Showing 81001 words to 84000 words out of 175193 words

Chapter 28 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

533

ayatul-kursiyyu.

Wani canjin yanayi Nasir da Maryam sukeji a cikin jikinsu wanda yabasu ?arfi sosai suka dunga bin karatun cikin sauri sauri kamar zasu haWiye harshen su, kuma suna tsaka da karatun ne maryam tafara kakarin amai, nan kuwa ta shiga kwarasa ta hanci ta baki ga aman wani iri domin kuwa aman kumfa ta dungayi harda zare zare mai launin ja a cikin sa.

*Rashida*

Jikinta ne yafara rawa ganin Abinda yake faruwa dasu maryam mai kamar al-mara, rasa inda zata nufa tayi dan haka sai ta juya da gudu ta shige Wakinta tare da banko shi ta jingina a ?ofar tana haki tare da runtse ido tanajin ?irjin ta na bugawa kamar zai faWo ?asa.

Rasa me zatayi tayi sai tayi saurin rarumar wayarta ta dannawa Amina kira, Amina na Wagawa Rashida ta fashe da kuka tace

"Shikkenan na shiga uku Amina, shikkenan asirina ya gama tonuwa, dan idan na haukace kashe kaina zanyi wallahi, bazan iya rayuwa cikin hauka ba Amina.

*Amina*

Cikin karaji ta katse Rashida tace

"Dakatamin mana haka? Ki saurara ki nutsu kifaWamin Abinda yake faruwa, tayaya hakan zai faru? Banfa gane ba malama.

Zama Rashida tayi a gefen gado tana cewa

"Komai ya lalace ya wargatse Amina, maganin da akayiwa Maryam baiyi tasiri akanta ba, haka wanda nake shafawa Nasir ya manta da lamarin ta shima ya tashi daga aiki, nan Rashida ta zayyanewa Amina Abinda yafaru tana ?ara sautin kukan ta.

"Haba Rashida, taya hakan zata faru alhalin ke shaidace aikin mai faWa da cikawa ba aikin hofi bane, kefa zaki bada labari, dan haka gaskiya ban yarda ba, a cikin kunnenki fa yace muddin ta sha?i haya?in nan ta gama aiki, shikkenan sai dai wata ba itaba dan idan ta samu taSin hankali bazata taSa warkewa ba dashi zata mutu, amma yanzu ki wani kirani kina faWamin aikin baiyi ba bayan a gabana aikin yafara aiki a jikin ta nan take.

Cikin ba?in ciki da tsawa Rashida ta tari numfashin Amina tace

"Wato ?arya zan miki kenan ko? Kina nufin sharri nakeyiwa malam aikinsa yaci nace baiyi bako? To shikkenan, idan ma bakida lokacin da zakizo kigani zan miki video ki gani idan yaso zaki yarda ai, tana faWin haka taja tsaki ta kashe wayar ta kwanta kan gadon tanajin yadda kanta yayi mata nauyin gaske kamar an aza mata bulo.

*Nasir*

Kallon Maryam yayi wacce baccin wahala da samun sau?i ya Wauketa taketa sharashi harda munshari, bayason ya taSata amma yanajin bazai iya barinta cikin wan nan ?azantar aman ba gaskiya, dan haka sai ya mi?e tare da shiga banWaki ya tara ruwa mai zafi da yawa a cikin baf san nan ya fito, Waukar Maryam Win yayi cak ya shiga da ita banWakin, kuma tunda ya Wauketa Maryam ta buWe idanunta tana kallon sa cikin tausayawa halin da yake ciki tunda ya karSi auren ta.

Tass Nasir ya sillawa Maryam wanka shima yayi, koda suka gama alwala sukayi domin gabatar da sallar la'asar wacce ta wuce su basuyi ba.

Bayan sun shirya ne suka gabatar da sallar la'asar Win, anan maryam ta zame ta kwanta dan wani gigitaccen barci ne yake fusgar kanta, ganin ta kwanta yasa shima Nasir ya kwanta kusa da ita tare da zame hular kanta yana shafa kanta a hankali har barci yayi gaba da ita, shima barcin ne ya Waukeshi domin har yanzu kansa a wani dummmm yake jinsa.

*Rashida*

Sai data gama kukan rashin nasarar da tayi san nan tatashi ta fito daga Wakin ta nufi Wakin Maryam dan taga halin da da take ciki, jitake ma Nasir yafita yabar Maryam Win tunda ta shafa masa maganin, san nan a zatanta zata tarar da Maryam Win cikin sigar hauka tuburun har an WaWWaure ta da igiyoyi, amma wani abin tashin hankalin da taci karo dashi shine yasa tayi taga taga zata faWi, badan Allah ya taimaka mata ta dafe ?ofaba to tabbas da yanke jiki zatayi ta faWi ?asa, kuma tana da tabbacin dazata faWin babu Abinda zai hanata kamuwa da cutar shan yewar Sarin jiki.

?ara zaro ido Rashida tayi bayan ta saisaita tsayuwar ta tana kallon Nasir da Maryam wanda suke ?an?ame da juna suna barci cikin kwanciyar hankali kamar babu Abinda yafaru dasu Wazu.

Baki ta toshe jin wani ?a??arfan kuka yana neman kwace mata, dan haka sai ta juya da sassarafa ta shige Wakinta zuciyar ta na tsallan daka da zafi kamar ana babbaka mata ita.

Waya ta Wauka ta kira Amina wacce sai da tayi mata wajen 11 misscall san nan ta Waga, da tsaki tayi mata sallama san nan tace

"Rashida, kuma menene? Gaskiya kin fara takura min fa, taya zaki zauna kiyi ta abu kamar mai taSin hankali? Nace kibar su kiga zuwa gobe tunda akwai sauran haya?in ki kuma haya?a mata, kuma tabbas idan kin haya?a mata ta sha?a wallahi bazata tsira ba, dan Allah kiyi ha?uri ki kwantar da hankalin ki Insha Allah zuwa jimawa zakiji sabon labari, san nan dan Allah karki kuma kirana domin hayateena a wajena yake, dan karki saka yafara zargina da wan nan wayar taki nima har asirina ya tonu, haba Rashida, misscall wajen Ashirin daga rana zuwa yanzu.

Kasa magana Rashida tayi sai kawai ta kashe wayar tana mai Wora hannu aka tana faWin na shiga uku na lalace.

A zabure kuma tayi kan gado tare da wangale ?afafu jin wasu allurai sun soke ta a ?asanta kamar balbalin bala'i, susa ta fara tana cije leSe domin abin ?aruwa yakeyi ba raguwa ba, haka ma nan take tafara susar kai da takejin wani a zababen ?ai?ayi ya rufto mata lokaci guda.

*Maryam*

A hankali take buWe idanunta domin sai takeji kamar ana tashin ta, tana gama buWe idon kuwa suka yi ido huWu da Nasir wanda ruwa ke jikin fuskar sa alamar alwala yayo, mi?a maryam tayi haWi da salatin Annabi san nan ta mi?e tanawa Nasir murmushi, koda tafito sallar suka gabatar ta magariba da isha'in domin ta rigada ta wucesu suna barci.

Hamma Maryam taketa saukewa akai akai, hakan yasa Nasir ya kula da yunwa takeji dan haka ya mi?e ya nufi kichen domin haWo mata shayi tasha dan tawarware cikinta.

Daman akwai abinci wanda Rashida ta dafa ta a jiye masa saboda tayi tunanin zai dawo da rana sai kuma ga Abinda ya faru, abincin ya Wauko duk da yaga alamar anci kuma yasan ?ila su halima ne domin ya gansu falon suna kallon cartoon.

Abincin ya kai mata tas kuwa ta share shi dan kwana biyun nan ita jitake bama ta ?oshi idan taci abincin.

*Rashida*

Tun jiya data ganowa kanta Abinda ya Waga mata hankali a cewar ta bata ?ara koda le?owa falon fa bare ta kuma zuwa Wakin Maryam Win, tana kwance tana fama da tashin hankalin Abinda ya damu rayuwar ta.

*Nasir*

Har ?arfe goma nasafe bai ga Alamar Rashida ba, kuma yasan tabbas bata kaiwa hakan bata fitoba, ganin bayan sun karya da maryam da yaran har lokacin ko ?eyarta babu sai kawai yatashi ya murWa handle Win ?ofar ya shiga, a kwance ya ganta ta lulluSa da bargo kamar mai barci, mamaki ne ya ishe shi ganin har ?arfe shaWaya saura tana barci? A ransa yake cewa

"Tome ya sameta? Yayi tsammanin bata da lafiya ne sai ya kawai ya ?ara da niyar yaye bargon ya taSa jikinta yaji ko lafiya.

*Rashida*

Tana kwance tana soshe soshen data kwana tanayi dan bata runtsa ba kwata kwata, kuma Abin mamaki ma duk inda yayi mata ?ai?ayin ta sosa sai taji ya Waye kurji ya fito a wajen, ga ?asanta shima dayaji uban ?uraje sunata sassoka mata, kamar zata haukace haka takeji, shiyasa ma ta?i fitowa falon saboda kar suga yanayin da take ciki maryam tayi mata dariya.

Shiyasa tanajin buWe ?ofar Nasir tayi saurin runtse idanunta dan ya zata barci takeyi ya kyaleta, amma ganin ha?onta bai cimma ruwa ba ta sallama dan tasan shi kaWaine zai iya bata taimako ma.

Nasir na yaye bargon yayi saurin yin baya domin ganin yadda cinyoyin Rashida suka kumbura kamar an hura mata su, bai kuma tsorata ba sai data wangale masa gabanta yaga wani dun?ulen nama ya turo gaban nata kamar an cusa shi, ga wasu ?uraje yaSa-yaSa ?an mitsi mitsi da suka yayyabe naman har wani ruwa ruwa ne ke tsattsafowa daga jikinsa.

A haukace Nasir ya wullar da bargon yayi kan Rashida yana jijjigata da menene haka? Menene wan nan?

FaWawa Rashida tayi kansa tana kuka har jikinta yana rawa tana cewa ya taimaka mata kar azaba ta kasheta, kafin ma yakai ga wata magana azabar ?unar da takeji a jikinta yasa ta saki jiki yaraf a jikinsa ta suma.

Cikin tashin hankali Nasir ya rufe mata jikinta da wani zani san nan ya Wauketa yayi ?asa da ita ko maganar su Halima baji yakeba wanda suka biyoshi suna menene ya samu maman su?

*Asibiti*

A hanzar ce aka Wauki Rashida zuwa Waki aka kwantar da ita, shi kansa likitan ya shiga tashin hankali da ganin jikin Rashida ba kaWan ba, san nan koda kasancewar sa gani bai taSacin karo da case irin na Rashida ba, dan haka a take suka fara bata taimakon gaggawa dan ganin ta farfaWo ma kafin sukai ga dubata matsalar tata.

Koda likitan ya fito neman Nasir yayi dan yanason ganinshi suyi wata magana mai mahimmanci, dan haka kallon Nasir likitan yayi da mamaki yace.

A zahirin gaskiya nayi mamakin irin wan nan ciwon haka, amma dan Allah menene musabbabin wan nan ciwon nata?

*Nasir*

Kai ya langwaSar a hankali cikin sanyi yana cewa

"Wallahi bansan Abinda yake damunta ba likita, nidai kawai mun wayi gari a haka kuma a zaba ce ta sakata suma, dan Allah lkita kayi ?o?ari ka bata taimakon da zata warware.

KafaWarsa likita ya dafa yana cewa

"Karka damu Nasir, Insha Allah zamuyi matu?ar ?o?ari wajen ganin mun kula da ita, kuma Insha Allah zata Samu afuwa kamar batayi ba.

Jinjina kai Nasir yayi yace bara yaje ya sanar da iyayen ta saboda kar abarta ita Waya.

*Hajja*

Salati taketa zabgawa tare da rarumar wayarta ta dokawa ya karimatu kira, tana Wagawa ta shaida mata halin da ake ciki tace ta nemi izinin mijinta ta samesu a asibitin.

Nasir ne ya Wauki hajja da autar ta nusaiba suka tafi asibitin, kuma koda suka isa sun tarar ya karimatu taje dan sunfi kusa da asibitin da gidan ta, hajja ce ta kalli Rashida ganin yadda aka wangale ?afafunta aka sa?ale su a sama saboda gurin ya dunga samun iska, kuka hajja tafashe dashi a sanda ta le?a cikin net Win da a kayiwa Rashida rumfa dashi saboda rufe bayyanar jikinta.

Da kyar su ya karimatu suka lallaSa hajja tayi shiru amma har lokacin bata bar furtawa Rashida addu'ar samun salama cikin gaggawa da takeyi ba.

*Bayan kwana biyu*

A wan nan kwanakin sam ya karimatu bata samun runtsa wa tayi barci, sam Rashida bata barinta barci saboda azabar ciwo, gashi maganin sha take kuma alluran akeyi amma shiru ciwo ya?i baya yana nan yadda yake kamar an shuka dusa, daWin daWawa ma wata iriyar zabura da ?an iface ifacen da Rashida takeyi shine yake Wagawa ya karimatu hankali, dan ita kaWai zakaga tana zabura tana ihu kamar zararriya can kuma sai ta fashe da dariya tana akira mata Amina ita tasan maganin da zatasha ta warke.

Ita Rashida sam tama fidda rai da rayuwa domin yanayin yadda take karSar gashi kamar ana zare mata rai haka take ji a faWarta, mafi Abinda yafi damunta yanzu bai wuce jin datake ana figar mata ?afafun nata wanda suke kamar gyanbo saboda azaba idan an taSa su, sai ta dungaji ana fincikar matasu ga gabanta da takejin kamar ana yanyanka shi saboda azabar da yake mata, daWin da Wawa sai ta dungajin kamar ana kiran sunanta da ?arfi kuma data kalli inda taji an kira sunan nata sai taga wasu fuskoki na gilma mata kamar ta dodanni, shiyasa take wan nan zaburar da ihun kamar zata fita a guje ta aza hannu aka taita sharara ihu saboda azabar dake nu?ur?usarta.

Yauma kamar kullum, Misalin ?arfe biyu na dare, sai ihu Rashida take da wayyo ta shiga uku kamar wata kafura, maimakon taita salati amma sai ihu saboda azabar ciwo, wan nan ihun ba ya karimatu kawai yake damuba harda sauran marassa lafiya da kuma likitocin.

Wata nurse ce ta shigo Wakin ranta a haWe take kallon Rashida tana cewa

Gaskiya kina damun rayuwar mu baiwar Allah, haba dan Allah, sai kace ba musulma ba, maimakon kiyita salati idan zafin ciwon ya dameki sai kiyi taiwa mutane ihu, gaskiya mungaji wallahi.

Baki ya karimatu ta buWe tafara bata ha?uri dan ita kanta Rashidan tafara bata haushi wallahi.

Wan nan nurse bata kallesu ba sai ma Wauko Allurar barci datayi ta zu?a ta bugawa Rashida a cinya dan gwara ta sumar da ita kosa samu su runtsa.

*KUTSE*

*PAGE 35*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION.*

*Rashida*

Kusan satinta biyu kenan a asibiti tana jinya, kullum kuma cikin sake mata sabbin magun guna akeyi da kuma allurai, amma Abinda zai bada matu?ar mamaki shine yadda kwata kwata ciwon baya baya sai gaba da yakeyi, san nan gashi har wan nan naman na gabanta yafara zama kore yana wari wari da Woyi Woyi da zubar da wani ruwa ruwa mai yau?i, kullum Rashida cikin kuka take da halin da take ciki, gashi idan akace ma za'ayi mata dressing ba yarda take yiba sai an WaWWaureta san nan take bari.

*Maryam*

Sauda ce akan cinyarta tanata mata kuka akan dan Allah idan zataje gurin maman su asibiti tatafi dasu, rarrashinta tafara tana ce mata tayi ha?uri maman tasuma ta kusa dawowa gida, ba komai yasa Maryam batason zuwa dasu asibitin ba sai dan karsuga halin da maman tasu take ciki.

Dakyar ta samu sauda tayi shiru bayan tabata alawa da biskit dan ta lallaSa su tafi makaranta karma su makara a dakesu, suna tafiya kuwa ta shirya basket Win abinci ta rufe ko ina na gidan tafita da niyar idan taje da wuri zata dawo kafin su halima su dawo daga makaranta.

Tana ?arasawa asibitin kuwa taci karo da Nasir shima zai shiga dan daga Waurin aure yake ya fita tun safe shiyasa bai jirata ba, cikin murna ta shiga motar tasa ya ?arasa da ita har bakin ?ofar Wakin yana tsokanarta da anya babu wata a ?asa ganin yadda taketa murjewa da kyalli kamar wata sabuwar amarya, ita dai Maryam shiru kawai tayi tana murmushi dan ita kanta wan nan canje canjen datake gani a gurinta tafara saka masa ayar tambaya, amma Abinda yasa kokonton nata ya dakata saboda ko watan daya wuce tayi period, shiyasa takauda batun ko ciki ne da ita a cikin ranta.

Suna shiga Wakin suka tsaya cak ganin an wullo musu kofi wanda yake Wauke da shayi ya zube a jikin kayan su.

*Rashida*

Idanunta nakan ?ofar shigowa, wataran haka takeyi sai takafe waje da kallo har sai ya karimatu ta juyo da fuskarta san nan zata daina kalla, yauma haka take, ta zubawa ?ofa idanuwa shiyasa tun tsayuwar Nasir da Maryam da yadda ya ri?o mata basket Win abincin hannunta suna tafe suna hira da murmushi yasa taji zuciyar ta ta tsaya da bugawa ta tokare mata ma?oshi kamar zata haWiyeta.

Wan nan ba?in cikin yasa tayi saurin zarar kofin kan table Win kusa da ita ta wurga musu, bataso ya tsaya a iya kayaba, so tayi ya tafi har gaban Maryam ya tarwatse akan fuskar ta wacce take tayiwa Nasir murmushin munafurci.

*Ya karimatu*

Da sauri ta rike hannun Rashida tamai dashi baya tana mata faWan Abinda tayi.

Su kuma su Nasir shigowa sukayi da sallama suna gewaye wajen da kofin ya fashe suka shiga Wakin sosai, gaisawa sukayi da ya karimatu tana satar kallon Maryam, a ranta take cewa

"A haka dai yarinyar nan kamar bata da matsala gaskiya, gata saliha da kuma fuska mai cike da annuri, amma kaga Mutum kawai, dan hakan ya bayyana akan fuskar Maryam bashi zai bayyanar da cewar mutuniyar kirki bace, sai kawai ta kawar da kanta gefe wajen Nasir tana amsa masa gaisuwar sa.

Tashi Nasir yayi ya isa gaban Rashida yana mata ya jiki Allah ya?ara sau?i.

Kamar Rashida bazata kulashi ba sai kawai ta fashe da kuka tace.

"Ai nasan kaida matarka murna kawai kukeyi da wan nan ciwon daya sameni, saboda baku damuba, jibifa yadda kuke farin ciki kuke rayuwar ku kamar babuni a duniya, sai kuma ta juyo kan Maryam tace.

"Ke dama idan zan mutu haka kika fiso ko? To Insha Allah bazan mutuba yarinya, wallahi sai kin rigani mutuwa, kuma karki ?ara zuwa inda nake, banza maciyiya amanar rayuwa, wallahi sai Allah ya tsine miki albarka, kuma kika sake kika cutar da yarana wallahi bazan yafe miki ba.

*Maryam*

Kasa tankawa tayi Saboda mamakin maganar Rashida, inda zata san yadda ta dage take mata addu'a akan samun warakar ta da tasha mamaki, ita ba azzaluma bace san nan ba macuciya bace, kuma harga Allah kullum a cikin gidan nan Nasir zancenta yakeyi, amma saboda bata da masaniya shiyasa take mata mummunan zato da mummunan fata.

Tashi tsaye maryam tayi tana murmushi tace

"Kiyi ha?uri maman halima, fatana a koda yaushe shine Allah yakawo miki waraka, san nan zan tafi kuma bazan sake zuwa ba Insha Allah muddin hakan zai sakaki farin ciki dan yanada kyau abarki kiji da Abu Waya.

Sai ta kalli ya karimatu tace

"Sai Anjima yaya Allah yabata lafiya, san nan ta kalli Nasir tace

"Zan wuce baban Halima, amma dan Allah ina neman izininka zanje gidan samira daga nan danna kwana biyu banje ba tun bayan suna ban kuma le?asu ba.

*Nasir*

Kwata kwata baiji daWin Abinda Rashida tayi musu ba, dan bata da lafiya aiba mahaukaciya bace, amma haka ya toshe bakinsa ya saki fuskar sa dan bayason Sacin ransa ya bayyana a gaban ya karimatu, kuma yanajin Maryam na zancen zata tafi shima ya ?udiri aniyar tare zasu tafi dan bazai barta tatafi ita kaWai ba.

Hannu ya Wagawa Maryam tare da bata makullin mota yace

"Kije bakin mota kijirani sai na saukeki a hanya idan kingama Abinda kikeyi sai ki kirani nazo mutafi.

Kai Maryam ta Waga tana fita waje tana cewa

"Tom shikkenan, Allah yasa kazo da wuri dan su Halima suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login