Showing 165001 words to 168000 words out of 175193 words

Chapter 56 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

523

yana kallon Jamila wacce suka ?arasa fitowa daga sashen Rashida suna huci, gabda ita ya ?araso yana mata kallon tuhuma, kanta ta sauke ?asa jikinta na Waukar rawa saboda ganin Sacin ran Nasir ?arara da tayi.

"Me kukayi a wajen Rashida? Nasir ya jefawa Jamila tambaya.

Shiru Jamila tayi ta kasa magana sai da Nasir ya kuma daka mata tsawa yace "bakiji ba? Koba tambayar ki nake ba?

In ina Jamila tafara tana "dam...dam..dammaaaa, dama me? Nasir yafaWa yana ?ara Waga murya, daman, rash,rash, Rashidaaa ce. Kafin ta ?arasa ma tuni Nasir ya bangaje ta ya faWa falon Rashida yana kiranta, turus yayi ganinta cikin jini ita da zita gashi basa hayyacin su.

*****

*Nasir*

Kallon umma yayi yana hawaye yana cewa "haba umma, taya zasuje su Wauki hukunci a hannu su kashe min mata? Ita idan Jamila bata da hankali ai su ya zalai masu hankali ne, kawai kuma dan ance kulu taci guba ta mutu sai kawai ace Rashida ce?

Cikin zafi Jamila ta han?aro tana "ai Wakin Rashidan ne na ?arshe da kulun ta shi....wani wawan mari Nasir ya sakarwa Jamila yana nunuta da yatsa yace "kul, a kul Winki ina magana kina ?ara saka min baki, yanzu ke Abinda kikayi hankali kikayi ko hauka? Saboda tsabar bakya kishina zaki kwashi ?artin maza suje su taSamin mata harsu nema lahantata? To sun jinyatata kinji daWi, gatacen akwance jina jina, wallahi tallahi kin bani mamaki Jamila, kuma kece babbar makirar da kika kitsa wan nan al-amarin, ya ?arasa yana kallon Maryam.

Cikin jimami Maryam take kallon Nasir tace "yanzu ya Nasir nice makirar? A hasale yace "kece mana, taya zamuyi magana dake karki sake ki faWi maganar nan har sai nayi bincike amma ki sanar dasu, shikkenan ni bazan ro?i alfama a wajenki ba kenan? BuWe baki Maryam tayi zatayi magana sai umma ta Waga mata hannu tace "karna kumajin kin tofa "A" a wurin nan, shiru Maryam tayi tana jin banbamin bala'in da Nasir keyi tana hawaye, sai daya ci mutuncin kowa a wajen Banda umma san nan ya tashi yafita wajen Rashida dake kwance maga shiyan ana saka mata ruwa.

Koda ya fita hana kowa tofa ko uffan tayi a falon, san nan ta umarci kowa tatashi tayi alwala tayi sallar magariba, a wan nan ranar haka kowa ya kwana da ba?in ciki fal ransu da kuma bu?atar wayewar gari domin suga matakin da Nasir zai Wauka.

Shima Nasir koda ya wuce wajen Rashida har gari ya waye bai kuma le?owa wajen su Maryam ba, sai wajajen ?arfe biyu na rana san nan ya shigo wajen Maryam fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Sai daya tsugunna ya gaida umma san nan Maryam ma ta gaisheshi, ya zulai ya gaisar ita kuma Jamila ta gaidashi, shi kansa yasan Abinda yayi jiyan bai dace ba shiyasa yaketa sunkuyar dakai kamar sabuwar amarya.

Gyara zama Nasir yayi san nan ya lalubo Abinda zai faWa dakyar yace

"Amm...dan Allah kuyi ha?uri akan Abinda yafaru jiya, rainane ya Saci sosai madadin yadda wan nan yarinyar takai mun maza wajen matata suka daketa, kema Maryam kiyi ha?uri akan Maganar dana faWa miki jiya. Shiru sukayi babu wanda ya tanka sai umma wacce take tausayawa Nasir wanda take ganin giyar soyayyar matarsa a cikin idanun sa.

"Babu komai Nasiru, nima ajiyan sai da nahanasu maida maganar, kuma na faWa musu ba'a yankewa mutum hukunci cikin fushi da kuma rashin makama, dan haka tabbas Abinda sukayi bai dace ba, kuma kayi ha?uri.

Lumshe idanuwa Nasir yayi yana ?ara gyara zama yace.

Abin da nakeso ku gane shine, zargi babu kyau, kuma dan kulu tafito daga wajen Rashida ta rasu ance guba taci ba shine zai tabbatar da Rashida ce ta saka mata gubaba, san nan ba'ayi bincike an tabbatar da maganar ba zakuce zaku Wauki doka a hannu, Yanzu da sun kasheta me zakuce? Kuma dan Allah dan darajar rasulillahi kuyi ha?uri kubar maganar nan, kunsan dai sanin gaibu sai Allah, san nan kulu ita ce zata faWi Abinda yafaru da ita har a sani a Wauki mataki kuma gashi bata raye, kuma ita Rashida ko tanada hannu a mutuwar kulu tunda bamu da hujja bazamu gasgata hakan ba, kuma dai ita ba fitowa zatayi tace ita ce sanadiyyar mutuwar kulu ba, to dan haka dan Allah muyi ha?uri duka mu fauwalawa Allah komai, muyiwa kulu addu'a san nan wanda yake da hannu cikin mutuwar ta ma mu makashi a cikin addu'a, Insha Allah muna nan daku asirinsa zai tonu da gaggawa.

Ajiyar zuciya ya zulai tayi tana share hawayen ba?in ciki tace "yanzu Nasir shikkenan ina zaune na zuba ido jinin ?ata yatafi a banza kenan? Shikkenan wanda ya kashe min ita yaci bulus ya zauna lafiya? Ha?i?a bakayi min adalci ba, amma tunda haka ne na barwa Allah komai da komai, ina fatan Allah yayi gaggawar sakawa hauwa kuma ya tona asirin duk wanda yake da hannu wajen mutuwarta, ina ?ara ro?ar Allah ya hanashi zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya jirkitar da tunani da hankalin sa ya tona asirin kansa, kuma Allah ya Wai-Waita shi yasa zaman lafiya ya gagareshi, Allah ya gigitashi ya wula?anta shi haWi da Wimauta shi, Allah karka barshi ya zauna lafiya duniya da lahira.

Kasa tanka mata kowa yayi sai data gama addu'ar san nan suka haWa baki wajen cewa Amin ya rabbil alameen, Nasir na zaune daSar ya kasa koda Magana, sai da yaga sun haWe kayansu zasu tafi san nan hankalin sa ya tashi yana tambayar su ina zasuje?

"Garin mu zamu koma Nasir, ya zulai ta faWa tana saka hijabin ta.

Ai bai kamata ku tafiba ya zalai, Abinda ba'ayi sadakar bakwai ba, yaufa kwana huWu kenan da rasuwar kulu, dan Allah ku zauna zuwa bakwai saiku tafi.

Girgiza kai ya zulai tayi tace "a'a Nasir, bazamu zauna anan gidan ba, zamu tafi cenne mu cigaba da zaman makokinta, san nan ma ai zaman mu bashi da amfani anan Win tunda komai ya ?are.

Nasir baiso su ya zalai zasu tafiba amma yanason ta kwantar da hankalin ta ta nutsu waje Waya, kuma idan suna nan ma tashin tashinar maganar nan anta yinta kenan, shiyasa ya yarda dasu tafi Win ko maganar ta ?are.

Ita ma umma a ranar tatafi suka WaWe duka suka bar Maryam da tashin hankali da kuma kaWaicin kulu, tunda zasu tafi take kuka har yanzu bata daina kuka ba, mutuwar kulu ta dawo mata sabuwa dal, jitake kamar idan ta rufe ido ta buWe zataga kulu a zaune tanawa ?an biyu wasan datake musu tana murmushi.

Kuka mai sauti Maryam take saki tana cewa "Allah ya tona asirin ki Rashida, Ubangijin rahama ya tsine miki albarka, haka kawai zaki Wauki ran yarinyar da bataji ba bata ganiba, me tayi miki ne? Menene ya shafeta a rigimar da mukeyi dake? Wayyo Allahna kulu ta , Rashida tayi mana yankan ?auna, Allah ya tsine miki albarka Rashida.

Ire-iren waWan nan magan ganun Maryam taitayi har Nasir ya dawo ya tarar da ita tana kuka.

Zama yayi a kusa da ita yakamo hannunta da niyar rarrashinta, da sauri Maryam ta fusge hannunta tana aika masa kallon banza san nan ta Wauki Wanta tayi Waki dashi tana shasshe?a, bata bashi damar ya biyota ba dan tana shiga Wakin ta saka key ta kwanta ta cigaba da kuka.

*Rashida*

Ba?aramin dukan tsiya taci a wajen waWan nan samarin ba, har data suma ji take ta mutu sai gashi kuma ta farfaWo, gaba Waya kammaninta sun sauya ga idanunta datake gani wani galmi galmi dashi, jitake tsananin buguwar da fuskarta tayi ne yasa idanunta raunana amma sai data fara warkewa san nan tagane da kyar idan dukan da akayi mata bai taSa mata idanun nata ba, ga wani ?aton ba?i daya dan Saro ya fito mata daga gefen kwayar idanun, mudubin hannunta ta ajiye tana cewa zita

"Zita gaba Waya na sauya ko? Duk nayi ba?i na rame ko? ?aga kai zita tayi tana ?unshe dariyar ta na hakwara biyun da Rashida tayi asara tace "eh kinyi amma ba sosai ba, amma idan kinaso ki dawo dai-dai sai fa kin daina wan nan tunanin.

Ajiyar zuciya Rashida tayi tace "bazan daina tunani da tsorata ba zita, wan nan yarinyar kulu rana WaiWai ne bata zuwar min a mafarki tana kuka tana cewa sai na biyata rayuwar ta, kinga kuwa taya ya zan koma dai-dai? Ga idona dayake barazanar daina gani Zita, yanzu fa wani dishi dishi nake gani kamar ba daidai ba, ina ganin gobe zanje asibiti a dubamin idanun nawa ko za'a samo matsalar, har likitan ?irji ma nakeson gani dan wallahi wani nauyi nakeji a ?irjina mai yaji yaji zita.

Baki zita ta kwaSe tana to!!! Wai duk ke kaWai? To Allahu shi baki lafiya, nima wan nan Winkin na goshina kullum kwana nake yana min ?ai?ayi wallahi, ?ila binki zanyi nima a duba min shi dai.

Yauma kamar kullum Rashida na kwance tana barcin da dakyar ta samu ya kwasheta, kamar a mafarki taji ana jan ?afafun ta anayo ?asa da ita, da sauri ta farka tana kai kallonta kan mejan nata, da idanunta wanda ganinsu yafara raunana ta gano fuskar kulu tana janta da ?arfi, wutsul wutsil Rashida tafara tana Wago fuskarta tana kurma ihu, wani gigitaccen mari kulu tasakar mata tare da saka zakwa zakwa faratanta ta karce fuskar tata da ?arfi har sai da jini ya fito.

Cikin ihun ta saka ?afa ta shure kulu baya har sai data matsa san nan tatashi da gudu tana kurma ihu ta fiti fala tana cewa

"Wayyo na shiga uku na lalace, wayyo Allahna, dan Allah kulu kiyi ha?uri, kiyi min aikin gafara, wallahi balai fina bane, kiyi ha?uri kibarni haka, nayi kuskure bazan ?ara ba wallahi, zanje wajen bokan daya bani maganin na zuba miki kikaci ya dawo dake.

Da yake Nasir ba'a wajenta yake ba yana wajen Maryam shiyasa babu Wanda ya kawo mata Wauki, ita kuma zita ta farka daga barci, tanajin komai amma ta?i fitowa sai ma kwanciyar ta data gyara tana sakin tsakin Rashida ta dameta da wan nan damuwar tata.

*****

Washegari haka Rashida tatashi ?ozai-?ozai furkai furkai da ita, gaba Waya a daren jiya bata samu runtsawa ba saboda tashin hankalin da take ciki, hakan yasa da sassafe ta nufi wajen boka dan ya rabata lafiya da kulu ko tasamu nutsuwa, kuma koda taje ta sameshi naWe da hannu amma yace mata bazai ganta ba sai sha biyu na rana baya ganin mutane da safe, haka taita zama har sha biyun nan san nan ya juyo gareta yace.

"Ke Satacciya mene ne kuma? Nifa kin dameni da matsalolin ki.

Hawaye Rashida ta share tace "boka ina cikin tashin hankali, tunda yarinyar nan ta mutu shikkenan fa nakasa zama Lafiya, kullum akwai masifar dazata zo min da ita, kullum sai nayi mafarkinta tana wahalar dani da wujijjiga ni, san nan yanzu abin ma yakai yakawo a fili nake ganinta tana ganamin azaba nidai dan Allah kataimakamin boka. Ta ?arasa tana fashewa da kuka.

Shi kuma boka maimakon yayi mata jaje sai ya tuntsire da dariya yace "shegiya Rashida, ke kinzata zakiyi ta cuta ki ?are lafiya? To ai kaWan kika ganima, kuma banda ke da?i?iyace kin taSa ganin inda mutum ya mutu ya dawo? Toba ita bace, Aljanun jikinta ne suke tsorata ki da razana ki, badan komai ba saboda kin rabasu da wacce suke ma?alewa a jikinta, tashi kitafi ki bani waje dan taki ta?are kuma.

Kuka Rashida ta fashe dashi tace "yanzu babu yadda za'ayi kataimakamin? "Babu. Boka yafaWa yana zaula mata bulalar jannunsa, zabura Rashida tayi tana Wan sakin ihu tace "idona fa? Kullum damuna yake da zugi da ?ai?ayi boka, gashi na fara ganin dishi dishi dashi.

Nan ma dariyar boka yayi yace "makancewa zakiyi. Rashidan zatayi magana boka ya daka mata tsawa yace "dalla malama tashi ki bani waje, banason raina ya Saci yanzun nan na huce a kanki, dan wallahi aljanu zan bawa jininki su tsotse, Rashida najin haka tatashi tana karkaWe jikinta tana kuka tana susa saboda wajen data zauna duk cinnaku ne bata saniba, shiyasa duk suka ciccije mata Wuwawu.

*KUTSE*

*PAGE 72*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Tanakan gadon asibiti a kwance yayin da ?afarta ke sa?ale a jikin wani ?arfe tasha naWi tayi ?atuwa, Zita ce ke kan kujerar kusa da ita a zaune tana hawayen tausayin yayar tata, san nan daWin daWawa ga kanta shima da yasha uban naWi kamar gwaggwaro.

Nasir ne ya shigo da wani file a hannunsa yana cewa zita wai har yanzu bata farfaWo ba? Kai zita ta Waga dan ko magana batason yima, fita Nasir yayi yana tunanin wan nan abin al-ajabin dake faruwa da Rashida a waWan nan satittikan, daga wan nan sai wan nan?

Ko sati Wayafa ba'ayi ba tatashi daga barci taji idanunta sun?i buWuwa, da kyar ta taimakon likita idanun suka buWu amma tace bata gani sosai, daga baya kuma ganin nata yadawo amma kuma haka kawai sai aga jini yana tsiyaya a cikin sa, gashi ba'a gama magance wata matsalar ba wata ta ?arawa afka mata.

Shidai baisan menene yafaru ba yana kwance kawai yaji anata bugun hauka, yana buWewa yaga zita tana kuka da rawar Wari tana nuna masa Wakin Rashida, kuma koda ya ?arasa sai yaga Rashidan a falo yashe jini yana tsiyaya a kanta, kuma suna zuwa asibiti akace wai ta samu karaya a cinya, shi Abinda yake tsoroma Allah yasa ba buguwa tayi akanta ba kwakwalwar ta tazo ta samu matsala.

Abin da ya faru kuwa shine

"Rashidan na zaune tana danna waya tana kallon status Win wata ?awarta kawai sai taga fuskar yarinyar da take kalla a wayar ta zamar mata fuskar kulu, da hanzari ta canza a kalar status Win sai taga duk status Win data buWe hoton kulu ne, ganin zata rikice yasa tayi saurin wullar da wayar ta zame ta kwanta dan daman barci ne ya?i Waukarta shiyasa tatashi tana danna waya, ai kuwa tana juyawa da niyar ta gyara kwanciyar ta sai jita an fuzgi gashin ta da ?arfi an jawota, kafin takai ga ihu har an buga kanta da bango, ihun ta saka san nan ta mi?e cikin azama tana wayyoo Allahna, da gudu tayi hanyar fita daga falo tana waiwaye ai kuwa bata an kara da wani Wan stape dake mararrabar falo da Wakunan ba tatafi baki Waya, nan da nan kuwa ?afarta ta sutale ta bugu da ?asa, ?afarta kuma ta gurWe tare da lankwashe wa cinyar ta ta Salle, wan nan shine Abinda ya samu Rashida.

Sai da Rashida tayi kyawawan satina biyu san nan ta farfaWo, kuma tana farfaWowa ta saka ihu tana kare dukan da kulu ke kawo mata tana dariya, da yake akwai nurses a kusa nan da nan suka kawo mata agajin gaggawa suka kuma turata duniyar barci.

*****

Wan nan shine sakamakon gwajin kwakwalwar da akayi wa Rashida, likita ya faWa yana mi?awa Nasir hoton, kallo Nasir yayi ya ajiye san nan yace "to likita ya kenan ake ciki? Nifa hankalina a tashe yake, dan nataSa jin ance idan mutum ya karye kuma baya hayyacin sa ba'a Worashi idan ba hakaba zai samu taSin kwakwalwa?

?an murmushi likita yayi yace "tabbas haka ne, amma karka manta a sanda kakawo Rashida asibitin nan ta farfaWo kafin ayi gyaran karayar, hasalima har zafin karayar da kuma na Worin tana sane da komai, sai bayan an gama Waurin ne ai tafara wan nan zaburar ai har hakan yayi sanadin data kuma faWowa daga kan gadon da take kwance kanta ya doku, wan nan shine yayi sanadiyar fita hankalin ta, amma Alhamdulillahi ga gwajin da akayi mata nan ai ya nuna kwakwalwar ta lafiya take, dan haka sai dai kutayata da addu'ar Allah yabata lafiya.

Da Amin Nasir ya amsa ya fita daga office Win jikinsa duk a saSule, wan nan allurar kuwa da aka yiwa Rashida ita ce ta lula da ita duniyar barci, wacce bata farfaWo ba sai tsakar dare, Nasir na kusa da ita a zaune yana faman gyan-gyaWi ta farka, har yanzu idanun ta galmi galmi take gani dasu, hakan yasa shima Nasir Win dishi dishi take kallonsa, hannu ta saka taWan taSa shi san nan Nasir yayi firgit ya buWe idon sa yana kallonta, cikin murna Nasir yake kallon Rashida yace kin farka? Kallonsa kawai take domin babu halin ta Waga kanta ma balle tayi masa alama dan yadda takejin kanta yayi wani gingirin gin Kamar an Waura mata dala da goron dutse, da sauri Nasir ya le?a tare da kiran nurse ya sanar da ita ta farka.

*Bayan kwana biyu*

Rashidan taWan fara samuwa amma duk da haka idan ka kalleta zaka gane tana cikin matu?ar damuwa furgici da kuma tsoro, gashi likita ya ro?i Nasir da ya daina zuwa kula da Rashida ya turo mace ?ar uwarta ta kula da ita dan har sauran pecient mata sun fara ?orafi da wucesun da yakeyi a kowane yanayi, da to Nasir ya amsa yana tunanin wacce zai kawo ta kula da Rashida, ita dai zita tayi yarinya da yawa bazata iya Wawainiyar Rashida ba, amma zaije ya lallaSa Maryam tazo tayi jinyarta duk da bataje ko sau Waya ta dubata ba kuma tasan sarai Abinda Ya sameta.

*****

Duk abubuwan da Nasir ke bu?ata sai da Maryam ta gabatar masa dashi, da yake yanzu ai yuka sunsha kanta da yawa saboda rashin kulu, ga kula da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gida ga ?an biyu da bawani wayo ne dasu ba, ga jaririnta ga ita kanta ga kuma Nasir, shiyasa gaba Waya komai ya dagula mata lissafi, tana gama ajiye masa cokali tatashi zata bashi waje, domin tun sanda kulu ta rasu tafara wani irin fushi mai tsanani dashi, ko kallon Wakinsa batayi balle ta yadda ya shigo mata nata, san nan duk kiran dazai mata da wayar dazai mata akan ta shiga Wakinsa yana son ganawa da ita bata sauraren shi, hakan yasa shi a cikin damuwa domin shi harga Allah bayan ci dasha da ibada to ibadar gado ita ce babbar ibadar da yake bawa ?ololuwar mahimmanci.

Hannun ta Nasir ya ri?e yana mata magiya yana cewa dan Allah ta zauna zasuyi magana.

Kamar Maryam bazata zauna ba sai kuma ta zauna ta kafeshi da ido tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login