka Wunguma suka shiga sashen Rashida, tasan sarai umma zata iya zuwa tace zata hanasu Waukar matakin gaggawa, dan haka sai tayi sauri ta zare mukullin falon Maryam ta fito tsakar gidan nata, mukullin ta kuma zurawa ta rufe falon ta baya san nan ta saka sakata.

Duk irin ihun dasu Rashida sukeyi suna jiyowa amma saboda samira ta kulle falon yasa babu wanda ya kawo musu Wauki, kuma sai dukan ?ofar Maryam take tana kuka akan samira tabata mukullin kota buWe su amma taki, sai da samira taga anwa su Rashida lilis sun fita hayyacin su san nan ta buWe ?ofar Maryam tana zare idanu, cikin Sacin rai umma ta Waga hannu ta zabgawa samira mari tana huci tana cewa

"Baki da hankali ne samira? Kinsan Abinda kikayi kuwa? Idan suka kashe su fa? Samira bataji zafin marin a ranta ba duk da tajisa a fatarta, dan ranta fess saboda su Rashida sun fara WanWana azabar da Allah yatadanar musu tun a duniya, ?asa tayi da kai tana murmushi a ranta tace "umma kiyi ha?uri, amma ita ma ai kisan kan tayi, kuma ai rama mugunta ga mugu ibada ne umma.

Hararar ta umma tayi tana Wan tureta tace "matsa ki bani waje kona sassaSa miki, shashashar banza kawai, umma na fara tafiya sai gasu Jamila sun fito sunata huci ita da samarin nan, katsaham kuma sai ga Nasir ya shigo gidan cikin sauri da sassarfa shida baban kulu, kallon tuhuma ya tsaya yana musu sai kuma ya kalli jikin samarin nan yaga duk jini ya Sata su, a hanzarce ya nufo wajen su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login