Showing 111001 words to 114000 words out of 175193 words

Chapter 38 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

551

sur kulle mai duma yayi a hannunsa sai kuwa ya she?e da dariya yace

"Ta haihu, sai ya kuma fashewa da dariya ya kuma cewa, ta haihu.

Zaro ido sukayi baki Waya suna cewa

"Wacece ta haihu mai duma?

"Kishiyar ki mana, mai duma yafaWa yana nunawa Rashida da tafin hannunsa, abin al-ajabi sai ga Maryam zaune akan gado kusa da babyn data haifa tana gyara masa kwanciya.

Cikin tashin hankali Rashida ta mi?e tare da dafe ?irji tace.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una na shiga uku, wayyo Allahna, take hawaye suka fara ambaliya a cikin idonta.

Shikuwa mai duma wata irin tsawa ya dakawa Rashida yace

"Anan kike kira mana Allah? Mun barranta dashi bama aikin Allah a nan sai Abinda ya hanamu

(Wa iya zubillahi, Allah ka hanemu taSewa ka yafe mana).

Irin tsawar da mai duma ya sakarwa Rashida yasa hartaya cikin bukkar tasa sai da ta Wan girgiza, a tsorace Rashida ta koma ta zauna maman mu ta dam?e mata hannu tana mata nuni data bashi ha?uri, ha?urin Rashida tabawa mai duma, san nan ya sassauto da fushinsa yace

"Har kibar wajen nan kiyi ta gasawa kanki mintsini mai zafi shine hukuncin ki, idan kuma ba hakaba zamu saka ?a?an aljanu suyi ta mintsinin ki har sai sun farfasa miki fata.

Tunda Rashida tafara mintsinin kanta take kukan azaba da hawaye masu Wumi, wani abin haushin kuma mai duma sai da ya tara ?o?onsa a jikin fuskarta saboda hawayen nata ya dunga Wiga a ciki.

Magana yafara cikin karaji yana cewa maman mu.

"Wan nan yarinyar ta Sata mana aikin mu na yau tunda ta ambaci Allah a wajen nan, komai namu ya lalace saboda haka yau ba zamuyi aiki ba sai gobe da yamma, dan haka goben da yamma ina tsammanin ganin ku, san nan abu na gaba shine

"Idan zaku tawo ta tabbatar da tayi futsari ta Wauraye hannayenta da kuma ?afafunta, kutashi ku bani waje.

Da hanzari Rashida ta mi?e tafita daga bukkar tana kallon yadda fatarta tayi jawur da shatin mintsinin datai ta gasawa kanta, suna tafe da maman mu tana kuka tana cewa ita ta ha?ura bazata iya masifa ba.

Sai da sukaje gida maman mu take cewa Rashida

"Banda shashanci irin naki har yaushe zaki biyewa banzar zuciyar ki kice wai kin fasa magani? Ita kishiyar taki ubanwa yace miki a zaune take? Har dai ai basai na faWa miki ba tunda gashi nan ta kame miki miji da ?a?anki a hannu sai yadda tayi dasu, yau kwananki nawa da zuwa garin nan? A lissafina kwanakin ki huWu kenan, tunda kikabar gidan batare daya saniba ya kiraki yaji kina ina? Bai kira ba ai, suma su hajjan ai babu wanda ya nemiki a cikin su, kinga kenan gaba Waya basa tataki kuma sun nuna miki dake da babu ke zasuyi rayuwar duniya, dan haka ko ke kince bazakiyi magani ba ni zan tsaya miki kai da fata nayi miki tunda ni uwarki ce mai son farin cikin ki.

Ita dai Rashida ranar haka ta wuni ta kwana da da raWaWin zafin mintsinin nan, barcin ma da kyar ta iyayi saboda yadda take jinyar zuciyar ta na mata suya na haihuwar da mai duma yace Maryam tayi, komai ta haifa oho? Namiji ne ko mace waya sani?

Washegari sai misalin ?arfe biyu suka fita daga gida zuwa wajen mai duma, da yake tafiyar akwai nisa sosai sai ana kiran sallar la'asar suka isa, duk sun gaji ga Rashida daman ita muddin ta shiga rana haka jikinta zaita ?ai?ayi ?ilama daga ?arshe borin jini su bar bazo mata.

Mai duma yana kallon Rashida ya sake fashewa da dariya yace

"Ya kikaji da tsatssaman jiki? Da sauri ta sunkuyar dakai tace

"Zillah tuni ya bani lafiya mai duma.

She?ewa yayi dariya yace

"Tabbas zillah zai dubeki yarinya meke tafe dake?

Anan Rashida ta zayyanewa mai duma yadda takeso ayi da Maryam da kuma Nasir harda su hajja baki Waya, kai har taya dangin mijinta bata bari ba.

Tashi mai duma yayi yafara kewaye ta da wutar ?o?on dake ciki sau bakwai san nan ya zauna yace.

"Kishiyar ki bazata taSuba yarinya, na duba naga ta yadda zan samu wata ?ofa ko ?ar mitsitsiyace wajen tura mata aikina tunda tana cikin jinin haihuwa amma abin ya faskara, amma bazamu sare ba, yanzun nan zan tura mata wani ?ullin dazai ta kewayata koda yaushe, zai ta kewayata ne har lokacin dazai samu wata ?ofar shigarta, to a san nan dole aiki ya cita ko dame take ta ?ama, kuma ?a mace ce kishiyar ki ta haifa, san nan akwai saura nan gaba wanda muddin tana raye to zataita haifosu amma mata saboda mijinki bashida kwan haihuwar Wa namiji.

Zan mallaka miki mijinki sai yadda kikayi dashi, haka yaranki babu mai ?ara kusantar inda kishiyar ki take.

Ran Rashida fess take kallon mai duma tana tunanin bata mintsini kanta a banza ba kenan, amma Abu Wayane yaso Sata mata rai koma tace ya Sata mata shine

"Dayace wai Maryam indai tana raye zatai ta haihuwa, to a kasheta mana ko kuma a lalata mahaifar ta, batayi wata wata ba ta shaidawa mai duma ?udirinta, nan take shima yace mata.

"Mutuwar ta ba yanzu ba yarinya, kuma mahaifarta bazata lalatuba, amma abu Waya zan baki muddin kikayi amfani dashi to mijinki ya daina kusantar kishiyar ki har abada, koda kuwa yanason kusantar tata zillah bazai bashi damaba domin zamu kashe gabansa indai yana tare da ita.

Anan mai duma yayita gudanar da mummunan aikin sa da zai samu Maryam da Nasir.

Ran Rashida fess suka koma gida bayan ta zazzagewa mai duma duka kuWin dake jakarta dan tace komai ta bashi bata biyashi ba, kuma indai har bu?atarta ta biya to tabbas zata dawo da wani kwamashon arzu?in mai ban mamaki wajen mai duma.

*Maryam*

Ba ?aramar wahalar na?uda ta shaba wanda daga ?arshe aka gano cewar bazata iya haihuwa ba sai dai ayi mata tiyata a ciro Wan dake Cikin ta domin yayi girman da bazata iya haihuwar saba.

Babu yadda Nasir ya iya a san nan ya kira ya Mansur yake faWa masa san nan ya kira umman Maryam ita ma ya faWa mata domin su tayata da addu'ar Allah yasa ayi lafiya a fito da ita lafiya, sai da akayi komai daya kamata aka shiga da Maryam Wakin tiyata take kuma babyn yace bai san wan nan ba bayason a yanka uwasa.

Nan da nan kuwa Maryam ta hautsine da wani sabon na?udan domin wan nan karan haka na ?udar tatawo gadan gadan, kuma cikin hukuncin Ubangiji sai gashi a lokaci ?an?ani Maryam ta santalo Wanta namiji mai kama da Nasir sak, murna likitocin suka hauyi kafin daga bisa suka gane akwai wani Wan, nan da nan shima Maryam tafara na?udar sa, bata wani daWe tanayi ba sai kuwa gashi ta kuma santalo yarinyar ta mace mai kama da Nasir itama.

Sosai likitocin suka kiWime da murna dan suma daman bawai sunason yiwa mace tiyata bane sai dai kawai idan dole ta shigo

Murna dajin daWi awajen dangi da abokanan arzu?i ba'a magana, domin a washegari ne ya Mansur da matarsa har da umma suka tawo dan tace tabbas tazo wajen Maryam taga ?an tagwayen jikokin ta, suma mutanen rogo a washegarin suka nufo kano domin dama sunso zuwa da salla amma da sukaji Maryam ta kusa haihuwa sai kawai suka bari har zuwa ta haihun.

Shima Nasir rasa inda zai saka kansa yaji daWi yayi domin ji yake kamar ba'a taSa yi masa haihuwa ba sai a wan nan karan, murna da Wauki rawar kai babu wacce ?an barka basa gani a wajenshi domin daina fita kasuwa yayi ya zauna ana zaman daSaron dashi.

Kwana biyu su umma sukayi sukace zasu juya sai ana gobe suna zasu dawo, anan maryam ta kacame da kuka tana ro?ar umma akan ita ta zauna dan Allah sai tayi arba'in ta tafi.

Sam umma ?i tayi tace ga zulai nan tasan zata kula da ita ala barshi idan tazo sunan sai ta zauna har arba'in Win, da wan nan maganar ta kwantar wa da Maryam hankali harta saki ranta suka rabu suna farin ciki.

Kididima da zirgili da shirye shirye a wajen samira kuwa ba'a magana, tunda Maryam ta haihu tayi busy dan shi kansa doctor sai ido ya kawo ya zuba mata, kullum sai taje, kuma da sassafe take fita bazata dawo ba sai dare, wani abin dariyar ma a wajen Doctor da samira ta shirya kayanta tsaf ana i saura kwana biyu suna tace masa tatafi gidan Maryam sai bayan kwana biyu da suna zata dawo, sata a gaba yayi yaita dariya yace.

"Wai dan Allah da gaske kike? Kai samira ta Waga tace Eh mana, ai kasan duk duniya Maryam bata da wata ?awa Aminiya kuma ?ar uwar dazata shiga tafita a cikin al-amuranta saini ko? Kaga danai ta zarya ana gulmata a unguwa ai gwara na tattara na tafi cen na tare idan an gama hidima na dawo.

Girgiza kai Doctor yayi yace

"Rigimam miyar matata, yanzu fa dazan hanaki sai kiga duk duniya ban taSa yi miki wani abin Alkairi bako?

Girgiza kai samira tayi tana dariyar ya?e dan har ga Allah sai da gabanta ya faWi da wan nan maganar tasa tace

"Nina isa nayiwa oga mummunan kalami? Ai dayake nasan kaiWin Mutumin arzi?i ne bazaka taba hanani ba shiyasa ma na shirya, dariya doctor yayi yace to shirya na kaiki, Allah yasa kuyi suna lafiya ku gama lafiya.

*Ranar suna*

Kowa yaga Maryam sai ta birgeshi ya kumaji yana son kasancewa da ita, Allah yabata wani kwarjini da kuma farin jinin jama'a, tayi kyau sosai ita da ?a?anta wanda da taimakon samira suka sha wankan ?an gayu na kece raini, anko sukayi ita dasu halima dan yaran sosai sukeji kamar maman suce ta haihu.

har taya su hajja sai da sukazo barka yau kuma ta turo nusaiba suna dan ya karimatu bata nan sun tafi umara ita da mijinta da yaranta duka.

Shima Nasir bai fita a ranar ba domin shima haWa ?ar walimar sa yayi dashi da abokanan sa.

Masha Allah yara sunci sunan iyayen su.

"Namijin shine aka sakawa suna.

"Nasir Nasir Ibrahim wanda Maryam tayi masa la?abi da (mahbub)

"Ita kuma macen aka saka mata suna.

Maryam Nasir Ibrahim wacce Maryam tayi mata la?abi da (muhibba).

Suna yayi suna san nan taro yayi taro sai dai ace Allah yabawa mai jego lafiyar shayarwa sukuma yaran Allah yaraya su da imani.

*Mafari*

Tunda Maryam ta haihu ta saba kullum bakinta Wauke yake da karatun Al?ur'ani da kuma azkar na safe da yamma, koda ba?i tayi bakinta baya shiru da hailala da salatin Annabi a zuciya, tasan tana jinin haihuwa kuma bata da damar salla ko kuma ta ri?e Al?ur'ani, wan nan yasa take iya ?o?arinta wajen ganin bata yar da ibadarta ba kamar yadda wasu masu jegon sukeyi.

(wasu masu jegon da zarar sun haihu shikkenan fa an ajiye ibada a gefe da duk Abinda yashafeta har sai sun tsarkake jikin su, wasu ma koda sun tsarkake jikin nasu tofa saboda yawancin wasan da jinin ke musu har zuwa arba'in wasu sittin shikkenan sai su jingine ibadar gefe har zuwa kwana sittin Win nan ba'a waiwayar ta, gaskiya mu gyara dan ba haka Musulunci ya koyar damu ba).

Wan nan ranar suna ta ?an biyun Maryam ta kasance rana mafi farin ciki a rayuwar ta dama duk wani mai ?aunarta, a wani Sangaren kuwa ta kasance rana ce mafi ba?in ciki saboda abin firgice da ba?in cikin daya samu Maryam dama duka mai ?aunarta.

Tun ana gobe suna Maryam take Wanjin faWuwar gaba kaWan kaWan, dataji zata dafe ?irji tana addu'a a ranta sai kuma ya saki, ranar suna kuwa ai sai ta shagala da sabga har taya azkar Win safiyar ranar sai ta manta batayi ba bare na yamma saboda sabgar tafi tun batsa a lokacin.

Tunda kuma ?an suna suka watse ya zamana sai ?an uwa, sai Maryam takejin jikinta irin babu daWin nan kamar dai gajiya taci ?arfinta, gashi wani barci takeji dan haka da kyar tabari akayi wankan daren nan ta nemi waje ta kwanta saboda ta Wan matse.

*KUTSE*

*PAGE 48*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Umman Maryam*

Kuka take harda shasshe?a saboda yanayin ciwon da Maryam ta tsinci kanta daga haihuwa, daman haka ne, tasan irin hakan takan faru da mata da yawa bayan haihuwa, wasu dasun haihu sai su haWu da lurura, wasu kuma sai bayan suna, wasu kuma bayan arba'in abin yake fara samun su sai suyita wahala ga shayar wa sunayi, amma tunda takejin case Win masu haihuwa tsakani da Allah bata taSa jin makamancin irin na Maryam ba, gashi dai yau satinta biyu kenan kwance a asibiti bata uhummm bata uhummm san nan komai sai anyi mata, sai dai a kwantar a tayar ga idanunta da suka Wan juye kuma bakinta ya karkace gefe, bama iya nan ba dan har fuskar tata ta shaguSe gefe guda.

Shi kansa ruwan nonon nata ya ?afe ya daina zuwa tunda tafara ciwon nan sai madara ake damawa yaran.

Hawayen da ya?i daina zubowa umma ta share tace.

Haka ke kuma jarrabawar taki tazo Maryam? Wan nan wane irin ciwo ne wanda ake ta magani amma abu kamar turi? Sai ta kuma kallon Nasir da duk yabi ya rame saboda fargaba tace.

Su kuma waWan nan me sukace?

Ajiyar zuciya Nasir ya sauke ya kalli umma cikin rauni yace

"Suma dai magana Waya suke furtawa cewar hawan jinine yayi mata mummunan kamu, amma umma ina tunanin gaskiya Waukar Maryam zanyi nafita da ita waje koma dace acen dan wan nan ciwon yana girgiza min zuciya ta, ya ?arasa yana saka kukan tausayin Maryam da kuma na yaran nata.

Kai umma ta girgiza tace

"?awai niyar zatayi yawa Nasiru, kawai a shawarata a barta anan Win muga Abinda hali zaiyi amma yawan canza asibitin ai bashi da daWi.

Kai Nasir ya Waga badan ranshi yaso ba yace

"Shikkenan umma Allah yasa a dace Win.

Da Amin ta amsa tana mai kallon Maryam da tunanin Abinda ya sameta a daren sunan ?a?anta.

*****

Barci sosai ke fusgar Maryam har bata iya gane lamura, dan dakyar ta iya tsayawa akayi wankan dare kafin ta kwanta domin ta Wan matse, tana kwanciya kuwa barci mai nauyi ya Wauketa, batajin daga sanda ta mallaki hankalin kanta zuwa yanzu akwai ranar data taSa kwanciya batare da tayi addu'ar barci ba, wan nan yasa take tunanin rashin yin addu'ar tata ne yasa taketa mugayen mafarkai kuma takeji kamar ana janta, hamma ta saki bayan ta farka a furgice tana kalle kalle, wani Wan duhu duhu ta gani yana ratsowa Wakin nata, futular a kunne take shiyasa take ganin mabayyanin duhun dake ratsowa yana tawowa inda take.

Da sauri tafara ?o?arin tashi dason kiran sunan Allah a bakinta amma wani nauyi ya danne ?irjinta zuciyar ta da bakin nata baki Waya , hakan yasa ta dunga zuba kakari jin an sha?e mata wuya ta kasa yin kakarin, da a zama ta sauko daga gadon da ?arfinta tayo waje tana kwara ihu, a wan nan dai-dai lokacin shi kuma ba?in aljanin da aka turo mata yayi sanadiyar shiga jikinta nan kuwa Maryam ta faWi a wajen babu numfashi.

Shikkenan fa tun daga ranar take fama da jinya mai tsananin da bata magana bata kallon kowa san nan bata iya motsi komai sai an mata, asibiti na farko da sukaje ca sukayi musu hawan jinine yayi mata yawa shiyasa ta haWu da faralayis, asibiti na biyu ma haka sukace haka wan nan da Maryam take kwance.

?agowa umma tayi a sanda taji kukan muhibba na tashi a hannun ya zulai , kar Sarta umma tayi ganin zulai na niyar sauko da mahbub daya fara mutsu mutsu a bayan shima, da yake akwai komai na kayan madarar su sai ya zulai ta haWa musu kamar yadda likita ya nuna musu ta bawa umma ta muhibba ita kuma ta bawa mahbub, a duk sanda Nasir ya kalli yaran nan sai yai ta kuka yana tausaya musu, yanzu shikkenan daga haihuwar su lalura ta hanasu sha?uwa da uwarsu? Babu nono babu Wumin jiki, shikam gaskiya yayi ala wadai da wan nan ciwon faraWWaya daya samu Maryam, amma babu komai indai akwai asubitoci da kuma magun guna a duniyar nan ya tabbatar da cewar zaiyi iya ?o?arin sa wajen samawa Maryam lafiya da yardar Allah .

*Rashida*

Tana zaune ne kawai a garin agadez badan tanajin daWi ba, itafa hankalin ta baki Waya yana kan mijinta da kuma yaranta, bata damu da halin da Maryam zata shiga ba, koma mutuwa zatayi ita bai dameta ba dan wajen sati kenan da suka koma wajen mai duma yake nuna musu Maryam a kwance kamar gawa ana jujjuya ta, wan nan ranar barci Rashida tayi harda munshari dan tunda Maryam tazo gidan nan bata taSajin nutsuwar zuciya ba sai wan nan ranar data ganta kamar gawa ana sarrafa ta.

Yanzu kawai zaman jiran zuwan Nasir takeyi, dan mai duma ya tabbatar mata da cewar an gama da babin Maryam saura na Nasir, shi kuma Nasir ta kwantar da hankalin ta tana zaune zaizo gareta da mahaukaciyar soyayyarta wacce ko iyayen sa na raye tace ya yankasu da hannunsa zai cika umarnin ta, domin ya riga yayi masa kiranye.

Kuma ita shaidace domin bayan kiran da mai duma yayi masa itama sai da ya mallaka mata haya?i a hannunta ta ri?e, bayan ta ri?e haya?in daketa tashin turiri sai yace taita kiran sunan Nasir har sau bakwai, sai data kirasa sau bakwai Win san nan yace ta saki haya?in hannunta ya tashi sama, duk umarnin da yabata dai haka tayi to shi yasa take da ya?inin dole Nasir yazo gareta su koma gida su shinfiWa rayuwar su susu kaWai.

*Zita*

Ri?e hannun Rashida tayi wanda yaji jan lallan sihiri san nan ta kalli ?afar tace.

Masheri Rashida kinga kuwa yadda lallan nan yayi miki kyau? Gaskiya ko macace ta ganshi wallahi sai yabata sha'awa ballantana namiji, tabbas nasan idan mijinki ya ganki suma zaiyi masheri.

Dariya Rashida ta saka tare da bawa zita hannu suka tafa tace.

Allah ko ?anwata? Kai zita ta Waga tace wallahi masheri, amma dan Allah idan zaki koma kitafi dani inason nayi makarantar boko dan Allah.

Shiru Rashida tayi na Wan lokaci san nan ta kalli yarinyar da dudu bata wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login