Showing 117001 words to 120000 words out of 175193 words

Chapter 40 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

540

taimako daga ko ina a wajen mutanen kirki, nayi murna kuma ina maraba da taimakon ki, munaso kam, Allah yabiyaki da gidan aljanna mungode sosai.

Dubu Wari hajja ta ajiyewa umma tana maiyi mata al?awarin Insha Allah gobe zatazo da wani malami wanda ya la?anci ciwuka daban daban, kuma yana ganin Maryam zai fassara abinda ke damunta kuma da yar dar Allah zai bata maganin samun warakar ta.

Da wan nan suka rabu su umma sunata yabon kyakkyawan halinta wanda yasha banban dana ?arta, ya zulai tace

"To umma ai ba itace ta haifeta ba, dan da ita ce ta haifeta ko kaWanne sai tayo halinta, dan barewa bazatayi gudu Wanta yayi rarrafe ba, inajin dai duk wan nan ba?in halin na Rashida da wula?anta mutane a gurin mahaifiyar ta tagada dan kinsan jini shu'umin abune.

Haka dai sukaita tattaunawa har aka kirawo sallar magariba san nan suka tashi.

Duk da Maryam ba iya motsin kirki take da kuma magana ba amma hakan baya hana umma Waura mata alwala a duk sanda lokacin salla yayi, koda ya zulai take tambayar umma dalilin haka sai tace mata.

Ai gwara a dunga mata alwalar zulai dan ya kasance ko da yaushe da tsarkinta a jikinta kota samu sau?in wasu al-a muran.

*Washegari*

Misalin ?arfe goma na safe hajja ta shigo gidan tare da nemawa malam izinin shigowa a wajen su umma, kansu suka lulluSe san nan malam ya shigo da sallama Wauke a bakinsa.

Yana kallon Maryam yace

"Subhan, kafin ya ?arasa faWar Abinda zai faWa nan take wata iska wacce shi kaWai yake ganinta ta taso daga jikin Maryam kamar guguwa tayo kansa tare da bugarsa ta watsa shi baya har sai daya faWi hular sa ta cire.

Tashi sukayi baki Wayan su sake da baki suna kallon malam da Maryam wacce ta kwalalo idanuwa waje tana hawayen jini


Kuyi ha?uri da wan nan wallahi ciwon ido nake da kyar na iya typing Win nan, ?urjine mai azabar raWaWi ya fito min a cikin fatar idona shine idon ya kumbura yaketa ruwa>?y?.

*KUTSE*

*PAGE 50*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Malam*

Wata irin alkafura yayi tare da mi?ewa yayi bissimillah ya isa gaban Maryam gadan gadan wacce take gurnani da hawayen jini, kwala kwalan idanunta data zaro ta zuba masa tafa jijjiga kamar ana kaWata, shi kuwa malam bissimillah yayi tare dayin wani tofi a hannunsa san nan ya dun?ule hannun ya bugawa Maryam aka Wa ?arfin gaske, cak jijjigar ta tsaya sai kuma Maryam tayi wani kukan kura ta zabura tare da mi?ewa tsaye ta dam?i wuyan Malam ta sha?e masa wuya.

Duk da haka malam bai tsaya dayin addu'ar da yakeyi da ?arfi ba yana tofawa Maryam duk da wujijjiga shi da takeyi tana hautsinashi tare da yi masa wani rikitaccen ihu aka.

Haka sukai ta kokawa da Maryam da malam a tsakar falon nan kamar zakuna, malam yana ?o?arin kada Maryam maryam tana ?o?arin kadashi haka sukai ta dan barwa.

Kuka umma take wiwi da addu'ar samun Lafiyar ?arta domin wan nan al-amarin nata daga gani iska ce mai ?arfi, banda haka yarinyar data ke kwance sai dai a kwantar ko a Wagata a jinginar itace nan tsaye kan ?afafunta suke kokawa da malam?

Shi kuwa malam cikin samun nasara da ?arfin addu'ar da yake kwararowa yaci galaba akan Maryam tare da Wagata sama ya dage ya bugata da ?asa, wata ?ara ta saki tare dayin lakwas a kwancen idanunta a rufe.

Da gudu umma tatawo kanta tana mamakin irin bugawar da malam yayi wa Maryam wanda tana da ya?inin idan da ?arar kwana to tabbas Maryam zata iya yin shahada, tana kuka takai hannu zata ri?eta malam yayi saurin dakawa umma tsawa yana haki yace.

"Kada ki sake ki taSata, kibarta, ba Maryam bace wan nan shaiWanin dake jikinta ne, idan kuma kikayi kuskuren taSa shi to zai cutar dake ne zai kuma yi miki mummunar illa.

A tsorace umma ta Wauke hannunta tayi baya tana mai rungumar ya zulai wacce itama hawayen kukan da take ya?i tsayawa.

Hajja ce ta shiga lallashin su tana basu baki akan suyi ha?uri Insha Allah matsalar Maryam tazo ?arshe.

Ganin da sukayi malam ya tsugunna ya bada hankalin sa ga Maryam yasa suma suka zauna daga cen baya suna kallon ikon Allah da kuma yadda zasu ?are.

Addu'a malam kawai yake babu ?au?autawa yana tofawa Maryam har dai daya ga tafara motsi san nan daga bisani ta buWe idanunta wanda suka rine zuwa kalar jini.

"Tashi zaune, malam ya dakawa Maryam tsawa yana bata umarni.

Tashi tayi ta zauna tana zazzare jan idanunta tana kallonsa, sai kuma tafara aman jini mai cike da datti zare zare yana kwararowa akan ?irjinta, daga nan kuma sai ta kyalkyale da dariya.

Cikin fushi malam ya dakar mata goshi yace

"Wanene kai? Daga ina kake? Nace wanene ya turoka?

Shuru Maryam tayi batayi magana ba sai ma gimtse baki datai masa alamar bazatayi magana ba, wani haushin ne ya ?ara dugun zuma zuciyar malam take ya dam?i a gararta yafara matsawa yana addu'a, kwarara ihu Maryam ta hauyi tana yayi ha?uri zatayi magana , kyaleta malam yayi yace

"Toka magantu ina jinka.

Wani irin hargowar jaki ne ya karaWe falon wanda su hajja basajinsa sai shi malam wanda yafara waige waigen ganin daga inda kukan jakin yake fitowa, ai kamar jira aljanin jikin Maryam yakeyi take kuwa wani ba?in haya?i yafara sulalowa daga jikin Maryam ya fice tare da hayewa kan jakin suka ratsa bango suka fita.

Ajiyar zuciya malam yayi yana kallon Maryam wacce take a kwance magashiyan sai Wan mammotsawa da takeyi kaWan kaWan, sunanta malam yafara kira yana.

"Maryam, Maryam, maryam.

Shiru maryam babu amsa sai idanunta data Wan buWe ta kalleshi san nan ta mayar ta rufe.

Girgiza kai malam yayi yana kallon hajja, san nan ya tashi ya matsa baya ya zauna kan kujera yana haki da mai da numfashi yace.

"Ha?i?a wan nan yarinya tana cikin jarrabawa mai yawa, turen Sa?a?en Aljanu akayi mata masu wahalar sarrafuwa, amma Insha Allah zamu ci galaba a kansu koma nace munci da yar dar Allah, rabin iskar tata tafita yanzun nan tabar rabin a jikinta, amma itama rabin Insha Allah zamu fitar da ita da ikon Allah mai kowa da komai, saboda haka ku kwantar da hankalin ku komai yazo ?arshe kuma kuma kucigaba da addu'ar.

Kai umma ta gyaWa tana hawaye tana cewa.

"Wanene wanda ya Wauki alhakinki Maryam? Wanene wanda ya Wauki ha??inki alhalin nasan baki cutar dashi da komai ba? Ha?i?a Wan Adam yana rayuwa a duniya ne a tsakanin abu guda biyu wato masoyi da ma?iyi, bazance Maryam bata da ma?iya ba amma nasan batada abokin faWa, kuma nasan halin ?ata bata da mugunta ko mugun halin da zata cutar da wani, amma duk da haka ina godiya da Allah daya jarrabi maryam da wan nan lalurar, Nagode, na kuma gode Allah, Kuma ina fatan Allah yabaki lafiya mai inganci maryam .

Da Amin duka suka amsa san nan malam ya Wora da cewar.

Kiyi ha?uri Hajiya ciwo baya nufin gajiyawa, kuma shi sharri Wan aike ne inaso ki zubawa sarautar Allah idanu, kina zaune zakiga ikon Allah.

San nan inason in sanar daku cewar, a kwai wani magani dazan aiko mata dashi a dafa shi san nan a bata tasha kuma a dunga mata wanka dashi harna tsawon sati Waya, san nan akwai rubutu zaki ganshi shima a dunga bata tanasha ana shafa mata akanta, sai haya?i da za'a dunga turara mata safe yamma da dare, Insha Allah wan nan Sarin na aljanin zai gudu da kansa ba tare da an sani ba.

San nan maganar Nasir da hajja tayi min, sai ya dakata ya Wan saki murmushin takaici yace

"Allah dai kawai ya kyauta, Nasir yana raye, kuma yana nan lafiya, kiranye ne akayi masa shi mai zafi, wala Allah abokin gaba, ma?iyi, ko abokin kasuwanci, gashi nan dai komai na iya faruwa, Zamu fara jefa masa addu'a muma ta yadda wancen aikin zai karye ya waiwayi gida da ikon Allah, addu'a tana da ?arfi, kuma Alhamdulillahi indai mukayi muna dacewa Allah yana karSa.

Jijina kai hajja tayi tace

"Gaskiya ne malam, wato abin akwai abin Waure kai, amma dai koma menene muna fata kuma muna ro?on Allah daya bamu mafita.

Da Amin suka amsa kafin daga bisani malam da hajja su tashi domin tafiya, har ?ofar gida umma da ya zalai sukayi musu rakiya suna musu addu'ar sauka lafiya.

*****

Tun daga ranar da malam yazo sukayi tata Surza shida Maryam kuma ya aiko da maganin da yace aka fara ganin cigaba.

?arin daman Maryam yana aiki sosai dan har takan iya kar Sar abu kota motsa shi, matsalar dai rabin jikin nata ne har yau a mace yake baya motsi kuma kanta a karye yake baya iya tsayawa dai-dai, amma sun sanar da malam kuma ya shaida musu suyi ha?uri su jira komai zai tafi dai-dai ta samu lafiya Insha Allah.

Wajen ?an biyu ma suna nan sunyi kuSul-Sul duk da babu nonon uwa da madara ake musu amfani, ?iba suke sosai gashi yanzu har sun fara wasa da kuma iya zama, idan umma tana kallon su ji take kamar ta rungume su taita rufzar kukan ba?in cikin rabasu da uwar su da akayi tun ranar sunan haihuwar su, babu sha?uwa irin ta uwa daWa, babu nonon uwa a gangar jikinsu, babu kulawa da nuna soyayya ta uwa a gare su, ire-iren wan nan tunanin da umma take shiyake sakawa taji bazata iya yafewa duk wanda yake da hannu wajen kwantar da Maryam Saboda mugunta ba.

Suma su halima tuni Ramadan ya Waukesu ya maida su gurin hajja domin abar su umma suji da abu guda Waya, da boarding yayi niyar kaisu amma umma da ya zulai suka hana sukace Nasir bayason yaransa suyi boarding, da wan nan ya kwashe su ya kaisu gidan hajja sukaci gaba da karatun su na boko da islamiyya acen, da farko umma ma ?i tayi tace ya barsu ai Wa na kowa ne kuma da Wa da dukiya ba'a musu mugunta, kuma kada karatun su ya taSar Sare saboda yawan canza musu makaranta.

?an murmushi Ramadan yayi yace, kibarsu sutafi umma, acen ma zasu samu ilimin dan nasan halin kwarai na hajja, san nan koma menene yafaru ai uwarsu ce taja musu, dan haka wallahi Wawainiya tayi muku yawa bazan barsu ba umma.

*Bayan watanni takwas*

Ha?i?a addu'a bata faWuwa ?asa banza, san nan duk lamarin da aka fauwalawa Allah to tabbas zai isar maka akansa, haka ne yafaru a wajen Maryam.

Bayan doguwar rashin lafiya har ta tsawon watanni tara da tayi sai gashi a yau ranar juma'a, ranar juma'ar data cika al-ummar gidan Nasir da farin ciki wacce bazasu manta da ita ba har abada a tarihin rayuwar su.

Kiraye kirayen sallar asubahi ake tayi a masallatan unguwar wanda ya karaWe ko ina da ina yake amsa kuwwa a kunnen dukkan Musulmi wanda yakeson saduwa da Allah cikin salama kuma zuciyarsa ta cika da farin ciki, a wan nan lokacin kamar daga sama Maryam taji wani ?arfi mai ?arfi ya shiga jikinta ya zaburata ya kewaye dukkan sassan jikin ta.

"Ya Allahhhh.

Maryam ta faWa tare da hun?ura daga kwancen da take ta mi?e zaune tana sakin wata atishawa mai ?arfi da amon gaske, da sauri umma ta kunna fitila wanda daman tashi tayi taje bayi dan ta Waura alwalar sallar asubar.

Da sauri tayo kan Maryam tana kiranta tana Maryam, Maryam, menene?

Hannun umma Maryam ta kama a hankali tana sakin wata mi?ar gajiya tace a hankali

"Ummana? barcin nan da nayi ya sakamin ciwon jiki, ko ina na jikina ciwo yakemin.

Fusge hannunta umma tayi tana matsawa baya tare da zama ta rufe fuska ta fashe da kukan farin ciki.

Da sauri ya zulai ta fito daga Waki tana hamma tana umma lafiyyy...., bata ?arasa ba tayo kan Maryam da gudu tana innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, Maryam, ko bake bace? Maryam.

Kallon ta Maryam tayi tana murmushin ya?e saboda wani irin ciwo da kwankwatsa da jikinta kemata tace

"Ya zulai, ina kulu?

Hannu ya zulai ta Waga take nunawa Maryam Waki tana in ina tana cewa.

"Tatt,tatt,tat tana WaW Waki., sai kuma ta kwasa da gudu tana kulu, kulu, ke kulu, zo kiga Maryam tatashi, Maryam tatashi.

Zumbur kulu ta mi?e tana muttsike idanu tace

"Aunty tatashi kuma umma? Kodai mafarki kikeyi?.

Mafarkin uwaki, ya zulai ta faWa tana mata da ?uwa, itama kulu da gudu ta sakko daga gadon ganin ya zulai tafita da sassarfa tana

"Allah mai iko, Allah maji ro?an bawa, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Maryam.

Ita kuwa kulu kan Maryam ta faWa tana aunty, kece haka? Alhamdulillahi, sai kuma ta fashe da kuka tana

"Alhamdulillahi da baki mutu ba aunty, Allah nayi maka godiya.

Kallon su umma kawai Maryam keyi tana mamakin Abinda yasa suka kiWime kuma suka gigice da ganin tatashi daga barci, gaba Waya barcin datai na awa nawa ne? tasan ita dai ta kwanta da gajiyar sunan ?an biyunta gashi wai har asuba tayi, ita wallahi barcin ma bai isheta ba ga ciwon jikin daya saka mata.

Umma na Wagowa daga sujudush shukur Maryam tace

"Umma wai menene? Kunata abu bana fahimta, gashi kunata ?ara sakani cikin duhun kai, wai meke faruwa ne?

Hawaye umma ta share tace

"Karki damu Maryam, zakiji komai Insha Allah, yanzu muje na taimaka miki kiyi wanka tukunna kiji daWin jikinki.

Da to Maryam ta amsa tunda tasan daman da sassafe ya zulai take mata wankan jegon, shiyasa tatashi da kyar tana dafa bango tanajin kamar zata faWi sai da ya zulai ta kamata tana kiyi a hankali jikinki babu kwari Maryam.

Tafiya Maryam tafara tanajin jikinta sakayau kamar ba ita ba, ji take kamar iska zata yi wancakali da ita ta faWi, shiyasa ta ri?e bango sosai tana tafiya saboda karta faWin.

Bayan ta umma tabi a niyarta ta tari ruwan a water heater tayiwa Maryam wankan, ita kuma maryam tana shiga banWakin ta tsugunna da kyar domin tayi futsari, futsarin tayi tatashi.

Tana tashi idanunta suka kai kan madubin dake banWakin ta kalli kanta, da sauri tayi baya tana runtse ido dacewar

"A'uzubillahi minasshai Wanirrajim, sai ta kuma buWe ido ta kuma kallo, ji take gamo tayi ashe itace, shafa fuskarta tayi wacce ta jeme ta komaWe ta malkwaWe babu nama sai ?asusuwa rankwal rankwal.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, subhanallahi Maryam ta faWa cikin karaji tana fashewa da kuka tare dayin baya baya zata faWi umma tayi saurin tareta tana fashewa da kuka.

*KUTSE*

*PAGE 51*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Kuka kawai take babu ?a??autawa har tana shasshe?a da haWiyar zuciya, ga ?an biyun ta a kusa da ita wanda suka tasa suka fara girma har suna tafiya da gwaranci a gabanta, rungume su tayi tana ?ara sautin kukanta tana tunanin ita kam me zata cewa Rashida a duniya? wallahi ko zata iya yafe mata komai billahillazi ba zata iya yafe mata wan nan cin zarafin data yi mata ita da ?a?anta ba, akwai abu mafi ba?in ciki a wajen uwa wanda ya wuce a rabata da Wanta a yayin da yake tsumma a rabashi da nono da Wumin mahaifiyar sa yana jariri? Sai ta ?ara kwala ihu ta saki yaran tare da dun ?ule jikinta waje Waya tana kuka mai tsuma rai da zuciya.

Yaranta wanda suke tsumman goyo? Wanda ta kwanta tare da gajiyar sunan su a tattare da ita amma ace sune suka girma haka? Sai ta buWe murya iya ?arfinta tace

"Allah ya isa tsakanina dake Rashida, nasan bani da wani ma?iyi wanda baya ?aunar rayuwata sama dake, wallahi nasan kece kika jefeni na kwanta, sai ta matso kusa da umma tana nuna mata jikinta tana cewa

"Dubifa umma, ki kalli yadda Rashida ta maidani ?ashi da rai, wallahi kasheni tasoyi ya zulai, ta faWa tana kallon ya zulai tare da matsawa kusa da ita.

Sai kuma ta kalli hajja tace

"?arki azzaluma ce Hajja, ta daWe tana cutar dani batare dana faWawa kowa ba, shi kansa nasir wani abin bai san tana min ba saboda bana faWa masa, duka, zagi, asiri da gori babu kalar wanda bata min, duka ban Waga kai ba shine zata rabani da yarana ta nemi kassara min rayuwa ta? Me yasa bazata kasheni idan hakan takeso ba? Me yasa zata Wora min jinyar da bazan iya da ita ba? Allah ya isa hajja, wallahi bazan yafewa ?arki ba kiyi ha?uri.

*Umma*

?o?arin rufe wa Maryam baki take tayi domin abin nata yayiwa har take ganin kamar ma tafara rasa hankalin tane saboda gigicewar da tayi, shiyasa tun farko bataso a faWa mata halin data shiga ba amma ya zalai ta?i sai data zayyana mata komai gashi nan tayi rikicewar da basuyi tunani ba.

*Hajja*

Kukan da Maryam takeyi da kuma rikicewar da tayi ne yasa zuciyar ta tayi wani irin karyewa itama tafashe da kuka, dan tun sanda umma tayi mata waya dasafe take sanar da ita Maryam ta warke Alhamdulillahi suna ?ara mata godiya takasa zama saboda farin ciki tace sai tazo ta ganta, har taya Jamila da ita da ya Mansur da kuma aunty matarsa sai da sukazo saboda jin daWin kyakkyawan labarin da sukayi, daman samira ma ba'a batunta domin tunda Maryam ta kwanta ciwo idan yau batazo ba to gobe zatazo, shiyasa umma na sanar da ita ko likita bata sanarwa ba saboda ranar aikin kwana yayi tayi tawowarta.

Kai hajja ta jinjina tana share hawaye tace.

"Bai cancanci ki yafewa Rashida ba muddin da saka hannunta a cikin kwanciyar ki Maryam, kuma koni bazan yafe mata indai hakan ya tabbata bake ba Maryam, amma duk da haka inason kiyi ha?uri ki daina wan nan kukan da kikeyi saboda kar zuciyar ki ta samu matsala, dan wan nan kukan ya saSawa Shari'a, kiyi ha?uri.

Ya masur ne yaja ajiyar zuciya san nan yace

"Ai hajiya Maryam bata da wata hujjar da zata ce Rashida ce ta jefeta tunda babu wanda ya faWa mata ko aka nuna mata shaida, dan haka bata da hujjar tuhumar ta gaskiya, dan Allah hajiya kiyi ha?uri absa magan ganun Maryam.

Cikin hasala Maryam tatashi tace

"Haka zakace ya Mansur? Ina ?anwar ka bazaka goyi da bayana ba? To wallahi ko kaffara bazan yiba Rashida ita ce sular rashin lafiya ta, da ace nasir yana nan da zai bada shaida akan maganata, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login