Showing 93001 words to 96000 words out of 175193 words

Chapter 32 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

530

koma gidan mijinta, idan ba haka ba gaskiya akwai ?ura babba.

Wayar ta ajiye tana tunanin wata sabuwar hanyar da zata Sullowa Nasir dan ya saurareta har ya mayar da ita gidansa, mi?ewa tayi ta shiga banWaki tare da Wauro alwala ta fito da niyar yin sallar isha'i, ba wai iya isha'in zatayi ba har da ramuwar la'asar da kuma magariba san nan tayi ishar, ita batajin komai idan tayi ramuwar salla, dan tana ganin ko batayi ta akan lokacin taba ai dai tunda zata rama ba ?inyi zatayi ba bata da matsala, shiyasa ko tanaji ana salla sai taga dama zata tashi tayita akan lokacin ta, idan kuwa bata gadama ba tofa wan nan sallar tanajin anayi zata ?i tashi tayi har lokacin ta ya fita sai daga baya ta rama kota haWa biyu ko Uku.

*****

Zaune Rashida take a gaban hajja tanata kuka dayi mata magiyar ta kirawo Nasir ta bashi ha?uri ta koma gidan ta wallahi ta tuba bazata ?ara ba.

*Hajja*

A ranta tanajin tausayin halin da Rashida ta tsunduma kanta, amma a fili sai ta haWe rai tana juya kai tare dacin Waci tace.

Ki dakata kitashi daga nan Rashida, saboda babu Abinda zan miki wallahi, nayi al?awarin na daina shiga sabgar aurenki Rashida, badan komai ba sai dan idan na shiga nan gaba ma kunya zaki bani ki mayar dani tsohuwar banza da hofi.

Dan haka wallahi ki tashi ki bani waje tun kafin ranki ya ?ara Saci akan wanda yakeyi yanzu.

Kasa tashi Rashida tayi sai shasshe?ar kuka da takeja tana jan hanci tare da kallon hajja cikin karyayyan kai duk dan ta tausaya mata.

Ita kuwa ganin Rashida bata da alamar tashi yasa ta danne abinda takeji san nan ta daure zuciyar ta tayi bissimillah tare da mi?ewa tsaye tafara tafiya ta shige Wakinta.

Bin bayan ta Rashida tayi da kallo tana share hawayen ba?in ciki tanajin a ranta dan hajja ba mahaifiyar ta bace shiyasa take mata mugunta, dan tanada ya ?inin da mahaifiyar tace wallahi bazatayi mata haka ba.

Ganin ta daWe zaune tana zaman jiran gawar shanun ganin hajja tafito ta kuma ro?arta amma shiru kusan awa bata fitoba yasa tayi zuciya tatashi ta koma Wakinta ta dannawa Nasir kira.

Nasir na zaune a office yaji wayarsa nata ruri babu ?a??autawa, kamar bazai amsa ba saboda wayar bata kusa dashi sai kawai yaja dogon tsaki ya nufi inda wayar take dan ?arar tama ta isheshi, yana dubawa yaga Rashida ke kira sai yaji ransa ya Saci sosai, madadin ya Waga sai kawai ya danno lambar tata ya dannata a cikin Black list dan hakan yafi masa da takurar datake masa kwana biyun nan.

Wayar Rashida ta wullar tana kwanciya ruf da ciki tana saka wani sabon kuka mai ciwon da babu wanda zai gane, sai datayi mai isarta san nan ta Waga wayar ta dake ta ?ara, tana dubawa taga amina ce hakan yasa tayi saurin tashi tare da Wagwa cikin Muryar kuka tace

"?awata.

*Amina*

Dariya ta saka tace

"Nasir dai, Nasir dai, ince ko keda Nasir Winne?

To kisha kurumunki na dawo jiya da daddare, dafatan zaki shigo yau ki karSi tsarabar ko?

Murmushin jin daWi Rashida tayi tana jin sanyi da sanyayawa a cikin ranta dan tasan hawayenta ya daina zuba saboda tunda ?awarta ta dawo tasan matsalar ta tazo ?arshe.

*****

Rashida bata wani Sata lokaci ba ta shirya ta fito ta fita batare data nemi izinin hajja ba, dan idan ba sa'a ba wallahi tsaf hajja zata hanata fita saboda ta ?unsa mata.

Rungume juna Rashida da Amina sukayi suna masu jin daWin ganin juna, cikin sha'awa Rashida ke kallon Amina ganin yadda tayi Sul-Sul da ita tayi wani fresh kamar an canzo an wanko ta, kasa shiru Rashida tayi tace

"?awata kinga wani irin haWaWWen glowing da kikeyi kuwa? Hnmm dan Allah menene sirrin ne?

Rufe baki Amina tayi tana kallon Rashida tace

"Ni kuma bakiga yadda nake kallonki ba kamar wacce aka sake? Ni wallahi banji daWin ganin kiba wallahi, dan wallahi duk kinyi duhu kin rame Rashida, ko kuwa duk matsalar nan ta Nasir ce ta sakaki a cikin wan nan halin?

Hawaye Rashida ta share tace

"Matsalolin Nasir da matarsa ne suka sakani a gaba Amina, nifa ina tunanin Rayuwa ta ta kusan zuwa ?arshe Amina, dan wallahi zuciya ta tana min zafin da bana iya runtsawa nayi barci, dan Allah ki bani shawara Amina,Rashida ta kama hannun Amina tana sakin kuka.

Shafa bayanta Amina ta shigayi cikin Sacin rai da tsananin tsanar Maryam harda nasir Win ma kansa wanda ya saka ?awarta a cikin mawuyacin hali.

"Ki kwantar da hankalin ki Rashida, wallahi ina tabbatar miki na rantse da girman Allah sai kinga bayan Maryam muddin muna raye, kumama ai dole ne ki koma gidan ki Rashida, taya zaki bar mata gidan da mahaifin kine yabashi Saboda ke? San nan gidan da kuka gina farin ciki a ciki? Kuma banda haka ma, komai naki fa yana gidan Rashida.

Kin bar mata komai naki, daga mijin har ragamar gidan naki, falonki da kayan cikinsa, kichen Winki da kayan cikinsa, harda Wakinki da kuma kayan Wakin naki, dan na tabbatar yanzu haka da kyar ne idan ba'a gadonki Nasir yake iskancewa da Maryam ba.

Wata irin dokawa zuciyar Rashida tayi da faWin wan nan maganar da Amina tayi, kuka ta kuma rusawa tana ta shiga Uku ta lalace ta baran kaWa ta mutu.

Dakyar Amina ta rarrasheta tace.

"Kiyi ha?uri Rashida dan komai yazo miki ?arshe, tabbas zaki koma gidan ki san nan ki kwace komai daga hannun waccen Maryam Win, karki sake ko cokalin da ubanki ya sai miki ta ?ara taSawa, tunda ai tsiya batabar iyayenta sun kawota da komai ba, banda talauci da fa?iranci haka suka Waukota sungul suka kawota kuma take Amfani da duka abubuwan ki kina kallo amma baki iya Waukar mataki ba, ai shiyasa takejin ta isa takai ta goga dake.

Tashi Rashida tayi dan ita tagaji dajin wan nan magan ganun aminar dake ?ara hautsina mata tunani, tana tashi kuma ta ri?e hannun Amina tana cewa.

Yau da kaina nakeson naje gurin malamin da zaki kaini saboda na warware masa matsalolina baki Waya.

Tashi Amina tayi tana yafa gyalenta tare da zarar mukullin motarta tace muje na rakaki ?awata yanzu yanzu, dan matsalar ki tawace, san nan ance da zafi-zafi ake dukan ?arfe.
*KUTSE*

*PGAE 40*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Gur fane suke gaban malam mai bugun ?asa sunyi ?asa dakai sunata baza idanuwa yana zanen ?asar da basu isa suce mai yake zanawa ba.

Sai da malam ya gyara zama tare dayin gyaran murya san nan ya kalli Rashida yace

"Lamarin ki da mijin ki abune mai faWi Rashida, akwai zama mai tsawo a tsakanin ku wanda a cikinsa akwai ?alubale marar iyaka.

Shiru yayi san nan daga bisani yace

"Bani labarin halin da kike ciki a gidan mijinki.

Ai kuwa nan Rashida tafara zayyanewa malam halin ba?in cikin da take ciki gashi tsawon wata biyu ace tana gida miji ya koreta saboda wata banza kishiya.

Sai da tayi shiru san nan malam yaWan nisa ya cigaba da zane ?asar sa san nan ya Wago yace.

"Kishi mai tsanani shine matsalar zamanki da Nasir, da zaki sau?a?a da babu Abinda maryam tafi ki a wajen Nasir, naga ma soyayyar da Nasir yake miki har yau ta Maryam bata doshi inda takin take ba, amma daman ita mace ba'a rabata da kishi, amma naki yayi yawa kiWan rage ko kaWanne.

San nan abu na biyu da baki saniba shine

"Kishiyar ki tanada ciki.

Daga Rashida har Amina a zabure suka Waga kai suna kallon malam, ita kam Rashida jikinta rawa yafara saboda tafasar da jininta yake ta dafe ?irji tare da fashewa da kuka tace

"Ciki kuma? Na shiga uku, Maryam Win ce keda ciki? Wai meyasa Nasir yakeson gur Sata min rayuwa tane? Meyasa yakeson kawo mana matsala a cikin zaman mune?

Sai kuma ta matsa gaban malam sosai har hannun ta yana shiga farantin ?asar tace

"Malam mataimakamin, ka a gazamin dan Allah, wallahi malam banason ?a?ana su gur Sata da ?an uba, nafison zu zama susu kaWai a wajen uban su damani, saboda wallahi ko mutuwa Nasir yayi bazanyi wani auren ba bare na haifi wasu ?a?an a wani gidan, dan Allah ka taimaka min, wallahi bazan iya Wauka ba .

Murmushi malam yayi yana yiwa Amina nuni data matsar da Rashida yace

"Me kikeso na taimaka miki dashi?

"A zubar da cikin san nan idan da halima a lalata mahaifar tata san nan a saka ya saketa saki uku dan girman Allah.

Rashida ta ?arasa faWin maganar tana shasshe?ar kuka.

Zane zane malam yafara san nan ya Wago ya fara haWe haWen maganin sa yace.

"Cikin zai zube idan kika bar baWa mata wan nan maganin a ?ofar Wakinta ta tsallaka.

Ya ?arasa faWa yana mi?o mata maganin.

Cikin raunanniyar murya Rashida tace

"Ai malam Yanzu bana gidan nasa, kuma san nan ya?i mayar dani Wakina, dan Allah malam kasa ya mayar dani kafin mu shiga watan azumi tunda baifi saura kwana goma sha Waya ba.

Nan ma wani kuratandu ya mi?a mata yace.

Kwallin shiri kenan, wan nan kwallin ban taSa bada shi ga wata ?a mace ta sanya shi ta wanke shi a banza ba, ki samu ki saka wan nan kwallin san nan ki shafa wan nan turaren, kuma sharaWin sa shi kaWai ne zaiga cikin idonki san nan ya sha?i ?amshin, kada kibari kowa yaji sa idan bashi ba, idan kuwa kikayi kuskuren wani yasha?e shi koya kalli cikin idonki to wallahi koda baban kine sai kun shiga cikin masifar da har ku mutu bazata warware agareku ba.

Ina tabbatar miki da zarar Nasir ya ganki kuma ya sha?i turaren nan to wallahi bazaki bar wajen da kuke batare da ya mayar dake gidan ki ba.

Ku tashi kuje na sallameku.

Tashi Rashida tayi farin ciki fal ranta ita kuma Amina ta dakata tana sosa kai.

Kallonta Malam yayi yace

" Yaya?

BuWe baki Amina tayi zatayi magana malam ya dakatar da ita yace.

"Bazan baki komai ba Amina, kibari sai ana gobe azumi ki dawo, dan naga duk Abinda zan baki yanzu bazaiyi aiki ba.

"Ri?on arzi?i Rashida tayiwa ledar hannunta tanajin matsalar ta ta yaye kenan, komenta gidan Nasir kamar anyi an gama ne, hira sosai suka dungayi har Amina ta sauke Rashida a gidan su tare da ?atuwar jaka wacce tsarabar da tayo mata ita da yaran suna cikinta.

Amina na tsananin son yara a rayuwar ta, amma son zuciya yasa ta Sarar da damatarta ta samun yara, dan a lokacin da take son auren mijinta tabbas boka mai tsidau ya sanar da ita cewar in har ta aure shi to bazata taSa haihuwa ba, kuma badan baya haihuwa ko ita bata haihuwar ba sai dan tsarin aikin tsafin da yayi mata ne haka, tanaji tana gani ta yarda da sharaWin kuma gashi tanada son yara.

Su halima suna ganin gata a wajen ta domin duk Abinda tagani na yara sai ta siya musu muddin ya burgeta, haka duk zuwa makan da zatayi wajibi tayowa su halima tsaraba mai yawa kamar ?a?an cikin ta.

Yanzu ma tulin kayan data siyo musu ita kanta yafi wanda tayiwa kanta tsaraba yawa.

Rashidan na shiga gidan ?irjinta yafara lugude saboda juyo muryar data tsani jini a rayuwar duniyar ta, da sanWa ta shiga falon ta zauna tana ganin irin kallon da ya Aliyu yake wurga mata.

Tun kan wani yayi wata magana ya Aliyu ya riga da cewar

"Daga gidan ubanwa kike ne?

?irjinta ne ya buga tayi saurin tura masa ?atuwar ledar hannunta tace

"Daga gidan ?awata Amina nake naje mata sannu da zuwa ta dawo daga umara wallahi.

Da izinin waye kika fita kikaje? Ke watau kunnen ?ashi gareki ko? Idan kika Sullo tanan aka tare ki sai ki kuma Sulla tacen ko? Wallahi Rashida ki kiyayi haWuwa ta dake, to banda ma baki da ishasshen hankali kina gida kina zaman idda amma ki saka ?afa kifita saboda kin siyar da tsoron Allahn ki?

Da sauri Rashida ta kalli hajja ta kalli ya Aliyu mai cewa tana zaman idda amma sai takasa magana .

Da sauri itama hajja tace

"A'a Aliyu, wane irin zaman idda ana zaune ?alau? Ai ba sakinta Nasir Win yayi bafa , kawai dai tunda ka Waukota kuka tawo gida bai kuma waiwayar taba, san nan Rashida bata taSa fitaba a tsawon watannin nan sai yau, dan haka dan Allah kayi mata ha?uri.

Ke Rashida tashi kishiga ciki kiyi sallar magariba, san nan akwai kayana da aka kawo daga gurin guga idan kin idar da sallar kije Wakina ki jeramin su.

Da to Rashida ta amsa san nan tatashi jiki a saSule ta fara tafiya zata bar falon, ledar data turawa ya Aliyu yayi ball da ita yana daka mata tsayawa da tazo ta Wauki tsiyar ta kafin ya cinna musu wuta.

Dawowa tayi ta Wauki ledar a Warare saboda kar ya kai mata duka tayi saurin barin gurin.

Kallon sa hajja tayi tace

"Inason ka sassauto Aliyu ka daina zafafawa Rashida a cikin gidan nan, ko ka?i kokaso fa jinin kace, nasha faWa maka tun ba yau ba amma bakajin magana ta.

*Aliyu*

Saukowa ?asa yayi ya zauna a gaban hajja tare da dafa cinyoyin ta yayi ?asa da kansa yace

"Zan tafi hajjata, kisakamin albarka, kuma Insha Allah zan gyara wasu abubuwan, ki cigaba dayi min addu'ar samun salama a cikin zuciya ta.

Dafa kansa hajja tayi tana murmushi tace

"Allah yayiwa rayuwar ka data zuriyar ka baki Waya albarka Aliyu, kuma Allah ya shirya min kai da kuma zuriyar ka baki Waya, katashi kaje gida wajen iyalan ka, san nan ka gaida min da yaran da matar gidan duka, kuma kace mata naji daWin dambun naman nan, Allah yayi mata albarka yasa yaranta su kyautata mata fiye da yadda take kayutata min.

*Bayan kwana biyu*

Ana saura sati a Wauki a zumin Ramadan kenan, duk wasu al-ummar musulmi farin ciki suke da maraba da zuwan wan nan wata mai Wumbun albarka, amma a Sangaren Rashida ba wan nan ne a cikin zuciyar taba, tashin hankalin ta Waya ta yadda zataga Nasir har tayi amfani da wan nan maganin da malam ya bata, wai ita ya zatayi ne wai? Kanta ya kulle baki Waya, gashi kullum gari ya waye cikin Maryam ?ara girma yake yi, to tabbas dole ne ta samu mafitar da zata Sulle da ita, dan muddin tayi sakaci Maryam ta haihu tofa wallahi kashin ta ya gama bushewa a rayuwar duniyar nan.

Wani al-murin murmushi Rashida ta saki a yayin da wata mafita tazo mata a ranta, tashi tsaye tayi tana nufar wardrobe Win ta, dube dube tayi san nan tayi tsaki ta fice daga Wakin ta nufi Wakin nusaiba.

Hajja bata nan tatafi cen garin su domin rabon kayan abinci da kuWaWen da tasabayi duk shekara idan azumi ya tunkaro, bawai bata alkairi bane sai a zumi yazo a'a, kullum cikin alkairi take da kuma taimakon wanda bashi dashi a rayuwar ta, kawai dai ta mayar dahakan kamar wajibine gareta rabon kayan abinci birni da ?auye da azumi, san nan ga zakkar datake fitarwa itama duk shekara, shine dalilin da yasa take Wabbaga al-adar ta kamar yadda taga Mahaifin ta yanayi a sanda yake raye.

Ba ?aramin daWin hakan Rashida tajiba, shiyasa tayi amfani da wan nan damar tayi Wakin nusaiba tana kwala mata kira, jin bata amsa ba yasa ta tuna da ita daman hajja take tafiya saboda ri?e mata jaka, wata sanyayar ajiyar zuciya Rashida tayi sanda ta buWe wardrobe taga tulin hijaban nusaiba a goge tsaf da kuma ni?af ko wanne jere a muhallin sa.

Hijabi Waya ta zaro ta Wauko ni?ab guda Waya ta saka tare da fita ta haye a dai-dai ta sahu dan bata bu?atar Waukar mota a wan nan yanayin.

Tasan kwari akwai bala'in cikowa a wan nan yanayin na a zumi da za'a shiga, duk da haka bataji komai ba haka taita kur Wawa har ta isa ?aton shagon Nasir wanda ya cika da jama'a anata siye siyen kayan salla.

Koda ta shiga Wage ni?ab Win tayi yaran shagon suka ganta, da sauri kuwa suka shiga gaidata san nan ta tambaye su ina mai gidan nasu yake?

Office Winsa suka nuna mata Alamar yana ciki, da sauri ta saki ni?ab Win tayi office Win batare da Kwankwasawa ba ta buWe ta shiga ciki.

*Nasir*

A furgice ya Wago ya zubawa Rashida idanuwa wacce ta kafeshi da ido tana kallon sa, yana niyar yin magana sai kawai ta juya ta buWe ban Waki tare da faWawa ta rufo ?ofar, wani irin mamaki ne ya rufe shi wanda da sauri ya mi?e ya nufi bayin yana cewa

"Ke...ke... Wai wacece wannan?

Yana saka hannu zai buWe Rashida ta buWe banWakin, ta cire ni?ab Win daga fuskar ta san nan ta cire hijab Win ta ajiye ta shafo turaren san nan ta rambaWa uban kwallin zuba mata ido Nasir yayi kamar yadda itama ta zuba masa ido suna kallon kallo kamar wanda yau suka fara ganin juna.

Wata iriyar ajiyar zuciya Nasir ya sauke yana ?ara sha?ar ?amshin turaren jikin Rashida, ga wani fusgar sa da kwallin idanunta keyi yana jansa kamar ya rungume ta.

Ita ma Rashidan wani irin shau?in sonsa da ?aunar sane suke fusgarta, ita kam batayi wa kanta fulako ba tatafi ta rungume Nasir, a tare sukayi a jiyar zuciya ita da Nasir wanda ya ?an?ameta a jikinsa kamar zai mai data ciki.

Sai da suka Wauki kamar minti goma a tsaye san nan Nasir ya iya SanSareta daga jikinsa, kuka Rashida ta saka masa tana cewa

Ni baban Halima? Ni?

Rufe mata baki yayi da nashi bakin yafara tsotsar bakin nata kamar yasamu alewa, sai da ya Wan rage zafi saboda Abinda yakeji san nan ya saketa tare da zaunar da ita a kan cinyar sa yace.

Banason jin kowacce irin magana a cikin bakinki Rashida, kiyi ha?uri da dukkan Abinda ya faru, kije gida ki haWa kayanki dana yara insha Allah zanzo Anjima mutafi gida.

Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya ziyarci zuciyar Rashida a take tafara murmushi da dariya tana godewa malam a cikin ranta.

*KUTSE*

*PAGE 41*

*Na*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Ha?urinta ya ?are na yadda Nasir yake yi mata yawo da hankali, kullum cayake mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login