Showing 75001 words to 78000 words out of 175193 words

Chapter 26 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

575

taga zata faWi.

Maryam na cire Rashida daga jikinta ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya tare da sulalewa ta faWi rajab a wajen ta zauna tana maida numfashi mai Wumin gaske.

Ba Nasir da yasan kyawawan halin Maryam ba, hattaya hajja da nusaiba sai da suka zaro ido haWi da kallon Rashida wacce tayi tsumu tsumu a tsaye ta haWe hannaye tana zubar da kwalla, da sauri nusaiba tayi kan Rashida tana faWin.

"Aunty Rashida, sai kuma takalli Maryam tare da wurga mata wani kallon rashin fahimta tace.

"A kan me zaki tureta haka? Me tayi miki?

Ita kuma Hajja kallon nusaiba tayi ta watsa mata kallon ta mutsu san nan tayi kan Maryam da sauri tana furta

"subhanallahi, sannu, menene ya sameki haka? Ta ?arasa tana ri?e hannun Maryam dan ta tasheta, jin jikinta na rawa yasa ta ri?eta gaba Waya Nasir na taya ta suka tashi Maryam tsaye suka zaunar da ita akan kujera jikinta na Sari.

Ba?in cikin hajja da kuma Nasir basubi takan Rashida ba yasa ta ?ara ke cewa da kuka tana ?an ?ame nusaiba tana cewa.

"Ban mata komai ba nusaiba, manufata ta Alkairi ce yanzu a gareta, na gane duka wasu kura kuraina dan Allah kuce ta yafemin, ta ?arasa tana tsugunna wa gaban hajja tana dafa hannayen ta.

*Hajja*

Ba ?aramin tausayi Rashida ta bata saboda har ga Allah taji babu daWin Abinda Maryam tayi mata ba, amma Wa na kowa ne shiyasa tabi Maryam domin ta tasheta, kuma dukkan yanayin Maryam ya nuna yarinya ce saliha marar hayaniya dan daga ganinta zatayi sanyin hali da lumana, amma Abinda yabata mamaki shine, menene yasa a lokacin da Rashida ta rungume ta ta runtse idanunta san nan daga bisani ta ture Rashida daga jikinta, ajiyar zuciya hajja taja a ranta tace

"Koma menene Allah yasan dai-dai a tsakanin su.

*Nasir*

Sai da yagama shan mamakin Abinda Maryam tayi san nan ya samu cikin sanyin gwiwa ya zauna tare da tan kwashe ?afafu ya cire hularsa duk saboda girmama hajja san nan yafara gaidata kansa na ?asa kamar yadda yaga ?a?anta suna yi.

Cikin fara'a da yalwar fuska hajja ta amsa gaisuwar Nasir tana saka masa albarka, yana Waya daga cikin Abinda yasa hajja take ?aunar Nasir saboda biyayyar sa da girmama mutane, yana bata girman ta yadda ya kamata kamar ita ce ta haifeshi, ha?i?a tasan ?arta Rashida tayi dacen mijin kwarai mai ha?uri da kawaici, shiyasa take mata addu'a a koda yaushe na Allah ya canza mata halayenta ta zauna lafiya da mijinta dan muddin Rashida tasake Nasir ya suSuce mata to har ta mutu bazata ?ara samun miji kamar saba.

*Maryam*

Itama ganin Abinda Nasir yayi yasa ta sauko duk da jikinta akwai zafi rau san nan yana mata rawa sosai bai hanata ?arasawa gaban hajja ta sunkuyar dakai ta fara gaidata ba.

Yarinyar tausayi take bawa hajja, shiyasa ta dafa kanta ganin tana hawaye ga Rashida ma nayi, rarrashin ta ta hauyi kafin daga bisani ta Waga kai takalli Rashida wacce taketa share hawayen daya ?i tsaya mata, kuma hawayen nata bana komai bane illah na ba?in cikin ganin Maryam da kuma yadda hajja ta kar Seta, itama hajjan ce tafara rarrashinta tana cewa suyi shiru dan kuka bazai canza komai ba sai dai kyakkyawar niya ta canza zuciyoyi.

*Nasir*

Wani abune ya danne ?irjinsa na rashin daWi domin duka matan nasa yanason su san nan bayason Sacin ransu ko kuma kukansu, shiyasa dan ya datse kukan ya farawa hajja magana cikin sigar ladabi da biyayya yace.

"Ina neman afuwar ki uwa tagari, ha?i?a nasan nayi laifi dana turo Rashida gida batare dayi miki bayanin komai ba, hakan yasa nace yau dai bara nazo na wanke laifina san nan na Wauki Rashida mukoma gida.

Murmushi hajja tayi tana kallon Nasir wanda yakasa kallonta tace.

"To Alhamdulillahi da komai daya faru ma, mu ?an adam ne kuma muna kuskure a koda yaushe saboda mu ajizai ne kuma tara muke bamu zama goma ba, dan haka Rashida matar kace Nasir, kuma ban san tsakanin ku ba dan tsakanin miji da mata sai Allah, amma dai kaima kayi ha?uri da dukkan abubuwan da suka faru dan yayansu ya sanar dani komai, kuma ina ?ara horar dakai daka kasance namiji mai adalci kuma jajir tacce a cikin gidan ka, yin hakan shine zai taimaka wajen haWin kan iyalinka kuma su sama maka farin ciki.

Rashida dai ?ata ce kuma Maryam ma ?ata ce, babu wanda zan bawa gaskiya nabar wani indai Shari'ar gaskiya akeso, saboda su sun san mai gaskiya da marar gaskiya a tsakanin su, shiyasa nakeso na tsoratar daku ha??in mutum, kunga ha??i? To kuguji ha??in mutun, domin tabbas ha??in mutum yana kai mutum cikin wutar jahannama, dan haka duka tsoratarwa ne zuwa gare ku, duk wacce ta cuci wata a cikin ku Allah zai saka mata, haka idan kuka zalinci mijinku ma wallahi Allah zai saka masa, dan haka ina muku nasiha daku zauna da juna tsakanin ku da Allah, ku haWa kanku kuyi zaman lafiya domin ku bawa mijinku farin ciki.

Ina fatan Allah yayi muku albarka baki Wayanku ya ?ara haWa kawunan ku ku zauna lafiya.

Da Amin baki Waya suka amsa san nan Rashida ta rarrafo gaban Nasir tana kuka harda sharSe majina tana ro?ar sa daya yafe mata.

Ajiyar zuciya Nasir ya sauke san nan ya sakar mata murmushi yace

"na yafe miki Rashida Allah ya yafe mana baki Waya.

Amin tace, san nan ta ta kuma juyawa wajen Maryam tare da ri?e hannunta tana furta cewar itama ta yafe mata.

*Maryam*

Rashidan na kama hannun ta taji wani raWaWin zafi kamar ana huro mata wuta na ?onata, batason tayi acting Win datayi Wazu saboda idanun mutane amma tabbas da ihu zata kwala ta kuma ture Rashidan, cijewa kawai Maryamu tayi ta kuma dake tana zubawa Rashida ya?e kamar yadda Rashidan take zuba mata murmushi.

A hankali Maryam ta zame hannunta daga na Rashida wacce ta ?an?ame hannun nata tana mata murmushi saboda tsabar mugunta.

Tana sakin hannun nata ta saki ajiyar zuciya, domin jitai kamar an kwara mata ruwan sanyi har zuwa ?afafunta.

Sai da nusaiba ta cika musu da addu'a san nan suka tashi baki Waya domin tafiya.

Itama Rashidan kayanta ta Wauko bisa umarnin Hajja da tace ta Webo tabi mijinta su tafi gida.

Sha tara ta arzu?i hajja ta haWawa Maryam, dangin turaruka da kayan kwalliya harda turmin atamfa da kuma lace mayafi takalmi harda jakarsa, rasa bakin godiya Maryam tayi kwai sai ta fashe da kuka na ganin ?aunar da hajja take nuna mata a gani Waya kawai.


*****

Koda Nasir ya Wauki hanyar gida babu wani a cikin motar dake kwakwkwaran motsin kirki a ciki, daman yaran tuni sunyi barci dan goma na dare ta kusa , sai da ya tsaya a yahuza suya ya saya musu kaya da youghout san nan suka nufo gidan, Maryam ce a baya dan haka itace ta fara fita dan daman koda suka fito daga gidan Hajja baya ta shiga tabawa uwar gida mai capacity gidan gaba ta zaune.

Da Wai-Wai da Wai-Wai ta fara fito da yaran kafin Nasir ya fito shima ya Wauki Halima , ita kuma zata Wau sauda kenan Rashida tayi saurin ri?e hannunta tana cewa

"Kibarshi na Wauketa, Maryam batayi musu ba da sauri ta sakar mata sauda saboda still dai taji wan nan zafin dake mata barazanar ?ona fata a duk sanda Rashida tazo ta taSa jikinta.

Murmushi Rashida ta sakar wa Maryam na zakici ubanki san nan ta kinkimi sauda suka haye sama ita kuma Maryam tabisu a baya tunda daman tuni Nasir yayi gaba abinsa.

*Nasir*

A falon ya tarasu ya ?arayi musu nasiha dasu zauna lafiya saboda shi wan nan rigimar ta ishe shi haka, cikin kirsa da ladabi Rashida keta maimaita ai babu Abinda zai faru indai daga ita ne.

Kazar yace suci saboda shi kwata kwata hankalin sama baya kan kazar yanakan Maryam wacce yaga taka sakin jiki ta kasa sukuni tunda suka dawo.

A ranshi yaji babu daWi da Maryam Win tatashi tace ta ?oshi barci takeji ta nufi Wakin su Halima zata buWe dan taje ta kwanta, kamar ya share saboda Rashida sai kuma yaji bazai iyaba sai yace

"Kije Wakina mana ki kwanta.

?an juyowa Maryam tayi tana dariyar ya?e tace

Ai maman halima ta dawo.

Mazewa Nasir yayi yace

"Ai nasan ta dawo Win ki kwana acen gobe idan Allah yakaimu ita sai ta karSi girki ai.

BuWe baki Maryam tayi zatayi magana sai Rashida wacce ta danne Sacin ranta tayi magana da kyar tace

"Haba,haba, ai babu komai kije ki kwanta Win hakan ma yayi ai, da yau da goben ai duka Waya ne, sai ma kawai tatashi daga falon ta Wauke kazar tare da nufar kichen dashi tunda itama bacin zatayi ba, tana fitowa tayi musu sai da safe ta wuce Wakinta tanata danne Sacin ranta.

Maryam tana ganin Rashida ta shige Wakinta tayi saurin zuwa wajen Nasir tana marairai cewa tana cewa

"Haba masoyina, hakan fa bai daceba, meyasa zakayi haka dan Allah? Kamata fa yayi ace ta kwana a Wakinka saboda ta daWe bata nan.

Kashe mata ido Waya Nasir yayi tare da tashi yana matsota yace

"So nake na kurSi zumar ki mai za?ina, kinsan fa bana gajiya da kur Sar zumar nan.

Dariya Maryam tayi tana zullewa daga ri?on daya kawo mata ta shige Wakin nasa da sauri bayan ta buWe, shima binta yayi a baya yana faWin zan kamaki ne tare da kashe fitulun falon yabi bayan ta.

Duk wan nan Abinda sukayi akan idanun Rashida ne kuma a cikin kunnuwan ta, kuka take tayi tunda ta shiga Wakin tana le?en su, tana ganin sun shige Wakin ta?ara fasa kuka marar sauti harda birgima akan gado tana furta kalmar Allah ya isa, kuma cak ta tsaya da kukan tana kyalkyalewa da dariya komai ta tuna oho.

Shi kuma Nasir yana shiga Wakin ya faWa wanka san nan yafito Maryam ta shiga, kuma koda tafito shafa'i da wuturi da bataiba ta gabatar san nan tayi addu'a ta mi?e ta haye gadon inda Nasir ke jiranta.

Ta rigada ta saba kwanciya akan ?irjinsa shiyasa yanzu ma ta haye ?irjin nasa dan a ?a'idar Nasir kwata kwata matarsa bata kwana da kaya a jikinta sai pant kawai koda kuwa wani Abin bazai shiga tsakaninsu ba, kuma yadda basa saka komai a jikinsu shima baya sakawa sai pant Win amma irin buWaWWen nan.

Tana hawa kuwa ?irjinsa fatar su ta haWu waje Waya take ya wani zabura tare da tureta gefe ya mi?e zaune yana sosa fatar ?irjinsa zuwa cikinsa da yakeji kamar sun saSule saboda ?unuwa.

*KUTSE*

? ?? *PAGE 31*

? ? ? ?? *NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Tana ganin Nasir ya tureta tare dayin wulli da ita gefe guda yana soshe soshen jiki ta zabura, kansa tayo tana kiran sunansa zata ri?esa yayi saurin kaucewa yana sauka daga gadon yana cigaba da susa a haukace kamar wanda aka zurashi a cikin buhun cinnaku, kuka Maryam ta saka tana rarumar doguwar rigar barcinta ta saka tana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'una tare da share hawaye masu ?una.

Da sauri ta nufi inda Nasir ke tsaye yana susa harda goga bayansa a bango kamar wani rago yana zare idanuwa waje.

Hannu Maryam ta saka aka tana subhanallahi innalillahi baban Halima kamar fa ka ?one.

*Nasir*

Idanunsa yakai inda Maryam ke nuna masa yana zare danu tare da buWe baki har yawun a zaba yana zuba ganin yadda ?irjinsa da fatar cikinsa sukayi burWun Wun kamar ya ?one dan sosai fatar ta Wago tare dajan ruwa, hawayen azabar kuWar da jikinsa ke masa kawai yake zubarwa yana kallon Maryam wacce tayi tsuru tsuru cikin tsoro yace.

" Wai dame kika ?onani ne Maryam? Me nayi miki na cancanci irin wannan sakayyar? Ai idan kika dage bakyason ki kwana dani zan ha?ura amma basai kin tilastawa kanki karSata ba har takai ga kin cutar dani, me yasa zaki min haka? .

Shiru Maryam tayi dan tarasa Abinda zata hasaso wanda ya haddasa wan nan lamarin dan ita tasan babu wani abu makamancin Abinda nasir yake tuhumar ta dashi.

Tsawar da Nasir ya daka mata a zafafe yana cewa

"Ba tambayar ki nake ba kin tsura min ido kina kallona? Sai kuma ya ?ara gantsarewa tare da tsugunnewa cikin azaba yace.

Wayyo Allahna tare da ri?e dantsan hannunsa saboda wata irin kuWa dayaji yana masa.

Kuka sosai Maryam take yi tana cewa Wallahi tallahi batasan komai ba dan girman Allah yayi ha?uri tana ?ara matsawa kusa dashi yana ?ara matsawa yana dakatar da ita.

Da yaga ma zata Waga mai hankali banda cutar datai masa acewar sa sai ya Waga murya yana nuna mata hanyar fita yace

"Zoki fita ki bani waje, dame zanji ne? Da cutar da kika ?a?a bamin ko kuwa da wan nan kukan ban zan naki?

Jiki a sanyaye Maryam ta fice daga Wakin tanajan jiki har tafita falo, maimakon tayi Wakin su Maryam sai ta zauna a ?asan kafet na falon ta ?ara saka wani sabon kukan.

Shi kuwa Nasir banWaki ya faWa yana yarfe hannu da tunanin Abinda Maryam ta shafa masa har jikinsa yayi irin wannan ?onuwar da tashin yake, yana shiga ya sakarwa kansa shaya take kuwa ruwan sanyi yafara zuba a cikin jikin nasa, wata iriyar ajiyar zuciya irin mai sanyin daWin nan ce ta suSuce masa dan jiyake kamar an tsunduma shi a rahama.

Sai da yayi wajen awa Waya ruwan sanyi na kwarara a jikinsa dan gani yake idan ya kashe shayar kamar ciwon ?aruwa zaiyi yafi na baya a zaba, dan haka yabar shayar taita zuba har sai da yaji barci yana fusgar sa daga tsayen dayake san nan yafara rage shayar a hankali ruwan yana zuba kaWan kaWan har ta gama mutuwa.

Jiyake idan yakashe ruwan azabar ?unar zata dawo masa, amma wani Abin mamakin sai yaji jikinsa sanyi ?alau kamar baiji ?unar ba sai dai raWaWi  raWaWi da wajen daya tattashi yake masa, haka ya kashe fitila ya kwanta yana tunanin ko a wane irin yanayi maryam take yanzu oho! ?ilama tanacen tana kuka, ya ayyana a ransa yana gyara kwanciyar sa, a ransa yake cewa rabuwa da ita zaiyi har zuwa safiya san nan zai waiwayeta, dan da gaske sai ta faWa masa Abinda ta shafa masa ajiki wan nan iftila'in ya sameshi.

Da kyar ya samu barci ya Wauke shi saboda Wan raWaWin dake damunsa, amma kuma barcin na Waukar sa shikkenan sai ya daina jin raWaWin.

*Maryam*

Ganin zama a falon bazai kaita ba ga kuma barci dake fusgarta tatashi da niyar ta buWe Wakin su Haliman ta shiga tunda har yau bata da Waki a cikin gidan, ta saka hannu kenan zata murWa handle Win sai ga Rashida ta ri?e hannunta tana jifanta da wani kalan kallo na tsana tana mata murmushi.

*Rashida*

Duk Abinda yafaru a cikin idanunta ne domin kuwa tana fashewa da wan nan dariyar tayi saurin fitowa ta laSe a bakin windown Wakin Nasir domin taji yadda zata kaya a tsakanin su, akan idonta Maryam ta kwanta a jikin Nasir, duk wani tu?u?in ba?in ciki dake dam?ar zuciyar ta amma sai ta saki murmushi dan tasan sauran zancen, tana ganin sa ya tureta ya sauka yana soshe soshen jiki ta fashe da dariyar mugunta, taji tausayin Nasir dan tanason sa kuma dole ce tasaka ta jefashi a wan nan halin dan har hawaye ta zubar masa a lokacin daya hau kace yana wan nan susar, kallon Maryam take cikin tsana tanajin kamar ta cafko nonuwan ?ar iska ta tsintsinke su ko zata huce takaicin ganin ta da take tsurara agaban mijinta.

Saurin barin wajen Rashida tayi ta shiga Waki ganin Nasir ya koro Maryam zata fito tana kuka.

Itama Maryam Win le?enta Rashidan takeyi, duk kuma iya zaman da tai a falon tana kallonta ta Wakinta, amma ganin zata shigar mata Wakin yara yasa tayi saurin fitowa ta nufota dan kar ta Wumama musu jiki da zafinta.

*Maryam*

Kallon hannun Rashida tayi wanda ta ri?e nata hannun saboda zata buWe Waki ta shiga, fuskar ta ta kuma kallo san nan cikin dakiya Maryam Win tace.

"Cikani mana.

Hararar ta Rashida tayi tace

"Na cikaki kije ina? Sai kuma Rashidan tayi saurin Wauke hannunta daga na Maryam tana wani yar farwa kuma cikin sha?iyanci tana hura iska daga bakinta zuwa hannun, cen kuma sai ta?ar kyalkyalewa da dariyar mugunta tace.

"Shuuuuuu..... Ya akaji da zafin jiki? Sai ta kuma she?ewa da dariya tace.

"Fire.... San nan ta ?ara hararar ta tace karki kuskure kishigar min Wakin ?a?ana, domin ke wutace mai zafi a cikin wutace.

Sai ta kum she?ewa da dariya tace "I said, fire. Tai mata gwalo ta wuce Wakinta tana mata girgiza.

*Maryam*

Cikin wani irin yanayi tabi Rashida da kallo domin lamarin Rashida ?ara ta azzara yakeyi da gaske, anya matar nan bata samu taSin hankali ba kuwa? Sai ta kuma kallon Wakin Rashidan tana tunanin toya akayi tasan tanajin zafin jiki? Anya kuwa matar nan ba ?ar duba bace?

Fasa shiga Wakin su haliman tayi kawai sai ta juya ta haye kan kujera tree sitter ta kwanta tanajin yadda zuciyar ta take mata tsalle da tunanin halin da Nasir yake ciki.

Tabbas badan kurarin Rashida Maryam tafasa shiga Wakin ba, ta fasa shiga ne saboda tunanin yadda zata ruWawa su halima jiki da zarar hannunta ya taSa jikin su take, shiyasa ta?i shiga ta dawo falon ta kwanta.

*Washegari*

Tun tsakar asuba Rashida ta fito falon ta zauna zaman jiran fitowar Nasir saboda munafurci, tana kallon Maryam a kwance ta takure akan kujera saboda sanyin asubar dake shigowa cikin falon, da akwai wuta shiyasa Rashida ta kunna duka fitulun falon suka haskake ko ina, kallon Maryam kawai Rashida take tana tsine mata a cikin ranta dan har ga Allah idan akwai wacce ta tsana a duniyar ta to bayan Maryam ce, bata ?aunar yarinyar ko mis?ala zarratan, shiyasa da take kallonta takejin kamar ta matse mata hanci har sai taga ta daina numfashi.

Tana zaune tana kallon yadda gari yafara haske amma batako motsaba balle tayi tunanin yin sallar asubar, daman sallar asuba ba damunta tayi ba tafi ganewa tayita da rana gatse gatse ko kunyar Allah bataji.

*Nasir*

Sai wajen bakwai da rabi san nan yafito daga Waki shima dan yanason yaga ya Maryam ta kwana ne dan yasan jiya bata samuyin barci mai daWi ba.

Rashidan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login