Showing 84001 words to 87000 words out of 175193 words

Chapter 29 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

560

makaranta, san nan ta ?arasa fita.

Itama ya karimatu fita tayi dan daman tanason Webo wasu zannuwa data wanke shine tatafi Webowa.

Tana fita kuwa Rashida ta kama hannun Nasir tace

"Nasan kana nan kana cin amanata Nasir, banason kana kwanciyar aure da wacce yarinyar zuciya ta batamin daWi, dan Allah idan ma kanayi ka daina kaji, kayi ha?uri kabari na warke idan yaso komai kakeso zan maka Insha Allah.

Shi Nasir abin nata ma dariya yake bashi, dan haka yasa sai da ya dara san nan ya ?ure gaban Rashida da ido wanda yayi wani iri, baki ya kwaSe cikin kyankyami yanaji a ransa ai baya tunanin ko Rashida ta warke zai iya cigaba da mu'amala da ita a yadda gaban nan nata yagama ruSewa yayi damage, har wani yammm yakeji tsigar jikinsa na tashi sai kawai ya cire hannunsa daga nata yace.

"Bakya bu?atar wani abu? Inason zanje kasuwa ne ana jirana.

Hawaye ne suka zubo daga kurmin idanun Rashida tace

"Babu wani jiranka da akeyi a kasuwa malam, kawai cin amanata kakeso kuje kuyi kaida waccen yarinyar mai zubin kunkuru.

Juyawa Nasir yayi batare da yace komai ba yafice yana nemawa Rashida shiriya dan fitinar Rashida ?arshe ce, tana kwance a gadon asibiti amma zuciyar ta bata daina fitinar ta akansa ba.

*Hajja*

Kallon malam lawal tayi tace

"To yanzu ya kake ganin za'ayi?

*Malam lawal*

Kai ya sauke ?asa yace

"Yanzu dai akwai wani aiki da zamu tafi jigawa nan da awa guda, kuma daman ni kawai suke jira, to shine nace idan bazaki damuba zamu bari zuwa nan da kwana uku sai naga jikin Wiyar taki, amma ga wan nan a fara bata tanasha kuma ana yayyafawa a jikin naman daya tsiro mata, Insha Allah kuma ina dawowa zan zo naga jikin nata.

Godiya sosai hajja tayiwa malam lawal san nan ya dire mata ?atuwar galan wacce take cike da ruwan tofi yatafi cikin girmama juna.

Hijabi hajja ta saka tare da fitowa ta umarci driver daya Wauko mota su tafi asibiti wajen Rashida.

Koda suka ?arasa haka hajja ta tarar da Rashida tana aukin kuka harda su majina, ga ya karimatu ta zuba mata idanu ta buga uban tagumi tana kallon ta.

Da sauri hajja ta ?arasa wajen Rashida tana salati tana tambayar ya karimatu Abinda akayi mata take wan nan kukan fitar hayyacin ?

Girgiza kai ya karimatu tayi tace

"Wallahi babu Abinda akayi mata Hajja, wai kawai Saboda Nasir yazo da kishiyar ta takawo abinci shikkenan ta tasa bala'i tanata kuka wai basu damu da ciwon taba kuma suna cen sunacin amanar ta.

Zaro ido hajja tayi tana nufar goshin Rashida ta dafa tace

"Yanzu akan wan nan Abin zaki zauna kina wahalar da kanki Rashida? Wai yaushe zaki daina Worawa kanki damuwa ne? Inafa tsoron ranar da jininki zai hau ko ki kamu da ciwon zuciya marar warkewa saboda takura zuciyar ki da kikeyi, kiyi ha?uri kinji ?ata, Insha Allah zaki cinye jarrabawar da Allah ya Wora miki dan ita kishiya ai jarrabawa ce.

?an yun ?urawa Rashida tayi tana rungume hajja tana cewa.

"Hajja bakiga yadda suka shigo suna nishaWi ba, kalli fa halin da nake ciki hajja, ai kamata yayi naga Nasir ya rame yafita hayyacinsa saboda ciwona da kuma rashina a kusa dashi.

Kai hajja ta Waga tace, kuma haka ne, amma Abinda na lura dashi Nasir mutumin kirki ne mai kuma dauriya da cinye damuwa, amma yadda yadamu dake Win nan ai da ace bashi da juriya wallahi da tuni ya rikice ya gigice, amma kiyi ha?uri kinji, kuma idan kika kwantar da hankalin ki Insha Allah kece gaba wajen Nasir har abada.

Da wan nan kalaman hajja ta samu kan Rashida har tayi shiru tana tunanin Nasir da Maryam da kuma aukin sauke ajiyar zuciya.

*Maryam*

Koda Nasir ya sauketa a gidan samira godiya taita masa saboda ba haka sukayi dashi ba, sunyi dashi zai rage mata hanya ne sai zuwa Anjima yaje ya Waukota, amma sai kawai yace bari ya kaita yaga Wan gidan samiran domin idan ya dawo bazai shigaba kawai fitowa zatayi su tafi.

*Samira*

Taji daWin ganin maryam da Nasir cikin farin ciki, domin rabon dataga Nasir Win ma ta daWe, dan ko gidan taje tofa ba ganinsa take ba sai dai tabada sa?on gaisuwa a bashi.

Gaisawa sukayi da ya Nasir yayi mata barka san nan daya tashi tafiya yabata dubu goma yace tasai wa yaro riga san nan yatafi.

Hira Maryam da samira sukayi sosai kuma koda suke hirar bakin Maryam bai buWe tabawa samira labarin halin da Rashida take ciki ba, kuma badan komai ba sai dan ai cutar Rashida ba abin bazawa bane tana kallon wan nan a matsayin sirrinta da kuma siirin mijinta, abin bai shafeta ba kuma koda ya shafeta bai kamata ace komai sai ta faWa ba, dan ko sanda tayi fama da zafin jikin nan bata faWawa kowa ba sai Allah wanda ya ?agi cuta da kuma waraka.

Sai wajen ?arfe huWu san nan Nasir yazo ya Wauki Maryam suka tafi gida, yanason yaje asibitin kafin ya koma gidan dan bayajin idan yaje zai iya fitowa yaje Win dan yau a gajiye yake, kuma yanason wan nan daren yazama na musamman tsakanin sa da Maryam dan rabon dasu keSe tun da yaji wan nan zafin na jikinta, tsoron kusantar ta yakeyi saboda kar yaje garin neman gira a rasa idanuwa, karyaje garin tsome ya fito a salube, amma kwana biyun nan ya Wanyi romance yaji babu wan nan zafin, dan haka yanzu ma yanada ya?inin tsoman bazai zame masa matsala ba, dan haka sai yace bara yaje asibitin sai suyi gida.

Girgiza kai Maryam tayi tace

"Kayi ha?uri yallaSai, bawai na?i tataka bane, amma ba dani zakaje bako? Saboda me? Nasir ya faWa yana kallon Maryam.

Saboda ai a gabanka tace bata bu?atar na ?ara zuwa wajenta ko? Dan haka nidai dan Allah ka ajiyeni a gida san nan ka wuce.

Asibitin yafi kusa da gidan samira, kuma yana daWan nisa da gidansa shiyasa yaso ya biya kafin yatafi gidan.

Amma jin Abinda Maryam tace sai kawai ya tsaya yace, idan munje ai a cikin motar zaki zauna ni sai na shiga nafito.

Girgiza kai Maryam tayi tace

"Baza muyi haka dakai ba yallaSai, kadai ajiyeni na hau napep sai na ?arasa, kuma kaga su halima sun kusa tasowa daga makaranta karsu dawo ba kowa a cikin gidan.

Da wan nan uzurin Nasir ya bawa Maryam kuWin napep yace taje gidan shi bara yaje ya dawo, cikin zolaya kuma yake cewa ta tanadar masa kanta kafin yadawo dan yau kwana zatayi kashe arna.

*Rashida*

Wata iriyar jijjiga ta dungayi a sanda hajja ta bata wan nan tofin ta farasha, badan komai ba saboda tana kurSar ruwan taji wani zafi a ma?ogaronta kamar ana babbaka mata ?irji da ma?ogaron ta, san nan kuma ana yayyafa mata a gabanta nan ma wani zafin ya ?ara ziyarar ta da kuma ?afafunta, wani irin haya?ine ya dunga fita a ko ina na jikinta nan da nan kuwa jikin nata yayi wani irin jajawur kamar an tsomata a cikin ruwan zafi.

Cikin tsoro hajja ta yar da galan Win ai kuwa sai ga shi galan Win ta fashe ruwan ya watse a wajen ya mafara gangara yana ficewa tare da gangarewa wajen shukar bishiyoyi.

Rike hajja ya karimatu tayi tana jijjigata tare da rungume ta a cikin jikinta ganin ta tsorata sosai har jikinta yana rawa, kan kujerar gefenta ta zaunar da hajja tana mata fifita dan gumi tuni yafara tsattsafo mata.

Ita kuwa Rashida wan nan ihun ta cigaba dayi tare da kakari tana ri?e ma?ogaronta da yake neman fashewa, bai fashe Winba sai wani aman daya yun?uro mata tafara kelayashi wanda babu komai a cikinsa sai tarin zaruruwa a duddun?ule jajaye.

Ganin halin da Rashida take ciki yasa hajja tatashi daga kan kujerar duk da har lokacin jikinta rawa yakeyi ta nufi wajen Rashida tana addu'ar duk datazo bakinta.

Sa'a Waya, sa'a biyu suka wuce.

Rashida ce kwance a jikin hajja tanata mai da numfashin wahala, domin koda tagama wan nan shan a zabar sai kuma cikin iKon Allah kumburin ?afar yafara sacewa ?urajen ma suka fara Sacewa, haka wan nan kumburin da ?asanta yayi shima ya koma sai kaWan kuma ?urajen kai suma sun baje gaba Waya.

Ajiyar zuciya kawai Rashida ke saukewa saboda salamar data fara samu, kallon yadda al-amarin ta ya fara saisaita sai kawai Nasir wanda zuwansa ya tsinci lamarin yacewa hajja.

"Hajja daman fa ni ina tunanin wan nan ciwon nata kamar bana asibiti bane, to amma Abinda yasa nayi shiru saboda shi neman magani anayinsa ako inane, kuma ganin wan nan al-amarin shi yasa nace ko zamu nemi sallama ne mu koma gida inyaso sai mu koma yi mata na gidan tunda gashi Alhamdulillahi sau?i ya fara samuwa.

*Hajja*

Kai ta jijjina tace " tabbas wan nan haka yake Nasiru, nima maganar da nakeyi kenan a cikin raina, domin tabbas wan nan ciwon bana asibiti bane na addu'ane saboda haka jeka maza ka faWawa likitan ya rubuta mana sallama mutafi gidan.

Tashi Nasir yayi yanajin daWin gano bakin zaren ciwon Rashida da akayi.

*Ya karimatu*

Yana fita tabi bayansa da harara san nan ta kalli hajja tace

"Wallahi hajja wan nan ciwon na Rashida jifane, wallahi daga gani jifane kishiyar ta tayi mata Hajja, kinga fa Wazu da tazo daman fuskar nan tata da murmushin jin daWin ganin Rashida da tayi a ciki, dan haka wallahi kafin Rashida ta koma gidanta dole ne ayi mata ?ai?ayi koma kan mashe?iya san nan a dafata ta dahu yadda asiri bazai kuma kamata ba.

Wata iriyar harara hajja take jifan ya karimatu dashi dan magan ganun ta ba ?aramin haushi suka bata ba.

Kai ya karimatu ta sunkuyar tana cewa hajja dan Allah tayi ha?uri.

Dakatar da ya karimatu hajja tayi tace

"Zaki rufemin baki kosai na gwaSeki? Daman akwai wanda ya isa yayi wa wani mutum abu batare da yardar Allah ba? To ?arya kikeyi, falya?ul Khairan auli yasumut karimatu, na hanaki aibata mutum tun ba yanzu ba, dan haka wallahi ki iya bakinki tunkan ki jawowa kanki fitinar da bazaki iya da ita ba, ita wacce kike la?anawa sharrin asirin kinsan yadda take a wajen Allah? Toki yi min shiru da bakinki anan shasha wacce ta girma wai har yanzu batasan ta girma ba.

*Nasir*

Tare da likita suka shigo yana duba jikin Rashida tare data ajjabin Abinda yafaru, dan Wazu tana ihun nan yazo yaga yadda jikinta yake komawa normal kamar tsafi, dan haka ko bayan yatafi office tunanin Abin ya rungayi kamar yaje ya?ara dubawa, shiyasa da Nasir ya nemi sallama bai musa masa ba yace suje ya ?ara dubawa.

*Hajja*

Baki ta saki tana kallon Rashida wacce tayi Ware Ware ta ri?e murfin motar Nasir wai ita wallahi sai ta bishi gida ba zataje gidan hajja ba, cikin mamaki hajja tace

"Yanzu Rashidan idan kikaje gidan naki wanene zai cigaba da jinyar ki acen? Gidana kuwa akwai ni akwai nusaiba san nan akwai ma'aikata da yawa, kiyi ha?uri kizo muje idan yaso kina warkewa sai ki koma, haba Rashida, kidunga aiki na hankali mana.

Shi dai Nasir shiru yayi yana kallon ikon Allah domin lamarin Rashida ya isheshi, matar da bata da lafiya tatafi gida tayi jinya amma saboda makahon kishinta take cewa zata koma gidan jage jage da ciwo ta zauna.

*KUTSE*

*PAGE 36*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Maryam*

Cikin mamaki?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da ta'ajibi take kallon Rashida wacce take tafe gwame gwame kamar ?ar kaciya, ita abinma yaso ya bata dariya amma sai ta cinye dariyar ta tace mata.

"To banda abinki ai gidan kine maman halima, wace macace ta isa tazo ta kwace miki shi? Ai babu, na baki amsa ma da

"babu.

Dan haka bissimillah shigo ki zauna Allah ya cigaba da bamu zama lafiya.

*Nasir*

?auke kai yayi daga kallon Maryam yana ajiyar zuciya da haWiyar yau, domin har ga Allah yau Win nan dai yaso ya gwangwaje ya more ya hole da Maryam amma wan nan uwar katse muradin ta ruguza masa komai dake cikin ransa, dan haka kawai sai ya wuce su yayi Wakinsa yana hasaso irin shigar ?ananun kayan da maryam tayi.

Tun da ya sauketa a hanya yace ta tanadeshi yau take farin ciki, ita kanta tayi missing Winsa ba kaWan ba dan da gaske dauriya takeyi Allah ma yagani, dan haka tana komawa gida tasha uban wankan ta ta kashe garkuwar jikinta da turaren da tasan yana bala'in son ?amshin sa, wasu ?ananun kaya ta Wauko sababbi wanda samira ta bata a cikin tsarabar da mijinta yayi mata ranar daya dawo daga Ingila.

Riga ce mai hannun vest wacce ta tsaru ta gaji da haWuwa sai kuma wandonta jeans iya cinya wanda yawancin jikinsa a farfashe yake an masa ado da zanen heart na flower da kalar rigar pink color, sai band Winta shima kalar riga da wandon a haWe, gaskiya kayan sun haWu dan a yaune da taje gidan samiran tayi mata kyautar su, shiyasa kawai ta sakasu dan ta kuma jawo ra'ayin Nasir da kuma ?ara kwaWaitar dashi ita, sai dai me?

Wani abin ba?in cikin tanajin dorr bell taje ta buWe dayake su halima tuni sunyi barci kawai sai taga Rashida tsaye tayi wani dagaje dagaje da ita ga busassun hawaye a fuskarta tana aika mata da wata uwar harara, gefen da Nasir ke tsaye ta kalla taga ya jingina da bango Ya zuba ta gumi yana kallon ?asa, wan nan dalilin yasa ta tsaya tana kallon su da mamaki takasa basu hanya.

Shine fa Rashida ta daka mata tsawa tana cewa

"Ke dalla malama kibawa mutane waje su wuce ko kuwa takaicin ganina ne yasa bazaki bani hanya na shiga gidana ba? Ko kuwa kin isa ki hanani shiga ne?

Ajiyar zuciya Maryam taja data tuna Abinda yafaru Wazu da sukayi ido huWu da Rashida, kallon inda rashin take zaune a gicciye tayi tanajin babu daWin Abinda Ya samu Rashidan, amma koma menene da sanin Allah.

*Rashida*

Tsaki tayi tana shirin mi?ewa da kyar domin tashi dan kuwa tafiyar ma wahala take bata, ta saba duk sanda zatayi wani motsi da sauri ya karimatu zatayo kanta domin taimakon ta, amma yanzu babu ya karimatu, gashi Nasir daya Waukarwa hajja al?awarin zai kula da ita tun shigowar su gidan ya shige Wakinsa har yanzu babu wani motsin fitowar sa, gashi futsari ya matseta so takeyi taje tayi ko zataji daWin mararta.

*Maryam*

Ganin Rashida tanata ?o?arin tashi tare da daddage hannaye ta tokare zata mi?e yasa tayi saurin tashi ta nufi inda take tana cewa

"Bara na taimaka miki maman halima, tafaWa tana kai hannu zata kamata.

Wani irin zabura Rashida tayi tare da doke hannun Maryam cikin masifa tace.

"Dalla malama cikani kada ki ?arasani, kokuwa nace miki ina neman taimakon kine, banza azzaluma, tun daga ranar da kika shigo rayuwata ban ?ara samun sau?i ba har yanzu, wan nan ciwon nawa ma inada tabbacin kece silar faruwar sa, kuma wallahi bazan yafe miki ba, sai ta saka hannu ta hankaWa Maryam tana cewa ta matsa tabata waje kota wula?anta ta.

Tsam Maryam tayi a wajen saboda tozarcin da Rashida tayi mata, daga taimako sai kawai abu ya zama fitina? Sai kawai Maryam taja jikinta baya a hankali tafara tafiya da baya dan har ga Allah ranta ya sosu da yawa, tana cikin tafiyar sai jin Rashida tayi ta fashe da kuka tana cewa.

"Shegiya karuwa marar lissafi , banda tsabagen rashin lissafi ji wata shigar rashin mutunci da tsananin karuwanci da kikayi a gidan mijina, inama ?alau nake wallahi dasai kinci uwarki a cikin gidan shegiya tan baWaWWiya, kuma Allah ya tsinewa wan nan harijin uban naki wanda yabawa mijina aurenki.

Wani irin dummmm, Maryam taji a kanta da ?irjinta kamar an maka mata guduma, take jikinta ya hau rawa idanunta sukayi jawur kamar wacce taci bala'i ta jiyo da saurin gaske ta zubawa Rashida jajayen idanunta wanda sai da Rashida ta tsorata da ganin su, wani irin ?ara Maryam ta saki ta ba?in ciki tayi kan Rashida gadan gadan ta Waga hannu ta taske fuskarta da mari, kafin tayi tunanin ?ara Wagowa Maryam ta?ara taske Wayan kuncin nata da mari.

Wani irin kururuwar ihu Rashida ta saki tana wayyo na shiga uku, wayyo na mutu na lalace, innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, baban Halima kazo Maryam zata kasheni.

*Nasir*

Yana kwance yayi rigin gine yanata tunanin halin dayake ciki tun daga aure Maryam har zuwa yanzu, shikam inane zai saka kansa ne? Rashida ta addabi rayuwar sa ta hana masa zaman lafiya da samun nutsuwa, yanzu dai jibi Abinda tayi Saboda tsabagen rashin son zaman lafiyar ta, ?iri ?iri hajja tayi tayi ta bita su tafi ta?i saboda tsabar fitinar zuciyar ta, har taya ya karimatu abin ya Sata mata rai musamman yadda ta dunga kun zuma ihu harta tara musu mutane wai bazataje gida jinya tabar mijinta da karuwa a inuwa Waya ba, saboda tsabar rashin mutunci wai shi take kira da yanabin karuwa, wai matarsa ta sunna ce karuwa, gaskiya Rashida ta cuceshi, shi anya kuwa bazai saki Rashida ya huta da fitinar zuciyar taba? Kullum akwai ta inda zata Sullo da wula?ancin ta, daga tabi tanan saita biyo tanan, wataran kamar mai hankali amma kuma kullum mayar da kwakwalwar ta take irin ta yara.

Yana cikin wan nan zancen zucin sai jiyo ihun Rashida yayi tanata kwala kiran sunansa, yana gado a kwance babu ko riga a jikinsa yayi saurin hantsulowa ya faWo ?asa tare da bazama yayi waje yana kiran lafiya dai?

Yana fitowa kuwa yaga Maryam a tsaye dun?ule da hannu zata taf kawa Rashida naushi.

Da sauri Nasir ya ?araso yana cewa

"Ke,ke,ke,ke, menene haka maryam? ya ?arasa yana ri?e hannunta dake rawa, ganin jikinta yana mazari sai kawai ya rungume ta a cikin jikinsa tsam yana kallon Rashida wacce take kuka kamar zatayi kukan jini.

Itama Maryam wani irin kuka ta fashe dashi tana furta "Babana, babana, babanafa.

Shafa bayanta Nasir yahau yi yana cewa tayi shiru ta faWa masa meya faru, kasayin shirun tayi sai kuka da rawar jiki kawai tana furta kalmar

"Babana, babana.

*Nasir*

Tunda yaji haka kuma yaga haka yasan wani mummunan abun Rashida ta faWa akan Maryam da iyayenta, dan haka sai kawai yaji ransa ya dugunzuma da Saci, take ya cire maryam daga jikinsa yana kallon Rashida wacce tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login