Showing 126001 words to 129000 words out of 175193 words

Chapter 43 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

550

yanzu ne yakamata ace sunji Wuminta kuma sun saba da ita koba haka bane umma?

Haka ne kam Jamila, domin yanzu ne zataja yaran a jikinta ta saba dasu su sha?u Insha Allah.

Da wan nan maganar aka kashe maganar ya zulai.

So suke safiya nayi su Wauki hanya shiyasa duk jikinsu yayi sanyi ?alau, ita kanta umma da Maryam Win har ma da kulu yau duk a saSule suka tashi yaran ne kawai ke budurin su a cikin gidan.

*Nasir*

Sai misalin ?arfe takwas na dare san nan ya iso garin kano, har ?ofar gidan Maryam mai motar ya kawosa ya ajiyesa, tunda ya tunkaro ?ofar gidan zuciyar sa ke lugude da faWuwa kamar zata faWo ?asa, da kyar yake iya Waga ?afarsa har ya isa bakin gidan yanajin kamar jiri zai zubar dashi a ?asa, daman ga raunin da Rashida tayi masa har ya fara sakashi sassanyan zazzaSi.

Hannu ya saka yafara buga gidan a hankali kamar mai tsoron hannunsa ya ?one.

*Maryam*

Wata irin dokawa ?irjinta yayi da karfin da har sai da ta dafe ?irjinta tace.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, san nan tatashi da sauri tayi hanyar falo zata fita.

Da sauri suma su umma suka mi?e tare da ri?eta sukace

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, lafiya Maryam? Meke damunki? Suka faWa suna ?are mata kallo tare da shasshafa jikinta.

Hannun su ta cire daga jikinta tace

"Bakuji yana buga gida yana kirana ba? Gurinsa zanje, nemana yakeyi.

Kuka umma ta saka tace

"Na shiga uku ni halisa, kar dai wata masifar ce zata kuma afko miki Maryam?

Jijjiga kai Maryam tayi tace

"A'a umma babu Abinda zai sameni cikin tsarewar Ubangiji, amma dan Allah kibari naje wajen shi umma.

"Shiwa wai? Ya zulai ta faWa hawaye na sauko mata.

"Ya Nasir mana, shinefa yake buga mana ?ofa.

Dai-dai nan kuwa aka ?ara buga gidan da Wan ?arfi har sai da sukaji bugun, zabura Maryam ta ?arayi tace kun gani ko? Wallahi shine, sai ta saka dariya hawaye na sauko mata tace kubarni naje gareshi umma.

Ri?eta umma da ya zulai sukayi tare da cewa Jamila taje ta buWe taga waye, a tsorace Jamila tafita tsakar gidan dan har ga Allah ta bada ya?inin aljanine yake bugawa tare da kiran Maryam.

Amma sai dai me? A hankali ta buWe ?ofar tare da le?awa kaWan dan taga me bugun mutum ne ko aljan? Wani ihun Jamila ta kwarara tana Alhamdulillahi

"Yaya.

Ihun Jamila ne yasa suka rankayo harda Maryam sukayo waje suga mene? take suka ga Jamila tana karSar kayan hannun nasir wanda ya shigo gidan yana ?ure Maryam da kallo.

Suman tsaye Maryam tayi a lokacin da sukayi ido huWu da Nasir wacce ta fice a hayyacin ta Saboda ciwo da rama, dokawa ?irjin Nasir yayi da ganin Maryam take ya sakarwa Jamila ragowar kayan ya nufo wajen ta.

Yana isowa wajenta Maryam tafaWa jikinsa tana kuka tana cewa.

"Naji a cikin jikina kaine kazo gareni, bana faWa miki ba umma, daman nayi mafarki ya Nasir yadawo gareni, kuma tabbas bana mafarki face ya zama gaskiya a gareni.

Shima nasir rungume Maryam yayi yana kuka sosai tare da kiran sunanta.

*KUTSE*

*PGAE 54*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Nasir*

Yana zaune rungume da ?an biyun sa wanda rabon daya sakasu a cikin idon sa bazai iya tunawa ba, kuka yakeyi yana shafa kansu yana magana kamar haka

"Bansan Abinda yajani ba umma, nidai kawai na dawo hayyacina na tsinci kaina a garin kaduna ne, bayin kaina bane umma dan Allah ku yafemin, wan nan zunubin duk laifin Rashida ne, itace ta tarwatsa min rayuwa ta, ashe har ciwon Maryam ma ita ce da alhakin sa, amma Alhamdulillahi Nagode Allah da Allah yasa Maryam bata mutu ba ta samu sau?i, danna tabbatar da ace Maryam ta mutu ha?i?a nima dole zan bita ko kuma na rasa hankali na baki Waya.

Ita ma umma ajiyar zuciya tayi tace ai Alhamdulillahi dai sai muyita godiya ga Allah wanda yayi cuta kuma yayi waraka, san nan inason ku sani Rashida ta samu sa'ane kawai da amincewar Ubangijin mu, amma da b????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ai bata iko ba ita bata isa cutar daku ba, kuma ya wassafe mata damar ne a kanku saboda ya jarraba imanin ku, dan haka ayi ha?uri komai ya wuce ita kuma Allah ya shiryar da ita idan tanada rabon shiryuwar, idan kuma bata da rabo Allah yayi mana ma ganinta.

Da Amin duka suka amsa san nan umma ta kalli Maryam da idanunta suka rine zuwa jajawur saboda kuka tace.

Ki tashi ki kai masa abinci Waki Maryam ya samu ya huta dan akwai gajiyar tafiya a tare dashi.

Da kyar Maryam tatashi bayan ta amsa saboda har yau jikinta ba wani kwari yayi ba sai dai ita macace mai juriya kuma marar ?orafi, dan idan bakai ka fuskanci tanada masala ba bata fiye faWe da kanta ba sai dai idan abin yafi ?arfinta.

Bin bayanta nasir yayi da kallo yana tausaya mata da jarrabawar da Allah yayi mata ta dalilin sa, bai san aurenta zai jawo musu musiba da tashin hankalin ba dabai fara karSar auren Maryam ba, amma duk da gashin da take karSa a hannun Rashida kullum Soye masa take batason ya sani Saboda kar hankalin sa ya tashi, ajiyar zuciya ya sauke san nan ya tashi ya nufi hanyar Wakinsa yanawa su umma sai da safe.

Koda Maryam tafito daga kichen Win ji tayi kunyar su umma duk ta dabaibaye ta, ji take bazata iya tsallake su ta wuce Wakin nasir ba kunya takeji, dan haka sai kawai ta juya ta koma dan ta tabbatar babu wanda yaga fitowar ta tunda hankalin su yana kan hirar da suke yi, amma batasan umma ta ganta ba, dan haka sai umma tayi murmushin su na manya tana mai jin daWin kunyar nan ta Maryam da har yau ta?i barinta duk da ta haihu.

Bissimillah umma tayi ta mi?e tana cewa su ya zulai dasu tashi suje su kwanta haka tunda tafiyar safiya zasuyi, Jamila ce ta saki hamma tace wallahi kuwa barci nakeji sosai amma ai mun fasa tafiya gobe umma.

Zaro ido umma tayi tace ikon Allah, to sai yaushe? Ito tunda yau laraba kawai mubari sai ran juma'a ko ya zulai?

Kai ya zulai ta Waga tace haka ne umma, san nan tatashi tabi bayan Jamila sunaji umma na faWan karfa sukai mazajen su ma?ura, dan sunyi kara sun musu kawaici musamman mijin ki zulai, bawan Allahn nan shekara guda kenan baya tare dake, kuma duk da haka bai gajiya ba duk sanda yazo garin nan sai yazo kun gaisa ya kawo miki abin arzu?i, gaskiya daga ranar juma'a baku ?ara kwana a garin nan.

Sunajin umma sukayi shiru domin sun san gaskiya take faWa dan ita kanta ya zulai bata taSa tunanin haka mijinta yake da mutunci da kara da kuma mai da matsalarta tashi ba sai da wan nan abin yafaru da ita.

*Maryam*

?ara le?owa tayi ta tabbatar da sun tashi daga falon san nan ta iya fitowa, duk da haka a tsarge take shiyasa ta fara tafiya saWaf saWaf har ta wuce Wakin Nasir a hankali.

?ofar a buWe take shiyasa kawai shiga tayi tana masa sallama, yana tsaye ya bata baya komai yake tunani dan da alamar ko sallamar tata baiji ba bare ya amsa, kwandon data jero abincin ta ajiye san nan ta nufi inda yake tsaye ta rungume shi ta baya tana mai ?ara nana masa siWaWWen ?irjinta a bayan, yo siWaWWe mana dan ciwo da rama duk sun zu?e su sun suWe mata su sun zama kamar babu.

*Nasir*

Har cikin Sargon sa yaji rungumar da Maryam tayi masa, jiyowa yayi yana mai juyo da ita ya rungume ta sosai a jikinsa yana shanshanar gashin kanta domin spray Win da tayi amfani dashi mai sanyin ?amshi ne, ba gajiya yayi da rungumar tata ba sai dai ya tausaya mata ne saboda ganin tsayuwar tayi yawa yasa ya saketa tare da ri?eta a cikin jikinsa suka zauna tare, akan cinyar sa ya zaunar da ita tana facing Winsa yana kallon cikin idanunta wanda sukayi rami tare da zurmawa ciki saboda rama.

Hannunta ya ri?e kam yana mai sunbatar bakinta yace

"Ina sonki da ?aunar ki Maryam, ina addu'a da kuma fatan ace matsalolin mu suzo ?arshe Saboda samun kwanciyar hankalin ki Maryam, bansan gaibu ba amma da nasan zaki shiga wan nan halin da bazan rabaki da farin cikin kiba, dan Allah Maryam ki yafe min, ina neman yafiyar ki dan nasan duk halin da kika shiga ta sanadiyyar aure nane, da baki aureni ba da bazaki tsinci kanki a cikin wan...
Bai ?arasa maganar saba Maryam tayi saurin Wora bakin ta a cikin nasa tare da rufe bakin nasa ruf hawaye na sauko mata dan duk kalan wan nan maganar batason yana furta su.

Jikin nasir ya mutu tare dayin sanyi ?alau dan daman can haka yake, muddin zaiji Wumin Maryam a jikinsa sai hankalinsa ya tashi bare yanzu da aka shekare batare daya ji Wumin jikinta ba, jin haka ne a jikinsa yasa yayi saurin ?ara mannata akan ?irjinsa yafara tsotse Wan ?aramin bakin nata mai masa zakin alewa idan yana tsotsa, nasir bai bar Maryam ta huta ba a daren nan sai da ya sauke duk wata bu?atar sa wacce yayi missing akanta san nan yabarta, ciwon jiki sosai Maryam tatashi dashi domin ba ?aramar gajiya Nasir ya tara mata ba wai nan yabita a hankalin saboda rashin kwarin jikinta baibi da ita ta yadda ya saba mata ba.

Shi kuwa Nasir manne yake jikin Maryam dan baiji yakai geji ba, dan baiwar Maryam ta musamman ce a gareshi ya sani, yasan tunda ya auri Maryam ya daina jin wani daWi da gamsuwa isasshiya da Rashida, ta yadda idan yana tare da ita hakan baya hanshi tunano Wumi da zagin da Maryam take dashi, hakan yasa baya gajiya da ita dan ma inda Allah ya taimakeshi bai taSa satar kwanan Rashida ya kaiwa Maryam ba.

Shafa kan Maryam yayi cikin so da kuma ?auna yana kuma tallafe zugaggun suWaWWun ?an biyun dake ?irjinta cikin zolaya yace

"Wan nan matasan ?an biyun sun bani mamaki Maryam, a haka kamar bazasuyi abin arzu?i ba amma kan ni nasan ?arin gishiri da sugar da suka bani a yayin da kike shayar dani madarar ?aunar ki.

Da sauri Maryam ta Waga kai tare da kwace abe baWanta tana Wan kai masa dukan wasa tace

"Sunyi fushi da kushesu dakayi a radu, sunce bazasu kuma yadda ka kawo musu caffa ba kuma no?ewa zasuyi.

Dariya nasir yayi ya kuma cakumo su yana cewa kuyi min afuwa na tuba dan Allah, idan kuka kuma komawa ciki ai babu nasir dan ba'a yayeni ba har yanzu, kubari dai na cigaba da maneji kafin muWau mataki a kanku.

Filo Maryam ta jefa masa tana kukan wasa tare da tashi zata sauka daga gadon shi kuma yayi saurin cafkota, bai bata damar bagana ba ya juyo da ita yana cewa ina sonsu a haka wasa nake musu, take kuwa ya ?ara kafa baki a Waya Wayan kuma yakama murza da hannu.

*Washegari*

Kasa fitowa Maryam tayi daga Wakin nasir saboda tsantsan kunyar dake damunta, batasan da wane ido zata kalli su umma ba amma tabbas tanajin kunyar ace ta kwana a Wakin miji, a ranta kuma tana tunanin ai bazasu zaci anyi komai ba tunda bata da lafiya shima Nasir Win bashi da nutsuwar zuciya, a babu yadda zatayi dai nasir ya tursa sata suka fita yana mata dariya tare da tsokanarta yana cewa.

"Kima daina wani sin?e sin?e dan kowa yaga wan nan no?a??un matasan nawa yasan sun samu promotion dan gasu nan sun Waga sunyi cas gwanin sha'awa saboda sun samu kulawa.

Da sauri Maryam tayi baya tare da zillewa zata koma tanajin kamar ta fashe da kuka dan zolayar da nasir yake mata ta isheta haka, shima nasir da sauri ya tareta da hannun sa yana cewa

"Kinsan Allah idan baki wuce munje ba sai na Waukeki a hannuna na fita dake har falo, kuma bazan ajiyeki a ko inaba sai agaban umma dan in tabbatar mata da cewar jiya ?ar autarta ta samu kulawa.

Tsayawa cak Maryam tayi tana kallon nasir da idon ta wanda suka canza launi zuwa jajaja hawaye na taruwa a cikin su, magana takeson yi amma tasan idan ta buWe bakin kuka ne zai suSuce mata, dan haka sai tayi shiru hawaye na saukowa daga idonta, sauri nasir yayi ya lashe hawayen yana girgiza mata kai yace.

"Idan zaki zubar da hawaye sau goma ni kuma zan kur Sesu sau goma zumata, idan kuma kina ganin da wasa nake cigaba dayi ni kuma naita shanyewa dan na tabbatar miki hawayen ki sun daina zuba daga yanzu da ikon Allah.

Jikinsa ta faWa tana Wan murmushi tana cewa.

"Nagode sosai da kulawar ka gareni habybyna, Allah ya cigaba da faranta mana rayuwa.

Da Amin Nasir ya amsa san nan ya ri?e hannunta suka fito falo kanta a ?asa dan bazata so ganin fuskar umma a wan nan lokacin ba.

Sai da sukaci abincin karyawa suka Wan taSa hira san nan nasir ya kalli umma yace.

Umma inason naje na karSo su halima idan kin amince.

"Ai bani da dalilin rashin amincewa nasir, ni kaina sanda Ramadan zai kaisu cen Win banso ba, saboda ya nace ne shiyasa na barshi, amma yanzu kam kaje ka Wauko yaranka babu mai hanaka Nasiru.

Suna cikin wan nan maganar sai ga sallamar ya Mansur shida Ramadan kamar haWin baki sun shigo, tashi Nasir yayi da sauri yana kallon su tare da tafiya garesu ya rungume su yana sakin ajiyar zuciya.

Sai da duka nutsa tukunna nasir yake cewa.

Ha?i?a banida abinda zan saka muku dashi sai addu'a, kun min dukkan Alkairin da bazan taSa iya mantawa dashi ba har ?arshen numfashi na, dan Allah kuyafe min a bokaina wanda bani da kamar su a faWin duniya.
Ri?e hannunsa sukayi suna hawayen tausaya masa da samun mace wacce bata gariba sukace

"har kullum mu godiya ce muke ga Allah wanda yabaku halin kuSuta daga sharri da kuma tsafi, san nan zamu kuma yi muku addu'ar Allah ya cigaba da tsare rayuwar ku harda ta yaran ku baki Waya.

Ya zulai ce tace nidai gaskiya hankali na bazai ?ara kwanciya ba har sai ka saki yarinyar nan nasir, wai mezaka ?arayi da wan nan annamimiyar Rashidan, gaskiya bazan Soye maka ba na tsaneta wallahi, kuma duk mai son ka dole yaji baya ?aunarta duba da yadda taso kassara rayuwar ka da kuma ta Maryam, Maryam fa ba iya matar ka bace ?anwar kace, ?ar uwa take a garemu dukan mu tsintsiya ne ma Waurin mu Waya, to kuwa kaga kowa a aka taSa a Cikin ku kamar an taSa mune baki Waya, dan haka gaskiya in har kanajin maganata a matsayina na yayar ka to bazaka ?ara zama da Rashida ba, lada ya isa haka, Abinda akayi ma Allah ya amfana.

Shiru falon ya Wauka babu mai kwakkwaran motsi ko alamar furta wata magana, ganin haka sai umma ta katse shirun da cewa .

"Ki sani zuai shi aure raine dashi, idan Allah bai kasheshi ba mu bamu isa da mu kashe saba duk da son mutuwar tasa da mukeyi, badan Maryam ?ata bace kuma kar aga son zuciya ta nima banason ka cigaba da zama da yarinyar nan ko dan kai Nasiru, saboda ko baka tare da Maryam to ha?i?a yarinyar nan bazata barka ka zauna lafiya ba, dan haka bari dai a nutsu komai ya dawo dai-dai sai asan abinyi kuma mu cigaba da neman zaSin Allah akan lamarin.

*****

Tare da rakiyar su ya Mansur nasir ya isa gidan hajja yanajin wani irin nauyi a ?irjinsa, so yake ya juya domin har ga Allah baya son ganin Abinda zai tuna masa da rayuwar Rashida dan Rashida gubace a rayuwar su, amma dan babu yadda zai haka ya danne zuciyar sa ya shiga gaban su ya mansur da suka fito daga mota suna kallonsa dan yaja musu gaba .

Koda suka shiga gidan Nasir baiyi mamakin ganin duka iyalan hajja a tare da itaba suna tai mata hidima dan yarane masu tsantsar biyayya a gare ta.
Suna ganin nasir suka mimmi?e suna kallonsa da al-ajabi, ita kanta hajjan yun?urawa tayi duk da jiki da take fama dashi a kwana biyun nan bai hanata kamo hannun Nasir ta zaunar a gabanta ba tana cewa.

"Nasiru, kaine nake gani ko mafarki nakeyi? Kai nasir ya Waga yace nine hajja, ina wuni na sameku lafiya? Kuka hajja ta saka ta fara tambayar sa da ina yaje aka nemeshi aka rasa?

Kai Nasir ya jijjina yana mai takaicin sanar dasu duk halin daya tsinci kansa shida matarsa ?arta kuma ?ar uwar su ce ta jefashi, kafaWar sa ya Aminu ya dafa yace

"Minyi jimamin rashin ka Nasir, Aliyu baya gari amma kullum shima cikin jajenka yake, kuma kullum addu'ar mu gareka bata barin fatar bakin mu, Alhamdulillahi da Allah yadawo dakai gida Nasir.

Kai ya Waga yace

"Nagode Allah sosai kuma ina muku godiya, mi?awa ya Aliyu hannu yayi kamar yadda ya mi?o masa yana murmushi, sai da suka gaisa san nan Hajja tayi karfin halin cewar

"Kabani labarin Abinda ya sameka har ka bar gida Nasir.

Kamar nasir bazaiyi magana ba amma haka ya daure yabasu labarin sharri da kaidin Rashida ne yasa yabar gida kuma ta kwantar masa da mata har tsawon shekara guda tana jinya.

Salati da sallallami hajja da kuma ya karimatu har da nusaiba suka hauyi suna sun shiga Uku sun lallace, shi kuwa ya Aliyu ido ya runtse cikin takaici da ba?in ciki yanajin jikinsa na rawa kamar zai kai duka Saboda Sacin rai, duk sanyi da ha?urin ya Aminu shi kansa saranda yayi tare da sarawa hatsabibanci irin na Rashida da rashin tsoron Allah.

*****

"Salamu alaikum.

Muryar Rashida ta karaWe cikin kunnuwan su Nasir dake falon a zaune.

Wani zum-zum-zum, jikin Nasir yafara dan har ga Allah bayason ganin fuskar Rashida a kusa dashi.

Ita kuwa Rashida bata damu da yadda Mutanen falon suka zuba mata idanuwa ba cikin tsoro da fargaba suna kallon ta, sai kawai ta saka kukan kissa tare da nufar inda hajja take zata faWa jikinta.

Wata irin mahan gurSa ya Aliyu yayiwa Rashida wacce sai da ta tafi baya-baya zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login