Showing 33001 words to 36000 words out of 175193 words

Chapter 12 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

558

ya cigaba da tuk'in sa.

*Sauda*

"Kanta tad'an lek'o gaban motar tace

"Mama wacece ballagazar? Kuma wace cin amanar?

Kamar an zuguri Rashida sai ta juyo, daman mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin a waki, sai kuwa cewa tayi.

"Maryam mana, aurenta Ashe.....

*Nasir*

"Cikin karaji da masifa ya danna harm da k'arfi tare da cin burki ya zubawa Rashida idanu, shifa gani yake kamar kanta yad'an tab'u a kwana biyun nan.

Dan haka kawai sai yaja kwafa tare da bud'e baki zai mata magana, da sauri Rashida ta datsi numfashin sa ta k'ara kallon sauda tana cewa

Kinaji sauda? Amanata ubanku yaci duk.....

Wata iriyar gigitacciyar tsawa Nasir ya dakawa Rashida yace

"Rashida, itama rashidan a hasale tace "Nasir

D'an yatsansa ya nuna mata cikin fad'a yace

"Kishiga taitayin ki dani Rashida, kisani zan d'auki kowanne rashin mutunci daga wajen ki akaina Amma baki isa na d'auki zubar min da mutuncin da kike da burin yi a idanun yarana ba, zan d'auki komai Amma banda zubar da mutunci, na fad'a miki.

Ba Rashida ba hattaya yaran tsayawa sukayi suna kallon Abban nasu domin kuwa tunda suke basu tab'a ganin yayi mata fad'a ba ko kuma ganin fushin sa haka a kanta.

*Rashida*

Cikin mamaki take kallon Nasir da yanayin sa, gaba d'aya ya canza idanunsa sunyi jawur da bala'i, wani gajeran murmushi itama Rashidan ta saki tace

"Ni, Nasir ni, yau nice kakewa tsawa da fad'a akan ka k'ara aure? Eh lallai Nasir, wato kasamu baki saboda hajja taci mutunci na a gabanka ko? Eh , lallai babu shakka, ai komai namiji yayi akan K'ara aure to ba laifin sa bane, nasan banga komai bama, to bara kaji, niba wulak'an tacciya bace haka bazan d'auki raini da wulakanci a wajenka ba.

*Nasir*

Wani irin b'acin raine yake tsokanar zuciyar sa, so yake ya sassokawa Rashida zagi Amma bazai iyaba saboda ba halinsa bane, to me zaiyi yaji sauk'i, yana wan nan tunanin yaji tafara masa wan nan banzayen magan ganun, dan haka cikin dak'ika da basufi biyu ba yataka wani uban burki da sai da suka kusa wuntsulawa san nan yajiyo a fusace yace.

"Fita daga motar nan Rashida, wani kallo Rashida ta watsa masa tace "nafita kuma?

Daga kai Nasir yayi yace fita, kifita nace, ya k'arasa yana mai bud'e mata murfin mota yakuma nuna mata waje yace fita.

"A hasale Rashida ta janyo jakarta tafito daga motar tare da kama murfin motar ta bugashi da k'arfi kamar zai karye, Nasir bai damu da Abinda tayi ba yaja motarsa zuciyar sa na tuk'uk'in bak'in ciki yafara shara gudu.

Yana wucewa Rashida ta tsugunna a wajen ta saka kuka mai cin rai tare da tunanin wulak'ancin da Nasir yayi mata, ita zai sauke a hanya? Kamar ita a gaban mutane yaci mutuncin ta, eh lallai Maryam tagama da Nasir tunda har yafara nuna mata iya karta, sai data gama kukanta san nan tatashi tafara tare napep domin ta hau ya kaita gidan, cikin sa'a kuwa bata wani dad'e tana nemaba sai gashi ta samu ta haye, tana hawa ta zaro wayarta ta dannawa yaya karimatu kira tanata kuka.

Yaya karimatu tana d'aukar wayar Rashida ta kuma fashewa da kuka har sai da mai d'an sahun ya juyo ya kalleta, cikin kukan take labarta mata Abinda Nasir yayi mata a mota kuma daga k'arshe yaci zarafinta ya juyeta a bakin titi yayi tafiyar sa.

Wani uban ashar da yaya karimatu ta lailayo ta watsawa Nasir tabbas da'a gabansa ne duk da lusarancin sa dasai sun kwashi 'yan kallo, cikin bala'in dake a zalzalar yaya karimatu tace

"Dan ubanki yanzu ina kika nufa to? Cikin shasshekar kuka Rashida tace "cen gidan zan tafi mana.

Yanzu ke saboda baki da tunani shine yayi miki wan nan wulak'ancin kuma ki tafi gidan nashi? Nikam Rashida bansan yaushe kika lalace haka ba, dan haka nace kijuyo ki dawo gida tun ban zazzageki ba.

Cikin kuka Rashida take cewa. "bazan iya dawowa gidaba yaya karimatu, kinsan dai halin hajja, daman ai dan yaga taci min mutunci a gabansa ne shine yasamu kafar wulak'antani, yanzu kuma idan na koma kinsan hajja cazatai banji maganar taba, kuma wallahi tsaf zata saka yaya ya zanenim jikina.

Ajiyar zuciya yaya karimatu tayi tace "hunmm ai shikkenan, daman hajja ai ita take badamu agaban mazajen mu, badan haka ba wallahi babu d'a namijin daya isa ya nuna mana yatsa koba dan soba kodan k'arfin dukiyar da muke da ita.

Yanzu ki wuce kitafi gidan, zanzo gobe Insha Allah, idan yaso masan yadda zanu b'ullowa lamarin naki, dan wan nan lamarin da alama shegiyar yarinyar nan ba haka tabar Nasir ba, to kuwa bazamu zuba musu idanu suci karansu babu babbaka a kanki ba wallahi.

Da wan nan sukayi sallama Rashida najin zuciyar ta tad'an sanyaya.

*Nasir*

Sai daya kusa zuwa gida san ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nan ya takaita gudun, kukan da sauda ta cika masa kunne dashi ne yafara damunsa, dan haka sai yanemi waje ya tsaya yace ta dawo gaba.

"Kin dawowa tayi sai ta mak'e kafad'a tana cewa "nidai mamana.

Dan murmushi yayi tare da kamo hannunta yace "kiyi hak'uri kinji, itama maman naku zata tawo gida yanzu.

Sai ta janye hannunta daga rik'on daya yimata tace "ni ban yarda ba, ai korarta kayi daga motar kace tafita tabaka waje.

"Kai Nasir yad'an juyar yana kallon Halima wacce tayi shiru kanta a k'asa kamar bata cikin motar, itama hannunta ya rik'o yace

"Halima, dagowa tayi ta kallesa da idanunta wanda sukayi jage jage da hawaye, a kid'ime Nasir yace "kuka kikeyi Halima?

Jijjiga kai Halima tayi tana cewa. "kayi hak'uri Abba.

Murmushi yayi dan ya sanyaya mata zuciya sai yace "nayi hak'uri Halima, me kukeso na siyo muku?

Jijjiga kai Halima tayi tace "babu komai Abba, muje gida dai ka huta naga kamar ka gaji, kallon yarinyar yayi sosai yana yaba hankalin ta da kuma hangen nesanta kamar wata babbar mace, shi sai yaga ma nan gaba kamar Haliman sai tafi Rashidan hankali, sai kawai yayi dariya yanajin nishad'i na mamaye b'acin ran nasa.

Tada motar yayi yad'an yi tafiya kad'an, a wani super market ya tsaya tare dacewa su fito, da gudu sauda tafito saboda tasan duk ranar da sukaje wanjen bakinsu da kunnensu kusan tsinkewa sukeyi saboda tauna abin dad'i.

Kallon sauda Nasir yayi yana jajanta k'uruciyar ta yana kuma ganin suffofin halayen Rashida a tare da yarinyar, girgiza kai yayi yace

"Kama iri d'aya, ya Allah ka sab'a halayen sauda da kuma Rashida.

Ita kuwa halima a sab'ule tafito kanta a k'asa tana tunanin mamansu data b'atawa Abban su rai yabarota a hanya.

"Siyayya sosai Nasir yayiwa yaran, suna fitowa kuma ya biya dasu yahuza suya sukayi takeaway san nan suka wuce gida.

*Rashida*

"Galala take kallon yadda suke cikin nishad'i kamar babu Abinda yafaru, shi kansa Nasir d'in popcorn yakeci yana danna waya dan data shigo falon kallo d'aya yayi mata ya d'auke Kai.

Abinda ya buga mata kwakwalwa kenan, ita? Ita Nasir zaiwa laifi san nan ta shigo waje ya kalleta ya shareta? Hnmmm, wasu hawaye taji suna shirin zubo mata tayi saurin mayarwa tana kallon yadda sukayi kaca kaca da falon, tunda ta shigo takejin kamshin kaza, Amma ga mamakinta data shiga kichen ta bud'e pridge sai bataga ko leda ba bare ta karda, kwafa tayi ta juya ta shige d'akinta tare da fad'awa kan gado ta saka sabon kuka.

Ita Nasir zai wulak'anta? Ta shigo gidan Amma ya d'auke kai daga kallonta saboda yana chatting da Maryam? Babban bala'in nan, wa billahillazi sai Maryam ta d'and'ana k'udarta a hannunta, zata dawo gidan, Allah yakaimu gobe yaya karimatu tazo su san abinyi, Amma ta rantse da girman Allah ko zatayi yawo tsirara wallahi tallahi sai taga bayan Maryam a wajen mijinta, da wan nan tunanin barci yayi a won gaba da ita dan ko sallar isha'i bata samu damar yiba.

*Nasir*

Yana zaune yana tunani, yagaji, yagaji da Abinda Rashida take masa, tunda yake a rayuwar sa bai tab'a yimata wani laifi ba, akan me dan yayi aure zatabi ta d'aga masa hankali, ita bata huta ba, shima bata barshi ya huta ba tanata hauka, yabarta tagama kishin nata ta dawo su dai-dai ta amma abu yaci tura, duk hanyar dazai bi wajen kwantar mata da hankali tak'i bashi dama, to wai me takeso yayi mata ne? Ko kuwa dan taga tanacin zarafinsa da kuma wulak'anta shi sai yabata lasisin cewar baisan Abinda yakeba.

Toya gaji, yagaji dan yaga abin nata babu tunani aciki, to banda rashin tunani taya za'ayi suna abu su biyu tafara saka 'ya'yansa a ciki? Zai iya d'aukar komai Amma banda gurb'ata masa tarbiyyar 'ya'ya, dan haka dolene ya zage yayi hab'b'asa ya nunawa Rashida ba rashin sanin ciwon kai bane yasa yazama solob'iyo kawai duk a cikin babin kyautatawa ne, dan haka wallahi ya k'uduri aniyar sai Rashida tazo da kanta ta nemi sulhu dashi.

Shiyasa koda yaga ta shige d'akinta kota kanta baibi ba ya raka yaran d'akin su tare da musu addu'a shima ya shige nashi d'akin.

"Juyi kawai ya dungayi ya kasa barci saboda yadda tunanin Maryam ya hanashi sakat, tunanin yadda ya dunga wulak'anta ta akan Rashida yake Amma duk da haka Rashidan bata ganiba, dan haka sai ya rarumo wayarsa tare da nemo number ta dan ya kirata, duk yadda yaso wayar tashiga tak'i shiga daga baya ma ya gane ashe blocking d'insa tayi, yatsa ya ciza yafara tunanin ya zamar masa dole yaje daura nan da kwana biyu ya dawo da matarsa.

*Bayan kwana biyu*

Zaman doya da manja aka shigayi tsakanin Rashida da kuma da Nasir, hattaya yaran nata bala'in haushin su takeji domin kuwa haushin Nasir datakeji ne ya shafesu, bata kulashi shima baya saurarenta, sai da takai ta kawo kullum da sassafe yake fita kafin ma tatashi daga barci, daman anyiwa yara hutu ba zaman jiran kaisu makaranta zai zaunaba, wan nan buris da lamarin nata da Nasir yayi shine ya kuma kid'ima ta ya fara gigita tunanin ta, ita kad'ai sai ta zauna taita kuka tanajin tausayin kanta yana kuma rufeta, tabbas idan batatashi ta kwaci 'yancinta wajen Nasir ba tanaji tana gani zata zama shara bola a wajensa, tunda gashi tun maryam d'in batazo sun zauna ba yafara juya mata baya.

Wan nan dalilin yasa ta d'auki wayarta takira yaya karimatu, yaya karimatu na d'agawa tafashe da kuka tace

" yaya baki zoba gashi bak'in cikin Nasir yana neman yayi ajalina.

Salati yaya karimatu tayi tace

"Wai bak'in cikin d'a namiji kika saka a ranki Rashida? To maza ki cigaba da saka bak'in cikin da namiji a ranki, kina nan kina takaicin sa sai dai kiji kin yanke jiki kin fad'i ko kuma ace kin kamu da hawan jini ko ciwon zuciya, kuma Abinda yasa kikaga banzo ba kwana biyun nan wallahi baban su anas ne bashida da lafiya, kwana biyu yanata fama da zazzab'i, dan ko fita ba yayi sai yau yafara fita office d'in, kuma yanzu nake zancen ki a raina nace bara na tab'a ki naji idan kina gidan na shigo.

*Nasir*

Kallon Ramadan yayi yace

"Ai inafad'a maka, ita kanta yanzu taga canji wajena, nasan abin yana nan yana bata mamaki, ina kallon fa yadda takemin kallon gefen ido idan ina zaune, ni kuwa bana nunawa ma nasan da zamanta saboda itace a k'asa na ita yakamata tayi min biyayya bawai ni nayi mata biyayya ba.

*Ramadan*

Cikin jin dad'i yake kallon Nasir yana cewa

" yo daman duk namijin daya bari aka rainashi a cikin gidan sa ai shine yaso, banda ma kabari Rashida taga wajen kwanan ka tayaya ma zaka dunga bari tana b'arin bama bamai a kanka? Ai wan nan matakin daka d'auka shine dai-dai, kuma kaga a wan nan tak'in zakayi k'ok'ari ka d'auko Maryam ka kawota cikin gidan ka kafa musu sharud'd'ai yadda zasu zauna lafiya, dan a wan nan lokacin daka fara dasawa Rashida shakkarka zakayi wan nan hab'b'asan, idan kuma kabari wan nan damar ta wuceka kai kasani, dan da dukkan alamun ka kafara karaya ko?

Jinjina kai Nasir yayi yana kallon hoton Rashida daya kamo tun d'azu a wayarsa yace

"Bazan b'oye makaba Ramadan, inason Rashida da k'aunarta kamar yadda take Sona da k'aunata, wallahi Ramadan Rashida tanamin biyayya san nan tana gudun fushina da dukkan abinda zai d'aga hankalina, Rashida tana kula dani sosai Ramadan, kawai na fuskaci canjin ta duk akan nayi mata kishiya ne, kuma kai kanka kasan Rashida wacece akan kishi, ta tsani kishiya, kai ko sunanta batason taji ana fad'i, kuma ba kishiya kad'ai ba, wallahi tallahi Rashida duk wanda zai rab'eni baso takeyi ba, musamman ace matane hnmmm.

Dariya Ramadan yayi yace

"To ai sai tayi hak'uri tunda Allah ya halatta maka ka k'ara, kuma gashi ka dab'bak'a sunna ka k'ara d'in, dan haka sai ta d'auki na annabawa, kai barafa kaji in fad'a maka, akwai mata masu tsananin kishi sama da Rashida, kuma haka akayi musu kishiyar sukayi hak'uri suka zauna lafiya, itafa tsabar sakene da kuma shagwab'a ta da kayi shiyasa baka ganin laifinta.

Ai kawai malam kaje ka d'auko Maryam ka kawota gidanka ta cigaba da karb'ar bak'in ka da mutunci, tunda daman Rashida bawai jituwace a tsakanin ta da iyayenka ba, dan da kanka ka gayan muddin sukazo gidan sai ta ta magan ganu da kuma cewar an mata kutse.

Haka dai sukai ta tattaunawa har lokacin tafiya kasuwar sa yayi ya zugi motarsa ya wuce.

*Yaya karimatu*

Tab'e baki tayi tace

"Kinsan dai mijina sai da ya auri mata biyar hardani ta shida, kuma sanin kanki ne ban tab'a barin koda mace d'aya tayi cikakken wata biyar ba yake korata gidan su, kuma abin sha'awar ma shine, tunda yake auren sa basu tab'a gurb'ata min 'ya'yana da jinin 'yan ubaba, duk wacce tazo haka take tafiya bata haihu ba, to ke duk bakiyi mamaki ba?

D'aga kai Rashida tayi tace

"Gaskiya kam da mamaki yaya, duk da nasan hanyar da kike bi ki koresun, kuma naga dai babu irin mallakar da banyiwa Nasir ba, Amma daga karshe gashi komai ya warware daga zuwan wan nan yarinyar.

Dariya yaya karimatu tayi tace

" To badole ya warware ba, taya zai zauna tunda ya kawo miki wacce harbinta ya haura naki zafi, to bara kiji, ai ba dan ya warware wai zama zakiyi ba, tashi zakiyi kicigaba da mik'a sadaka ana taimakon ki, kuma kinsan taimako baya aiki har sai kin had'a da kissa da kisisina ko?

Yanzu wattsakewa nakeso yi kitashi ki tallafi mijinki, saboda kina wan nan shashancin a haka shi kuma hankalin sa zai karkata kan waccen yarinyar, dan haka yanzu Abinda nakeso dake shine

"Kitashi kiyi masa girki mai dad'i, ai kinsan Abinda yafiso a cikin abinci, ki dafa masa kiyi wanka ki goga kwalliyar ki yadda kika saba, yana dawowa ki rakashi yayi wanka, daya fito gabatar masa da abinci, daga nana kuma ki d'ora da bashi hak'uri da kuma nuna amincewar ki, sauran aikin kuma kibarmin ni nasan yadda zanyi dasu dukan su.

Ajiyar zuciya Rashida tayi tanajin d'an kunci kad'an a ranta, danfa ita indai akan kishiya ne gaskiyar magana bazata iya wani makirci ba, saboda idan tanason abu kawai tanaso idan kuma tanak'i to tabbas bazata tab'a son saba.

*****

*Maryam*

Duk da tana cikin kewa da rad'ad'in mutuwar baban su Amma tanajin dad'in zama da Samira.

Tun jiya ta dawo domin Alhamdulillahi an samu nasarar yiwa ummanta aiki kuma jikinta yayi sauk'i sosai, hakan yasa koda aka sallamesu gidan ya mansur aka wuce da ita, matar ya mansur macace mai kirkin gaske, tabbas yasan zata iya kula da mahaifiyar sa shiyasa yakai mata gidanta, kuma a bayyane yake zata iya d'in, ganin haka yasa ya mansur yace Maryam ta koma gidanta tunda an rigada anyi sadakar bakwai, kuma koda Nasir yazo bata barima sun had'u ba balle yasaka ran zata bishi, haka jiki babu kwari ya juya yadawo kano da tunanin Abinda Maryam d'in take nufi kala kala a ransa.

Ita kuma washe gari da sassafe tatawo kano, amma maimakon ta dawo gidan Nasir kai tsaye sai tayi gidan samira, ba k'aramin dad'i samira tajiba da Maryam d'in tabi shawarar ta tatawo gidantan har sai Nasir ya nemeta.

*Nasir*

Wayar hannunsa ya cigaba da juyawa yana tunanin inda Maryam d'in taje bayan tatawo, tun wajen azahar sukayi waya da Mansur kuma ya sanar dashi cewar tatawo tun safe, babban tashin hankalin sa kuma still yanata kiran wayar tata har yau bata bud'e shi akan blocking d'in sa datayi ba.

Yana zaune a kasuwa yana wasik'ar jaki sai kawai zuciyar sa ta raya masa wani abu, murmushi yayi ya mik'e da sauri tare da zarar motarsa ya durfafarwa gidan samira.

*KUTSE*

*PAGE 16*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Nasir*

Bugun k'ofar gidan samira yake babu k'ak'k'autawa tamkar wani yaro, ya buga yafi sau a K'irga Amma ba'a bud'e ba, hakan yasa ya nemi waje a cikin motar sa ya zauna yana mamakin irin bugun da yayiwa gidan Amma ba'a bud'e ba.

Toko basa nan? Wata zuciyar ta tambayeshi, sai ya kaWa kai yace tabbas basa nan, Amma kuma ina zasuje?

Bashi damai bashi amsa shiyasa ya zubawa k'ofar gidan idanu yana tunanin ta inda zaiga b'ullowar su, ilai kuwa yana zaune a motar yaga mai napep ya sauke su, me napep d'in na barin wurin yayi saurin fitowa yana musu magana ganin samira ta bud'e gidan zasu shiga.

*Maryam*

Ko a suma take taji muryar Nasir zata gane, hakan yasa dataji maganar sa kawai ta tsaya cak Amma bata jiyo ba, ganin Samira ta fasa bud'e gidan ta juya tana fad'in.

"A'a ya Nasir kaine da yamman nan?

Shi kuma Nasir sai cewa yayi

"Kyace haka mana tunda kin d'aukar min mata kun tafi yawo bada izinina ba.

Da sauri Maryam ta cire hannun samira daga jikin mukullin ta saka hannunta ta bud'e gidan tare da fad'awa ciki ta banke.

*Samira*

"Da sauri ta tare gate d'in Amma kafin kace mai ya datse dan bata kawo hannu da wuri ba, sai kawai ta saka hannunta ta fara bugawa tunda tasan Maryam d'in na tsakar gidan batakai ga shiga cikiba, ganin Maryam d'in tak'i bud'ewa yasa ta zaro wayarta daga cikin jakarta ta danna mata kira.

*Maryam*

Tana jikin gate d'in tanajin yadda Samira ke bugawa Amma bata bud'e ba, bazata bud'e ba tunda dai tasan idan ta bud'e Nasir sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login