Showing 27001 words to 30000 words out of 175193 words

Chapter 10 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

567

magana akan tataso su tafi Nasir na jiran su, dan ko sama da k'asa zata had'e babu inda zataje tabar ummanta a wan nan halin, san nan ma kwata kwata batajin zata iya bin Nasir da sunan wai su tafi tare yakai ta gidan sa, dan wallahi tallahi ta rantse da Allah bazata komawa Nasir a wan nan yanayin ba, itafa kwata kwata auren sa gaba d'aya yafice a ranta dan batajin zata iya zama da miji kamarsa kuma ta buga kishi da mace kamar Rashida.

Shiyasa data gaji da maganar sai kawai ta juyo tana shasshekar kuka tace.

"Bazan bishi ba yaya, bazan tab'a binsa ba, taya zan tafi gida Alhalin umma tana wan nan halin, yaune fa za'ayi mata aiki, kuma kawai sai na bisa? Idan na bisa nabar umman da waye? Kuma bama haka ba, yaufa kwata kwata kwanan baba uku da rasuwa, fisabilillahi basai abari sai anyi bakwai ba kafin ace natafi, ni wallahi bazan tafifa.

*Mansur*

Ganin Maryam na hak'ik'an cewa da kuma tumami kamar wacce aka jefawa masifa yasa yace

"Ke menene haka? Saboda kawai nace kije kutafi da mijinki zaki na yimin wasu magan ganu? Nace miki baza mu iya kula da umman bane, bayan ni baga matata bama, ko kuwa an rawaito cewar dole ne sai kin zauna anyi bakwai d'in san nan zaki tafi? To bara kiji.

Tunda har mijinki yace kitafi to kitashi kibishi.

Kwanciya Maryam tayi cikin ba'kin ciki tace.

"Zan bishi yaya tunda haka ka zab'ar min, Amma dan girman Allah kabari sai anyiwa umma aikin nan san nan natafi, idan ba haka ba wallahi hankalina bazai tab'a kwanciya ba, dan Allah ka taimaka min.

Sosai tausayin ta ya ratsa zuciyar mutane da yawa dake cikin d'akin, dafa kafad'ar Mansur jalila matar sa tayi tace.

"Dan Allah Abban amir kabarta ta zauna ko zuwa ranar bakwan baba ne, kaga lokacin insha Allah anyiwa umman aikin nan harta samu lafiya, idan yaso sai ya dawo ya d'auke ta ko kuma kai ka kaita dan Allah, tak'arasa fad'a hawaye na zubo mata.

Kai ya Mansur ya jijjiga yace

"Shikkenan, ta zauna d'in Allah ya nuna mana.

San nan ya juya yafita.

A zaune bayan motar ya tarar da samira tana waya, sai kuma Nasir wanda ke waje ya jingina da motar Amma idanunsa da hankalin sa duk suna bakin k'ofar gidan.

Mansur na fitowa Nasir yayi saurin taryar sa yace.

"Ina Maryam d'in?

D'an murmushi Mansur yayi yace

"Tana ciki, daman fitowa nayi muyi magana, wato a gaskiyar magana Maryam ta kafe tace bazata tafiba sai anyi wa umma aikin nan, kuma dana duba sai naga hakan ne yakamata ayi, kaga inyaso ranar bakwan baba sai ku tafi tare idan kazo.

*Nasir*

Har ranshi baiji dad'in wan nan maganar ba, Amma ganin wan nan d'in uzuri ne babba sai kawai ya d'aga kai yana murmushin yak'e yace.

"Tohm shikkenan d'an uwa, Allah yakaimu ranar nagode sosai, Allah yasa ayi aikin lafiya kuma Allah yajik'an Baba.

Da Amin ya mansur ya amsa san nan ya shige gida shi kuma Nasir ya juya ya shiga mota jikinsa a sanyaye ya tada mota.

*Samira*

Har sun fara tafiya sai kuma taji bazata iya shiru ba sai kawai tace.

"Ina Maryam d'in?

"D'an juyowa Nasir yayi kamar bazai magana ba sai kuma yace.

"Tace sai anwa umma aiki san nan zata tafi.

D'aga kai samira tayi tace

"Gaskiya ne kuma hakan yayi dai-dai Allah yasa ayi lafiya, Amma nikam gaskiya ina ganin abubuwan dake faruwa tsakanin ka da Maryam kamar ba dai-dai bane, naga tun ranar da akayi rasuwar ko magana bakuyi ba har yau wai meke faruwa ne?

Cikin d'an zafi zafi Nasir yace

"Ai ke zan tambaya, tunda nidai nasan Maryam batasan kowa ba a kano sai ni sai kuma ke, kuma Abin mamaki sai akace min wai kunje gida tare, kuma danazo gidan sai naga zahiri, kenan a gurin ki Maryam take zaune tun ranar Amma saboda munafurci kika k'i sanar dani, saboda kinason ki tozarta ni a idanun duniya.

*Samira*

Wata dariyar rainin hankali tayi tace

"Ai tozarci ka rigada ka gama samunsa tunda har ka banzatar da amanar da iyayen Maryam suka baka, kai dan Allah bakiji kunya ba da har kake nuna rashin jin dad'i dan na sauke Maryam a gidana? Kenan burinka ta b'ata a garin kota shiga mawu yacin hali saboda bata da kowa a kano sai Kai?

Tona sauketa a gidan nawa, me zakayi? Baka da wani Abinda zaka iya tunda baka da k'arfin halin dazaka iya had'ata da matarka kazama namiji a tsakanin su, saboda haka sai ka zauna da matarka mai girma ita kuma da kukewa ganin kas k'an tacciya sai kabarta ta zauna a inda aka san mutuncin ta.

*Nasir*

"Wani irin burki ya buga yaja motar ya kafe, juyowa yayi ya tsurawa samira jajayen idanun sa da suka kaWa sukayi jawur kamar gauta, hannunsa ya d'aga mata tare dayi mata nuni yace.

"Fita, kifita kibar min motar nan tunda ba motar mijinki bace kuma bata uban....

*Samira*

"Da sauri ta daga masa nata hannun itama tace

"Dakata, dakata min malam, karka soma zagin iyayena, dan wallahi mantawa zanyi da wani mutuncin dake tsakanin ku da yayyena da kuma girman da kabani na rama Abinda kayi min, kuma wallahi bazan fita daga motar nan ba, niba Maryam bace ni samira ce.

*Nasir*

"Kallon samira kawai yakeyi yana mamakin yadda take tsagal galewa take zuba masa rashin kunya, Samira fa? Kamar samira? Yarinyar da aka haifeta a hannun su Amma itace yau yake fad'a take fad'a? Hnmmm lallai wan nan zamanin akwai abin tsoro.

Haka yanaji yana gani ya kuma tayar da motar ya cigaba da tafiya yana mamakin samira wacce ta hakim ce a motar tana danne danne a waya gashi ta had'e girar sama data k'asa.

*Bayan wasu a wanni*

Sun shigo garin kano lafiya kuma haka suna shigowa Nasir yaja burki yana jiran samira tafita ta bashi waje yaja motarsa ya cigaba da tafiya domin zuwa gida.

Amma abin mamaki sai yaga ta cake ko motsi batayi ba bare tayi niyar fita, dan haka sai ya had'e fuska sosai tare da bud'e murya irin taji tsoron nan nashi yace

"Zaki iya fita.

'yar dariya samira tayi a ranta Amma a fili sai tace

"Ai banzo inda zan sauka ba.

Kamarya bakizo inda zaki sauka ba? ina kuma kikeso na kaiki malama?

Kwantar dakai samira tayi tace

"Gidana mana.

Dukan sitiyarin Nasir yayi yace

"Ke karki raina min hankali kinji ko? Kibar ganin ina binki yadda kikace kiyi zatan dasan rainane, dalla fita daga motar nan kona sab'a miki.

D'an yun k'urowa samira tayi daga jikin motar tace

"Haba Nasir, kataimaka min mana dan A??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????llah, idan ka saukeni anan zan wahala, dan Allah ka kaini gida dan darajar iyayenka, ta k'arasa tana masa kalar Abin tausayi.

Har ga Allah Nasir bala'in haushin samira yakeji saboda yadda bata duba girman sa ba tayi masa rashin kunya, shi bayason raini kwata kwata a rayuwar duniyar sa, kayi masa komai amma banda raini ko rashin kunya yanzun nan zai tsaneka, badan yaso ba sai don Allahn data ambata yasa ya tada motar ya k'ara harbata kan titi suka cigaba da tafiya, sai da suka shigo cikin gari sosai san nan ya kuma jan tunga ya tsaya.

Ganin ya tsaya yasa samira ta gane mai yake nufi sai tace

"Goron dutse gidan mai

Bai tanka mata ba yacigaba da tafiyar har sukaje wajen, yana tsayawa samira tayi hamdala tare da cewar

"Nagode sosai ya Nasir, Allah yajik'an rai, sai ta nuna masa gidan tace

"Ga gidan nawa, san nan ta zaro mukullin gidan ta bud'e ta shiga.

Shima tada motarsa yayi ya bad'eta da k'ura yabar wajen yana sakin kwafa.

Dariya samira tayi a fili sosai tace

"Aini kujera ce ya Nasir, muna nan da kai wataran sai ka nemi shiri Dani, kuma tana sane takafe akan sai ya kawota gida saboda yaga gidan nata dan tasan dolen dolen sama sai yadowo gidan neman Maryam, dan wallahi ko Maryam ta dawo garin bazata koma gidan saba nan gidan nata dai zata dawo su cigaba da zama har lokacin da zai fahimci wayeshi.

*Nasir*

Sai daya sauke samira ya nufi hanyar gidansa san nan yaji wata iriyar fad'uwar gaba, me zaicewa Rashida? Humm umm Jan, ana wata ga wata, yasan yau babu zaman lafiya, Amma tilas ya dage ya nunawa Rashida zamansa take ba zamanta yake ba, anan ma gabansa ne yafad'i yace a ransa

"Zan iya kuwa? Sai kuma wata zuciyar tasa tace masa

"Mezai hana? Sai kace ba namiji ba? Kana nan tsoron Rashida ya cika maka zuciya har ya fito fili mutane sun fara ganewa, to gaskiya ka gyara kazama namiji dan yanzu lusari kake.

Wani b'acin rai yaji ya diro masa lokaci d'aya, sai kawai yaji zuciyar sa na tsukewa da fara jin haushin Rashidan, duk tabi ta kid'ima shi, gaba d'aya yazama wani su su su, gashi ta jawo mutane suna masa kallon wawa har sun fara soka masa magana.

Jibi fa abinda Ramadan yagama gaya masa, san nan saboda raini duba fa maganar da samira ta gaggaya masa yau, gaskiya zai zauna ya duba yaga ta ina yayi sakacin da mutane suke kallo masa, da wan nan tunanin yayi da kiya har Allah yakaishi gidan lafiya.

*Rashida*

"Tana zaune duk abin duniya ya mata yawa, ita kamar ma bata jin dad'in jikinta haka takeji, shiyasa duk kasala ta rufeta, ta kwanta nan ta tashi nan duk ita kad'ai, tana wan nan kwanciyar kawai taji bugun Horn d'in motar Nasir, zumbur ta mik'e ta lek'a ta windon sama ai kuwa sai ta ganoshi zai shigo da motar suna gaisawa da jama'ar kofar gidan, da yake k'ofar gidan akwai masu sana'a Amma bawai kasuwa ba.

Akwai mai business center, san nan akwai shagon d'inki, kuma akwai wata yarinya da take sai da wainar fulawa da awara da yamma, kamar biyar haka take? farawa tatashi bayan isha'i, wan nan yasa layin nasu baya rabo da gilmawar mutane.

Da sauri Rashida ta koma ta kwanta tana haki tanajan numfashi saboda jaraba, jira kawai take Nasir da Maryam su shigo ta tashi ta wanke fuskar Maryam da mari, bama Maryam ba jitake yau har Nasir d'in bazai tsira daga bala'in taba, saboda sun cutar da ita har tayi jinya a dalilin su, kuma saboda sunga bata d'auki fansa ba shiyasa suka maidata wata shiri-shiri, dan haka zasu shigo.

Tana wan nan sak'ar har batasan sanda Nasir d'in ya shigo ba sai jitayi ya dafata yana cewa

"Lafiya kuwa?

Da sauri ta zabura ta ture hannunsa tana maka masa mugun kallo, shima kallon yake mata tare da k'arewa gidan da akace sunyi gobara kallo cike da mamaki.

Ganin ya tsura mata ido babu Alamar irin nadamar daya saba yi mata yasa tace.

"Munafuki, algun gumi, kagama san ran naka da waccen shegiyar san nan yanzu ka lallab'o wajena? Tanama ina? Sai tatashi tsaye zumbur tafara waige waigen nemanta da lek'e lek'e, shidai kallon mamaki kawai yakeyi mata dan Rashida tafara bashi tsoro, shine ma munafuki kuma algun gumi? Sai kawai ya mik'e yace.

"Ke Rashida, wai meke damunki ne? Meyasa kina girma kullum kinacin k'asa?

Sororo Rashida ta kalleshi tana nuna kanta tace

"Ni kake kira Rashida? Kuma ina girma inacin k'asa? Cab'b'ijan, ta rike k'ugu tana jijjigawa, san nan taci gaba da nuna kanta ta fashe da kuka tana cewa

"Ni Nasir, ni, nikakewa haka saboda kayi auren cin amana? Duk Abinda nayi maka a rayuwa ka manta? Hnmm ai shikkenan, saboda yanzu baka k'aunar mu nida yarana har yaya karimatu ta kiraka a waya tace maka munyi gobara Amma ka share ka rabu damu saboda waccen yarinyar.

Kwana biyu, kwana biyu fa kuna tare, kwana biyu kuna tare da wata bani ba?

Sai ta kuma saka kuka.

Harga Allah bayason tashin hankali Rashida bare kukanta, abin na mintsinin zuciyar sa, shiyasa gwiwa sage ya k'arasa inda take da niyar rik'ota ya rarrasheta, abinka ga butsuwar mace sai tayi baya tana jijjiga kai tana cewa

"Karka soma tab'ani, banaso kaje kawai nabar mata kai, bazan kuma yarda dakai ba Nasir, dan kayimin Abinda na cire wata aba mai suna yarda a raina, bazan k'ara yarda da wani halitta ba.

Sai ta saki k'ugun tayi hanyar d'akinta da gudu ta shige tare da banko k'ofar.

Jikin k'ofar Nasir ya tsaya yana bugawa yana ta bud'e masa Amma fafur tak'i, ganin hakan yasa kawai ya fad'a d'akin sa tare da shiga wanka ya sakarwa kansa shaya.

Ita kuma Rashida tanajin ya shige d'akin sa tayi saurin fitowa da mayafi yafe a jikinta tafice daga gidan, dayake gidan babu nisa da titi sai kawai tana fita ta tarar da napep ta shige tana matsar hawaye.

*Nasir*

Sai da yad'an kintsa san nan ya fito danya koma wajen Rashida k'ila lokacin ta samu sassauci, Amma yana fitowa sai kawai yaga d'akin a bud'e , da sauri ya shiga sai yaga bata nan, band'aki ya duba nan ma yaga bata nan, sai kawai yafara nemanta a gidan Amma ya nemeta sama ko k'asa ya rasa, su kam yaran baima gansu ba daman d'azun daya shigo, sai kawai ya zari mukullin motarsa shima ya fice.

Kuyi hak'uri da wan nan =?O??v?

*KUTSE*

?? *PAGE 14*

? ? *NA*

? ? ? *MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Hajja*

Cikin mamaki mai tsanani take kallon Nasir da maimaituwar magan ganun daya gama gaya mata wanda suke faruwa tsakanin sa da Rashida.

A karo na biyu hajja ta kuma jan tsaki tace

"Ashe kai lusari ne a cikin mazaje nasiru? Yaushe lalacewar Rashida takai harta dunga wan nan haukan akan kishi ban saniba? Duk bama wan nan ba, zan maka fad'a ne kad'ai a gaban Rashida ba'a bayan idanun taba, 'yar autar ta takira tace ta mik'a mata wayar ta.

Danne danne hajja tayi a cikin wayar tare da dannawa Rashida kira , bugu d'aya biyu Rashida ta d'aga da sallama a bakin ta.

Hajja bata nuna mata komai ba ta amsa gaisuwar datake mata faran faran san nan tace.

"Kina inane haka naji kamar hayaniya Rashida? Da d'an in..ina abakin Rashida tace

"Uhummm, uhumm, ina gida hajja.

D'aga kai hajja tayi kamar tana ganinta tace

"Tohm shikkenan gani nan yayanku zai kawoni gidan naki na dubaki, naji ance kinyi fama da jiki kwana biyu.

Wata irin kidimewa Rashida tayi da sauri tace.

"Amm.. daman hajja nad'an fitane yanzu, naje gidan yaya karimatu, Amma yanzu zan koma gidan.

Kai hajja ta d'aga san nan tace

"To ai tunda kin samu lafiya kenan babu amfanin zuwan namu, saboda haka tunda kinfita kibiyo ta gidan sai na ganki ko?

Da sauri Rashida tace

"To hajja gani nan.

*Rashida*

Fuska a d'an dame ta kalli ya karimatu tare da cewa

"Ya karimatu kodai Nasir ne yakai k'arata wajen hajja?

Dariyar takaici yaya karimatu tayi tace

"Shiya soma? Shid'in wa dazai je wa hajja da aibinki? Ai shima baya faraba,. Karfa ki damu ki wuce kije ai jiya danaje gida nake gayawa hajjan kinyi rashin lafiya , har takemin fad'an ba'a sanar da ita ba.

Ita dai Rashida jiki babu kwari ta zari jakarta da mayafinta tafita domin tafiya gidan hajja dan yaran ma daman yau kwanan su biyu a gidan yaya karimatun sunje hutu.

Tun daga farfajiyar gidan nasu ta hango motar Nasir, kuma tana ganin motar sai da gabanta ya fad'i, kenan Nasir ne yazo kawo k'arar ta wajen hajja saboda yayi aure? Ko kuwa nemanta yazoyi gidan hajja tace bata zoba shine yafad'a mata wani Abin?

Bata damai bata amsa sai ta shiga, dan haka sai ta had'iye fargabar hajjan ta shige gidan tanata salati domin tasan gamonta da hajjan muddin akan Nasir ne babu dad'i.

*Nasir*

Yana ganin Rashida ta shiga gidan a sab'ule kamar marar laka sai yad'anji kamar bai kyautaba daya tawo gidan hajjan, ai bai san ba gidan tazo ba dan dayasan gidan yaya karimatu tatafi dacen zaije ya bata hak'uri ya tawo da ita.

Tun daga yanayin da hajja ta kafe Rashida da ido take auna mata wani kallo zuciyar ta tafara tsinkewa, da sauri ta tsugunna a wajen da niyar tafara gaida hajjan ta tsinci hajjan na cewa

"Da izinin wa kika fita daga gidan ki zuwa gidan karimatu Rashida?

Kafin tace komai ta fara rushewa da kuka tana bud'e baki da niyar yin magana.

Cikin b'acin rai hajja ta daka mata tsawa da cewar.

"Rufemin baki dan ubanki, me akayi miki daga tambayar ki zaki fara nunamin kalar makirci? To wallahi maza ki had'iye kukan nan ki kuma ki yayeni.

Tsit Rashida tayi tafara goge hawayen nan da nan suka k'afe kamar anyi ruwa an d'auke.

A karo na biyu kuma hajja ta k'ara maimaita tambayar data yiwa Rashida tace

"Da izinin wa kika fita daga gidan mijinki kika tafi gidan karimatu?

"Ajiyar zuciya Rashida ta sauke tace

"Daman..daman...

Katseta hajja tayi da cewar

"Kika kuskura kikayi min k'arya Allah yana kallon ki, dan basai nace miki komai ba dan nasan zaki karb'i hukunci a wajensa.

Da sauri Rashida ta saita kanta tare da kimtsa kalamanta tace

"Daman munyi rigima ne dashi hajja, shine na fito saboda na samu salamar zuciya.

Kauda kai hajja tayi cikin mamaki tace

"Saboda kawai kun samu sab'ani shine zaki fita bada izinin Saba? to yanzu tsinuwar mala'ikun yaya zakiyi da ita?

Kuma ma menene musabbabin yin rigimar taku?

Kallon Nasir Rashida tayi hawaye na sakko mata san nan ta kalli hajja tace.

"Hajja cin amanata fa yayi, yaje yayi aure ban saniba, san nan ya d'auko matar tasa ya dawo da ita gidana ta zauna yanata min k'unbiya k'unbiya, sai da matar tasa ta gaji dakanta san nan ta fito tafad'a min, kuma baiji kunya ba ya gasgata lamarin nata, idan yaso ko had'iyar zuciya zanyi na had'iya ba damuwar sa bace tunda yana da wata matar.

*Hajja*

Murmushin takaici tayi ta kalli Nasir wanda yayi tsilli tsilli a wajen tace.

"Me ka gama gayamin yanzu akan auren ka Nasir? Shin ita Rashidan baka sanar da ita yadda yanayin auren naka yazo dashi ba?

*Nasir*

K'asa ya kumayi da kansa yace

"Nayi nayi ta saurareni na sanar da ita gaskiyar al-amarin tak'i hajja, duk sanda naso muyi magana sai tayiwa maganata gurguwar fahimta, shiyasa na kasa sanar da ita.

*Hajja*

Kallon Rashida tayi bada sigar wasa ba tace

"Mijinki yanason ya sanar dake yadda auren sa yazo a babu shiri baki nutsu kin saurare shi ba, saboda haka inason yanzu ki tsaya ki saurareshi, idan yaso idan kinga dama ki yarda idan baki gadama ba ki cigaba da shirme, sai ta koma kan nasir tace

"Kasanar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login