Showing 123001 words to 126000 words out of 175193 words

Chapter 42 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

565

Kaduna dakai da matarka Rashida, amma yanzu cikin ikon Allah ka samu sau?i yanzu komai ya wuce.

Cikin kiWima Nasir ya tashi gabansa yana faWuwa yace

"Yanzu kuna tunanin Rashida tace tamin kurciya ta Wauko ni ta kawoni nan?

Babu wai nasir Rashida ce, idan kuma kana tunanin ba haka bane yanzu muje gidan naku da ka gaji da zama a hotel ka siya kuke rayuwa a ciki.

Hankali a tashe nasir ya saka kukan takaici da ba?in cikin Abinda Rashida tayi masa, yama rasa mai zaice dan bashi da bakin dazai iya magana, kuka kawai yake yana kiran sunan maryam hankalin sa a matu?ar tashe.

Kuka sosai Nasir yayi da tunanin halin da Maryam take ciki da ?an uwansa a wan nan tsawon shekara Wayan, me zaice musu idan ya koma? anya ma Maryam tana raye kuwa tunda yasan a cikin ciwo yabarta? ya zama wajibi a gareshi yanzun nan ya tashi yatafi garin kano .

Mi?ewa nasir yayi yana laluban wayarsa a aljihun sa, da sauri doctor yace masa ga wayar taka nan a hannuna, hannu nasir ya mi?a masa ya karSa yafara lalubar number Ramadan a wayar tasa amma bai gani ba, cikin mamaki yayi searching Win sunan amma babu ita babu Alamar ta, lambar ya zulai ya ?ara nema ita ma babu, cikin kiWima ya kalli wayar tare da jujjuya ta, ganin ba wayarsa bace sai yayi saurin karSar wayar Doctor ya saka number sa a wayar tasa ya kira, sai yaji kwata kwata lambar bata tafiya, mi?awa doctor yayi wayar sa yana sakin huci yace.

Wan nan ba waya tabace, layin ma ba nawa bane, me yasa zakiyi min haka Rashida? A zafafe ya dun?ule hannu ya daki iska cikin ?arfi yace

"Rashidaaaaaahhhhh, san nan ya fice da hanzari yana sakin huci kamar mayun wacin zaki wanda ya daWe baici abinci ba yau ya fito nema.
*KUTSE*

*PAGE 53*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Bin bayan Nasir doctor yayi yana kiransa dan bai kamata ya barshi yafita ya Wau hanya a haka ba, amma kiran duniya nasir ya?i tsayawa har sai daya dan gana da ?ofar gida san nan yaci birki, ba komai yasa ya tsaya ba sai dan ganin babu motarsa a ?ofar gidan san nan idan yace ma zai hau machine bai san inda zaice a kaishi ba.

Dafa kafaWar sa doctor yayi yana murmushi yace

"Kabari na saukeka a gida dan nasan baka san hanya ba.

Nasir bai juyoba baiyi kuma magana ba domin jinsa yake kamar akan iska an masa rawani da gugan ?arfe yana rinjiyar sa.

Tafiya sosai mai Wan tsawo doctor yayi san nan ya isa unguwar malali locost da nasir, a ?ofar wani ?aramin gida plat ya tsaya tare da kallon Nasir da har yanzu idanun sa basu dawo dai-dai ba yace

"Wan nan shine gidan da kuke zaune.

BuWe murfin motar nasir yayi tare da fita yana kallon doctor yace

tana cikin gidan?

?aga kai Doctor yayi yace

"Tana ciki.

Runtse ido nasir yayi yanajin wani irin ?una da tsanar Rashida ta dabai baye rayuwar sa, bai san idan ya shiga me zai faru a cikin gidan ba shiyasa yafara addu'ar da zai saka ya samu nutsuwar zuciyar dazai iya tun karar Rashida dashi, kwankwaksa ?ofar yafara yanajin kamar ya haura saboda azamar da yake dan an?i buWewa, cen kuma sai yaji murya ana waye? Tambayar waye ya ?ara har gitsa fushinsa sai kawai yasa ?afarsa ya dunga dukan gate Win da ?arfin masifa.

Cikin tsoro zita ta buWe ?ofar da sauri tanayin baya dan ganin nasir a har gitse ya faWo gidan yana watsa mata wani mugun kallo mai kama dazai cinyeta Wanya, bai santa ba kuma bai damu da yasan ko wacece ita ba yayi cikin gidan a hautsine yana kwalawa Rashida kira.

*Rashida*

Kamar a mafarki taji Muryar Nasir na kwaWa mata kira dan barci take, Wan juyi ta fara tana mi?a cike da juyayin mafarkin da tai wai Nasir ya biyota da wu?a zai fille mata kai, da sauri ta duro daga kan gadon tana zare ido jin kiran da gaske ne kuma yana tawowa hanyar Wakin da take.

Tunkan tayi wani yun?uri nasir ya faWo Wakin yanawa Rashida wani irin kallon tsana, juye juye Rashida tafarayi tare da mintsinin kanta tanason ta farka daga wan nan mummunan mafarkin da takeyi.

Marin da Nasir ya kwashe fuskarta dashi ne yasa tayi wani alan kafuri ta wuntsula baya tanajin idonta na dama na mannewa saboda zafi da raWaWin marin daya afka masa, shi kuwa nasir bai matsa daga inda yake ba sai huci da yake saki ?irjinsa yana sama yana ?asa, da gudu Rashida ta dawo gabansa tana ri?e rigarsa cikin in ina tace.

"Lafiff..fiya nasir? Menene?

Gashin kanta ya dan?a da ?arfin tsiya yaja baya yace kece Rashida, me yasa zaki min haka? Me nayi miki? Saboda kawai ina sonki zaki dunga cutar da rayuwa ta?

Cikin azaba Rashida tasaka kuka tana neman kwace gashinta a hannun nasir tana cewa

"Me nayi maka? Me akace nayi maka nasir? Dan Allah karka yarda da kowa a kaina, duka basa ?aunata kasani kuma.

Cikin zafi Nasir ya saketa tare da kuma tsinka mata mari kafin ya haWa jikinta da bango Ya shs?e mata wuya yana zazzare mata ido yana magana cikin kaushi yace.

"Na rantse da Allah na tsaneki Rashida, ban?i naga gawar ki a gabana ba, kuma wallahi badan ha??in rai ba da da hannuna zan kasheki Rashida.

Kakari Rashida ta hauyi tana zare idonta da sukayo waje sukayi ja jawur, ji take kamar numfashinta zai Waure saboda a zabar matsar da nasir yayi mata, dan haka sai ta saka hannu tana niyar cire hannun Nasir daga wuyan ta tana bubbuga ?afafu.

Kamar mace haka Nasir ya kafawa Rashida baki a hannun ya gartsa mata wani uban cizon dabai saki hannun ba sai da yaga jini na Wiga a hannun alamar ya fasa mata fata, ita kuwa Rashida babu bakin yin kuka dan haka sai wutsil wutsil take da ?afafu dan tabbas tasan a wan nan karan rayuwar ta tazo ?arshe.

Ihun da zita taketa kwararawa ne yasa doctor ya fito daga motarsa yana shigowa gidan da sassarfa dan dama bai tafi ba, daman ya tsaya ne koda wani abin zai faru a gidan domin yaga Nasir kamar yafita daga hayyacin sa so kawai yake yaga Rashida ya cimmata, dan haka yana ganin zita ta fito tana wan nan ihun sai kawai yabi bayanta yana furta subhanallahi.

Ai kuwa yana shiga Wakin da yaga zita tayi ya tarar da nasir ri?e da wuyan Rashida idanun ta a waje sai faman yararar da yawu da majina take saboda a zaba, Shegiya mai taurin zuciya, doctor ya faWa a ransa yana ?ara duban Rashida dan ya tabbata wallahi ko wani namijin a kayiwa wannan sha?ar da tuni ya suma anyi asibiti dashi, amma ita saboda taurin zuciya ta?i koda sulalewa ?asa tana tsaye ?am kan ?afafunta duk azabar sha?ar daya tabbatar tana WanWana.

Da sauri doctor ya kawar da wan nan tunanin yayi kan nasir yana SanSare hannunsa daga wuyan Rashida yana cewa.

"Kabari nasir, karfa ka kashe ta ka jawowa kanka masifa, nasir, nasir ya faWa da ?arfi yana jijjiga shi.

Yaraf hannun nasir ya sauka ?asa yayi luuuu kuma zai faWi nasir yayi saurin tareshi ya faWa a jikinsa, da sauri nasir ya kalli Rashida wacce hannun ta yake kan wandon Nasir data ri?e gabansa tamau tare da gimtse gaban nasa da farata.

Cikin mamaki da al-ajabin wan nan tam baWaWWiyar matar doctor ya daddage ya buge mata hannu san nan nefa itama Rashida ta zube a wajen tana haki da sauri da sauri da maida numfashi.

Kiran sunan nasir doctor yafara yana Wan mammarin sa amma bai farfaWo daga suman da yayi ba, da sauri doctor ya zari ruwa akan Wan ?aramin fridge Win Wakin ya kwarawa nasir a jiki take ya Wauko a jiyar zuciya ya farfaWo tare da ri?e gabansa wanda yake masa azabar suka da raWaWi.

Yana kallon Rashida ya saka ?afa ya shureta cikin azaba yana cewa.

"Ni zaki kashe Rashida? Ni? Sai kuma ya zubura yayi kanta yana zai sakar mata naushi doctor yayi saurin taresa yana hararar Rashida yace

"Kedai kinyi a sara, banda kashe kishiyar ki da kikeso kiyi shima mijin bazaki barshi ba saboda ke ?ar bala'i ce?

Zumbur Rashida tatashi tana raba ido ganin doctor zai fita da nasir wanda baya iya tafiya sosai, da gudu ta ri?e ?afar nasir tana kuka wiwi tana cewa.

"Dan Allah Nasir kayi ha?uri karka tafi, wallahi idan katafi mutuwa zanyi, dan Allah karka tafi wajen Maryam , Maryam fa da ?an uwanka ba ?aunarka suke ba, nice kaWai nake ?aunar ka , nikaWai ce ya dace ka zauna da ita.

Cikin ?arfin hali nasir ya saka Waya ?afar tasa yayi ball da Rashida yace.

Ki saka a ranki na tsaneki, kuma wallahi, tallahi, billahi idan naje gida naga maryam ta mutu wallahi sai na dawo na Wauki ranki da hannuna, kuma wallahi duk inda kika shiga saina nemoki na Wauki fansar ran Maryam a gurinki koda ?ar?ashin ?asa zaki shiga wallahi saina tono ki.

Bin bayan doctor yayi suka fita yana Wingisawa har sukaje wajen mota doctor na al-ajabin yadda Rashida ta kama gaban nasir zata tsinke, cikin takaici ya saki dariyar da saida nasir ya kalleshi, wato ta kasa kwatar kanta kuma bazata jikkata ita kaWai ba, gaskiya wan nan matar duniya ce kuma zama da irin su haWari ne.

Tada motar doctor yayi yafara tafiya yana tunanin ko asibiti zai kai nasir ya duba shi?

Bai faWawa nasir ba amma a take nasir ya bashi amsar tambayar sa da cewar

"Ka kaini tasha zan hau motar Kano.

Girgiza kai Doctor yayi yace

"No, bazaka tafi a wan nan yanayin ba, kabari muje asibiti a dubaka tukunna.

Shima nasir kai ya girgiza yace

"Banajin zan iya ?ara ko rabin awa a cikin garin nan da yafi muni da duhu a idona, dan Allah ka kaini tasha kawai na hau mota kafin zuciya ta ta daina aiki.

Kai doctor ya jinjina yace to shikkenan, Allah ya saukeka lafiya.

Da Amin nasir ya amsa san nan ya fita daga motar bayan sun isa tashar.

Akwai cikakkiyar mota wacce daman mutum Waya ake nema motar ta tashi, suna ganin Nasir sukayi saurin taroshi suna cewar yazo ya shiga, bayajin zai iya shiga wan nan motar sai kawai ya yace a sama masa drop dan sauri yake yi, drop Win kuwa yayi duk da uban kuWin da suka cika masa hakan bai dameshi ba tunda ai biyan bu?ata yafi dogon buri.

*Rashida*

Cikin guguwar tashin hankali ta mi?e tana ihu ta fara wura wurar neman wayarta dan tanada ya?inin tabbas aikinta ya gama lalacewa, idan ba aikin tane ya lalace ba taya nasir Win da tagama mallakewa zaiyi mata wan nan tsatstsan Wanyen aikin? Da kyar ta gano wayarta wacce take hannun zita tana dannawa, cikin Sacin rai Rashida ta finciki wayar daga hannun ta tare da zabgeta da marin ba?in ciki ganin tana mata game tace.

"Ke dan uwarki bama ki damu da Abinda ya sameni ba ko? Shine harda Waukar wayata kifara game saboda ba matsalar ki bace? to wallahi garin ku zan mai daki dan bazan haukace da matsalolin kuba.

Dafe da kunci zita takebin Rashida da kallo wacce taketa safa da marwa tana kiran waya babu ?a??autawa.

Maman mu na Waga wayar Rashida ta kuma fashewa da kuka tace

"Maman mu na kaWe har ganyena, asirina ya tonu aikina ya Saci, dan Allah ki taimaka min kiyiwa mai duma bayani koda abinda zai taimaka min.

Daga cen Sangaren maman mu na zaune tanacin abinci haka tai saurin mi?ewa dafe da ?irji tace

"Na shiga uku ni amabuwa, idan aikin ki ya lalace ai nima nawa yagama lalacewa, maza yimin bayanin Abinda yafaru dake yanzun nan na bazama gurin mai duma duk da yamma tayi sosai.

Nan da nan kuwa Rashida tahau zayyanawa maman mu Abinda nasir yayi mata tanata kuka kamar zata haWiye zuciyar ta.

Salati maman mu ta zuba tace

"CaSSijan, lallai muna cikin lukutar masifa Rashida, amma banda wawiya ce ke maimakon daya sha?e?i kema kiyi masa Abinda zakuyi mutuwar kasko sai kawai ki zauna ya kasheki a banza?

Cikin kuka Rashida tafara tarin da taketayi tunda nasir ya sha?e mata wuya tace

"Ai hakan naso maman mu dan wallahi danaga da gaske zai kasheni shine nakama gabansa da farata na na matse na murWe har sai daya suma, dan dana mutu nabarwa Maryam shi su cigaba da rayuwa babuni gwara mu mutu gaba Wayan mu idan yaso a bunne mu a waje Waya, dan ko a lahira banason Nasir ya ba?unci wata mace bare na barshi araye shida wata a duniya suna cin karan su babu babbaka.

Duk da suna cikin alhini da tashin hankali amma bai hana maman mu she?ewa da dariya ba tace

"Lallai barewa ba tayi gudu Wanta yayi rarrafe ba Rashida, wan nan abin da kikayi shiya ?ara tabbatar min dake Win tsatson muce kuma Rashida ita ce ta kawoki duniya.

Akwai wani saurayi da Rashida tayi a garin nan kafin a kaita aikatau gidan ku, in faWa miki wan nan saurayin kawai sai yazo ya yau dareta suka fara soyayya da wata ?awarta, ita kuwa Rashida saboda kishi da zafin cin amanar da sukayi mata yasa wataran ta tar fasu, ranar da aka saka aurensu a ranar ta cimmasu, faWa sosai ya kaure ita da ?awarta a yayin da saurayin yazo shi kuma raba faWa yafara tarewa budurwar sa, ai kuwa cikin Sacin rai Rashida ta dam?i gaban Wan banza ta murWe shi da ?arfi har sai da ta kaishi ?asa, yayita kwarara ihu amma Rashida bata barsa yaci bulus ba, ai kuwa daya kwanta yana wan nan kururuwar haka ta dage ta dunga sakarwa ja'iri naushi a gabanshi har sai daya daina motsi.

Sai kuma tayi shiru tace

"Kibari agama da wan nan matsalar zan baki labarin, amma fa daga ?arshe ansha gwagwarmaya da aka gane Rashida ta kashe gaban Wan banza lafiyar da zaiyi auren ma Rashida ta kaishi ?asa, har ?ara aka kai Rashida, da babar mu taga masifar tayi yawa shine suka salallaSa suka gudo Nigeria aka nema mata aiki a gidan ku san nan rigimar ta mutu, amma ina faWa miki har yau ba'a ga miciji tsakanin dangin su da namu dan ma da taimakon mai duma aka samu rigimar ta mutu.

A jiyar zuciya Rashida tayi tace

"Nifa maman mu wan nan abin ba Abinda ya shafeni bane ba, kawai Abinda nasani yanzu matsalata ce a gabana, dan Allah maman mu ki taimaka kije kisanar da mai duma yasan yadda zaiyi dani kafin kwaSata ta gama jan gwaSewa.

Da wan nan Rashida ta kashe wayar tana kallon zita dake kukan marin da Rashida tai mata tace.

"Dallacen rufe min baki kafin na zane miki jikinki , Shegiya marar hankali, tashi kibani waje kafin nayi ?asa ?asa dake.

*Maman mu*

Tana kashe wayar tafara bawa yarinyar ta labari yayar zita, tazo gidan ne gaida maman mu sai kuma wan nan wayar ta Sarke a gabanta.

Ajiyar zuciya yayar zita taja tace

"Maman mu kenan, amma naga kamar kina farin cikin lamarin, kin nunawa Rashida iyakar gaskiyar ki kema kina cikin tashin hankali amma naga abin ba haka bane.

Tsaki maman mu tayi tace

"Ke dalla tafi cen wawiya, an faWa miki a banza na tura zita wajen Rashida? Ai saboda ta samu miji mai kuWi ta aura ne ta hanyar Rashidan, to kuma kinga tunda wan nan matsalar tafaru ai ta kwana gidan sau?i, yanzu ina zuwa wajen mai duma sakawa zanyi nasir Win da Rashidan keso kamar rai ya saketa saki uku, daga nan kuma sai ya kutsamai da zita cikin zuciyarsa nasan bazai taSa tsallakewa ba sai ya aureta.

Kai yayar zita ta dafe tace

"Haba maman mu, ai wan nan cin amanar zumunci ne, kuma ita zitar kawai sai kawai a kutsata a zuciyar da babu sonta a ciki? Gaskiya ban yarda ba maman mu kenan kutse kikeso kiyiwa Rashida da zita.

Zama maman mu ta gyara tace

"Kwarai kuwa, ita uwar Rashida ba kutsen tayi ba? Ko ban taSa baku Labarin kutsen da taiwa mutanen kirkin nan ba? To wallahi yadda uwar Rashida tayi kutse itama zita ta ?arfin bala'i zan kutsatsata gidan Rashida koda kuwa zata rataye kanta ne.

Girgiza kai yayar zita tayi tace

"Haba maman mu, shikkenan mukuma a kutse zamu ?are don Allah ? Inace kem....

Rufe min baki dallah, kome zaki faWa wallahi saina cika ?udurina, kuma kikace zaki sake min ?orafi wallahi saina tsine miki albarka, Shegiya wacce bata son cigaban ?an uwanta, a'a. shikkenan saboda ke kina fama da talauci shikkenan kowa sai ya ?are a cikinsa ko? Ko kuwa ba?in ciki kikewa Abinda ?ar uwarki zata samu? Shashashar banza marar hankali.

Yayar zita tanaji tana gani ga magana a bakinta amma sam mama ta?i bata dama tayi a dole ta haWiyeta, ?arshe ma tana gani maman tatashi ta Wauki soso da sabulu ta zagaya domin ta Wauraye jikinta ta cale wajen mai duma, dan da zafi-zafi ake dukan ?arfe a cewar ta.

*Maryam*

Alhamdulillahi jikinta yayi sau?i sosai dan har takan iya wasu al-amura da kanta wanda basu fi ?arfinta ba, yanzu ma tana kishin giWe tana kallon yadda yaranta keta wasannin su da kuma tsalle tsalle, tana matu?ar son yaran nan kamar me a rayuwar ta, suna kama da nasir kama ta sosai wacce kana ganin su kasan sun fito daga tsatson sane ko ba'a faWa maka ba, daga gefe kuma ya zulai ce a zaune ita da Jamila sunata haWa kayan su na tafiya gidajen su, dan tun washegarin da Maryam ta farfaWo umma tace ya kamata su tafi tunda matsalar Maryam takau, shi kuma nasir koda daga gidajen sune su cigaba dayi masa addu'a Insha Allah addu'ar zata bishi har inda yake.

Babu yadda zasuyi haka suka sha kukan su musamman ya zulai dan kwata kwata batason tafiya tabar ?an biyunta wanda takejin kamar ita ta haifesu saboda ?auna, dan haka ya zulai ta cewa umma dan Allah dan Annabi tabar mata ?an biyu tatafi dasu saboda ta saba dasu kuma ba shan nono suke ba.

Tunkan umma tayi magana ma Jamila tace

"Haba ya zulai, ai bazai yiwu ba, karfa ki manta rabon yaran nan da jikin mahaifiyar su tun ranar sunan su, kinga kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login