Showing 66001 words to 69000 words out of 175193 words

Chapter 23 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

541

cikin gidan, kuma harda kike cewa anci amanar ki aiki godewa Allah tunda ba irin cin amanar da uwarki tayi akayi miki ba.

*Hajja*

Da sauri ta Wagawa ya Aliyu hannu tace

"Ya isa Aliyu, wan nan wane irin shashanci ne? Meyasa baka da hankali ne?

Da sauri ya Aliyu yace "kibari a faWa mata komai hajja, dan dukkan alamu sun nuna cewar batasan wacece ita da kuma kutsen da sukayi mana ba.

Kuka hajja ta fashe dashi tana rufe bakin Aliyu tana cewa

Kabari Aliyu, kabari kada nayi fushi dakai, fushina masifa ne a gare ka.

Shiru ya Aliyu yayi yanajan kwafa tare dayiwa Rashida wani mugun kallon daya daWe yana Wauke kai daga gareta dan kar ta dunga tunanin kamar baya ?aunarta, kuma shi ba ?aunarta ne ba yayi ba, kawai idan ya kalleta sai ya dunga tuna irin butulci son zuciya da kuma rashin imanin da uwarta tayi musu daga sanadin aiki, badan Allah ya rufa asiri ba da tuni yanzu basu san makamar su ba tunda kafin uwarta ta mutu sai datayi wa babansu mugun asirin daya juya musu baya san nan daga baya ya koresu dan har kusa sheganta su yayi yace wai su ba ?a?ansa bane, sai da akai ta case san nan yadawo yace ?a?ansa ne amma wallahi sai yaje kotu anyi takarda baya sonsu kuma san nan yabarwa hajja su ma'ana ya yafesu a matsayin ?a?ansa, badan taimakon addu'a da taimakon Allah ba ai da tuni suna watan gaririya a rayuwa, shiyasa bai taSa kallon Rashida a matsayin ?ar uwarsu ba sai dai ?ar ma?iyiyarsu wacce taso kassara rayuwar su, dan ma kawai taci darajar hajja ta shayar da ita ne amma wallahi da bazai taSa yi mata kallon Rahama ba har abada, shiyasa kwata kwata basa jituwa dashi, badan hajja ma ta buga masa wurning da tsoratarwa a kanta ba Billahillazi da tuni ya mayar da ita dan gin uwarta.

*Rashida*

Mi?ewa tayi cikin ba?in ciki tana kallon ya Aliyu da idanun ta sukayi jage jage da hawaye tace.

Ai daman nasan ba ?aunata kakeyi ba ya Aliyu, to kasani banice na halicci kaina ba, kuma da kake cewa uwata ta muku kutse ai shi aure rabone kuma Allah yayi zanzo ta sanadiyyar haka, dan haka yawan gorin da kake min ya isheni haka.

Da sauri hajja tace

"to tunda kinsan Aure rabone sai kiyi ha?uri da Maryam ki karSeta a matsayin ?ar uwa sai ki zauna lafiya.

*Rashida*

Hannu ta Wagawa hajja alamar bata son maganar ta tace.

Daka tamin hajja, ai badan kin basu goyon bayaba da bazasu dungayi min gori kala kala ba akan zuwana duniya, tabbas kuma badan nononki nashaba da Allah kaWai yasan inda rayuwa ta ta dosa yanzu, kuma tabbas da kece kika haifeni da kin damu da ?arin auren mijina.

*Hajja*

Hawayenta ya?i tsayawa haWi da kallon Rashida wacce ta kasheta da mamaki, ita Rashida zata na gayawa dan ba ita ta haifeta ba Shiyasa bata damu da auren mijinta ba?

Da kyar hajja ta fuzgo kalma tacewa Rashida ....ni...ni...kike....

Bata kai ga ?arasawa ba sai jin ?arar marin da ya Aliyu ya saukewa Rashida tayi, da sauri ta jiyo ta ri?e hannunsa ganin yana niyar ?ara mata, hajja na kuka ta kalli Aliyu wanda shima hawayen yakeyi yana nuna Rashida da yatsa yana kar kaWawa.

Daman shi Aliyu sarkin fushi da zuciya ne, Allah yayi shi da ba?ar zuciyar da har rashin lafiya yakeyi idan ranshi ya Saci, shiyasa yanzun ma jikinsa rawa yakeyi saboda hanashi ?arasawa Rashida hukunci da yayi niya,

Ita kuwa Rashida da gudu ta shige Wakin hajja ta saka mukulli ta rufe ta cike tare da kwanciya kan doguwar kujera tana raira kukan dake saka zuciyar ta yaji yaji da ?una ?una.

*Ya Aminu*

Shigowar ya Aminu ce ta saka hajja tayi kansa tare da faWawa jikinsa tana kuka, ri?eta yayi a jikinsa yana kallon ya Aliyu cikin tuhuma wanda yaketa cin Waci idanunsa jajawur kamar zasuyi aman wuta,

"meya faru? Nace mai kayi? Ya Aminu ya tambaye shi yana neman kujera da ?o?arin zaunar da hajja.

*Ya Aliyu*

Hannu ya Waga yafara magana harda dukan ?irji yana cewar

"Wan nan ?ar iskar yarinyar ce ta zagi hajja saboda tasamu kana Waure mata gindi tanayin duk Abinda takeso.

"What? Ya Aminu yafaWa yana kallon hajja wacce ta dafe kai tana share hawaye.

Kauda kai ya Aminu yayi daga kallon hajja yace

Ina Rashida take? Nuna masa Wakin hajja ya Aliyu yayi yace

"tana ciki ta rufe, kuma wallahi zama zanyi anan har sai tagaji ta buWe dan wallahi yau sai na SaSSalata na zubar da ?asusuwan banza.

Da sauri ya Aminu yayi hanyar Wakin zai buWe yana kwala mata kira.

Saurin tashi itama hajja tayi tace

"Kada ka Wauki zafi da Rashida Aminu, domin Rashida bata zageni ba, kai kasan ko giyar wake Rashida tasha bazata iya zagina ba.

Kallonta ya Aliyu yayi yace "bata zagegi ba hajja?, rashin kunya ga babba ko iyaye ba zagi bane?

Zama hajja tayi tare da nunawa ya Aliyu hanyar waje tace.

"Ka wuce katafi gidan ka Aliyu, bana son sake jin wata magana daga bakinka, kuma inason komai ya wuce daga nan wajen.

Cikin ?unar rai ya Aliyu yazo gaban hajja ya tsugunna tare da yin ?asa dakai, hannu ta saka tare da shafa kansa tayi masa addu'a san nan yatashi yafita yana mai mi?awa ya Aminu hannu sukayi musabaha, yana fita ya faWa motarsa yanajin zuciyar sa naci gaba da tafasa na rashin kakkarya Rashida dabaiyi ba.

Ya Aminu, wajen ?afar hajja ya zauna yace

"Ranki ya daWe akwai wani abinne?

Girgiza kai hajja tayi tace

Babu komai Aminu, kaima zaka iya tafiya.

?aga kai yayi ya kalleta yace

"Ranki ya daWe Rashida fa?

Kansa ta dafa tare dayi masa addu'a tace "katafi kabar min ita.

Da to ya Aminu ya amsa san nan ya tashi yayiwa hajja sai da safe yafita yana mai tausayawa Rashida da halin data saka kanta a ciki akan wani banzan kishi.

Yana tafe yana tunanin halin da Rashida ta shigo gidan sa.

*****

Daman koda Nasir yace Rashida tatafi gida sai ya nemeta ya shige Waki bai kuma fitowa ba, haka itama Maryam Wakin su Halima ta shige bata kuma fitowa ba tunda batasan me zatace mata, ganin duk sun shige Waki yasa ta mi?e tana hawaye ta tattara yaranta suka fice tare da hawa napep tunda motarta ta lalace.

Rasa ina zatacewa mai napep ya kaita tayi, dan tasan karonta da hajja babu daWi, dan bazata iya zuwa gidan Hajja tace wai Nasir ya korota ba, haka bazata iya zuwa gidan ya karimatu ba dan tasan dariya zata mata, kuma ba jituwa sukeyi da ya Aliyu ba bare tace zataje gidansa, daman dai baya garine da sai taje dan matarsa ?awarta ce.

Da sauri Rashida tacewa mai napep yakaita cort road gidan ya Aminu, tasan shi kaWaine zai karSeta ya tausaya mata har ma yataya ta ya?in da zata kwato ?ancinta.

Sa'ar datayi tana shiga gidan ta tarar yana nan sunata table Chinese da yaransa, da yake daga chikin garden Win gidan yana hango wanda zai shiga falon, kuma yana ganinta ya nunawa yaransa su yace

"Oyah, muje ga aunty Rashida cen tazo, da sauri suka tafi zuwa falon suka sameta tana rufzar kuka afra matarsa nata aikin rarrashin ta.

Turus ya Aminu yayi yana kallon Rashida yace

"Ke kuma me akayi miki dakike wan nan kukan kamar zaki haWiyi zuciya? Kallonsa Rashida tayi tana ?ara sautin kukansa tana bawa ya Aminu labarin cin amanar da Nasir yayi mata.

Yaran baki Waya afra ta kora Waki san nan tace

"Ke yanzu Rashida saboda kawai Nasir ya ?ara Aure sai kibi kitashi hankalin ki haka har ki zubar da mutuncin ki agaban kishiya? Gaskiya Rashida kin faWo wallahi, kuma ba haka yakamata iyayen gida masu aji su yiba, to ai wan nan kin Sarar da garinki ne.

"Hannu Rashida ta Wagawa afra tace

"Kinga malama saurara min, bafa dake nake maganata ba da yayana nake, ke asuwa da zakiyi min shisshigi? Ai daman nasan ke bawai ?aunata kikeyi ba dan haka babu ruwan ki.

"Tsawa ya Aminu ya dakawa Rashida yace

"Idan rashin mutunci ne ya kawoki gidan nan maza tashi kificemin daga gidana, ashe har yanzu bakida kunya Rashida? Duk da afra matata ce laifine dan tabaki shawara? To banda ma shashanci ke yanzu Abinda kikayi tarbiyyar ce? Tarbiyyar da hajja tabaki kenan?

To bara kiji, ni bana goyon bayan rashin gaskiya, dan wan nan abin da kikayi tsabar rashin gaskiya ne? Ni yanzu sai akace miki bazan ?ara Aure ba saboda muna son juna da afra kuma mun samu fahimtar juna? To sam ba haka bane, shi aure ai lokaci ne, ko kuwa ba'a aure aka aureki ke? To nidai idan kinajin maganata maza kitashi ki koma gidan ki.

Majina Rashida ta share tace

"Shinefa yace na tawo yaya, kuma shikkenan baizo ba sai na Wauki ?afa na koma kamar mara gata? Gaskiya bazan koma ba nidai.

?an murmushi ya Aminu yayi yace

"Kece kuwa mai cikakken gata Rashida, amma kinsan bazan iya ajiyeki a cikin gidana batare da hajja ta saniba ko?

KeSe fuska Rashida tayi tace

"Dan Allah karka gayawa hajja yaya, wallahi raina zai Saci sosai, nidai kabari na zauna dan Allah.

Girgiza kai ya Aminu yayi yace

"Wallahi bazaki zauna min a gida hajja bata saniba Rashida, kema kuma kinsan haka ko? Dan haka dole na faWa mata tasan da hakan kafin daga baya taji labari raina yafi naki Saci, domin kuwa kinsan halin Hajja ita ba kanwar lasa bace, san nan kinsan halin fushinta sarai ko?

?aga kai Rashida tayi tana share hawayen daya gangaro mata.

Ajiyar zuciya afra tayi tatashi tana taSe baki dan daman ba wani shiri sukeyi da Rashidan ba, dan ita Rashida akwai Wagawa da kuma isa musamman idan taga tafika, kuma daman afra ba ?aramar wahalar Rashida tasha ba saboda basu da kuWi, tunda ya Aminu yake neman aurenta take adawa da auren dan babu yadda zatayi ne ya Aminu ya aureta, har habaici da take yada mata idan sunje sabga ta dunga ce mata wai ya Aminu ya gur Sata musu asali da ?ar yaku bayi.

Sai da hajja ta lura ta taka mata burki san nan ta samu zaman lafiya.

Bin bayanta Rashida tayi tana harararta musamman da taga ya Aminu ya rufa mata baya sun barta a falo zaune.

Wajen magariba kuwa ya Aminu yacewa Rashida ta shirya su tafi ya kaita gidan hajja tasan da barowa gidanta san nan su dawo, jiki babu kwari ta biyoshi suka tawo, kuma da tasan zasu samu ya Aliyu a gidan wallahi da bazataje ba, sam sam basa jituwa da ya Aliyu duk da matar sa ?awarta ce, shi mutum ne mai bala'in son girma da Wagawa yayi ta faWi da nuna isa wai shi babba.

Suna zuwa kuwa suka tarar dashi a falon hajjan ya wani hakimce suna hira, yana ganin Rashida ya haWe rai dan shi bayason raini shiyasa baya shiga sabgarta saboda bata da kunya, koda ta gaidashi da kyar ya amsa yana wani haWe girar sama data ?asa, kuma wai buWar bakinsa sai cayai wai me tazoyi a daren nan kuma ina yaran sai kace wajensa tazo.

Ita kuwa Rashida kasa kallon tsakiyar idon hajja tayi saboda yadd suke mata kwarjini, ya Aminu ne yafara shaidawa hajja Abinda Ya kawo su, kuma yana cikin musu bayani aka kirasa daga wajen aiki shine ya tashi ya fita waje yana amsa waya har Abinda yafaru ya faru batare daya saniba.

*Rashida*

Kuka kawai takeyi tanajin ya zama dole tabar gidan dan da ala duka ba ?aunarta suke ba, ko ita hajjan da take nuna mata ?auna tasan ba kamar yadda take ?aunar ?a?anta ba, dan da kamar yadda take ?aunar ?a?anta take ?aunarta wallahi bazata bari ya Aliyu ya zazzage ta ita da mahaifiyar ta wacce take ?asa ba, saboda haka sam batayi nadamar magan ganun data gaggayawa su hajja ba, kuma wallahi da ya Aliyu ya sake ya kuma taSata wallahi dasai ta nuna masa tana da gata wanda yafi nasa.

*Nasir*

Bashi yafito daga Wakin nan ba sai wajen magariba saboda Allurar barcin da kayi masa, yana rama sallolinsa ya fito yayin daya tarar da Maryam ita kaWai a falo tana kallo hankalin ta kwance, kallonsa tayi da murmushi a ranta har ya ?araso inda take zaune, kiss yabata a kumatu yana cewa

"Zumata ke kaWai? ?asa tayi da kanta tanajin kunyar san san nan tace

"Ina wuni ya jikin? Da sauki yace yana rarraba idanuwa dan yaga baiga yaran nasa a falon ba.

Sai ya kuma kallonta yace

"Ina su halima suke ne?

Kallon sa Maryam tayi tace

"Mamansu tatafi dasu ai.

Nan da nan fuskar Nasir ta canza yace

"tatafi dasu kuma?

?aga kai Maryam tayi tana kama hannunsa tace

"Karka damu masoyina, dan Allah kabar mata su saboda kar zafin yayi mata yawa.

Cike da Sacin ran maganar Maryam Nasir yace

"?acin rai yayi mata yawa fa kikace? Ni duk yadda take Satamin rai bakya gani kenan? San nan bakya ganin haukar datai minne? To wallahi sai ta dawo dasu na rantse da Allah, kitashi kibani abinci naci ya ?arasa faWa yana kokawa da Sacin ransa dan a tunanin da yayi bai kamata ya huce fushinsa akan Maryam baiwar Allah yarinya mai tsananin ha?uri ba.

*Maryam*

Jiki a sanyaye tatashi ta nufi dining inda ta ajiye abincin da tayi masa, haWowa tayi ta kawo masa ta ajiye, yana kallon abincin yayi murmushi yana kamo hannunta yace

"Allah yayi miki albarka Maryam, ha?i?a kina faranta min rai, Allah yabaki yara na gari, da Amin ya amsa tana saka masa cokali a gabansa.

"Sakwara ce da miyar ni?a??en nama gata ta daku tayi laushi kamar wacce akayi da flower.

Sai da yagama ci san nan ya mi?e ya koma Waki, jallabiyar sa kawai ya zura tare da zarar mukullin motarsa yayiwa Maryam sai ya dawo yafice daga gidan.

Harya fara tafiya sai kawai ya tsaya ya kira ?aramar wayar dake hannun halima, ringing Waya tayi ta Waga yace.

Halima kuna ina?

Kallon sauda tayi wacce ke game a TV game tace

"Muna gidan su ya haneef Abba, da to kawai ya amsa ya nufi cort road dan yasan haneef Wan gidan ya Aminu ne.

Yana ?arasawa ya kira Halima yace su fito ita da sauda, ko minti biyu ba'ayi ba sai gasu sun fito suna murnar ganinsa, mota ya buWe musu sauda ta shige gaba ita kuma Halima ta shige gidan baya.

Sai da ya tabbatar sun zauna sosai san nan ya tada motar suka bar harabar gidan ya nufi nashi gidan dasu.

*KUTSE*

*PAGE 28*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

A zabure tatashi da waya a kunnenta tare da buWe baki zata ?unduma ashar amma data tuna dawa take magana sai ta sai ta bakinta tare da fashewa da kukan ba?in ciki tace

"Yanzu tsakani da Allah ya Aminu har Nasir yazo ya Wauki su halima amma ace ba'a saniba sai daga baya? Ita afra menene amfanin barinta a gidan tunda bazata iya kula da yaraba? Nikam gaskiya ba'a kyauta min ba yaya.

*Ya Aminu*

Katseta yayi yana cewa

"Ke da Allah dakata, ke wace irin wawiya ce ne? Yara ba yaransa bane? Ko kuwa kin fishi iko dasu? Koda na kirasa na tambayi Dalili ai cayayi tun farko sai da yace karki kuskure ki tawo masa da yara amma saboda ke kunnen ?ashi ne dake shine kika taso ?eyar su kuka tawo.

Kuma duk ruwan rashin mutuncin da kike shukawa a cikin gidan ya sanar dani komai, san nan dan bakida da mutunci har ki iya buWar baki kiyiwa Nasir gorin gida ko? Wai bara na tambayeki Rashida.

" A lokcin da Abba ya mallakawa Nasir gida shawara yayi dake ko kuwa cayai ke yabawa ba Nasir ba?

To tunda haka kika zaSa sai kiyita Rashin nutsuwar ki da kuma zaman gida, ?itt, ya kashe wayar dan zuciyar sa a zafafe take kuma bayasan ya zurafafa dayi mata faWa har zuciyar sa ta tunzuro shi yayi mata Abinda zai Sata mata rai baki Waya.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?

Yana kashe wayar Rashida ta ?ara fashewa da kukan da tun da tazo gidan hajja shine aikinta, zama tayi akan gadon dake Wakin nusaiba autar hajja tana latsa wayarta domin ta kira aminyar ta Amina.

Amina na Wagawa Rashida ta fashe da kuka tana cewa

"Asiri na ya tonu Amina, wai yau nice Nasir ya koroni gida wai bani da tarbiyya nazo gida ayi min tarbiyya Amina, ni, wai ni Nasir zai wula?anta.

*Amina*

Kwance take amma saboda kiWima sai data mi?e zaune ta saka wayar a hansfree tace.

Ya koroki gidafa kikace? Nasir Win? Akan wata kucakar yarinya marar aji da ilimi? Gaskiya kinyi sake Wan zaki ya girma Rashida, kuma tun asali wallahi kece kika bawa kanki matsala, taya ya zakina fito da makaman ya?inki fili saboda rashin iya mu'amala, kinga mumafa duka munada kishiyar nan kuma kinsan dai nice naje na tarar amma yanzu saboda tsabar iya bariki na da kuma kissa da makirci na nice nake ri?e da gida, ita kanta uwar gidan ta zama hoto sai Abinda nace akeyi daga mijin har ?a?anta da kuma uban gayyar, gaskiya kin faWo kuma kin bada mata.

Kuma inaga bakya amfani da waWan nan magun gunan dana karSa miki ko?

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke tana share hawaye tace

"Wallahi ina Amfani dasu, ni Yanzu na rasa ya zanyi da Nasir a rayuwa ta, kinga dai da magani yana bala'in kamashi, amma yanzu duka maganin dake jikinsa ya warware san nan kuma wani baya kamashi, nifa gaskiya kawai asarar kuWina nayi inaga.

Ba dole kiyi asarar kuWiba Rashida tunda bakida ha?uri kuma baki iya kirsa ba, shifa asiri koda zaici sai kin haWa da kissa irin tamu ta mata dan haka wallahi sai kin mi?e tsaye kin kwato mijinki, idan ba hakaba kina kallo kwaWo zai miki ?afa tunda waccen tunkiyar taki itama naga idanunta a buWe suke, kuma da dukkan alamun maganin da takeyi yafi ?arfin naki wallahi.

Sai Rashida ta fashe da kuka tace

"Amina Nasir ba ?aramar yaudarata yayi ba, Nasir ya ha'inceni Amina, cafa yayi min ba sonta yake ba amma yanzu bala'i sonta yake, a gabana fa naji yanace mata zumata, me yake nufi dani kenan?

Salati Amina tayi harda tafa hannaye tace

"Iyih??? Nasir Win? Gaskiya Nasir yaci mutuncin mu wallahi, tunda yake dake ya taSa ce miki zumar sa? Sai ita? Wato yana nufin tafiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login