Showing 90001 words to 93000 words out of 175193 words

Chapter 31 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

563

kwanaki saboda samun Lafiyar cikinta, gashi babu wani wadataccen ruwa a jikinta san nan jininta ma yayi ?asa shiyasa takejin yawan jiri akai akai da kuma ciwon kai.

Koda ta farko daga barcin da aka sakata na dole sai takalli Nasir wanda ya zuba mata idanuwa yana murmushi, jiyake kamar ya tasheta ya rungume ta ya faWa mata Abinda likita ya faWa masa, wata zuciyar tace masa

"Ai ta sani, kaine dai baka saniba.

Kawar da zancen zuciyar tasa yayi yana shafa kwantancen gashin kanta wanda bata fiye masa kitso ba dan yanzun ma a tsefe yake amma yasha gyara na gaske.

Samira Nasir ya kira yake sanar da ita zancen rashin lafiyar tata dan duk duniya anan kano yasan Maryam bata da kowa sai shi da samiran, shiyasa duk Abinda ya shafi lamarin Maryam yake saka samira a ciki saboda sune makusan tanta.

Sosai samira taji babu daWi domin jin Maryam take tamkar wata tsoka ta jikinta, kallon inna mai zamar mata wankan jego tayi tace.

"Inna wai Maryam ce bata da lafiya har an kwantar da ita a gadon asibiti, shine nace ko zakije ki zauna da ita don Allah har a sallameta tunda kinga yanzu na Wan iya wasu abubuwan da kaina.

Salati inna ta saka tana faWin kai Allah dai ya yayewa Maryam wan to lalurar, yanzu ciwon har yakai ta da kwanciya asibiti? Ai kuwa zanje yanzu ma kuwa , dan haka maza ki kirawo mijin nata kice masa yazo ya Waukeni dan jinyar mace ai sai mace.

Ba ?aramin daWi Nasir ya jiba da Samira ta kirasa take faWa masa sa?on inna, yaji daWi sosai dan haka sai kawai ya mayar da akalar motarsa hanyar gidan Samira dan daman yaje gidan ne ya Wauko su halima san nan ya Wan Webowa Maryam kayan bu?ata.

Sai da ya Wauko inna ya kaita asibitin san nan yace bara yaje yakai su halima gurin mamansu ya dawo, da to inna ta amsa tana shafa fuskar Maryam wacce tayi ?ar kuyas da ita da yake Maryam ba macace mai ?iba sosai ba.

*Rashida*

Ba ?aramin daWin ganin su halima tajiba, dan har ga Allah rashin su da kuma rashin mijinta kusa da ita yana bala'in taSa zuciyar ta, wajen sati guda fa kenan da zuwanta gida amma koda wasa Nasir bai taSa kiranta yaji ya jikinta yake ba, san nan ko a labari bata taSa jin wani yace ya kirasa ba bare ace an ganshi ya wuce kota layin gidan ba, tasan yanzu Nasir ya tsaneta baya son ganinta, ita kanta batasan Abinda yahau kanta tatafi zata ?ona Nasir ba, idan ma ?onawar zatayi ai Maryam ya kamata ta ?ona tunda ita ce mace ta farko data shiga hurumin ta ta Sata mata lissafin dake zane cikin kwakwalwar ta, amma ba komai tasan dole zai wuce dan Nasir bai isa ya iya fushi harna tsawon wata guda da ita batare daya nemeta ba.

Yanzu kuma ganin su halima ba ?aramin faranta ranta yayi ba, dan ta zata tare dashi suke, amma da taji hajja na tambayar Halima babansu sai taji tace wai saukesu yayi a gate ya tafi saboda sauri yakeyi auntay ce bata da lafiya an kwantar da ita a asibiti.

Take murnar Rashida ta koma ba?in ciki zuciyar ta ta shiga har bawa da ?arfi da ?arfi dan idan akwai Abinda ta tsana bai wuce a ambaci sunan maryam da Nasir a guri Waya ba, ita fa ba Maryam kishiyar taba, wallahi yanzu ta tsani duk wata mace mai suna Maryam a rayuwar ta, tana da ?awaye guda biyu masu suna Maryam, tun sanda ya bayyana Maryam kishiyar tace shikkenan ta goge lambar su a wayarta kuma koda sukayi mata magana a chart nunawa tayi ma bata sansu ba san nan tayi blocking Win su bayan ta gurza musu rashin mutunci na babu gaira babu dalili.

*Hajja*

Subhanallahi, meya samu aunty taku ne? Ciwon har yayi tsananin kwanciya a asibiti? Allah sarki Nasiru, kaiiii, wan nan yaro yana haWuwa da jarrabawa a kufe a kufe, daga wan nan sai wan nan? Allah sarki Allah yabata lafiya, Insha Allah zan kirashi na dubata.

Ran Rashida bai so Abinda hajja ta faWa ba, amma ya zatayi? Ita bata isa tayiwa hajja magana ko ?orafi akan hakan ba dan yanzun nan sai ta ?ara mata Sacin rai akan wanda take ciki.

Sauda ta cire daga jikinta tatashi sum sum tayi Waki domin idan bataje tayi kuka ba tanajin zuciyar ta zata iya bombing baki Waya, tana shiga kuwa ta rufe ?ofar tare da sakin kukan ba?in cikin banzatar war da Nasir yayi mata.

Sai da taci kukanta ta gode Allah san nan ta share hawayenta tare da Waukar wayarta ta kira Amina take sanar da ita halin da take ciki .

*Amina*

Shewa tayi tana cewa

"Insha Allah mutuwar tace tazo, matsiyaciyar mace sai kace mayya, ni wallahi nafara tunanin idan yarinyar nan ba mayya bace Rashida, masifa taita samunta amma saboda naci ta?i tafiya gidan su tabar miki mijinki, amma kibari na dawo, Insha Allah ina dawowa zamu Sullo mata tawani hanyar.

Hanci Rashida taja tace

"Sai ca kikeyi wai kun kusa dawowa Amina, tun kafin fa nafara ciwon nan kuka tafi amma ace har yanzu baku dawoba? Gaskiya bana wan nan umarar taku tayi tsawo, kusan sati huWu, baki taSa kaiwa haka ba.

Dariya Amina tayi sosai tace

"Kedai bari ?awata,ina gaban Ubangiji ina wankin zunubai ai, yaushe zan tawo ban gama wankan tsarki ba? Kedai kijirani, ina gama tsarkakewa zaki ganni Insha Allah, amma ?ila sai nan da sati biyu, dan Alhaji yace zaizo yayi umara ta sati biyu sai mu tawo tare dashi .

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke tace

"To dan Allah nidai kiyi ki dawo Amina, abubuwan nan fa sun cunkushe min, ni ina tsoron Nasir ya sakeni wallahi, dan idan ya sakeni ban san inda zan saka kaina ba, dan wallahi zan iya mutuwa muddin ya sakeni akan waccen yarinyar.

Gashi tunda na dawo gida fa babu kira babu aike, ga hajja ta canza min baki Waya ko hira batayi dani daga gaisuwa shikkenan, ke idan kin dawo ma wallahi har maganin wancen mugun zaki saka ayi min.

Mutum kwata kwata babu imani da tausayi a ranshi, tun sanda ya kusa aikani lahira fa har suka koma abuja baya min magana, ko gaisheshi nayi baya ma kallona bare na saka ran zai kulani, ke ran nan fa da yazo gidan dana gaisheshi wallahi bakiga tsawar daya dakamin ba yace wallahi duk sanda ya ?ara zuwa gidan nan na buWe zunubabban bakina nace zan masa magana wallahi sai ya bugemin baki ya zubar min da hakwarana, wai dan zalinci harda cewa wai wallahi ko hakwaran basu zubeba sai ya ban ?are ni ta ?arfin bala'i ya zaremin su sala-sala, kijifa mugu, wai sala-sala kamar ya samu sulalallan nama.

Dariya Amina ta fashe dashi harda hawaye tace

"Kinsan ya Aliyu badai sanin luggar mugunta ba, wallahi kinsan sarai zai aikata Abinda yafi haka.

Tsaki Rashida taja tace

"Au wai dariya ma na baki? Lallai ma Amina, nagode.

Wallahi ba haka bane ?awata, kawai dai sala-sala Winne yabani dariya.

Itama Rashida Wan darawa tayi kaWan dan ita dariyar Aminan ce ta bata dariya, tace wallahi Amina, wai sala-sala, ai shiyasa tun daga ranar ban ?ara kuskuren kallon saba bare nayi masa magana, ke sai na daina fitowa falon ma idan naji yazo, dan zan iya fitowa nayi kuskuren kallonsa yace hararar sa nakeyi ya samun hujjar cin karansa babu babbaka a kaina, to shi nakeso ayi min maganin sa, so nake a juya zuciyar sa a kaina Amina, yadda zai daina yi min faWa ya daina takura min kuma duk Abinda zanyi karya ga laifina.

*****

Kwanan Maryam biyar a asibiti san nan aka sallameta, kuma a lokacin Jamila ?anwar sa tazo gidan nasa domin tunda suka ji Maryam babu Lafiya tana kwance a asibiti tace sai tazo ta dubata, ita take kwana a cikin gidan ita da Nasir amma kullum sai ta dafa abincin nan sau Uku a rana ankai musu asibitin, duk da Maryam ba wani cin abincin take ba amma ai inna tanaci.

*Maryam*

Tayi murna sosai da ganin Jamila domin ko banza taji tana da wani Wan uwa kusa da ita, tanajin daWin yadda Jamila take kula da ita domin ta Wauketa kamar ?anwar ta ba matar wanta ba tunda ta girme ta sosai, shiyasa wataran har kwalla Maryam take tana godiya ga Allah da yabata masoya da yawa, amma a duk sanda ta tuna cewar Rashida bata ?aunar ta takanji komai ya fice mata a rai domin Rashida itace wacce ya kamata tasota su zauna lafiya tunda inuwa Waya kullum suke sha ita da ita.

Haka tunda taji zancen cikine da ita taita murna tana godewa Allah da shikkenan Rashida dole ta ha?ura tunda Allah yayi ikonsa gashi itama zata ajiye kwai a cikin gidan mijin nasu.

Tanason cikin nan ta kuma kwallafa rai a kansa kamar yadda Nasir ya keson cikin ya kwallafa rai shima a kansa kamar yanzu ne za'a fara yi masa haihuwa saboda rawar kai da zumuWin da yake yi.

Ita kanta Jamila ba ?aramar gigita tayiba a lokacin dataji labarin Abinda Rashida ta aikata, kuka taitayi tace wallahi sai ya saki Rashida dan bazata kashe musu shi ba ta mayar dasu marayu gaba da baya, daman Nasir Win suke gani a matsayin uwa uba da kakanni tunda kowa nasu ?asa ta lulluSe idanun su, a wan nan ranar Rashida tasha zagi sosai a wajen Jamila dan da kyar su samira suka rarrasheta tayi shiru duk da suma labarin a binda Rashida tayi ya gama kaWa ?a?an hanjinsu.

Cikin kuka Jamila take cewa

"Muda gidan yayan mu amma bamu da ?anci ko gata idan munzo, ta tsanemu muda yaran mu dan duk sanda mukazo da kukan wula?ancin da take mana muke tafiya, babu damar mu Wan hawo wajen yayan mu ko mu hawo muWan yi hira a saman nan, damun shigo zata fara toshe hanci da ya tsina fuska ta fara feshe feshen turare wai wari mukeyi, wallahi banda yaya lantana tana tausata billahillazi da tuni nayiwa Shegiya dukan tsiya in yaso na dauwa ma a kurkuku.

San nan yanzu dan tana ba?in ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?cikin Allah ya wankewa mana zuciya damu da yayan mu yabamu mace ta gari a cikin dangi shikkenan sai ta nemi kaita kushewa? Wallahi to bazamu yarda ba dan nan gaba wallahi duk Abinda yasamu Maryam sai munyi Shari'a da ita tunda ai ba auratayya ta haWamu da Maryam ba daman can jinin muce kuma ?ar uwar muce.

*KUTSE*

*PAGE 39*

? ?? *NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Duk hanyar da tasan zatabi wajen ganin tajawo hankalin Nasir ya dawo gareta ta bita amma shiru kakeji wai malam yaci shurwa, sosai tayi ?o?arin ganin ta fake da yaransa domin ta samu galaba akansa nan ma shirinta baiyi tasiri ba.

Ranar da yazo Waukar yaran da ya mayar dasu gida su cigaba da zuwa makaranta ma fafur Rashida ?i tayi a cewar ta ba zata bar yaranta a hannun kishiya ta gallaza musu ba, dan tasan Maryam bata ?aunar ta saboda haka bazata ?aunaci wani daya shafeta ba, dan haka wallahi sai dai ya mayar da ita gidansa su cigaba da zama cikin ha?uri ko kuwa yabar mata yaranta a kusa da ita in yaso ita ta cigaba da Wawainiya dasu.

A lokacin da Nasir ya tsinci wan nan text Win nata a wayar sa dariya kawai yayi na jinjina girman fitina irinta Rashida wacce i yanzu da take zaune a gidan su tsawon wata biyu amma hakan baisa tayi laushi ta ha?ura ba, shi ba zaiyi bikon Rashida ba kuma yayi rantsuwa da girman Allah, saboda gaba Waya zamansa da ita ya riga yafita daga kansa dan bazai iya da jarabar taba, shifa yadda yakejin daWin zama da Maryam kamar me ji yake ya ha?ura da wata mace a rayuwar sa muddin Allah ya ?addaro masa hakan.

Baiyi shawara da kowa ba yabi umarnin zuciyar sa yaje super market yayowa su halima siyayya sosai ta makaranta harda Abinda Bama damuwa dashi sukayi ba, yana dawowa gidan hajja ya nufa yana tunanin ta yadda zai bada kayan akaiwa Rashida dan bazai shiga gidan ba, dan yasan idan yashiga Kunyar hajja kaWai ma ta isheshi zuciyar sa ta sauko akan Rashida.

Dan haka take ya Wauki wayarsa ya kira nusaiba autar hajja dan da itane zai aika sa?on nasa, Allah yaso tana kusa da wayar shiyasa yana kira bata daWe tana ringing ba ta Waga da sallama a bakinta tana gaisheshi.

Bu?atar son ganinta ya aika mata san nan tace to, babu daWewa kuwa tafito da zumbullen hijab Winta tunda daman ita ba masoyiya mayafi bace ba.

?ara gaisawa sukayi sosai san nan cikin kunya nusaiba tace da Nasir

"Amm..amm..daman ya Nasir inason na baka ha?uri akan Abinda yafaru tsakanin ka da ya Rashida, dan Allah ka yafe mata ta koma gidanta wallahi sharrin shaidan ne, kuma tace bazata ?ara ba, wallahi ya Nasir bakaga yadda ya Rashida ta shiga damuwa da faruwar wan nan lamarin ba wanda ni shaidatace akan cewar ko barci bata iyawa saboda kuka da kuma ambatar sunan ka, dan Allah ka yafe mata kodan yaran dake tsakanin ku.

Murmushi Nasir yayi tare da zubawa nusaiba idanuwa yace.

Ai nusaiba tuni na yafewa yayarki, kawai dai inason ta Wan ?ara hutawa ta kuma samu nutsuwar zuciya ko zata samu ta zauna lafiya nan gaba, dan haka dan Allah kibar zancen yayarki tukunna zuwa nan da kwana biyu, daman sa?one zan baki ki kaiwa yaranki dan Allah saboda makaranta.

Shiru nusaiba tayi tana kallon Nasir wanda ya buWe Boot Win motar sa yana fito da jibgin siyayyar da yayi.

Sai da ya gama fito da kayan san nan ya kalli nusaiba yana mata murmushi yace

"Saboda makaranta nayowa yaranki siyayya, dan Allah ki gaida min dasu sosai, Nagode da bani lokaci nusaiba, ki isar min da gaisuwa ta a wajen hajja.

Cikin girmamawa nusaiba ta amsa san nan ta kirawo wani ma aikacin gidan nasu tace ya shiga da kayan cikin gidan.

Nasir na tafe yana tunanin yaransa da shau?in son ganin su, domin rabon daya gansu tsawon sati huWu kenan, a kai a kai dai halima takan Wan kirashi su gaisa san nan ta fara bashi ha?uri akan maman su, a duk sanda tayi masa wan nan maganar yakan katseta da cewar ta maida hankali a karatun ta zai kirata zuwa Anjima, haka wataran itama sauda zata kirasa ita sai dai ma ta fashe mishi da kuka tana faWin ya taimaka yazo ya Wauke su su basa son gidan hajja.

Murmushi kawai Nasir yayi yana mai bayyanar da farin cikin fuskar sa a dai-dai sanda ya shiga cikin gidan sa yayi karo da Maryam mutuniyar kirki mai kulawa da dukkan lamuran sa, rungumar ta yayi yana mai sauke numfashi tare da shafa cikinta wanda yaWan turo kaWan ta cikin riga yana mata sannu tare da sakinta yana mai yaye rigar tata yana kallon shafaffen cikin nata wanda girman yaron cikinta yasa shima ya turo yayi dai-dai a tsakiya abin gwanin sha'awa.

Kiss ya sakawar cikin nata yana Wagowa da murmushi da baya barin fuskar sa a duk sanda yake tare da Maryam, yana son kasancewar sa tare da ita domin sanyin ta yana mai saka shi nutsuwa kowanne lokaci.

*****
Maryam

Sai data tabbatar yaci abincin sosai ya ?oshi san nan ya samu hutu Maryam tayi murmushi tana kama hannunsa tana matsawa a hankali san nan tace.

Inason ka dawo min da yarana gida dan Allah saboda nayi missing Winsu sosai wallahi, inajin babu daWi ne a duk sanda na buWi idanuwa naga babu su a kewaye dani, ta ?ara sa tana share hawayen da suka zubo mata.

Tattausan hannunsa ya saka akan kumatunta tare da fara share hawayen dake zarya akan kuncinta yana jijjiga mata kai tare da murmushi yace.

Ki daina kuka Maryam, nima kaina inason ace suna kusa dani amma hakan bazai samu ba a yanzu dai sai dai nan gaba kaWan Insha Allah.

Murya na rawa Maryam tace

Saboda me?

Saboda maman su ta hana Maryam, Nasir yabata amsa yana shafa cikinta.

Hannunta ta Wora akan nasa tana cewa

"Ka dawo da mamansu haka, zaman yayi yawa baban Halima, itafa rayuwa kullum darasi ake ?ara Wauka a cikinta, ha?i?a kuma i yanzu nasan mamansu ta ?ara samun darasin da bazata kuma gangancin maimaita kuskuren taba.

Hannunta nasir ya saka a nasa yana rausayar dakai yace

"Kayya maryam, Rashida tayi nisa sosai, banjin akwai ranar da zata zubar da mugayen makaman data Wiba fa, kedai kawai abar zancenta Maryam, nifa wallahi zamana haka babu ita yafi min daWi sosai da sosai.

Hawaye maryam ta share tace

Bazan ji daWi ba kuma bazan taSa yafewa kaina ba muddin ya zamana nayi sanadiyyar rabuwar ka da uwar ?a?anka, kun jima kuna gina soyayyar ku tun daga ?uruciya har zuwa auren ku, wallahi na kwashi babban zunubi daya kasance nashiga tsakanin ku har nayi sanadiyyar Satawar ku, dan Allah ka yafemin ya Nasir, Maryam ta ?arasa tana kuka sosai dan da gaske Abin yana mata zafi kuma yana taSa zuciyar ta fiye da yadda mai tunani zaiyi nashi tunanin.

Rarrashinta Nasir yafara yana share tasa kwallar a fakaice saboda kada Maryam tagani hankalin ta ya ?ara tashi , ha?i?a idan yace Rashida tafita daga zuciyar sa yasan ya yaudari kansa, san nan idan yace tunaninta na hanashi sukuni wataran sai aga kamar yasamu ta Suwane musamman yadda ta kusan kaishi lahira akan kishi, toya zaiyi da ransa, shikansa yasan son da yakewa Rashida jarabtace ta Ubangiji daya halicci zuciyar sa, tabbas son da yakewa Rashida bayawa Maryam shiya sani, amma itama Maryam Win yana sonta da ?aunar ta, haka zalika girmanta da kuma mutuncinta da yake gani yatake ya mur?ur kushe na Rashida saboda kyawawan halayen dake gareta.

*Rashida*

Cikin mamaki take kallon alert na dubu Wari da Nasir ya saka mata a cikin account Win ta, kuma juyawa tayi tana kallon tulin kayan daya kawo Wazu wai na makarantar su halima, itafa abin ma mamaki yake bata wallahi, wai me Nasir yakeji da ita ne? Ko kuwa yana nufin bazai mayar da ita Wakinta ba shiyasa yayi wan nan siyayyar? San nan ga uban kuWi daya turo mata, to wai me zatayi dasu ne ? Itafa siyayya ko kuWi ba sune matsalar taba, matsalar Waya ce shine ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login