Showing 24001 words to 27000 words out of 175193 words

Chapter 9 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

522

biyu tukunna ko Allah zai saka a kunna wayar sai a ganota.

"Idanun Nasir jawur yace "haba dan Allah Ramadan, ya kakeso nayi ne? Nace maka akwai babbar matsala ne, wai meyasa bazaka fuskanta ba? Bansan me zancewa iyayen yarinyar nan ba, idan fa naje garin nan babu ita wallahi akwai k'ura dan bansan menene zai faru ba.

Cikin jin haushi Ramadan ya harareshi yace

"Ai ina tunanin tunda kanada Rashida a cikin gidanka ai matsalar ka ta yaye, to banda ma abinka naga kaine ka saka kanka a cikin matsalar, to meyasa zaka dameni? Kuma wallahi muddin baka dawo hankalin ka kasan kanka ba a banza soyayyar Rashidan da gudun fushinta zaiyi ajalinka.

Tashi Nasir yayi cikin fushi yace

"yanzu Ramadan ni kake fad'awa haka dannazo wajenka neman taimako?

Kai Ramadan ya girgiza yace

"Ko d'aya ba haka bane, kawai Abinda yake a zahirin gaskiya na fad'a maka, dan haka ruwanka ne kayi karatun ta nutsu, ruwanka ne kuma ka kuma dumliya.

Yana gama fad'ar haka Ramadan ya fice a fusace yabar masa office d'in, daga fitar Ramadan zuwa fitar Nasir sai da aka d'auki tsawon minti arba'in, shi bai fita ba kuma shi bai samo wata makamar ma, haka dai jiki babu kwari sai gashi ya fito gwiwa a sage yanajin kamar yafasa zuwa dauran saboda bai shirya tuhuma a wajen Mansur da ummansu ba.

Sai da ya sauke numfashi san nan ya jawo wayarsa wacce aketa kira tun d'azu Amma ya rasa k'arfin gwiwar dazai iya d'auka, sunan ya karimatu daya gani yasaka gabanshi fad'uwa, kamar bazai d'aga ba sai kuma ya d'aga murya a sanyaye yace.

"Salamu alaikum.

"Ai jinake wayar tawa ma bazaka d'auka ba tunda yanzu ka fara canza hali daga cikin halin da muka sanka dashi.

Yak'e Nasir yayi yace

"Haba babbar yaya, me yayi zafi haka?

Tsaki ya karimatu tayi tace

"Ai ba zafi yayi ba Nasir gobara ce tatashi.

Da sauri Nasir ya zaro ido yace

"Subhanallahi, gobara kuma yaya? Gobara a ina?

Da sauri ya karimatu tace

"A gidanka mana, idan kaga dama kazo kaga halin da mutanen gidan suke ciki, idan kuma kaga dama ka gama uzurinka sai ka dawo.

Wani irin mugun tashin hankali ne ya ziryaci Nasir, gobara kuma? A gidana? Hasbunallahu wa ni'iman wakeelu, wan nan wacce irin jarabta yake cikine?

A take ya juya kan sitiyarin yafara sharara gudun bala'i yana ta tunanin yadda suka kwashe da Rashida kafin yatawo, ashe ita tasan me zai faru dasu shiyasa takafe bazai tafi yabarta ba.

*****

Tun daren jiya data jiwa kanta ciwo da glass akan ya ambaci sunan maryam ake drama, babu yadda baiyi ba suje koda chemist ne Amma fafur Rashida tak'i, kuka taitayi tana cewa yabarta jinin ta tak'are ta huta da takaicin sa, daman shirun dataji na Maryam a kwanaki biyun nan bawai sakinta yayi ba? Ashe yana nan kudun dune da aurenta akansa Amma har yazo yana nuna mata kamar bashi da wata sai ita.

Duk yadda Nasir yaso ta saurare shi k'i tayi, haka ya zauna ya dunga mata rantsuwar baima san inda Maryam d'in takeba tun ranar daya sauketa Amma tak'i yarda, ganin tak'i yarda dashi yasa ya tashi yafita daga gidan, cen jimawa sai gashi damai chemist d'in shine fa aka lallab'a akayi mata dressing d'in wajen da kyar tana kuka tana komai.

Idan ran Rashida ya b'aci har yaranta tsoron zuwa kusa da ita sukeyi , ballantana Nasir wanda suke kwana d'aki d'aya, a wan nan ranar ma k'in kwana d'aki d'aya yayi da ita saboda yasan halin tijarar ta akan kishi sai su kwana suna rigima d'aya, yasan halin Rashida sarai akan kishi, to wai shi meyasa ma yayi mata kishiyar? Shifa ko abokanan sane suka Ka'ra aure muddin tasani to ranar baza'a kwana lafiya ba, haka zataita shiga da fita tana masifa har sai an kwana biyu dayin Abin, kuma daga san nan wan nan abokin nasa ta tsaneshi kenan ko son jin mai irin sunansa tayi sai ta zageshi, kuma duk yadda zatayi sai ta san yadda tayi ta lalata mu'amalar sa dashi, koda basu rabu baki d'aya ba sai mu'amalar su ta raunana.

Tunda Rashida tashige d'akin bai kumajin motsin taba, haka yadunga zuwa yana kasa kunne ajikin k'ofar d'akin nata Amma sai yaji shiru, da farko yafara jin tana 'yan koke koke daga baya kuma yaji ta tsit.

Sai da safe bayan ma yashirya ya fito sai kawai sukaci karo da ita, kallon sama da k'asa tai masa san nan tace

"Wai harka shirya?

A d'an tsorace yace

"Eh zan tafi, kinsan daura da nisa dole sai na fita sassafe idan inason dawowa yau da wuri.

"Gira ta d'aga tace

"Uhum, babu laifi, Allah ya tsare, Amma banji ka saka turare ba, kuma gaskiya sabon kaya zaka saka kaida ake zaman makokin baba kuma surukin ka.

Har ranshi yad'an ji sanyi sai yayi tunanin kota d'an sakkone ashe shi bai saniba gadar zare take gina masa.

D'aga kai Nasir yayi yace

"Kumafa hakane, wallahi duk a rikice nake, yauwa ina sabbin d'in kin nan?

Da sauri Rashida ta d'aga kai tana tunani tace

"Uhummm, kamar fa yana d'akina, "Eh suna d'akina, muje sai kazab'i d'aya kasaka.

Bin bayanta Nasir yayi yana d'an jin dad'in sakin da Rashida tayi suka shiga d'akin.

Suna shiga ta zare mukullin k'ofar ta rik'e a hannunta, shi kuma juyawa yayi ya zaro ledar kayan, kuma tunkan yakai ga d'auko wa Rashida tayi wuf tafice tare da banke k'ofar ta saka mata mukulli.

A firgice Nasir ya biyota yana cewa

"Rashida, Rashida ke, kizo ki bud'e min, wan nan wane irin shashanci ne wai? Rashida.

Tana zaune ta hakimce tana danna waya a d'ayan hannun nata da babu bandage, tanajin irin kiran dayake mata amma tayi masa banza, haka Nasir ya dunga had'ata da Allah da annabi akan ta bud'e shi Amma fafur tak'i, har alk'awarin idan ta bud'e shi yafasa fita yayi mata Amma tak'i sauraren shi.

Sauda na kusa da ita tanacin kwai yayin da idanun Halima sukayi kwalo kwalo da Abinda mamansu takeyiwa Abban su, ita bata saba daganin duk wan nan ba, wai akan me komai ya canza a gidan ne, ta k'arasa a ranta tana cewa

"Allah sarki Abban mu.

Jin Nasir ya dameta da bugu yasa ta mik'e tana cewa

"Kadameni fa, duk kabi kacikan kunne da safen nan, ni bara naje nayi wanka, idan kagaji da bugun kayi barci shikkenan, idan ma baka gajiba to ni banida lokacin ka.

D'akin Nasir d'in ta bud'e ta shige tana mai turo k'ofar, ashe Abinda Rashida bata saniba shine, ta manta tabar mukullin akan kujerar data zauna, akan mukullin ma ta zauna dan kar wani sumatsi yafaru dashi, sai kuma akayi sa'a sanda tatashi sai tabar mukullin dan ta manta dashi.

*Halima*

Tana ganin maman tasu tatashi tabar mukullin tayi saurin mik'ewa tana cewa

"Wallahi saina bud'e shi.

kallon ta sauda tayi tace.

"Babu ruwanki ya Halima, kinga dai tsakanin sune, kuma maman mu tace mudaina shiga tsakanin ta da mijinta.

Hararar sauda Halima tayi tace

"Koba tsakani ba? Nabi tsakanin da gudu ba wando, wallahi sai na bud'e, ta zari mukullin tayi hanyar d'akin maman nasu.

Tana zuwa kuwa tayi saurin saka mukullin ta bud'e tana cewa.

"Abba.

Da sauri ya taso daga kan gadon ganin Halima, yayi ma zatan Rashidan ce shiyasa yak'i ko motsi dayaji zata bud'e k'ofar, dan yayi niyar yau saiya nuna mata fushinsa sosai wallahi, yayi alk'awarin yau sai tafara shakkar abubuwan datake masa, Amma ganin Halima yasa yayi saurin tashi yana cewa.

"Ina maman taku?

Kallon d'akinsa Halima tayi tace

"Tana wanka.

Da sauri ya gewaye haliman ya wuce yana cewa

"Kuyi min addu'a sai na dawo, san nan yafice yana wiwaye kar Rashidan tafito.

Rashidan batasan meke faruwa ba, sai kawai jin k'arar tada mota tayi da kuma fitarta, da sauri ta sakarwa kanta shaya domin ta d'auraye kumfar data sab'a a jikinta, ko kumfar bata bari tagama wankuwa ba tayi saurin zarar tawul ta d'aura tafice tana goge fuskar da rabinta da goshinta duk kumfar ce.

Tana fita ta kalli d'akinta ta ganshi a bud'e, baki ta saki Had'i da juyawa ta kalli Halima ta kalli sauda, da sauri sauda ta nuna Halima tana cewa

"Wallahi ya Halima ce , sai danace karta bud'e ita kuma tace sai ta bud'e, shine ta bud'e masa yafita.

Cikin fushi Rashida tayi kan Halima gadan gadan tana neman abun dukan da zata zaneta, ganin d'aukowar ma b'ata mata lokaci ne yasa ta d'aga hannun nata wanda ta manta da ciwo ajikinsa takaiwa Halima duka, da sauri Halima ta zille ai kuwa hannun Rashidan ya sauka a jikin bango har sai da yayi K'ara, ita ma cikin azaba ta saki Ka'ra tanajin kamar ta furtawa Halima kalmar Allah ya isa.

Wan nan zafin ciwon da kuma jinin daya cigaba da zuba yasa Rashida zubar da hawaye ga tuk'uk'in bak'in cikin fitar da Nasir yayi yasa taita kuka tanajin zuciyar ta kamar zata kumbura, da kyar ta iya zura doguwar riga taja hannun sauda tana makawa Halima harara suka fita wajen me chemist domin yak'ara duba hannun nata.

*****

Nasir yana tafe yana cewa

"Daman ban tawoba, meyasa data rufeni Halima ta bud'e ni, daban tawo ba da duk Abinda yafaru bai faruba, da zai farun ma da ina cikin gidan, gobara fa? Meya samesu? Meya tadata.

D'aukar wayar sa yayi ya dunga kiran ya karimatu bata d'aga ba, haka ma wayar Rashidan a kashe, kiran duniya yayi musu Amma sunk'i d'agawa.

Gaf yake da barin gari sai ga kiran ya Mansur, kamar bazai d'aga ba sai kuma ya d'aga a karo na biyu daya kirasa

"Sallama ya Mansur yayi masa yace.

"Wai ina katsaya ne baka k'araso ba? Maryam tazo tun safe ita da samira da mijin samiran kuma sunce kana hanya, anya kuwa lafiya?

*Nasir*

Me zaiyi? Murna zaiyi ko kuka? Maryam tazo? Maryam fa? Aina aka ganta? Tana nan lafiya kenan? D'aga kansa sama yayi yana tunanin Abinda zai cewa Mansur.

Gashi, gashi gida suna buk'atar sa gashi kuma Maryam ma tana buk'atar sa, to ina zai nufa? Wacece tafi cancanta?

*Bayan awa uku*

Salatin da yaya karimatu ke zabgawa kad'ai ya isa yasa gabanka yayita fad'uwa, data dire wani salatin zata d'auki wani, kafin ta k'arasa wani ta kuma caf kar wani.

Kuka Rashida ta fashe dashi duk da daman shi takeyi tace

"Me Nasir yake nufi? Banida mahimmaci nida yarana a wajen shi kenan? Har ki kirashi kice munyi gobara Amma ya shashantar da zancen ya cigaba da sabgogin sa? Ni Nasir zaiwa haka? Ni? Ta k'arasa tana nuna kanta.

Ajiyar zuciya da salati yaya karimatu ta kuma kwasowa tace.

Ai ga zahiri nan Rashida, tabbaci Nasir yake baki yasamu wacce tafiki, yo yasamu wacce tafiki mana, ai tunda yaci moriyar ganga dole ne ya yada korenta, banda bashida da mutunci har na kirasa da karan kaina nace masa akwai matsala Amma yaron nan yayi burus, saboda me nace ki kashe wayar ki? San san nan saboda me nak'i d'aukar tawa dayake kira, ai bawani abin yasaba, saboda hankalin sa yafi tashi, saboda ruhinshi da gangar jikinsa su dugun zuma duk inda yake yabaro ya tawo.

Amma gaskiya Nasir ya shayar dani madarar mamaki, me yasa ba'ason kishiyar? Ai saboda haka, musamman ma taki kishiyar datazo a bazata, tazo a munafurce, ai wallahi Rashida bama ke kad'ai ba komu da muke'yan uwanki billahillazi bazamu taba son waccen tsinanniyar yarinyar ba, cab'b'ijan, kuma wallahi bari kiji na baki ban tararan bayani bana raba d'ayan biyu Nasir yana wajen waccen yarinyar, ai in fad'a miki wallahi da mutuwar uban nan nata zasuyi amfani sufara gina soyayyar da sai dai kiji a salansa, Amma ki kwantar da hankalin ki, mu'yan gidan mu bama boranci , kibar ni dasu wa billahillazi sai sun san sun tab'o iyalan Bello tabo.

*****

*Maryam*

Tana jingine a kafad'ar samira wacce suketa kuka tare saboda rad'ad'in rashin baba da kuma tausayawa halin da ummanta take ciki, ga mace a kwance dakyar take iya magana bama a maganar ci dasha daman wan nan bama azo wajen shiba, gashi anyi anyi da ita akaita asibiti Amma tak'i, shigowar maryam cema da suman datayi tasa jikin umman nasu yad'an yi k'arfi, dan sosai hankalin ta yatashi da ganin suman da Maryam tayi a gabanta, kuka take tana dan Allah Maryam kitashi kitashi kada kibi mahaifin ku kubar mu mumu kad'ai, banson rasa ki 'yata, gwarani natafi na barki dan yanzu kuka tsoma hannu a gwagwar mayar duniyar, dan Allah maryam kitashi.

Da taimakon ya mansur da kuma na sauran matan wajen aka samu Maryam ta farfad'o dakyar, shima tana farfad'owar tafara rawar kyarma saboda zazzab'in daya rufeta.

Har yanzu zazzab'in ne a cikin jikinta amma yayi sauk'i ba kamar d'azu ba, a d'akinta datake kwana da suke zaune, duk wanda kake gani awajen nan yana jimamin rasuwar baba sosai, kowa umma yake bawa mutuwa saboda rashin lafiyar datake fama da ita sai gashi baba mai lafiyar dashi ke jinyar tama yatafi yabarta.

Wan nan fa shi ake kira ta masa jinya shikuma ya mata mutuwa, daman haka ne basai mai jinya ke mutuwa ba, ita mutuwa lokaci ne da ita da lokacin kuma yayi za'a amsa kiran ubangiji.

*Mansur*

Rik'e yake da hannun Maryam yana d'an matsa mata yana cewa

"Kiyi hak'uri Maryam, addu'a baba yake nema ba kuka da tashin hankali ba, yanzu abu d'aya zakiyi masa ki masa gata.

Addu'ar dazai dunga samu daga gareki itace gatanshi.

Yanzu kuma zamu maida hankali kan rashin lafiyar umma musan yadda zamu b'ullowa al-amarin ta, dan haka kiyi hak'uri ki share hawayen nan kinji, shi kukan mutuwar iyaye ba'a gamashi har sai ranar da Allah yakawo maka taka tukunna.

Fatan mudai Allah yajik'an baba ya kuma bawa umma lafiya.

Da Amin samira ta amsa dan Maryam bakin ta yayi mata nauyi bama iya maganar takeyi ba.

Sai a san nan Mansur yace

"Na ganku ku kad'ai ina Nasir d'in?

Sai a san nan gaban Maryam yafad'i har ta iya dago kai ta kalli ya Mansur da jajayen idanunta.

Ita kuma Samira da sauri tace

"Am..am..am daman..Daman..

Sai ya Mansur ya katseta da cewar.

Ai daman jiya da yazo yace yau da safe zaizo da Maryam, namayi tunanin tare kuke sai na ganku ku kad'ai, shi d'in yana ina?

Yakai matarsa asibiti ne bata da lafiya, shine mukai waya dasu sai kawai yace maryam ta biyo mu kar mu b'ata lokaci shima zai tawo da zarar sun kammala da asibitin.

D'aga kai Mansur yayi yace

"Allah yabata lafiya, san nan yatashi yanawa maryam sannu ya fice.

Yana fita daga Maryam d'in har samira suka sauke wata ajiyar zuciya, ita kanta samiran mamakin yadda akayi ta iya shara wan nan k'aryar takeyi, k'arya ba sabonta bane shiyasa k'irjinta bugawa kawai ya dungayi yana sama da k'asa.

*Nasir*

Yana yanke hukunci yayi reverse ya koma hanyar daura, zuba gudu yayi tayi yana hasashen yadda zaiga Maryam da halin datake ciki, yasan bai kyauta mata ba, inama taje da har ta iya wan nan kwanakin cikin nutsuwa? Bashi damai bashi wan nan amsar har sai yaje gareta.

Yasan tanacen tanata kuka kamar zata k'arar da hawayen ta, so yake yaje gareta, ya ganta tana kuka ya rarrasheta, kuma yayi alk'awarin Insha Allah bazata k'ara kuka da zubar hawaye ba indai a dalilin sane.

Abinda yafi bawa Nasir mamaki shine.

Da zumud'in son ganinta ya shiga gidan, dan koda ya zauna a wajen suka gaggaisa da mutane zumbur ya mik'e yana tambayar Mansur ina Maryam?

Da kansa ya shigar dashi d'akin Maryam duk da ba yaune ya fara shiga d'akin ba, Amma yau na dabanne, jiyake kamar yana shiga ya rungume ta ya rarrasheta.

"Amma me?

Daman ya mansur ma bai shiga d'akin ba, yana nuna masa inda take yafice, shikuma Nasir da sallama ya shiga d'akin yana kafe Maryam da kallo wacce ya ganta lamo a jikin samira tana sharar hawaye, Amma suna had'a idanu ta kuma d'aure fuska ta d'auke Kai, Abin ya bala'in bashi mamaki sosai, sai kawai ya tsaya yana kallonta, dajin jikinsa na mazari domin ya isa gareta kawai sai yafara takawa zuwa inda take zaune.

*Maryam*

Tanajin sallama da muryar Nasir gabanta yayi bala'in fad'uwa, da sauri ta damk'e hannun samira dake cikin nata ta kuma runtse idonta, itama samirar kama hannun nata tayi tare dayi mata Alamar babu komai, hakan yasa har ta iya daga kai suka kalli juna.

Wani kallo data gwammace daman bata aika masa shiba, dan wan nan kallon sabuwar tsumin soyayyar sa ta tado mata da ita, hakan yasa tana ganin yafara takowa gabanta tai saurin tashi tare da gewaye shi ta fice daga d'akin, ganin duk inda ke gidan ba bak'o bane a wajensa yasa tafice daga gidan baki d'aya ta shige mak'ota.

Da mamaki Nasir yabi bayanta yana tunanin Abinda yayi mata da zafi haka har yake gano sabuwar k'iyayyar sa a idanun Maryam, jiki ba kwari yafara tafiya yana tunanin k'ila ya ganta a soro idan ya fita, Amma yana fita sai yaga wayam, hakan yasa ya zauna a cikin rumfa yana wurga idanuwa da bazasu domin ganin ta inda Maryam d'in zata b'ullo.

*KUTSE*

? ?? *PAGE 13*

? ? ? ? ? *NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Bayan kwana uku*

Kwana uku ringis su Maryam sukayi a daura, bama Maryam ba har Nasir wanda ya kasa sukuni da kuma sakin jikinsa saboda yanayin yadda Maryam ta watsar dashi ta ban zatar dashi kamar ba mijinta ba, kuma tunda sukaje magana kota kallo ce tak'i barin ta had'a su dashi ballatana ta baki, wan nan Abin yayi bala'in damun Nasir wanda har sai da yakasa hak'uri yayi wa samira magana.

*Samira*

Ajiyar zuciya ta sauke tace

"Kayi hak'uri ya Nasir, kasan Maryam sarai da aniya, kuma duk Abinda takeyi bawai tanayi bane da san ranta, kasan yadda mutuwar nan ta daketa sosai, san nan ga rashin lafiyar umma, wan nan dalilin yasa ta kasa sukunin da zata saurare ka, Amma dan Allah ka k'ara hak'uri Insha Allah idan tadawo nutsuwar ta zata saurare ka.

Kai Nasir ya rausayar yace

"Shikkenan babu damuwa, zan jira har lokacin da zata samu nutsuwar insha Allah, Amma dan Allah ku shirya da wuri saboda kada dare yayi mana.

Da "to" kawai samira ta amsa ta shige cikin gidan tana musu fatan Allah ya dai-dai ta tsakanin su.

*Maryam*

Tana zaune gaban umma tana share hawayen tau saya mata da take, yauce ranar da aka saka mata ta aiki kuma yauce ranar da baba ya kwana uku da rasuwa, takasa kallon ya Mansur dake mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login